Wednesday, 24 January 2018

Kashe Fitila 7

*KASHE FITILA*💡7

*Batul Mamman*💖

Gani tayi kukan bazai kaita ko ina ba ta yanke shawarar washegari zata kira Mama ta fada mata. Dole ma a dauki mataki don ba bauta tazo yiwa kowa ba.

Shirin bacci tayi sannan ta koma dakin nasa. Kwance ta same shi akan abin sallah da gani sallah ya idar bacci ya dauke shi. Tausayinsa kuma taji, ya mayar da kansa tamkar agogo. Bashi da hutu kwatakwata duk domin ya farantawa su Maamu. Tsaki taja a fili tana tunanin yadda zata bullowa lamarin da ya tunkaro ta.

"Saboda zan kawo mahaifiyata gidana shine kike tsaki haka Gimbi?"

Muguwar faduwar gaba taji. Shi kuwa ya mike tsaye yana kallonta rai a bace. Bakinta yana dan rawa tace "haba my dear, kada kayi min mummunar fahimta mana. Dazu da kanka ka gani ina murna harda kukan..."

"Kukan bakinciki ba. Da farko har ga Allah nayi zaton dadi kika ji ganin yadda na damu da yanayin da mahaifiyata take ciki. Bata da wurin da zata kira gidanta. Sai da nayi wanka na biyo bayanki naji kina kuka sosai a dakinki."

Rasa bakin magana tayi shi kuwa ya cigaba da magana cikin kunar rai
"Duk duniya bayan Maamu babu wanda ya cancanci kyautatawa daga gareni kamar Yaya Harisu. Ban taba boye miki asalina ba. Amma abin mamaki kina nuna bacin ranki akan kyautatawar da zanyiwa wanda suka zama jigon rayuwata. Idan bazaki iya zama dasu ba sai na auri wadda zata iya"

Tun da ya fara magana  bata tanka shi ba sai yanzu da ya ambaci kishiya.

"Kayi kadan kace zaka auro wata ka ajiye a gidan nan. Ko ka manta cewa nawa ne. Suna na ne a jikin takardun gidan"

"Dadin abin nima ina da nawa. "

Ta turo baki cike da tsiwa. Tsiwar da a da take bashi sha'awa idan tayi
"Haka nan zaka kare rayuwarka kana yiwa wani kato bauta. Sai shegen aure da tara iyali. Kai kuma an barka da siyan shinkafa da ragon suna"

Shiru yayi har sai da ta gama maganarta tukunna sannan ya tako gabanta fuskarsa babu annuri ko kadan. Ja ta rinka yi da baya yana binta

"Yaya Harisun ne kato Gimbi?" Ya fada a hankali amma kana jin muryarsa har wani rawa take yi saboda bacin rai.

Duk da a tsorace take amma ta kule da yadda yake zare mata ido akan 'yan uwansa.

"Karya nayi ba katon bane? Ko baiyi biyunka ba"

Bata karasa magana ba taji ya gwabje mata baki. Nan take jini ya soma zuba saboda fashewar lebenta na kasa.

Cikin kuka tace "Awaisu ni ka fasawa baki?"

"Idan baki fita daga dakin nan ba sai nayi miki abin da yafi wannan."

Murya ta soma dagawa tana kuka "babu inda zani, gidana ne ba naka na. Idan kaji haushi ka fita ka koma naka"

Fitar yayi zuciyarsa tana tafasa. Wai akan iyayensa da bashi da tamkarsu shine Gimbi take yi masa abin da bai taba tunanin zata aikata ba. Lallai ba'a shaidar mutum. Yasan halinta na kyankyami da ji da kai. Shiyasa yake mamakin irin son da take masa farkon haduwarsu. Falo yaje ya samu yaransa uku sunyi bacci sai Haris da yake karasa homework. Tashinsu yayi daga su sai kayan baccin jikinsu suka fice. Motarsa ya bude suka shiga suna tambayarsa inda zasu je. Bai basu amsa ba ya rinka dannawa mai gadi horn. Yana budewa ya fita a guje.

Karar horn din ce ta fito da Gimbi. Tsoronta kada da gaske ya fita daga gidan. Sai dai abin mamaki ba shi babu yaran.

Nan fa hankalinta ya kara tashi. Mai aikinsu Laminde ta shure da kafa tana bacci itama a falon ta tambayeta ina su Daula

"Hajiya gasu nan suna hamok. Jiransu nake yi su karasa aje a kwanta."

Ta galla mata harara "ina kika gansu. Aikin banza babu abin da kika iya sai bacci"

Waje ta fita inda mai gadi ya tabbatar mata da yaran Alhajin ya fita. Haka ta rinka kiran wayarsa yaki dauka. Karshe ma kashewa yayi yana kallon yaransa suna bacci a makeken gadon dakinsa. Gidansa na Apo ya tafi dasu.
******

Da sassafe yaji ana buga gate ya leka ta taga. Maigadinsa ya gani yana ta washe baki ya budewa Gimbi gate ta shigo. Ko rufe kofar motarta batayi ba ta fito ta shiga gidan cikin sauri.

A falo ya sameta yace kada ta tasar masa yara.

"Wane irin wulakanci ne zaka daukar min yara cikin dare"

"A iya sanina lokacin da muka tare a gidan nan ke kadai kika shigo sai akwatunan kayanki. To mene ne na bacin rai don na kwashe yaran da jinin Maamu yake yawo a jikinsu"

"Wai duk saboda maganar jiya da bata taka kara ta karya ba kake min wannan cin kashin harda fasa min baki"

Ya tabe baki "ina jin baki san girman uwa bane"

Neman sulhu take yi domin tun aurensu basu taba samun sabani irin haka ba. Kwantar da murya tayi ta soma magana
"Duk laifinka ne, ta yaya zaka shirya kawo Maamu batare da neman izinina ba? Nima fa ina da hakki akan ka. Kuma abu irin wannan sai ka fara shawara dani kaji nawa view din"

"Neman izininki? Wai dama haka kike ne ko kuwa sabon salo ne kika fito dashi kawai don baki son dangina. Ba fa tun yau na san kina nuna musu kyama ba. Sharewa kawai nake yi saboda babu wanda ya taba korafi cikinsu."

"Kaga ni ba rigima nazo muyi ba. Maganar fahimta nazo da ita. Idan kana so ka ginawa Maamu sabon gida a Fika is up to you. Amma batun mu zauna tare is out of the question. Zama da suruka baya taba haifar da alkhairi"

Duk yadda yake son ta a daidai wannan lokacin yayi nadamar aurenta. Rasa bakin magana yayi yace mata kawai ta fita idan ta gama. Ganin wankin hula zai kaita dare ta ja motarta ta tafi gidansu. Tana kuka ta zayyanawa Mama abin da ya hadasu. Mama ta dubeta sosai ta girgiza kai.

"Idan kika kure Awaisu ya sakoki zaki gane kudi da gata aikin banza ne idan aka rabaka da iyalinka. Ke da ya kamata ki nuna masa kinfi kowa farinciki shine zaki bata masa rai akan mahaifiyarsa. To yayi miki adalci ma da bai hadoki da takarda ba. Shashashar kawai. Idan ma zugaki akeyi ki sani aljannarki tana karkashin kafar mijinki. Shi kuma tasa tana tare da mahaifiyarsa. Kada ki zama mace mai kashewa mijinta fitilar rayuwarsa Gimbi. Uwa haske ce, uwa rahamace. Da kika shiga matsala ai gaki a gabana."

"Mama yanzu goyon bayansa kike yi"

"Ki kiyayeni Gimbi. Kuma ki wuce yadda kika bata mishi rai ki bashi hakuri ku sasanta. Idan Alhaji yaji maganar nan ki kuka da kanki. Kinsan halinsa sarai. Bar ganin yana sonki hakan bazai hana ya saba miki ba"

Dukar da kai tayi ta gama jin fadan Mama ta tashi ta koma sabon gidan.

Amir ne ya fada mata baban nasu yana daki ta shiga da sallama. Kafin ya amsa ta durkusa gwiwoyi a kasa a gabansa tana kuka. Kamar ya basar sai dai Gimbi matsayinta daban a zuciyarsa.

Tasowa yayi yazo gabanta. Cikin kuka da nuna nadama ta rinka bashi hakuri da nuna masa ta gane kuskurenta. Kukan da tayi tana ajiyar zuciya yasa dolensa ya hakura tare da yi mata nasiha. Cikin dan kankanin lokaci ta shawo kansa suka daidaita.
*****

Zaune suke cikin daki su biyu ta dubi kanwar Mama wadda take binta bayan ta bata labari.

"Anti Bebi wannan ita ce matsalar da ta tunkaro ni. Kuma Mama ta bashi goyon baya"

"Ki bar komai a hannuna 'yata. Indai ina raye babu wanda ya isa ya takura miki. Tun da dadewa nace kizo muje a mallaka miki shi a tafin hannuki kika ki yarda ke dadi miji. Yau ga irin abin da nake ta hango miki ya faru. Ke ko babu boka babu malam yayi kadan kinji ko.  Shi din me? Mijina na uku ma duk taurin kansa sai da ya koma albashinsa ma a hannuna yake balle wani Awaisu."

Kalmar karshe ta sosawa Gimbi rai sai dai biyan bukata yafi dogon buri

No comments:

Post a Comment