Friday, 23 December 2016

KIYYAYA CE KO SON ZUCIYA? 10th


17
Tsayin kwana goma ana wasan ɓuya tsakaninta da Haidar amma bai samu nasarar kamata ba. Duk ƴhanyar da tasan zasu ƴhaɗu tana kauce masa. Tana jin dadin aikin Iya da Habiba saboda suna tsafta sossai. Fadila kuwa tun daga ranar bata sake dawowa gidan ba iyakaci su haɗu da Haidar su sha sharholiyarsu. Hakama Ahmad babu abin da suka fasa wajan gudanar da mu amalarsu ta bayan fagge.
***
Bahijja tunda suka tattara suka bar Nigeria take farin ciki, saboda koba komai Khalifa ya yi nisa da Ummi kwatsam kuma bayan auransu da wata huɗu har tana da karamin ciki wata uku nan ta samu labarin auran Ummi ta hanyar Hindatu. Hakan yasa ta saki jiki lallai Khalifa ya zama nata ita kaɗai. Matsalar farko da suka fara fuskanta Bahijja muguwar kazamace gashi ta haɗu da laulayi mai matukar wahala. Khalifa mutum ne mai tsananin kyankyami nan da nan suka fara haurawa amma daya lura tana fama da laulayi hata karatun ajiyeshi yake ya kula da ita da gidan. Saboda yadda ya ɗora kalata a kan cikin burinsa kullum Allah ya bashi baby girl yasa mata Aisha Ummyter duk kudurinsa bai taɓa gigin furtawa Bahijja ba saboda duk yadda takai da fara a ya sake yayi wani batu kan Ummi to kuwa zasu haura bale taji wannan batu.
     Haka Khalifa ya cigaba da kulawa da ita har cikinta ya shiga wata huɗu zuwa lokacin ta daina amaye-amayen amma sai Khalifa ya lura kazantar ba cikin ne kaɗai ya haifar da ita ba tun asali ɗabi arta ce nan fa suka soma dambarwa tsakaniksu ya zama sai hancinin juna da hattara. Bai kara shiga tashin hankaliba saida ya shiga ɗakin baccinsu wanda ya kaurace masa ya koma na saukar baki saboda tace bata son turaransa shi kuma baya iya hakura da kamshi. Duk tabi ta ɓata bangon da miyau har wani hamammi hamammi ɗakin yake kansa har wani juyawa yake ya fito yana kwala mata kira cikin kiɗima.
"Bahijja! Bahijja!! Bahijja!!!". Tana jinsa taki amsawa a haka ya risketa a fallo ta yi kaca-kaca da shi tana shan ice cream. Turus ya tsaya yana karemata kallo cikin takaici.
      "Bahijja wannan wane sabon salon wulakancine? Kina ji ina yi miki maga kika yimin banza?".
Saida ta yi yatsina sannan ta kaleshi kallon uku ahu ta numfasa tare da rike kugu ta kaleshi.
"Gaskiya dai Khalifa baka da imani, ka manamin ciki ina fama sannan kazo kana yimin ihu aka kamar wata ɗiyarka?".
Mamaki da takaici suka kashe Khalifa amma ya kane ya sassauta murya.
"Bahijja sanina dake yar gayu na sanki, amma dubarki cikin kazanta kaya daban-daban bama wannan ba Bahijja kinji yadda ɗakinki yake tsamin miyau haba My wife kamar bake ba".
Wata dariya ta saki da tasa Khalifa tsayawa kyam yana kare mata kallo ta cigaba da kyakkyatawa sannan ta dubeshi galala.
"Khalifa amma wallahi kai mugune, dame kakeso inji? Kana kallo bacci gaggarata yake saboda cikinka amma wai kake tuhumata da rashin gyarama gidanka to ni wallahi bazan jura ba don haka saidai ka zaɓi ɗaya yar aiki dana bukata tun fari kaki ɗaukowa wai kai kyankyami gareka yanzu ɗaukarta ya zamema wajib ko kuma ka maidani kasata".
    Mamaki takaici suka yi masa rubdugu bai tanka ba ya bar mata ɗakin, zagewa ya yi ya gyara ko ina na gidan har ɗakin girki nan ya dinga karo da kwanikan busasshan abinci kayan miya kuwa wasu duk sun ruɓe haka ya gyare tsaf ya kuna turare. Sai kusan magarba ya gama tun la asar sannan ya dafa ruwa ya tasata gaba har banɗaki ya yi mata wanka ita kanta tsami take kanta kuwa uwar anakiyya ce dankare makare ya saɓeta tas yana mita tare da nuna mata illar abin da take yi amma jinsa kawai take yi shi ma wanka ya yi ya fito suka ci abinci yana ta janta da hira. Suna gamawa ya kwashe kayan ya kai kichen bai fito ba saida ya wanke ga mamakinsa bata falo yana shiga bedroom ya riski harta kwanta cikin ɗaure fuska ya dubeta,
"kin wanko bakinki".
Turo baki ta yi tana gunguni, ta kular dashi amma ya kanne ta wuce ya rakata da idanu ta yo jika-jika ta dawo.
       Hannu ya kai da niyyar janyota jikinsa ta daka tsale tana huci tamkar mesa,
"wallahi ba zaka taɓani ba fita kabarmin ɗaki".
Ransa ya ɓacci baisan sanda ya kwaɗa mata mari ba ta dafe wajan tana dalaro harshe sai ya fice ya bar mata ɗakin.
***
Kwanci tashi Ummi ta share wata guda, tsakaninta da Haidar sai ido kawai ta saki jiki rayuwarta take yi shima ƴhaka babu ruwan wani tsakaninsu. A haka addimission ɗin ta ya fito Baffa da kansa ya tako ya kawo mata ta yi murna sossai cikin satin ta soma zuwa makaranta.
         Da farko bata da matsalar komai amma bata share wata biyu ba Haidar ya ɓulo da wata tsurfa sai ya daidaici tafiyarta makaranta yake aiken driver hakan yasa ta jingine driver take tuka kanta zuwa makaranta. Suna waya sossai da Ummu da Abbu da kuma Baffa haka duk ranar juma a Baffa kan kawo musu ziyara in baizo ba wani satin wani zaizo ƴhakan yasa duk juma a da rana tafi yin girkin gargajiya saboda Baffa.
***
Da wuri ta dawo makaranta kasancewar bata da lacture, tana tura kofar falon warin sigari ya yi mata salama ta toshe hancinta idonta ya sauka kan Ahmad daya haɗa mata karamin hadari a fallo. Ganinsu tare da Fadila yasata yin murmushin mugunta ta cusa kai ɗakin tare da sallama babu wanda ya amsa cikinsu ta wuce ɗakinta kai tsaye gudun karsu ɓata mata rai.
"Yar kyauye".
Muryar Haidar ta katseta ta juyo a fusace ya jefa idanunsa cikin nata take ya nemi hautsinata ta ɗauke kai ya cigaba.
"Ke yanzu da wannan katon hijabin kike zuwa makaranta kamar matar liman wallahi nidai an gama dani?".
Dariya suka sa gaba ɗayansu, cikin tsiwa ta furta,
"faɗi muradinka ina da aikin yi in kuma kaki in kama gabana".
Taku uku ya yi mai karfi sai gashi gabanta ya danke bakinta ya haɗa da mukulin hannunsa ya datse take wajan ya fashe sai jini, bakinta ya hau motsi zata yi magana amma tana shakarsa ya nunata da yatsa.
"Dilla jeki kimin abinci, nagaji da cin na kanti kuma kikaimun kwaɓa duk yawansa saikin cinye".
      Har zata juya zuwa ɗakinta saitaga rashin dacewar abun ta ajiye jakarta kai tsaye ta faɗa kichen ta soma wanke bakinta sannan ta buɗe ma adanar kayan abinci. Komai akwai a ajiye dan haka ta janyo ta soma haɗa abin da take ganin zata iya haɗawa jallop ɗin kuskus ta yi wadda taji kayan lambu da lemon zoɓo mai haɗe da gwaba cikin kankanin lokaci ta kammala ta jera kan daining kanta a kasa ta karasa in da suke,
"nagama".
Ta faɗa murya a sanyaye bai tankaba ta kwashi hand out ɗinta ta shammaci idonsa ta takewa Fadila kafa da tsinin takalminta ta wuce da sauri tana jin ihunta kota juyo bale ta dubi kurarsu. Tana shiga ɗaki ta watsar da kayan hannunta tana sharar kwalar takaici wai ita ta yi wa Fadila girki ta jima zaune sannan ta faɗa bandaki ta sakarwa kanta ruwa. Ummi na bada baya suka mike zuwa daining ɗin, Ahmad na buɗe abincin kamshi ya yi masu salama musamman daya hango mutumin Chuchu wato kihi nan suka himmatu wajan ci sai karar cokula ke karaɗe ɗakin Ahmad kuwa faɗi yake,
"Haidar kai ai kana da gidan abinci a gida".
Shi kuwa ya tsare gida sai ciccin magani yake. Fadila kuwa ta shaka karshema ture abincin ta yi ta kasa ci. Tas suka cinye abincin suka mike da niyyar barin gidan har sun kai bakin kofa Haidar ya juyo Fadila ta tsareshi da ido,
"ina zuwa prince?".
"Ina zuwa tawan".
Cikin sauri ya tura kofar ɗakin Ummi daidai lokacin ta fito daga banɗaki ɗaure da tawul ya yi kuri yana dubanta cikin sauri ta yi wuf ta suri hijabinta ta zura ya kama kame-kame ta sadda kai kasa.
"Ki dafa min abinci kafin na dawo".
Kafin ta yi wani yunkuri ya fice ta lumshe ido tare da sakin ajiyar zuciya.
    Haidar na bada baya Fadila ta dubi Ahmad,
"boss meka fahimta da sauyin man ɗin nan".
"Hmm! Fadila mamaki kike ban kawai kibarsu suyi rayuwarsu in fa kika matsa aka yi auran nan zamu cutu mu duka. Saboda zakimin nisa".
Ta yi masa kallon uku kwabo,
"kama rainamun wayau boss wallahi kai mugune kana tunanin in bar Haidar da waccan kwailar. Wallahi bazata saɓu ba kana tunanin zanci gaba da rayuwa hakane? Alakarmu dakai babu abin da zai sauya kasan cikin wata nan zan soma aiki nayi apply bankinku kuma sun ɗauke ni".
"Da gaske kike Fadila?".
"Da gaske Ahmad!".
Dariya suka yi tare da tafa, daidai lokacin Haidar ya kawo kai harabar gidan karaf a kan idonsa ras gaban Fadila ya tsinke ya faɗi.

[
ƊCikin kaɗuwa Fadila ta janye hannunta ya ɗauke kai tamkar bai gani ba ya shiga mota. Jiki a sanyaye suka rufa masa baya suka shiga amma dake yan duniya ne jansa suka hau yi da hira tamkar ba abin da ya faru. Shi dai bai tanka ba har suka sauke Fadila suka sake ɗaukar hanya Ahmad ne ya ɗan tsaraka da shi ya dubeshi,
"prince su Muhammad nasan zuwa suga madam nace su bari in tuntuɓeka".
"Kasa lokaci nida kai ai duk ɗaya ne".
Ya bashi amsa a gajarce jikinsa a sanyaye ya amsa da,
"to".
***
Da dare Ummi ta shirya masa lafiyayyan abinci ta ajiye ta wuce ɗakinta hakama da safe. Abin mamaki tas yake cinye abincin cikin kankanin lokaci ya yi sabo da abincinta ko ina yaje yaci sai ya riski bambancin ɗanɗano na abincin. Ummi kuwa karatunta take cike da kwanciyar hankali bata da wata damuwa saboda tayi maganin Fadila zuwa gidanta kasancewar duk randa ta tako gidan sai tayi silar sata kuka.
***
"Yanzu kai Haidar sai yaushe ne zaka yi maganar auranku da Fadila ka duba fa anshare wata huɗu da kwanaki da auranka?".
"Mommy kiyi hakuri ina so ne ko wata shida a kara saboda banasan Daddy yaga laifinki ina fara batun haka zaice kece kika sani".
Ta yi jim sannan ta nisa,
"haka ne Haidar kafini tunani a nan amma ka kiyaye ina sane da sirangalin da kake yi tsakanin wajan mahaifinta da uwarta kana gani yanzu duk wata dukiya ta mahaifinka ubanta yake juyata ai duk ma kai kaja ka karanci business ka ɓige a wani karatun likita".
Murmushi ya yi tare da shafa sumarsa,
"Mommy kenan ni kuma shi nake so".
Bata tanka ba ya yi mata sallama ya fice, yana bada baya Nabila tabi bayansa saɗaf-saɗaf sai da taga shigarsa gidan Abbu sannan ta dawo tana kunkuni.
"Hmmm! Mommy ai na gaya miki can yake zuwa rannan fa har abinci nagansa yana ci a gidan".
Cikin kaɗuwa Hajiya Sadiya ta zaro ido tana kaɗa harshe shigowar Baffa ya katse musu zancan.
***
Cikin gajiya ya shigo ɗakin tun daga main parlour ya soma kiciɓus da robar ruwa d a tarkacan chaculate ya yi tsaki ya wuce kai tsaye yana gab da shiga ɗakin baccinsu yaji wani suuuuu luuuuu yaf ya faɗi kasa kansa ya bugu da kujera ya na shirin mikewa hannunsa ya tankwaɓi wata roba karama wani karni ya daki hancinsa. Yammm! Tsikar jikinsa ta zuba zuciyarsa ta tsinke sai amai ya taso masa. Daidai lokacin ta taso da katon cikinta ta fito ganinsa a kasa ta gwale ido tana mamaki.
"Khalifa lafiya?".
Wani takaici ya mamayeshi bai tanka ba ya mike ya wuce ɗakinsa ta saki tsaki tana faɗin,
"aikin banza mutum sai mitar tsiya".

***
Tsakanin Hindatu da Ummi aminci sai abin da ya yi gaba musamman da suka kasance a makaranta ɗaya kuma department ɗaya gashi duk abu ɗaya suke karanta. Kamar ko yaushe zaune suke sun fito kafteriya Hindatu ta dubi Ummi tana faɗin,
"wallahi Ummi cikin nan ya soma yimin nauyi kuma duka duka wata biyar kenan fa".
Ummi ta kwashe da dariya tace,
"da alama ɗan Baba ko ɗiyar Baba zata yi nauyi".
Suka yi dariya daidai lokacin wayar Hindatu ta yi kara ta ɗaga da walwala tana faɗin,
"yaya ina yini ya aiki?".
Fuskarta ta sauya daga yanayin fara ar tana tuna tsantsar tausayi da damuwa,
"kayi hakuri zata sauya yaya na rasa menene yake damun Bahijja wallahi?".
Sun jima suna magana sannan ta katse kiran tare da sauke ajiyar zuciya,
"waɗansu matan basu da kai Ummyter".
Ummi data fahimci da Khalifa ake magana saita yi dabarar kauda zancan.
"Allah dai ya kyauta Hinduwa".
"Allah Ummyter tausayin yaya nake ji Bahijja wahal dashi take ga muguwar kazanta".
"Ina ga aikin ne ya yi mata yawa kibashi shawara ya nema mata mai tayata koda shara ne ita taji da girkinsa da kuma gyaran bed ɗinsu".
"Shikenan Ummi bari in masa message amma fa mata da yawa muna kuskure shiyasa sai kiga maigida ya juyamana baya bayan laifin duk yana wajanmu. Wata hata kwaliyar kanta bata iya ba bale azo batun tsara abinci uwa uba gyaran gida ga rashin iya tsara zancan daya dace a furtawa miji komai yazo bakinsu kwaɓawa suke kamar sa anin juna. Nan da nan kiji ana tashin jijiyoyi tsakanin ma aurata aure ko shekara ba a rufa ba".
Tana karasa maganar tana turawa Khalifa message ɗin ya yi mata reply da ya gode Ummi kuwa murmushi ta yi kasan ranta tana jin kamar da biyu Hindatu ke mata wannan bayanin lokaci ya yi daya kamata ta saduda aure dai an ɗaura kotana so kobata so sunan Haidar mijinta. Karfe ɗaya dai-dai suka bar makaranta ko wace ta shiga motarta sai gida kafin Ummi ta karasa gida ta haɗa gumi tsabar tunani tana zuwa ta yi parking ɗin motarta ta yi wa Baba maigadi sallama ta wuce ciki.
            A tsakar gida ta yi kiciɓus da Habiba cikin riga da zani na atamfa duk da sunsha jiki amma a goge suke tsaftar yarinyar na burgeta suka gaisa saiga Iya ta fito cikin hikima Ummi tace,
"Iya wai Habiba bata zuwa makaranta ne?".
"Eh! Bata zuwa ban sata ba".
Jinjina kai ta yi ta ce,
"ya kamata asata amma kibari zan tuntuɓi maigidan".
Godiya ta yi mata sossai ta wuce ciki suka wuce sashinsu. Karewa ɗakin kallo ta yi ya yi tsaf ta yi murmushi ta faɗa bed room ɗinsu tsaf ta gyarashi ta yi wanka ta ɗaura alwala ɗaya da rabi ta yi sallah ta fito. Tunanin farko daya zo mata in da zata sami mabuɗin ɗakin Haidar saita tuna kofofin iri ɗaya ne dan haka ta ciri na kofarta ta wuce sashinsa saida ta biya ta sake duba sashin su Iya ta tabbatar sunci abinci sannan ta wuce.
     Cikin nutsuwa ta buɗe sashin wannan shi ne karo na farko data shiga sashinsa tun zamanta a gidan tsayin wata biyar. Tsaruwar ɗakin ya bata mamaki kamar na mace saidai rashin gyara kura amma komai a tsare yake a muhalinsa tsaf. Banɗaki ta fara shiga nan ta riski singlet ɗinsa cikin kwandon wanki guda takwas da wandunansu duk farare tattaresu ta yi ta jikasu a wani botiki karami ta zuba ruwan hypo data gani a ajiye cikin banɗaki ta tattare zaninta ta yi ta hau wanki banɗakin fes ta wankeshi sai sheki yake cikin mintuna sha biyar sannan ta jawo kayan data jika kwamin wanka ta shiga ta wankesu tsaf karfe biyu daidai ta kammala ta fito ta shanyasu a harabar sashinsa. Ta koma ta hau goge kurar ɗakin saida ta tabbatar da tsaftarsa lokacin biyu harda rabi da minti biyar ta kule ɗakin bayan ta fesheshi da abun kamsassa ɗaki. Kai tsaye sashin Iya ta nufa ta ɗauki Habiba suka wuce cikin gida ta bata aikin firar doya ita kuma ta nufi ɗakinta ta ɗan kwanta ta huta zuwa mintuna.
         
          Misalin uku da rabi daidai ta mike ta koma sashinsa ta riski kayan sun bushe kwashewa ta yi ta shiga ciki ta zubesu tana shirin fitowa suka kawo wuta babu wani jinkiri ta goge kayan fes, lokacin agogo ya nuna mata karfe uku da minti arba in da biyar ta mike kenan zata bar ɗakin ta tuna bata gyara masa cikin firinji ba dan haka cikin sauri ta karasa ta buɗeshi ras gabanta ya faɗi sakammakon ganin tarin kwalaban giya kanta ya sara ta dafe tare da furta,
"ya Allah!".
Hawaye ƴya kwaranyo mata tausayin kanta dana Baffa ya tsinka zuciyarta, yanzu haka Haidar yake rayuwa a haka zasu rayu da juna karkashin turbar ɓata lallai yanzu ne ya kamata ta yi karatun ta nutsu ta cecci rayuwar ɗan uwanta tilas ta ajiye KIYYAYA gefe ɗaya ta rungumi rayuwarsa duk cikin zuciyarta take wannan tunanin. Tsaf ta kwashesu ta je ta yi floshing ɗinsu a masai kwalaban kuma guda huɗu ta haɗesu tanata dube-duben in da zata sami leda ta ɗaure can ta hangi wata leda viva baka kusa da kayan kallo cikin azama ta janyota ta zazzage kayan ciki ai Ummi saita karasa sumewa babu komai ciki sai tarin blue film ƴhata numfashinta tafiyar sauri sauri ya dinga yi ta yi maza ta kwashesu buɗe ɗankalinta ta ɗauresu kwalaban giyar kuma ta naɗesu cikin ledar ta kai sashinta ta ɓoye.

Saida ta yi sallah sannan ta mike ta haɗa film ɗin da kwalaban cikin wata ledar babba ta ɗaure ta  bawa Mansur tare da gargaɗinsa kar ya kwance yaje can wajan gari ya yasar a juji. Cikin sanyin jiki ta dawo cikin gida ta kwashi turarrukanta masu tsada taje ta jera masa kan mirror anan sake mummunan gamo da pics ɗinsa da Fadila marasa kyan gani ɗibarsu ta yi ta yi musu gutsi-gutsi ta watsar a shara ta baro ɗakin ranta a jagule duk sai taji ta kara tsanar Haidar lallai Fadila gubace cikin rayuwarsu. Kicin ta nufa ta zamu Habiba ta ɗora doyar harta kusa dahuwa dan haka ta zauna suna ɗan taɓa hira tare harta isa yi ta sauke suna hira tana nunamata yadda ake dakan sakwarar tana yi tana naɗeta a leda tana gamawa ta ɗora miyar agushi haɗe da ganyan ogun ta yi masa farfesun bandan kifi da kunnun aya sai magarba suka kammala ta zuba musu nasu ta basu ta wuce ɗakinta ta yi sallah tare da zama tsakanin sallahr magarba da isha i karfe bakwai da rabi aka kira isha ta mike ta bi masallaci ta ɗora shafa i da wuturi tana idarwa ta faɗa banɗaki ta yo wanka ta fito.
          
       Cikin doguwar rigar atamfa ta shirya rigar bata da ado amma samanta da roba aka yi ɗinkin ta kamata cif ta fito da zubin dirinta. Ummi doguwar mace ce mai zubin kwalbar lemo coca cola tatarta kuwa chaculate ce mai haske tana da manyan idanu masu haske ɗauke da kwayar ido baka siɗik hancinta bashi da kara sossai yana da ɗan faɗi shiyasa Haidar kece mata mai nannan hanci. Fuskarta doguwa ce sossai bakinta madaidaici kif bata da yalwar gashin kai iyakarsa kafaɗa amma ya wadaci goshinta wanda hakan yasa wasu ke mata duban mai gaggarumin gashi girarta bata da cika sossai amma baka ce tana da shape da tsayi kamar an gyarata. Bata yi wata kwaliya sossai ba hoda kawai ta murza tasa man leɓe tare da gyara girar ta yane kanta da karamin mayafi kalar atamfar tasa takalmi flate ta fesa turare ta fito falo. Zama ta yi tare da lumshe ido tana tuna abin da tagani ɗakin Haidar kwala ta taru cikin idonta tana kokarin maida ida aka turo kofar ɗakin ta yi hanzarin  kai idonta kan kofar das gabanta ya faɗi suka yi kalon kalo da shi wata muguwar harara ya watsa mata tayi saurin ɗauke idon ta cikin karfin guiwa ta mike ta tunkari in da yake duk da gargaɗin da zuciyarta take yi mata.

No comments:

Post a Comment