Thursday, 29 December 2016

Dan Adam 6

A kwana a tashi ba wuya a wajen Ubangiji, har ga shi ana sauran kwanaki hud'u bikin Haidar da Intisar. Wannan ya janyo Ihsan komawa gidan Hajiya Mama don taya 'yar uwarta shirye-shirye. Alokacin tuni su Hajiya Babba sun iso Kano don anan za'a yi sha'anin bikin kasancewar mijinta, Gen. Ahmad Danzaki, uba ga su Usman, shima dan asalin Kano ne.
    Mami ta yiwa Ramma da Ummi kyautar atamfa turmi d'aya na anko. Ramma ta had'a ta kai musu dinki wanda ya zauna d'as a jikinsu. Ana washegari za'a soma biki, suka ziyarci Hajiya Mama wacce ke fama da shirye-shirye. Amina ta ji dadi kwarai na ganin Ummi. Anan gidan Mami ta barta tare da Fahad suka fita zuwa babban shagon siyar da kayayyakin kicin, hakanan su Ihsan suma sun fita wajen gyaran Amarya.
  Ummi ta dubi hannun Amina da suka sha kunshi.
  "Anti na kasa dauke ido daga kunshin nan naki wallahi, yayimin kyau sosai."
   Amina fuska a sake ta amsa mata sadda take gyara zaman tsintsiyar hannunta wanda take shirin yin shara.
   "Idan kina so muje na rakaki sai na dawo, wallahi yarinyar ta iya kunshi, baki ganta ba kuma ba wata babba ba."
  Ummi ta zaro ido, ga koshi ga kwanan yunwa.
  "A'a, banason fad'an Mami, idan suka dawo basu tarar da ni ba ai nasan ba zata kyaleni ba."
  Amina ta dara kadan. "Kedai akwai matsoraciya, ni na fadamaki har babban gida sai sun shiga tunda Gwaggo ta zo (surukar Mami kuma yar uwar mahaifinta). Na tabbatar su da mu gansu a gidan nan sai Magriba. Bari nayi shara na rakaki, keda kike fara tas ma ai sai ya fi yi miki kyau a kaina."
   Ummi tayi tsuru da ido bata kara cewa komai ba, tana kallo Amina ta kammala share tsakar falon, ta wanko hannunta sannan ta yafa gyale.
  "Muje."
  Ummi ta girgiza kai.
  "Ai baki isa ba, tunda har kina so wallahi sai kinyi, saidai wani ikon Allahn ya hana. Idan kudin kike ji, kada wannan ya dameki, zan biya."
  Dakyar ta shawo kanta ta amince suka tafi. Babu nisa sosai, saida Amina ta ga an soma yi sannan ta taho bayan ta rok'i alfarmar mai kunshin akan ta sanya a raka ta gida. Ba wani mai yawa akayi mata ba, saidai duk kushen mai kushe bazai kalli hannu da kafafun Ummi ba ya ce baiyi kyau ba. Bak'in lalle ne, hakan yasa babu jimawa sosai ya bushe adalilin iskar dake kad'awa. Ta wanke a gurguje, alokacin anyi sallar la'asar, gaba daya fargabanta bai wuce na kada ya zamana su Mami sun dawo ba. Saidai cikin ikon Allah daga su Mamin har su Intisar babu wanda ya dawo. Amina ta rude ganin yanda Ummi tayi kyau.
   "Kai amman lallen nan yayi miki kyau sosai masha Allah, sauranki kitso."
  Ummi ta murmusa.
"Anti nikam banason kitso wallahi bansan dalili ba."
  Amina ta harareta kad'an.
"Eh mana, don kinga kina da gashin ne ai, amma idan kana da kyau saika k'ara da wanka. Gashinan yanzu kunshi yasa kin fito a Mace."
  Sukayi dariya. Koda Ummi ta idar da sallah, tare suka shiga kicin tana kallon yanda Amina ke had'a girke-girke. Abin sai ya bata sha'awa matuka, don duk iyakar girkinta a gidan Mami, bai wuce dahuwar kwai da indomi ba. Amina ta bata shawara akan ta k'ara zage damtse wajen lura da yanda su Mami da Ramma ke girke-girke. Anan suka shantake wajen hira, har Amina na labarta mata batun wani saurayinta wanda shi kadai take saurara, har a yanzu haka ya soma matsawa da batun turo magabatansa.
   "Allah Sarki, toh Anti ki ba shi dama mana."
  Amina ta murmusa.
  "Ba anan matsalar take ba, dangin mahaifina ne abun ji, kina ganin yanda suka wancakalar da lamuranmu, ina gudun kada azo a samu matsala ne."
  Ummi ta gyada kai.
  "In sha Allah babu abinda zai faru, ki gwada ba shi dama."
  "Ai ko na k'i ko na so babu yanda na iya, tunda dai ina kaunarsa haka kuma Innarmu ta ba shi wannan damar har ta sanar da ni muddin ya kara tuntu6arta da maganar zata kwatanta mishi gidan su Mahaifina, kinga kuwa ai bani da ta cewa sai addu'a."
  "Gaskiya kam, Allah Ya yi miki za6i."
"Amin, bari mugani, idan banyi lattin gama dahuwa ba, zan kaiki ki gaida Inna."
  Wani sanyi ya mamaye kirjinta.
"Toh Anti."
   Ba haka suka so ba, don lokaci k'urarre suka kammala, alokacin kuma Mami suka dawo, duk da haka ba su bar gidan nan ba sai bayan Isha'i, wannan yasa Amina yi mata alkawarin duk randa suka k'ara zuwa zata yi kai ta.  Koda Mami ta ganta da kunshi babu abinda tace, illa iyaka ta tambayi yanda ta samu kudin, ta shaidamata Amina ce ta biyamata, daga wannan bata k'ara uffan ba.
   Washegari ya kama ranar  Kamu wanda za'a gabatar a wani tsadadden dakin taro wanda ake ji da shi sosai a birnin Kano, wajen da sai wane da wance. Tun misalin karfe uku na rana, dakin Mami kaf suka shirya, a ranar ma Ummi ta kara fashin makaranta wanda ko kadan ba haka ta so ba, saidai tasan Mami ba barinta zatayi ita d'aya. Daya cikin kayan da aka dinkamata tun farkon zuwanta ta sanya don kuwa Ramma ta sanar da ita cewa sai ranar yini za'a sanya anko.
   Tsari da kwalliyar wajen ya burgeta kwarai, banda wak'a babu abinda kakeji yana tashi a filin taron, waka marar sauti sosai, acikin nutsuwa akeyinta. Har shagala tayi wajen kallon gogaggun yan boko mata wadanda suka ci ado har suka gaji, sai faman fara'a suke kowacce na harkar gabanta. Tana nan zaune tana rarraba idanu, ta ji an dafa kafadarta. Amina ta gani, suka washewa juna hakora, haka kawai itama Ummi ta tsinci kanta da tsantsar farinciki kai kace bikin wani nata akeyi. Amina ta ci kwalliya kamar ba ita ba duk ta chanja.
   "Kedai Ummi kina da ban haushi, bansan meyasa bakyason gyara fuskarki ba wallahi, kalli dai yanda yanmata suke cakarewa, amma ke inaga ko hoda bakya shafawa, kodai baki da ita ne?"
  Ummi tayi dariya har hakoranta suka bayyana a fili.
  "Anti nida ban iya kwalliyar ba?"
  "Ai ba lallai sai kinyi mai zafi ba, ko hoda kadai kika shafa kika saka jan baki mai kala a le66anki ya wadatar, ji yanda kika hadu, wallahi da ace kina kwalliya na tabbata sai kin fi haka."
  Ummi ta rausaya ido tana dariya.
"Ko?" Suka dara gaba d'aya.

   Babu jimawa sosai Amarya ta iso filin da Angonta. Baki bud'e Ummi ta dubi Amina, alokacin wuri ya hargitse, k'arar kid'a ya yawaita da ihun mutane da masu daukar hoto. Ta so ta tambayi Amina daman namijin na zuwa kamu? Saidai babu damar hakan sakamakon hayaniyar da tayi yawa awajen, sunyi kyau matuk'a. Gaba dayansu fararen kaya suka sanya, Haidar cikin farar shadda, yayinda itama Intisar ta had'e cikin shadda dinkin doguwar rigar da ta sha aiki. Su Ihsan da sauran kawayen Intisar suna take musu baya, hakanan shima ango, abokansa na Abuja da na nan Kano kalilan cikinsu sun samu halara, yayinda wasu suka barwa gobe daurin aure. Ba anko sukayi ba, saidai shadda brown kowannensu ya saka, na wani yafi na wani turuwa.
   Sunyi kyau kwarai, sai kirari ake yiwa Ango da Amaryarsa har suka isa mazauninsu. Duk raba idanun Ummi bata ga yayyun Haidar ba da kuma Faruk. Har akayi nisa da sha'anin, mata ne kawai da daidaikun matasan wajen wadanda dukkansu yan uwansu ne na Adamawa sai kuma yan uwan mahaifin Haidar Danzaki da ma'aikata.
   Sun jima sosai a wajen, an ci an sha, har saida aka kusan tashi sannan ta hangi mota ta faka daga can gefen na amarya da ango. Su biyar ne suka fito daga motar, Yaya Ridwan ne sai wasu wadanda suka fi kama da abokansa, a hannunsa kuwa, wata kyakkyawar yarinya ce wacce bata fi shekaru uku ba tana bacci saman kafad'arsa. Har aka tashi daga wajen babu Faruk da Babban Yaya.
     Duk da irin gajiyar da Ummi ta kwaso, wannan bai hanata watsawa jikinta ruwa ba kafin ta chanja sutura ta kwanta.
                      ☆☆☆

No comments:

Post a Comment