*KASHE FITILA*💡8
*Batul Mamman*💖
A kwanakin da suka biyo baya Gimbi ladabi take yiwa Awaisu sosai. Tsakanisu tamkar wani abu bai faru ba. Tarewarsu a sabon gidan da ake jiran sai bayan babbar sallah idan sun dawo daga hajji kuwa tuni ta rushe. Kusan duk abin da suke bukata daga tsohon gidan sun gama kwashewa.
Gimbi ta gyara dakin da Maamu zata zauna tamkar wata amarya. Dayake komai sabo ne idan ka shiga kamar kada ka fita. Dakin Daula da taci burin gyaransa ma saboda tilon 'yarta sai da ta matsawa Awaisu aka karo wani gadon a matsayin na Rumana. Karshe ta yiwa Maamu da Rumana dinki kala biyar biyar ta kawowa Awaisu.
Shayi yake sha yana duba wasu takardu ta kawo ledoji manya biyu ta ajiye tare da durkusawa a gabansa.
"My dear ga tawa 'yar gudunmawar"
Daya daga cikin ledojin ya bude. Kaya ya gani a dinke duka super holland har biyar. Ya kalleta da alamar tambaya. Rausayar da kai tayi tana kifta idanu alamun zata yi kuka.
"Nasan babu wani abu da zanyi ya wanke wautar da nayi maka kwanakin baya. Amma don Allah ina mai sake neman afuwarka. Na tsorata ne da jin labaran zama da surukai har naso bata aurena akan labaran wasu da nake ji"
Tayar da ita yayi sannan ya matsa yadda zata iya zama kusa dashi. Ya kama hannunta ya rike.
"Bazanyi miki alkawarin cewa kullum cikin zaman lafiya zamu kasance ba idan Maamu tazo. Amma ina so ki sani ba wai don ita ta haifeni ba, Maamuna bata da rigima ko kadan. Mace ce wadda yanayin kaddarar rayuwa ta sanya mata mugun hakuri da kawaici. Ina jin ba domin Baaba ba da a sangarce ma zan tashi saboda tsabar hakuri irin nata. Tabbas banji dadin abin da kika yi ba amma na hakura. Da kinsan yadda nake mafarkin zama inuwa daya da ita nasan baza kiyi waccan maganar ba tun farko"
Sake bashi hakuri tayi tana kuka da alkawarin gyara kuskurenta ta hanyar bin Maamu sau da kafa.
*****
"Anti Bebi lokacin tafiyarmu sai kara matsowa yake fa. Ni wallahi bana son yin tafiyar da mutanen nan. Dukkaninsu babu wata alamar wayewa. Muje airport su janyo a rinka kallona"
Dariya sosai Anti Bebi tayi sannan ta soma magana da shakakkiyar muryarta wadda tsabar gayu da make murya wurin janyo hankalin maza ta koma haka
"Ki samu ya barki muje wurin da nake fada miki. Kuma kiyi a hankali kada uwarki taji labari. Kinsan dai ba shiri muke da ita ba"
Gimbi ta tsuke baki jin an zagar mata uwa. Ita kanta bata fiye shiga sabgar Antin tasu ba sai da wannan abin ya faru. Yadda Anti Bebi da Mama basa kama a fuska haka suka bambanta a hali. Yanzu haka aurenta na shida kenan. Abin mamaki masu kudi take aure suyi ta mata bauta. Sai ta tara abin da ta tara ta nemi sanadin da zasu saketa. Mama ta gaji da fada da nasihar ta tsame hannunta daga lamuran kanwar ta ta.
"Shi kuma mijin naki ki barni da shege, idan Wangesi na tsangaya ya fara aiki akansa ina fada miki sai juya alkalami yafi miki wahala akan yadda zaki rinka juya shi son ranki. Shi din banza..."
Mikewa Gimbi tayi tana rataya jaka rai a bace. Anti Bebi tace
"Me aka yi kuma zaki tafi muna magana"
"Haba Anti, zamana a nan kin zagar min uwa kin koma kan mijina. Ina sonsu bazan jure zaginsu da kike yi ba"
Dukan cinya tayi irin na matan da suka ga jiya suka ga yau.
"Karyar banza, Amina dai zan yarda kina sonta tunda ita ta haifeki. Amma indai Awaisu ne karya kike yi Gimbi. Duk matar da take son mutum take kin iyayensa ko 'ya'yansa na wani auren kallon munafuka nake yi mata. So da ya amsa sunansa shine ki rungumi duk abin da mijinki ya nuna yana so ki taya shi ririta shi"
Ganin Antin tana ya6a mata magana ta fice ko sallama babu. Dama can ba wai tana ganin mutumcinta bane. Tun suna yara sun san tayi kaurin suna a dangi saboda fitinarta. Yanzu ma dole ce ta kawota. Zata nemarwa kanta mafita.
*****
Bayan kwana biyu Awaisu yake sanar da ita cewa nan da sati uku su Maamu zasu taho Abuja domin ta nan zasu tashi. Kuma an kusa fara dibar alhazai. Sanan za'a taho da Rumana tun yanzu domin taya Laminde zama da su Haris da kuma sabawa ita ma da gidan. Da murnarta ta dauko takarda tana yi masa list na abubuwan da take so a karo musu na kayan abinci da kayan masarufi domin tarbar baki. Yadda take yi masa dole duk wani sauran zargi da bacin rai da yake ransa ya kawar dashi.
Bayan ya fita a gigice ta kira Anti Bebi har ta manta abin da ya faru tsakaninsu. Ita kuwa tana ganin kiran taki dauka. Sai da ta kira yafi sau biyar sannan ta amsa tana magana da kyar wai ita a dole anyi mata ba daidai ba.
Gimbi bata yi fushi ba ta fada mata yadda suka yi da Awaisu. Anti Bebi tace idan zata iya ta je ta sameta a gida washegari su tafi wani kauye a Nasarawa state inda Wangesi na tsangaya yake.
Da daddare kuwa ta karantawa Awaisu karya da gaskiya saboda kada ya ga bata dawo gida da wuri ba daga bankin da take aiki. Shi kuwa sanin yanayin aikinsu bai kawo komai a ransa ba sai addua da yayi mata.
Washegari tana zuwa wurin aiki tayi karyar ciwon ciki ta samu manaja ya yarje mata komawa gida. Daga nan bata zame ko ina ba sai gidan Anti Bebi. Ko zama batayi ba suka kama hanya. Dreban Anti Bebin ne ya kaisu. Tayi mamaki sosai yadda taji suna hirar malamin tsibbun tare dashi. Ashe shine ya hadasu ma.
*****
Wangesi ya bata layu da guraye da zata saka a cikin gidan wanda su Maamu suna zuwa zata ji ta tsani gidan saboda zafin da zaiyi mata. Saboda yarda da shirkarsa da yayi har alkawarin dawo mata da kudinta yayi idan Maamu ta iya kwana uku a gidan batare da ta matsa a mayar da ita Fika ba.
Gimbi murna ba'a cewa komai. Tana zuwa gida tayi duk yadda yace ayi da kayan da ya bata ta zauna jiran lokaci.
Ranar da zasu zo ta kama asabar. Tun kafin asuba ta farka ta shiga kitchen tana ta dafa kayan tarbar baki. Laminde ma a nan ta sameta. Awaisu kuwa zuciyarsa fes ganin ta sake tana nuna masa ta fishi murnar zuwansu.
Dama dreba ya tura aka dauko su. Motar na shigowa yaran suka fita a guje suna murnar ganinsu. Haris tamkar ya shige cikin Harisu don murna. Ba karamin son kawun nasa yake yi ba. Maamu ce karshen fitowa daga motar. Kafar dama ta fara saukewa cikin sanyin muryarta tace "Bismillah tawakkaltu alallah"