💫INA DARAJAR TA KE ?💫
KHADIJA SIDI...✍🏽
0⃣1⃣
La'asar ce sakaliya damina kam Alhamdulillah ta yi kyau a karamar hukumar Bichi da ke karkashin birnin Kano.Sassanyar iskan daminar da ke kadawa shi ya sanya rassa da gayayyakin jikin katuwar bishiyar mangoran da ke tsakiyar tsakar gidan gasar rausayawa. Wato koke koken tsuntsayen da suka dasa gidajen su bisa bishiyar sam be hana jiyo koke koken bayin Allah da ke zaune bisa tabarma karkashin bishiyar ba.
Yakumbo tsohuwa mai kimanin shekara tamanin a duniya ce zaune da ‘ya’yan ta biyu,Hajiya Mairo wacce ita ce babbar d’iyar Yakumbo a mata da kuma Hajiya Binta wacce ita ce autar Yakumbo,Sai kuma kishiyar Hajiya Mairo Hajja Fadi,da kuma facalar su Hajiya Zubaida. Kamar yanda Yakumbu ke rera kukan ta mai sauti haka ma yaran na ta biyu. Hajja Fadi da Hajia Binta ne ke ta kokarin ba su hakuri.
A wannan yanayin ne Alhaji Umar ya shigo wanda shi ne dan Yakumbo na biyu idan aka dauke Alhaji Nasiru Babban dan ta wanda Allah yayiwa rasuwa shi da matar sa a sanadiyar hadatsarin mota da ya rutsa da su kwana arbain da shud’e,d’iyar su daya kacal ta sira da ranta. Tsaye ya yi yana nazarta halin da ya tadda su ciki,da ga bisani shi ma ya samu waje can gefe ya yi zaman sa ba tare da ya tanka musu ba.
Sai da ya tabbatar sun yi shiru sannan ya fara jawabi "Dukkan mai rai mamaci ne,kowa lokacin sa ya ke jira. Yau gashi Yaya Nasiru da uwar gidan sa sun kwanta dama har an kwana arbain,Allah ya ji kan su da rahama’’ Gaba daya suka amsa da ameen. Bai gushe ba ya cigaba da fadin "Na so ace yau aka raba gadon na su amma kasancewar rashin haduwar dukiyar ta su gaba daya a yau ya sa zamu dan jinkir ta zuwa wani dan lokaci,amma kafin nan akwai maganar d’iyar ta su wato Aliya,ina so a ba ni damar daukan ta a matsayi na na mahaifin ta,dan cigaba da daukan nauyin ta har zuwa lokacin da Allah zai fitat mata da miji ta yi aure.....’’
Kana Yakumbu ta nisa murya dashe tsabar kukan da ta yi ta ce’’Ban tari numfashin ka ba Karami[sunan da ta ke kiran sa da shi kenan]maganar Habeebti dai ka yi hakuri ka bar ta hannun kanwar ka Mairo ba dan komai ba sai dan rigon d’iya mace sai d’iya mace,ba wai na rainawa iyalin ka ba ne,amma dai hankali na sai yafi kwanciya sanin ta na hannun na ta"
"Shin ta sanarwa maigidan ta ya kuma amince?..’’ ya tambaya ne ya na mai duban Hajiya Mairo wacce ta ba shi amsa da fadin ’’Eh ya amince,ya ce ma yau dinnan zan iya tafiya da ita Yaya Karami’’kana ya ce toh Alhamdulillah hakan ma yayi sai a fada ma Aliyan ta shirya ko?..’’ya tashi ya na fadin idan kun gama muna waje tare da yaran na ku.’’ ya sa takalmin sa ya fita. Yakumbo tace da Hajiya Mairo ta je ta tsaya kan Habeebti ta san tana nan tana sanar ta ta na kuka,idan ba haka ba ba za ta shirya da wuri ba.
💫💫💫💫💫
KHADIJA SIDI....✍🏽
0⃣2⃣
Hakan ko aka yi,cikin kuka ‘yar budurwar ta shirya.Habeebti da dama yaya bare sarki ya aiko,komai na ta a hankali ta ke bare kuma dadindawa ga mutuwa mai yankan kauna ta dauke mata iyayen ta da duk duniya da su kadai ta shaku idan an dauke Yakumbo,dan ita ko hutu gidan mutane ba ta zuwa sai kuma yau gashi za ta koma gidan wasu can da zama duk da dai kanwar mahaifin ta ce.
Wajan sallama ma da su Yakumbo sai da aka kara wani sabon kukan,tun Alhaji Umar na ba su hakuri har ya koma fada fada sannan ya samu su ka nutsu.
Dawud Babban dan Hajiya Mairo aka bari da jidan kaya ya na sawa bayan mota. Ya na gamawa tuni suma sun shige mota. Hajiya Mairo tare da kishiyar ta da facalar ta a baya,sai kuma Habeebti a gaba.
Cikin kamala da nutsuwar da duk wanda ya san Dawud ya san shi da su, ya shiga motar ya zauna gami da dawo da murfin motan ya rufe. Ya sanya mukulli ya na kokarin kunna motar a hankali ya kai duban sa ga Habeebti wacce idanun ta sun yi ja jawur fuskar ta shara-sharaf da hawaye kan ta sunkuye tana wasa da kasa hijabin ta,a hankali ta dago idanun ta ta daura bisa fuskar sa a raunane,murmushi ya dan sakar ma ta sannan ya maida hankalin sa ga kan titi,ita ma Habeebti kallan ta ta mayar ga wajen motar. Ta na ji ya kunna motar ya na mai karanto ayatul qursiyu domin neman kariyar Allah da ga sharrin karfe. Nan su ka dauki hanyar birnin na dabo..
💫💫💫💫
0⃣3⃣
Aliya Nasiru wacce ake kira Habeebti d'aya ce tilo wajan mahaifanta marigayi Alhaji Nasiru da Marigayiya Hajiya Asma’u. Haifaffiyar jihar Kaduna ce,Unguwar rimi,shekarun ta goma sha takwas da haihuwa,ta gama secondry sch kenan tana jira result ya fito ta sami shiga jami’a Allah ya yiwa mahaifan na ta rasuwa.
Habeeti baka ce,doguwa,ita ba a za a kira ta mai kiba ba haka kuma ba siriya ba ce,tana da manyan fararan idanu dan su suka fi komai girma a fuskar ta,irin idanun nan ne da ake ma lakabi da sleepy eyes,ga su farare tas kamar wanda aka diga zaiba. Hancin ta ba yabo ba falllasa haka ma tsayuwan bakin ta wanda shi ba karami ba,ba kuma babba ba,maganar gashi kuwa tana da shi daidai na ta na zaman falo,ya kan tsaya mata daf da kafada. Wato idan aka dauke baiwa na kyan idanu da Allah ya yiwa Habeebti sai kuma baiwa na diri mai kyau,dan kuwa a dire ta ke sosai,ita kan ta ta san da haka shiya ya sa nan da can ba ta zuwa sai da hijabi,k'arya ne ka ga Habeebti a waje ba tare da hijabin ta ba haka ta ke sa shi birmeme har k'asa.
Kasancewar ta d’aya tilo wajan iyayen ta be sa ta sangarce. D’iya ce mai daraja,tarbiya da kuma sanin ya kamata. Ilimi na arabi da boko ba wanda ba ta samu ba. Komai na ta a hankali ta ke yin sa,tafiya idan ta na yi kamar tana tausayawa kasa haka maganar ta abin kallo ne,sam ba dai ka ji Habeebti tana daga murya ba,haka kuma idan tana magana a sannu a hankali cikin nutsuwa ta ke yi kamar ta na tsintar kalmomin da za ta furta.
💫💫💫💫💫
0⃣4⃣
Hajiya Mairo kasancewar ta k'anwar mahaifin Habeebti ya sa ta dauki Habeeti da amincewar maigidan ta Alhaji Shamsu. Cikin garin kano suke da zama tare da dan uwan sa Alhaji Hamisu cikin wani katafaren gidan su da yar karamar katanga da ba ma ta ci a klira takantar ba ta raba su. Matan Alhaji Shamsu biyu,uwar gidan sa Hajja Fadi sai kuma Hajiya Mairo. Sam basu fiya shiri ba amma hakan be hana hadin kan ‘ya’yan su ba ko kuma kamantawa idan wani abun d'ayan su ya tashi. Salma ita ce babbar d'iyar sa wacce ta kai kimanin shakara talatin da shida,kuma ita ce babbar d'iyar Hajja Fadi,mai bin mata Dawud ne,saurayi mai kamala,mutunci da dattako,dan Hajiya Mairo wanda ya ke da shekara talatin da uku,sai kuma Haroun dan Hajja Faddi wanda ya ke talatin daidai,sam ba ya ji,saurayi ne mai bud'ad'd'an ido ga rawan kai da bin abokan banza wanda hakan ya sa ake ma sa kallan dan duniya,kuma da ga kan sa Hajji Fadi ba ta kara haifan da namiji ba sai mata har uku,wanda duk sun tasa a yanzu sun zama yan mata,sun hada da Halima,Maryam da yar autan ta Aysha mai shakera shabiyar a duniya. Ita ko Hajiya Mairo maza biyu su ka bi bayan Dawud,Ayub da dan auta Akib. Duka duka idan aka had'a ‘ya’yan Alhaji Shamsu takwas kenan.
Alhaji Hamisu da Hajiya Zubaida kuwa kasencewar ba su yo aure da wuri ba haka kuma Allah be ba su haihuwa da wuri ba,babbar d'iyar su shekarun ta ishirin a duniya,mai suna Hindatu ana kiran ta Huda,wacce halin ta ya kusa zama d'aya da Haroun,dama kuma ita ce abokiyar shirin na sa duk gidan. Sai kuma k'anwar ta Bilkisu yar shekara goma sha biyar,sai kuma yan biyu mace da namiji,Fadila da Fadil.
💫💫💫💫💫
0⃣5⃣
KHADIJA SIDI.....✍🏽
Ba su suka isa kano ba sai dab da magarib. Bashakka tsarin kowani b’angare na gidan yayi, daga b’angaran Hajja Fadi har na Hajja Mairo yawan dakunan su d'aya,haka kuma kowannan su d'auke ya ke da k'atan falo,sai dai kitchen d'aya su ke amfani da shi kasancewar ba sa raba girki.
B'angaran mazan ne can gefe guda.Dawud da Haroun da ke su ne manyan samarin kowannan su na da falo da d'aki da band'aki,sauran mazan kuma d'aki d’ai d’ai kawai gare su.
Kai tsaye kowa na shi b'angaran ya shige. D'akin da aka sauki Habeebti ma ba laifi,ita kan ta ya ma ta kasancewar komai da ta ke bukata akwai ciki musammam ma band'aki dan ko gidan su ma haka d'akin ta ya ke.
Bayan ta yi wanka ta huta ne Hajiya Mairo ta takura ta a lalle ta fito falo cikin 'yan uwan ta ta zauna,dan kam bak'unta ya k'are yanzu nan gidan zaman ta ne. Simi simi tana wannnan tafiyan na ta,ta fito sanye da hijab. Zaune ta tadda Hajiya tare da Dawud,shi ma ya yi wanka ya sauya shigar sa cikin k'anana kaya,jar riga da bakin wando,abun ka da farin mutum,kayan sun karb'e shi sosai. Dawud dogo ne,mai k'ark'arfan jiki,sam be da k'iba amma ya na da fadin kafad'a. Fari ne,ko da yake duka ‘ya’yan Alhaji Shamsu da na Alhaji Hamisu ba bak'i,sai dai wani ya fi wani fari,kirarin gidan ne ma ‘’gidan farare ma su hancin biro. Sai kuma wasu yan kananan samari biyu wanda ko za ka sa wa Habeebti wuka ba za ta iya banbance ma waye waye a cikin su ba.
Fitowar ta ya sa gaba d'aya su ka maida hankalin su gare ta. Dawud ne ya fara da ‘’Anty blacky in ki ka ce a d'aki za ki kunshe kan ki lalle wannan bakin na ki sai ya wuce hankali kuma..’’yana magana ne cikin zolaya dan ba tun yau ya san Habeebti ta tsani sunan nan da ya ke kiran ta ba, tun ran da ya fara sa ta a ido, randa su ka taba kai ziyara akaran farko gidan su,duk da kuwa ba wani sabawa su ka yi ba.
Kallan san ta yi na d'an sakkanni sannan ta sami waje can gefe ta yi zaman ta ba tare da ta bashi amsa ba.
💫💫💫💫💫
0⃣6⃣
KHADIJA SIDI....✍🏽
Hajiya Mairo ce ta amsa masa da cewa ‘’Yanzu kam Habeebti ba ta da amsar tsokanar nan ta ka,amma bari ta saki jiki ta dai na bakunta,za ta zama daidai da kai....’’duka su ka yi dariya.ita kan ta Habeebti sai da ta tsinci kan ta ta na mai murmusawa. ‘’Ga yan uwan ki na san Dawud kad'ai ki ka sani,zumuncin yanzu sai a hankali,wannan Ayub kenan ina ga shi ne kuke sa’anni’’ Fad’in Hajiya Mairo kenan yayin da ta ke ma Habeebti nuni ga Ayub. Habeebti ta murmusa yayinda shi kuma Ayub ya ce’’wellcome to the family’’ ‘’Thank you’’ ta amsa da sassanyar muryar ta.’’Ni kuma Akib sunana’’ fadin Akib kenen ya na washe baki,gaba d'aya su ka sa dariya.
Haka dai su ka ci gaba da hirarrakin su,jifa jifa suna sa Habeebti ciki ita kuma ta na k'ok'arin ba su amsa duk da kuwa sam ba ta sake ba,da za su bar ta ta kwanta abin ta da sun taimake ta.
Nan Hajiya Mairo ke ma ta maganar yan matan gidan,wato su Halima,ta yi mamakin ma da har yanzu ba su shigo ba dan kuwa ta san halin su da san mutane,ta k'ara da "ina san ki yi zaman lafiya da kowa a gidan nan,na san ki da sanin ya kamata,ki bawa kowa girman sa amma na miki tsakani da mutum d'aya,wato Haroun,ban yarda kin sakar masa fuska ba saboda..." "Haba Hajiya be kamata ki furta haka ba.’’Dawud ne ya katse ta cikin nuna bacin rai...."Toh uban Haroun’’A fusace Hajiya Mairo ta shiga ba sa amsa "kai ko shi wanda ya ke shi haifi yaran nan ka na dai kallon yanda ya ke fama da shi,yaron da be ganin kowa da gashi,sam be da daraja bare kima dole na ma d’iya ta katangar k'arfe da shi"
Tashi Dawud yayi rai a bace,ba tare da ya sake tankawa ba dan shi ko yaya mutum ya girme shi ba ya fad'a ya na fad'a bare kuma mahaifiyar shi,kana ya ce "Allah ya kyauta,ni na tafi sai da safe’’ ya sa kai ya fice ya na ji Hajiya Mairo na ‘’Allah ya tashe mu lfy,dole ka tafi ai kai mai d'an uwa wato an tab'a na ka,da haka ya ke san ka da ba haka’’ Ta mai da hankalin ta ga Habeebti da ta kasa gane halin nan na Haroun da ake yawan kokawa akai,duk da kuwa shi kan sa Haroun din ba ganin sa ta tab'a yi ba. Hajiya ta ce ki na ji dai ko..’’ Habeebti ta gyad'a ma ta kai,Hajiya ta ce ‘’Toh fa tsakanin ki da shi nesa-nesa...’’
💫💫💫💫💫
0⃣7⃣
KHADIJA SIDI....✍🏽
Ayub ne ya tashi,ganin dai shi ma maganar ta mahaifiyar ta su ba dad'i ta ke ma sa ba,ya ce’’Hajiya ni ma din dai sai da safe...’’kan Hajiya ta ba shi amsa Akib ma ya bi bayan sa ya na sosa k'yeya ya na fadin ‘’ni ma dai hakan ta ke..’’baki bud'e Hajiya ta bisu da kallo har su ka fice,ta dawo da hakalin ta ga Habeebti ta na fad'in ‘’kin ga yan butan uwa,za ku dawo ku same ni ne’’
Habeebti ta kwak'ulo murmushin dole,dan ita ma din da za ta sami dama da irin ta su za ta yi,dan Allah Allah ta ke ta ji hak’ark’arin ta a k'asa. Da haka da haka Hajiya ta ci gaba da zayyanawa Habeebti muyagun halin Haroun,ita kuwa baiwar Allah sai jera hamma ta ke ta na fad'in "toh,Allah ya shirya,Allah ya kyau ta’’ har dai ta samu ta gudu d'aki da uzirin za ta kwanta bacci.
Ta na shiga d'aki ta cire hijab din ta,ta fara shirin kwanciya sai ga wayar Anty Zuwaira,k'anwar Maman ta da ke aure a Abuja,da ke yawancin dangin mahaifiyar ta can su ke da zama,amma asalin su yan garin Bauchi ne. Bayan gaisawan su ne ta ke tambayar ta ya ta ga yanayin gidan,ta ce dai ba matsala ko.....?Habeebti ta amsa ma ta da ba laifi.
Daga d'aya bangaran Hajiya Zuwaira ta ce "Aliya mu masu kaunar ki ne,kuma kin san an fi karfin mu ne da yanzu hannun mu ki ke,da kin ji zaman be mi ki dad'i ki yi magana mu dawo da ke gun mu’’ Habeebti ta amsa ma ta da toh. Ba ta gushe ba,Anty Zuwaira ta k'ara da’’maganar raban gado......’’ "Dan Allah Anty Zuwaira maganar nan ki bar shi yanzu’’Habeeti ta yi saurin katse ta. Ajiya zuciya Anty Zuwaira ta yi,ka na ta ce’’toh for now we let it be,amma gaskiya ba za mu sa ido mu bari a zalince ki ba...’’ ‘’Uhum’’shi ne amsar da Habeebti ta ba ta,dan ita ba dukiyar ba ce a gaban ta ba,da masu duk'iyar za su dawo da duk ba haka ba. Ganin dai Habeebti ga ta ga yanda ta ke ya sa Anty Zuwaira yi ma ta sallama tare da alk'awarin za su na zuwa akai akai su na ganin ta,haka kuma ita ma din za ta na zuwa mu su hutu.
💫💫💫💫💫💫
0⃣8⃣
KHADIJA SIDI...✍🏽
Aje wayar Anty Zuwaira ke da wuya wata wayar ta shigo,ganin sunan mai kiran wayan sai da ta dan murmusa,gami da daukar wayan ta kara a kunnan ta ba tare da ta furta komai ba. Daga d'ayan b'angaran ya ce "Aliya Habeebti....’’jin haka ta murmusa da ma abun da ta ke jira ta ji kenen dan duk duniya ba wanda ke kiran ta ta ji dadin sunan kamar wannan bawan Allah,mai suna Al-amin,wanda ya ke san ta na kwaran gaske,kuma ya kai kudin auren ta ga magabatan ta watanni biyar da su ka wuce.
Bayan rasuwar mahaifan ta shi kad'ai ta ke jin muryar sa hankalin ta ya kwanta,idanu lumahe ta furta ‘’yes dia,da har na yi fushi..’’daga d'ayan b'angaran ya d'an numfasa jin muryar ta, Habeebti mai magana a sanyaye a ko da yaushe ko da kuwa ran ta bace ya ke,ya ce’’ Na sani,kai na bisa wuya na,afuwan ba dan halina na"
Murmushi ta ke,yayin da ta saki jiki su ka yi hirar su har su ka gama ya ma ta alk'awarin shigowa Kano da ke Kaduna ya ke da zama,ya ce da ya gama wani aiki da ya ruke za ta gan shi.
Kafin su yi sallama ya ce toh ta d'aga hannu ya mata adduar bacci. Wayyar bisa kunnan ta ta d'aga hannayen ta biyu,tare su ka fara karanto Qulhuwallahu,sai Falak'i da Nasi,Ayatul Qursiyu,Amanar rasulu, su ka kare da ‘’ Bisimikallahumma amutu wa ahaya’’kana ta tofa a tafin hannun ta gami da shefe jikin ta gaba d'aya.
Bayan ta aje wayar ne ta na mai farin ciki da Allah zai azurta ta da miji na gari, wanda ko da yaushe ya ke tunasar da ita ubangijin ta. Ta sake karanto wasu adduo’in,ta kwanta ta na mai duban gabas gami da tawassali ga Allah wanda ran ta zai koma gare Shi yayin da za ta shiga yanayin bacci,idan ya ruke shi ya ji kan sa,idan kuma ya sake shi ya kiyaye shi.....
💫💫💫💫💫💫
0⃣9⃣
Satin Habeebti daya a gidan ta saba da yan matan gidan,musammam Maryam,Huda ce kadai ba sa ga maciji saboda halayyar su ta shabanban. San da ta cika sati biyu Dawud ya raka ta ta yi registration din post utme na ABU,wanda za ta yi a b'angaran BSC Nursing. Sanye ya ke cikin manyan kaya,yadi ne fari kyal,ga farar hula karkace bisa kan sa,idanun sa sanye da farain glass wanda ya k'arawa siririn hancin sa tsayi da kyau.
A hankali ya ke bin sautin karatun Sudais da ke tashi cikin motar. ita kan ta Habeebti ya na ma ta kyau,kuma ta lura da dayawa matan cafe din da su ka je suna satar kallan sa."matsalar namiji mai kyau kenan matan su su ta fama da matan waje,Allah ya raba ni da auren irin su Dawud" Abun da ta fada kenan cikin ran ta,
Zaune ta ke gaban motan tare da shi,kamar yanda ta saba sanye da hijabin ta fuskar nan ba kwalliya amma da ka kalle ta sai ka kara saboda kamala da ke tattare da ita. Cikin dabara ta ke satar kallan sa ba tare da ya sani ba,ita dai ba wanda ta ke san gani kamar Haroun,dan kuwa ta sha jin su Huda da Halima su na musun wai Haroun ya fi shi kyau,Maryam da Ayaha na cewa su dai kawai sun san kamar su daya,duka da Abban su su ke kama....ba zato ta ji ya kashe karatun ya juyo ya na kallan ta,ta dan yi firgit cikin jin kunyar ya kamata ta na satar kallan sa,sai a sannan ta gane ashe sun tsaya a traffic amma sam ba ta ma sani ba.
Cikin dan kame kame ta ce ‘’umm uhm ya ka kashe karatun’’....
Murmushi ya sakar mata yayin da aka ba su hannu,ya d'aga kafa motar ta tashi yayin da ya maida hankalin sa ga tukin da ya ke,kana ya ce ‘’hira na ke so na yi da 'yar uwa ta wacce ba ta san magana’’. Murmushi ita ma din ta yi jin furucin sa. Kana ya k'ara da ‘’mai ya sa ki ke san Nursing’’ sai da ta d'an dau lokaci kafin ta ce "well ni a nawa Nursing is the best course for d'iya mace,plus aikin taimako ne sosai,ga lada ga kuma job opportunity ga salary,ba yanda za a yi mutum ya gama karatu in dai b'angaran health ne ya tsaya ba aiki,sai dai ma aiki ya neme shi.....’’ ita tsakani da Allah ta ke ma sa bayani,ba ta lura da yanda ya zuba ma ta ido cike da mamakin yanda ta iya magana,cikin nutsuwa da hankali gashi ta na magana kamar ta na zaban kalmomin da ta ke fad'a...ta k'are da..’’ka ga kuwa lalle abun yi ne...’’darawa ya d'an yi,kana ya ce’’Ashe haka ki ka iya magana shi ne ki ke min baki ciki kullum ki tsuke baki girim......’’jin haka ya sa ta kau da kai gefe ba shakka ya fara tsokanar na sa kenan.
Jin ta yi shiru ya san ba k'ara magana za ta yi ba,shi kuma duk duniya babu abun da ya ke son jin irin maganar ta,dan haka ya yi saurin k'arawa da ‘’maganar aikin dare fa...kar fa ki zo mijin ki ya ce ba ya so...’’kallan sa ta yi fuskar ta dauke da fara’a jin an tab'o maganar Al-amin, "ai kam in dai Al-amin ne bai da matsala,dan kuwa shi ma Doctor ne...’’ "owk....’’ amsar da ya ba ta kenan jin ran sa ya dan sosa da shi kan sa ya kasa gane dalili.
💫💫💫💫💫
1⃣0⃣
Har su ka isa gida be k'ara tanka ma ta ba. Jin hayaniya da hargowar samari ya sa shi hangen b'angaran su da ke can gefe,ita kanta Habeebti sai da ta dan kai idan ta gun jin hanayar da ke tashi. Dawud na murmushi ya ce sarkin abokai da jama’a ya dawo kenan,cikin rashin fahimta ta tambayeshi wa fa?" Ya ba ta am sa da
"Haroun kenan’’ har za ta fita ta tsaya tare da fad'in "wayyo na kuma’’cikin nuna damuwa ya tsayar da k'ok'arin b'ude motar da ya ke ya ce ’’me fa?’’ ta ce ‘’mantuwa wlh,na yi niyar mu biya chemist in siyi maganin migraine,kwanannan ina jin sa sama-sama" kai ya gyada tare da fadin ."kar ki damu ki na tare da pharm Dawud guda ba za ki rasa magani ba,wannne ki ke sha? "
"Amitriptyline hydrocloride" ta ba shi amsa. Kana ya ce anjiman nan zai kawo mata ko ya bawa Akib ya kawo mata. Godiya ta ma sa,yayin da ta shige ciki.
Idanun sa kan ta har ya dai na hangen ta,ba shakka Habeebti tana burge shi,ba dan wannan Al-amin ya ke kowa ya masa shigar k'arfi ba da bashakka ya yi matar aure..da wannan tunanin shi ma ya fito kai tsaye dakin Haroun ya wuce.
Washagari gidan Anty Salma su ka yi niyar zuwa. Huda ce shugabar tafiyar tuni ta shirya cikin k'anan kaya riga da siket shud'i,kan ta ba dankwali sai ta ta nad'a d'an karamin mayafin ta,ta yi kyau kwarai kamar d'iyar turawa da ke ita ma fara ce doguwa siririya. K'anwar ta Bilkisu ce ta ce za ta bi ta amma Huda ta yi kememe ta hana,ita gaskiya ba za ta fita da yarinya ba,tun Mahaifiyar su Hajiya Zubaida wacce su ke kira Ummi na sa baki har ta hakura ta k'yale ta. K'yas k'yas ta na taku d'ai d'ai sanye da takalmin ta mai tsini kannan na rawa kamar mazari ta nufi b'angaran su Halima.
Ta tadda Halima da Maryam sun shirya,Halima ma kusan irin shigar Hudan ta yi,Maryam ce ta sa abaya,duk sun yi kyau abun ku da kyawawa. Su ma d'in fama su ke da Aysha ita a lalle sai ta bisu,Huda kuwa ta kara zuga su tun da ta ki zuwa da Bilkisu lalle kuwa ba yanda za a yi a tafi da ita.
Har sun nufi mota Halima ta ce "laa na manta Hajiya fa ta ce idan zamu tafi mu kira Habeebti.....’’ ‘’mstw.." Huda ta ja tsaki..."ni fa ban san yarinyar nan ta fiya kauyenci,kullum ta na sim-sim sai ka ce mara laka,ya ma akayi ku ka bari Hajiya ta san za mu fita....ku wallahi ba a yin sirri da ku...’’ ‘’Ga ba uwar surutun da ta fada ma ta nan ba’’ Halima ta yi nuni ga Maryam da tuni ta shiga zare ido kasancewar ita ce k'aramar cikin su..’’mswt...’’ Huda ta kara jan tsaki,ai sai ku kira ta,kusan dai Ya Haroun ne zai kai mu ba Ya Dawud ba,ku ka bata lokaci wlh ya ce ya fasa sai kun biya ni fitar da na yi asara...’’duka dariya su ke mata,dan kuwa sun san halin Huda in dai kan Haroun ne za su iya ganin harigido. Da sauri Maryam ta nufi b'angaran Hajiya domin kiran Habeebti,su kuma su ka k'arasa motar Huda na kokarin samin Haroun a waya.
💫💫💫💫💫
1⃣1⃣
Maryam ta tadda Habeebti ta idar da sallar walha kenan,ta ce ta yi maza ta fito su na jiran ta a mota,a gurguje ta fice ta bar ta ta na karasa shiryawa. Atamfar ta ta sa,riga da siket,sun kama ta kyam abun ta sun ma ta kyau,ta shafe jikin ta da humra da turaren ta mai suna escada magnetism,sannan ta dauko hijabin ta fari kyal ta sanya,k'afafun ta sanye da takalmin ta ja,da ke atamfar ta ta ja ce,da ka gan ta ka yar gayu,yar gayun ma very decent nd classy.
Sai da ta yi ma Hajiya sallama sannan ta kama hanyar fita. Ko da ta fita ba ta hangi su Halima ba,ta k'ara takawa waje sosai ta na raba idanu,nan idanun ta su ka sauka kan sa,lokaci guda ta ji gaban ta yi mummunar fad'uwa sai da ta tsinci kan ta ta na mai ambaton’’lailahailla anta subahanaka inni kuntu minal zalimin..’’
Ba shakka ba dan ta san zahiri ba da ta ce Dawud ne zaune bisa mota,amma ina wannan farin sa be kai na Dawud ba duk da dai shi ma farin ne,kamar sa da Dawud d'aya....sanye ya ke cikin k'ananan kaya,bakar riga wacce ta kama shi sosai da bakin wando,sai kuma ya daura wata rigar a
samar bakar mai dogon hannu blue,ba tare da ya sanya botulan rigar ba.
💫💫💫💫💫💫
1⃣2⃣
Ba kamar Dawud ba,kan sa akwai gashi da yayi lub lub kamar kan dan kwara.....a hankali ta ke kallan su,dan kuwa ba shi kadai ba ne,zaune ya ke bisa mota,Huda ce tare da shi hannun ta cikin na sa,waya ne a hannun shi,daga ita har shi hankalin su na kan wayar.
A hankali ta ke k'arasawa in da su ke,ta zo dab da su kenan,ta ji muryar Dawud da sam ba ta lura da shi ma ya taho ba ya na fad'in ‘’Haroun ina za kai yan matan gidan haka ne...’’shi ma sai a sannan ya lura da Habeebti,ya na duban ta ya ce harda Anty blacky kenan.."
D'agowa Haroun ya yi jin maganar Dawud,dan ya ga wacece Dawud ya ke nufi,ya ce ‘’Anty blacky.....’’a hankali idan sa ya sauka kan Habeebti da ta masa bazata...."B-E-A-U-T-I-F-U-L....’’a hankali cikin jan kalmar ya karasa,Shi kan sa be san ya furta hakan ba...dan kuwa gaban sa yayi mugun fad'uwa yin ido biyu da Habeebti. Ita kan ta idanun sa ne su ka tsora ta ta. Yanda idanun ta su ke manya haka na shi su ke da girma,sai a sannan ta k'ara gane banbancin sa da Dawud,ba shakka dole su Huda su ce ya fi shi kyau,hez handsome,down to earth.
Darawa Dawud ya yi tare da fadin Anty blacky beoutiful indeed,cikin sauri Habeebti ta yi kasa da na ta idanun,da har ila yau Haroun kallan ta ya ke. Ganin haka Dawud ya ce "ba ka san Aliya ba ko.?" "ALIYA" Haroun ya maimaita,"yes Habeebti d'iyar Hajiya’’ idanun Haroun kan ta ya ce "owky,sannu Aliya Habeebti’’
Da sauri ta kalle shi jin ya fad'i sunan ta kamar yanda Al-amin ke fad'i,ganin yanda ta yi ne ya sa ya ce "ko ban iya fad'a ba ne"....ta yi saurin cewa no ba haka ba ne,cikin girmamwa ta ce "ina wuni"......ya amsa da "lfy lau.."
Huda ta zame hannun ta daga na sa,cike da kishi ta ce " Ya Haroun mu tafi dan Allah" "Wai ina zuwa haka"...Dawud ya k'ara tambaya a karo na biyu. Huda ce ta ba shi amsa da gidan "Anty Salma" yayin da ta ke shirin shiga gaban mota. Haroun ma saukowa yayi daga motar ya na fad'in bros bari na kai su na dawo.. Dawud ya gyad'a ma sa kai,idanun sa kan Habeebti har ya shiga motar. Dawud ne ya bud'ewa Habeebti bayan motar inda su Halima ke zaune cikin rab'a,bayan ta zauna ya rufe motar,ta na ji Halima da Maryam na gulmar ta da Dawud,har da k'yak'yacewar da dariya. Kallan su kawai ta yi,ko da ta dan d'aga ido tsautsayi ya sa ta kalli mirrow din gaban mota,karaf sai tsintar idanun ta ta yi cikin na Haroun....
💫💫💫💫💫
1⃣3⃣
Dasauri ta yi k'asa da na ta idon,ba shakka dole Hajiya ta ce ta yi takatsantsan da Haroun dan kuwa sam be ma ta kama da mutumin arziki ba. Gaba d'aya kasa sakewa ta yi dan kuwa hirar da Huda ta ke ma sa be hana shi sa idanun sa kan Habeebti ba,motsi kadan sai ta ga sun hada ido. Allah Allah ta ke su isa gidan Aunty Salman,gashi gidan da nisa har uwa uba janbilo.
Da isar su ta yi maza ta fito daga motar har da dan tuntub'an ta,ta na ji ya na ‘’k'arfe nawa zan dawo na d'auke ku’’ Huda cike da murna ta ce ‘’da yamma’’ dan da cewa yayi ba zai dawo ba,amma ganin Habeebti ya sa ya ji dole ma ya dawo dan shi kam be gaji da ganin ta ba.
Ciki ta shige abun ta duk da zuwan ta gidan na farko kenan ita kan ta Aunty Salman ba sanin ta ta yi,amma Haroun ya sa ta yi karfin hali,sam ji ta yi jinin ta be hadu da Haroun ba,musammam dan zaman da su ka yi yanzu ta dan karanci kadan daga cikin halayyar sa.
💫💫💫💫💫
1⃣4⃣
Karba ta murna Aunty Salma ta mu su,ta na ganin Habeebti ta gane ta. Falon ta su ka baje su na ta hirar su,sai da Anty Salma ta yi da gaske kan Habeebti ta cire hijabin ta sannan ta cire. Huda ce ta ce ‘’ai in dai wannan ce daki kadai ta ke zama ba hijabi’’ Aunty Salma na dariya ta ce "kar ki damu Habeebti gida ba maza,yara na uku ne kacal kuma duka mata ne,Maigidan kuma ba ya gari" kunya ne ya rufe Habeebti,su Halima kuma dariya su ke mata. Aunty Salma ta ce ‘’ai ni kam da Huda gwara irin su Habeebti sau dubu,kai ni wlh Dawud ma na yiwa sha’awan ta....’’ nan fa Halima da Maryam su ka hau shewa,su na fad'in da ma sun gano ya Dawud har wani rawan jiki ya ke...ai kuwa ya bari biri ya gan sa....Anty Salma na dariya ta ce ’’kai kuji yara marasa kunya,yayan na ku ke ma tsiya haka...’’ ita kuwa Habeebti jin maganar ta su ta ke kamar yasasshen zance dan ita Allah ya riga ya zaba ma ta miji.
"Wai ku ba za ku fitar da miji a mu ku aure ba ne..ke Halima ya ake ciki ne..’’ Aunty Salma ta tambaya ta na mai duban Halima, Kana Halima ta ce’’ Aunty Salma ni fa har yanzu ban ga wanda ya kwanta min ba ne..’’ ‘’ina za ki sami wanda ya kwanta mi kuwa ki nan ki na mafarkin samin prince charming,irin mazajen littafi....’’ Maryam ce ta yi saurin katse ta,tuni Halima ta kai ma ta duka,ta yi saurin kaucewa.
Cike da mamaki Aunty Salma ta ce ‘’an banu,ke kuma wasikar jakin da ki ke karantowa kan ki kenan Halima....ai mazan littafi sai irin matan littafi’’ baki cune Halima ta fara magana ‘’Aunty Salma ai ko nima din ba laifi kalle ni fara dogo mai saje mai matan littafin za su nuna min,bare ma ai abun rabo ne makwabcin ka ya biyawa matar ka hajji.....’’gaba d'aya su ka sa mata dariya wanda hakan ba karamin kular da Halima yayi ba,da ba ta san sanda ta zunguri Maryam ta na fad'in ‘’dallacin ba gwara ni ba,ita fa wannan ko samari ba sa kulata sai dai alhazawa ma su katan timbi"
💫💫💫💫💫
1⃣5⃣
Magarnar Halima ba karamin ba tawa Maryam rai ta yi ba,jiki sanyeye ta ce ai ba komai su ma din mutane ne. Aunty Salma ta dafa ta tace ‘’kar ki damu kin ji,ko da Alhajin ne ai na gari shi ake bukata,ina adduar nan da na koya mi ki,ki na yi ko’’ ta ji sanyi cikin ran ta jin kalaman Anty Salma,ta ce’’ina yi sosai,a sujjada har ma karshen ta hiya. Tsaya ki ji ta.....
ALLAHUMMA JA’ALNA ZAUJAN SALIH. WARZUQNA ZAUJAN SALIH. WARZUQNA ZURRIYATAN SALIH. ALLAHUMMA GAFIR WALIDAYYA WARAHAMHUMA KAMA RABBAYANI SAGIRA.’’
Jin ta karanto adduar da kowace d'iya mace ya kamata ta na yi,kuma ya kamata iyaye su koyawa ‘ya’yan ta tun suna k'ank'ana ya sa Anty Salma murmusawa,ta na fad'in ‘’ai tun da ki ka ce Allah kin gama magana,the best is yet to come’’ Huda ta shune ta da baki "no wonder yarinya ta ke dad'ewa ta na sallah,ashe sallar rokan miji ta ke...’’ ita da Halima su ka sa dariya har da tafawa. Aunty Salma ce ta ce yara kenan,ba sallar rok'an miji ba,idan ma hajjin rok'an miji ta ke ta yi din,ai ba mijin ba kawai,na gari shi ake fata,ba kusan shi ne rabin rayuwar d’iya mace ba,ke da baki sallar rokon mijin wa ki ka tsayar?.’’nan fa aka ji Huda shiru,fuska cike da dariyar mugunta Halima ta ce ‘’ya Haroun’’
Dariyar da Habeebti ta ga sun sa gaba d'aya ban da Huda ya sa ta kallan su cike da mamaki,dan dariya idanun Aunty Salma har da kwallan,ta ce ‘’lalle yarinya kin kama gaibu,gwara kowa da ke ko da yake dama irin ku d'aya sai ku je can ku k'araci rawan kan na ku....’’rai bace Huda ta tashi ta bar mu su falon. Nan fa aka sa faifan Haroun,dama gasu idan aka dauke Habeebti dukan su ciki d'aya su ka fito. Yanda ya ke tara mu su abokan banza masu yawan gaske a gida su ke ba ta labari. Halima ta k'ara "aikam jiya tsautsayi ya kai Abba d’kin ya Haroun d'in ma baya nan sai yan hayaniyar sa,sun turnuke d'akin da warin kayan maye,kin ji fad'a kuwa gun Abba’’
Aunty Salma ta ce "ya salam,ai dole ya yi fad'a,kuma a ma sa magana ya ce shi ba ya sha,zai ki mutane ne,shi ko Dawud be burge sa dan Allah,daga shi har abokan sa a nutse abun shaawa’’ ‘’ai kam Abba ya ce kar ya sake kawo masa abokan banza gida’’ fadin Maryam kenan. Aunty Maryam ta ce yes he is ryt,ko dan mutuncin yaran sa mata be kamata ba,Allah dai ya shirya’’ gaba d'aya su ka amsa da amin.
Sai yamma likis Haroun ya dawo daukan su,sai a sannan ya shiga su ka gaisa da Aunty Salma,har kebewa su ka yi ta dan masa fad'a. Za su tafi ta ba su cards na walimar kanwar mijin ta wanda za a yi gobe. Sun tafi da alkawarin za su zo InshaAllah.ya Haroun zai kawo su.
💫💫💫💫💫
1⃣6⃣
Haka ma hanyar komawar su gida,idanun Haroun kan Habeebti,cikin ran ta fad'i ta ke idan ma kai maye ne ka ci kanka,dan kuwa hirar sa da aka yi a gaban ta ya sa gaba daya ya kara sire mata.
Garin Allah na wayewa su Halima su ka fara shirin had'a kayan biki,dan kuwa dangin mijin Aunty Salma yan gayu ne dole su kure a daka. Da yamma ta yi yan mata sun gama cin ado amma shiru ba Haroun ba alamar sa. Huda ta yi kiran wayar sa amma sam ya ki shiga. Kai tsaye bangaran Hajiya su ka wuce,dan daga Ummi,har Mama wato mahaifiyar Haroun suna can,su ma din wunin biki zasu.
Ganin yanda su ka zumburo baki ya sa su Ummi tambayar lafiya..kamar za su yi kuka su ka ce "Dan Allah Ummi ku ce da Ya Dawud ya aje mu ma,ya Haroun ya ki ya zo" Ana haka sai ga Dawud ya shigo cikin bakar jamfa. Jin abun da su ke fada ya ce sam be san sance ba,sai da Hajiya ta sa baki sannan ya hakura.
Kowa ya fito fes da shi,hatta Bilkisu da Aysha ma ba a bar su baya ba. Habeebti ce kadai ba ta fito ba.
Hajiya ta bi ta har daki ta na tambayar lafiya kuwa,ile kuwa sai ga ta kwance cikin bargo. Baki bude Hajiya ta ce ‘’Ha’a Aliya ba za ki bi mu ba ne...’’da kyar Habeebti ta iya bude baki ta ce Hajiya wallahi ciwan kai,migraine di ne ya tashi,mun yi da Ya Duwud zai kamin magani ina ga ya manta’’ ‘’ayya Allah ya sauwake,zan tuna ma sa yanzu idan mun fita sai ya sa ko Ayub ne ya kawo mi ki,gidan duka mun fita,Talatu ce kadai can ta ke wanke-wanke’’ Habeebti ta ce toh Hajiya,adawo lafiya.
Ba karamin rashin jin dadin rashin lafiyar Habeebti Dawud yayi ba,kafin ma su bar gidan ya yi kiran Ayub a waya dat lalle ya zo ya kawowa Habeebti maganin. Cikin mota mai suna Quest su ka dunguma sai gidan biki.
Haroun kuwa ya na can taron wani abokin sa,sanin duk lalacewar Haroun da ake ganin ya na yi sam be iya shashaye ba ya sa abokan sa hada baki su ka ba sa wata kwaya mai karfin gaske ba da sanin sa ba ya sha,amma da ke jinin sa mai karfi ne a hankali ya ke dibar sa. Ganin haka ya ce da daya daga cikin abokan sa wanda sam be da hannu cikin abun da aka ma Haroun,sai ma nuna bacin ran sa da ya yi,ya mayar da shi gida. Kai tsaye gidan ya mai da shi,ko sallama be ma sa ba da kyar ya ke tafiya ya shige gidan. Da ke kan sa juye ya ke,maimakon ya wuce bangaran su,sai tsintar kan sa ya yi falan Hajiya,nan ya yi zaman sa kan kujera hannun sa biya ruke da kan sa.
Jin motsi a falo ya sa Habeebti yin tunanin Ayub ne ya kawo ma ta magani,dan kuwa idan shi din ne ba d'aki zai shigo ba dan ba sa shigo mata d'aki.
💫💫💫💫💫
KHADIJA SIDI......✍🏽
1⃣7⃣
A hankali ta tashi,a daddafe ta sanya hijabin ta,ta na bin bango saboda sarawar da kan ta ya ke ta fito falan.
Maimakon ta ga Ayub sai ganin Haroun ta yi. Gaban ta ya yi mummunar faduwa,har za ta juya sai kuma ta sake tunani ta iya yiyuwa shi din aka bawa sakon,dan haka a daddafe ta k'arasa gareshi......jin tafiya ya sa ya d'ago a hankali,idanun sa sun sauya sun yi jajur,kallo daya ta ma sa ta yi saurin kau da idanun ta gefe,murya a sanyaye dan ciwo sam ba ta lura da ainihin halin da ya ke ciki ba ta ce da shi ‘’kai ne aka bawa magnin ka kawo min...’’ jin ta ambaci magani ya sa hannu a aljihu ya shiga lalube,sai gashi ya fidda wani dan sachet ya mi ka mata ba tare da ya tanka mata.
Ta karba ta na juyawa,sannan ta sa hannun ta fito da tablet din ciki,maimakon ta ga wanda ta ke tunanin gani sai wani daban ta gani,jikin sa an rubuta Diazepam,maimaita sunan ta yi,kai ita dai hankalin ta be kwanta da sunan maganin ba dan ba ta ma san shi ba, ta koma d'aki ta d'au wayar ta numbar Dawud ta kira,bugu uku ya d'aga,ko hayaniyar su Huda ba su ji ba da ga ji kuma driving ya ke.
Ya na d'agawa ya ce ‘’Habeebti driving na ke ga Karota can ina hangowa,ya kawo mi ki maganin ko’’’jin haka sai hankalin ta ya dan kwanta ta ce ‘’eh amma wani ne daban..’’ya ce ‘’eh ba a sami wancan ba ne,sai na ce ya kawo mi ki wannan ki dan sami sauki,za ki iya shan kwaya biyu for now,na aje su Huda na fito na duba mi ki da kai na’’ amsa ma sa ta yi da toh,sannan ta aje wayar.
Ta dan yi jim kad'an,tunanin zaman Haroun a falon Hajiya ta ke. Ko da ya ke ba mamaki ma ya tafi tun da magani ya kawo ma ta.da wannan tunanin cikin ran ta fito za ta kitchen neman ruwa.
Ga mamakin ta in da ta bar shi nan ta gan sa zaune. Kai tsaye kitchen ta wuce,ta ga Talatun ma ta gama wanke wanke har ta gyara wajan ta yi tafiyar ta.
Ruwa ta samu ta dan zauna ta sha maganin,toh amma sai mai....maimakon ta ji saukin da ta ke tunanin za ta ji,sai ma wani jiri da ta ji ya na diban ta. Hannun ta bisa kan ta,ta ke bin bango,abu kamar wasu karamar magana ba sai ta zama babbba ba. ciwo sai dada k'aruwa ya ke kamar ana dad'a hura shi..a daddafe hawaye fal fuskar ta ta iya karasawa falo,tun ta na iya takawa har ta kasa ta zube kasa,da rarrafe ta karasa gaban Haroun ta na fad'in taimakamin dan Allah Haroun,kai na Haroun....a hankali ya sauka ya durkusa gaban ta duk da jirin da ya ke ji ya na diban sa,da kyar ya ke iya fadin Habeebti....Habeebti...Habeebti.......
Allah kadai yasan iya lokacin da su ka yi a haka,kamar cikin mafarki ta ji hannu na bin jikin ta,da sauri ta girgiza kan ta da karfin da yayi saura a jikin ta ta ke kokarin tura hannun,ta na kokarin bude idanun ta da tuni su ka yi nauyin gaske,ko da kuwa ta bud'e idun ba gani ta ke yi ba.....murya can kasa ta ce ‘’Haroun menene haka,me ka ke min haka...Haroun ka ji tsoran Allah’’ can nesa ta ke jin muryar sa,be fad’in komai sai sunan ta ‘’Habeebti...Aliya....Habeebti....Aliya...’’hijabin ta ta ji ana kokarin raba ta da shi,nan ta hada duka karfin da ke jikin ta,ta buge shi,ta yunkura za ta tashi,sai kuma ta yi luuu ta dawo kasa....daga nan ba ta kara sanin halin da ke ciki ba,wannan ya ba shi damar cin galaba akan ta.....
💫💫💫💫💫
1⃣8⃣
Bangaran Hajiya kuwa tun da ta je biki hankalin ta ya kasa kwanciya,bini bini sai ta ce ta bar yarinya a gida ni Mairo,kai da dai hankalin ta ya kasa kwanciya sai ta kira wayar Habeebti,amma shiru ka ka je ba a d'agawa,sai da ta mata miss call har biyar,hakan ya sa hankalin ta tashi,ta fara neman wayan Dawud,shi ma sai a kira na biyu ta same shi,cikin fargaba ta ce Dawud maza zo ka mai da mu gida,na kasa samun Habeebti a waya. Daga d'aya b'angaran ya ce "d'azu mun yi waya ta ce da ni Ayub ya kai ma ta magani...." "kai gwara dai ka zo mu tafi" fad’in Hajiya kenan ta na mai fad'uwar gaba. Kana Dawud ya ce gashi nan zuwa dama ya samo mata maganin da ta ke sha ne,gashi zai dauko su Huda sai ya zo su tafi gaba daya. Hajiya ta ce toh dan Allah ka yi sauri.
Sun dan bata lokaci ba yanda Hajiya ta so ba,tafiya su ke amma Hajiya sai fad’a ta ke ma Dawud duk sanda ta kira wayar Habeebti ba ta d'aga ba. Motar kowa ya yi shiru,Ummi da Mama ne ke bata baki,ita kuwa fad'i ta ke ‘’uhum in ba Habeebti na sa a ido na ba hankali na ba zai kwanta ba’’
Ayub ne ya fara isa gidan hannun sa d'auke da maganin da Dawud ya ce ya siyowa Habeebti,gidan shiru ba kowa idan ka d'auke maigadi da ke can cikin d'akin sa ya na sharan bacci. B'angaran Hajiya Ayub ya wuce ya na mita,fadib ya ke ‘’an bar gida wayam wai haka akwai mai gadi,idan gidan za a d'auke kwacakwam har a d'auke ma ba wanda ya sani....’’ Cak ya tsaya ganin abun da ya firgita shi,wannan masifa da mai ta yi kama....fadi ya ke "Innalillahi wainnailahair rajiun....."ya yi mugun ganin da makiyin sa be fata ya gani....Habeebti ce kwance hajaran majaran da ga ita sai rigar ta da under siket da ya tattare zuwa gaiwar ta,abun da ya fi dagawa Ayub hankali shi ne ganin Haroun kwance kusan rabin jikin sa kan Habeebti ya ke,duk da wanda sa be bar jikin sa ba amma hatta belt din sa wulge ya ke can gefe...ya ma rasa me zai yi,shin me ke faruwa haka...Haroun ne ya yaudare ta har ta ba shi kan ta.?....toh idan ma hakan ne su rasa in da za su yi lalacewar ta su sai falon Hajiya.....jinin da ya gani ya yi jirwaje jikin siket din Habeebti ne ya sa shi kara lura da yanayin ta,sam daga ita har Haroun ba sa cikin hankalin su...
Sai a sannan ya fargaba,yayi wulgi da ledar maganin da ke hannun sa,ya karasa in da su ke da sauri jiki na rawa ya dauki hijabin ta da ke aje gefe da niyar rufa ma Habeebti,nan fa sachet din magani ya fado,idanun sa kan magani yayi saurin rufa ma Habeebti Hijabin ya na mai tura Haroun gefe guda,ina ko alamar tashi be yi ba hakan ya tabbatar ma sa da hez under drugs,ita ko Habeebti a sume ta ke. Sachet din da ya fadi ya bi ya dauka,hannu na rawa ya karanta sunan maganin...DIAZEPAM.....
Nan fa komai ya fito ma sa a zahira,ba shakka Haroun ya ba ta kwaya ya gama da yar mutane...tuni idanun sa su ka rufe ya shiga jibgar Haroun,amma ina ko gizo,da gudu ya fita sai gashi dauke da ruwa mai sanyi karara,ya juye shi roba guda bisa kan sa...nan ya tashi a gigice ya na kokarin kamo Ayub din da be san sanda ya wulga ma sa rubar a fuskar sa ba ya na fadin tashi ka kashe mu su yar mutane,Haroun ka cuce yar mutane,ka cu ce mu,ka cuci Hajiyar mu,ka cuji zumunci,Haroun ina darajar ta mu ke.......?
💫💫💫💫💫
1⃣9⃣
A rikice ya ke duban Ayub kamar lokacin ya fara ganin sa,kalaman sa ke rud'a shi yayinda ya ke kokarin nazartar in da ya ke. Ganin Ayub na Kuka wiwi ya sa shi bin in da ya da Habeebti ke kwance tamkar matacciya. Kamar wanda aka zungura ya tashi da hanzari,wandan sa na kok'akarin zamewa ya yi saurin rikowa sai a sannan ya lura da rashin belt din sa a jikin sa,ya maza ya dauko ya saka.
A kid'ime ya yi kan Habeebti har da buge Ayub ya na fad'in me ya same ta?me na mata?ganin Ayub ya kasa ba shi amsa ya sa shi fara girgiza ta da k'arfi,amma ina ko motsawa ba ta yi ba.gaba d'aya zufa ya wanke fuskar sa. Hijabin ta da Ayub ya rufe ta ya yaye. Ganin abun da Ayub ya gani ya sa shi yin baya a razane,lokaci guda kuma yayi saurin sanya ma ta hijaban yayinda ya dauke ta yayi waje a guje. Ayub na biye da shi.
Fitowar su yayi daidai da shigowar motar Dawud,ganin Ayub da abun da ya dauko ya sanya Dawud yin wani wawan parking da sai da motar ta yi kara....kan ma ya fito Hajiya ce ta fito ta na salati cike da ihu.
Fitowar Dawud da su Mama lokaci guda ne,a tare su ka yi kan Haroun kowa na tambayar menen ya Faru?me ya sa me ta?Hajiya ce ta fi kuwa rud'ewa ganin da ga Ayub din har Haroun an rasa mai ba su amsa...a rud'e ta ke jijjijiga Habibti da ke langwab'e hannun Haroun,da dai ta ga ba ta motsi,sai ta koma jijjiga Haroun wanda zufa kadai ke fita daga koina a jikin sa. Ganin ba amsa ta Koma ga Ayub,wanda ganin ya kasa magana fadi ya ke Hajiya mu kai ta asibiti,asibiti Hajiya.....
Dawud ne ya yi kokarin karb'ar Habeebti amma Haroun ya yi k'yememe ya hana shi,dan haka kawai sai su ka d'unguma su ka shige mota ba tare da sun san ainihin abun da ya faru ba. Su Huda kuwa nan gida aka bar su suna jiran tsammani.
💫💫💫💫💫
KHADIJA SIDI....✍🏽
2⃣0⃣
Kai tsaye ba su Zane koina ba sai Star general hospital. Gabayan su da gudu su ka sauko,Haroun ne gaba,Hajiya wacce hannun ta biyu bisa kanta,da Mama,Ummi,Dawud da Ayub biye da shi.
Ba a yi wata wata ba fmly Doctor din su ya sa aka karbe su,cikin k'ank'anin lokaci aka kwantar da Habeebti yayinda Doctor da taimakon Nurses su ka shiga duba ta.
A reception Hajiya sai kai kawo ta ke,abun takaicin daga Haroun har Ayub an kasa samin mai bayani. Ayub in Banda Kuka babu abun da ya ke,Haroun kuma can gefe ya ke,shi ne ya tashi,ya zauna ya kuma tashi,ya ma kasa tsayawa gu d'aya. Dawud kuwa tsayawa yayi bakin kofar d'akin,ji ya ke tamkar ya bud'e ya shiga.
Fitowar Doctor ya sa su yin kansa da sauri,suna tambayar Doctor ya ake ciki? Cikin rud'ani Dawud ya ruk'o hannun Doctor ganin yanda fuskar sa ta yi alamar tashin hankali.
Kallan su ya yi daya bayan daya,kafin daga bisani ya ce "wacece mahaifiyar ta?" " gani" Hajiya ta bayyana kan ta da sauri. "Doctor ya ce za mu yi magana da ke a office d'ina pls"? Ya wuce Hajiya na biye da shi,haka ma Dawud da Ayub.
A cikin office din Doctor ya nemi su Ayub su ba shi waje,Hajiya ta ce ba komai suma 'ya'yan ta ne.
💫💫💫💫💫
2⃣1⃣
Sai da ya dan yi shiru sannan ya ce "Hajiya Alhaji na gari ne?" Cike da fargaba Hajiya ta amsa ma sa da "Eh wani abun ne Doctor,dan Allah me ya same ta?" Maimakon ya ba ta amsa,sai ya ce da Dawud ya kira Alhaji,Wato baban su ya ce lalle lalle ya zo as soon as possible. Jin haka Hajiya ta dad'a rud'ewa,fad'i ta ke "mutuwa ta yi ne ka kasa fada min?" Hannu na rawa Dawud ya kira Alhaji,jin haka ya ce minti ishirin ma yayi yawa,gashi nan karasowa.
Kan Alhaji ya karaso Doctor ya cigaba da yiwa Hajiya tambayoyi,shin menene dangantakar ta na ainihi da Haeebti,a susuce ta ke ba shi amsa,ta ce "d'iyar yayan ta ce,marainiya aka ba ni ruk'o. Ya k'ara da "Shin a ina aka dauk'o ta a wannan halin da ta ke ciki?"
Sai a sannan Ayub ya ba su labarin yanda ya tadda Haroun da Habeebti ba tare da ya fadi ainihun ta'asar da aka ma ta ba,amma ita Hajiya tuni jikin ta ya fara ba ta,dan hannu biyu ta d'ora a kan ta ta na fadin "ni Mario na shiga uku,na banu.."
Ana haka Alhaji wanda shi da Dawud da Haroun kamar an tsaga kara haka su ke ya shigo. Ganin sa Doctor ya tashi ya bashi hannun cikin girmamawa,tare da bashi wajan zama.
💫💫💫💫💫
2⃣2⃣
Ba tare da b'ata lokaci ba Doctor ya ce da su" Wato a zahirin gaskiya wannan yarinyar an bata magani ko na ce kwaya mai karfi ainu,Dawud you ar a pharmacist,am very sure kasan effect din Diazepam." " innalillahi wainnailaihirajiun! Ina Habeebti ta sami Dia.-ze-pam...,menene gamin ta da shi,kadde shi ta ke tambayana akai na ce ta sha har biyu..." Doctor ya gyada kai"tabbas ko da d'aya ta sha in dai jinin ta be da karfi zai ma ra illa,kasan dai masu irin rashin lafiyar da ake bawa magani,wanda su ma din sai ya tsanan ta,bare har biyu,kasan overdose din maganin har kisa ya ke...."
Wani sabon Kuka Hajiya ta sa Alhaji ya shiga tsawatar mata,yayin da Dawud ke fad'in ."kwarai kuwa,ni kuwa na san wannan Doctor,shikenan na kashe Aliya" kwalla idanun sa ke fitarwa. Amma me?sai ji su ka yi Doctor ya ce "ba wannan ne kadai ba,an yiwa yarinyar fyad'e...." Dum...haka Hajiya ta ji jin ta ya d'auke,lokaci guda haske ya dishashe mata ganin ta ya d'auke,tuni ta yi luuuu za ta fad'i,yayinda Alhaji yayi saurin rik'ota duk da shima din a kid'ime ya ke,nan jikin shi ta fad'i sumammiya.....
Dawud kuwa tuni idanun sun rude,ba ma ya ganin gaban sa bare ya san halin da Hajiya ta shiga ya fita a guje tamkar zakin da ya shekara goma be ga nama ba ya hangi nama,labarin da Ayub ya basu ke ta yawo akan sa....gaba d'aya muryar sa ta cika asibitin,kira ya ke " Haroun!Haroun!!Haroun!!!!!!!!!!!"Ba Haroun ba,duk wanda ke cikin reception din sai da su ka tashi a rikice,suna jiran tsammani....
💫💫💫💫💫💫
🗣
No comments:
Post a Comment