Sunday, 25 December 2016

Sakaci 14

           💔💘 *SAKACI* 💘💔

    

                      1⃣4⃣

© Fatima A Garba

Hassan:

Ashe Hassan tun ranar da aka kama mu ya tattara yabar garin, Ya Umar harda biyan police akan su nemoshi amma ba'a ganshi ba.

                        ******

Mama ta daina zuwa aikin rana, na safe kawai ta ke zuwa Ya Umar ya siyo mana kayan abinci dai-dai na buk'ata, yana matuk'ar kulawa da mu, duk wani d'an kud'in da yake samu na bautar k'asarshi da kuma d'an bige-bigen da ya keyi a kan mu yake k'arewa.

Daga Ummi har mahaifinshi ba wanda ya nuna damuwa akan kud'in da yake kashe mana, sai ma dai dad'a goya mai baya da suke yi.

Ya Abdallah ma bai zauna ba, tunda dama ya jima da daina zuwa school saboda rashin kud'in da za'a biya mai na zana waec d'inshi, kullun zai fita yin dako da shi d'in ne muke samun na cefane kuma har yake k'ok'arin siyamin duk wani abu na kwad'ayi wanda baifi k'arfinshi ba.

A wannan lokacin ba ma yin kwana biyu Ya Abdallah yake siyo mana nama asa a miya, Mama takan yimai fad'a akan yadinga ta ra kud'in dan yasamu ya biya kud'in waec d'in, amma kullun Mama ta fad'a mai haka, sai ya ce:

"Mamana ki daina damun kanki karki manta namiji baya tsufa da karatu a hankali zanyi, amma na fiso na inganta farincikin ki dana Farida"

Kullun ya fad'i haka sai mun zubar da hawaye, kuma Mama ba ta gajiya da Saka mai albarka.

                      ***********

Akwai wata ranar jum'a da bazan ta6a mancewa ba.

Ya Abdallah ne ya fito daga d'akin kwanan mu sanye da kayan leburancin, kallonshi na yi nace "Ya Abdallah har zaka fita"

Fuskarshi k'unshe da murmushi ya ce "zan fita Farida Umar a mana addu'a domin yau na fita da kaza zan dawo"

Murna fal zuciyata nace "kai Ya Abdallah kace karna cika cikina yau" dai-dai wannan lokacin Mama ta shigo d'aki ta kallemu ta ce "wai me ake tattaunawa ne"

Na fad'a ma ta, murmushi Mama ta yi sannan ta ce "Bawan Allah karka takura kanka da aiki fa kazo wani cutan ya kamaka kasan halin da muke ciki"

Murmushi Ya Abdallah yayi kafin kuma yace "Mamana ki daina damun kanki, addu'arki kawai nake buk'ata, yanzu dai fad'a min mai zan taho dashi idan ina dawowa"

"Kullun a cikinta nake, bazanyi *SAKACI* da na yi a baya wurin yi muku addu'a ba, kubewa zaka taho dashi d'an albarka" Mama ta fad'a.

"Farida Umar mai kikeso na taho miki dashi" Ya Abdallah ya tambayeni, "Ya Abdallah ka tahomin da atile idan zaka dawo"

Ya ce "toh shikenan amma ga wancan farar yadin ki wanke min don Allah ta fita kafin lokacin masallaci" na ce "angama har aron dutsen guga ma zan d'auko na Ya Umar na goge maka"

"A'a Farida karki sa ke koda zancen wasa kice zaki zama mai auro, mutum ya godewa Allah da duk abinda Allah ya bashi, nikam idan kika wanke dakyau ya wadatar"

Murmushi Mama ta yi had'e da cewa " wallahi Abdallah idan kana wasu maganganun sai naga kamar ba d'an shekara goma sha bakwai zuwa sha takwas ba, sai naga kamar kawuce shekarunka, akwai ka da sanin ya kamata"

"Sai na dawo Mama" Ya Abdallah ya fita, fitar da ta kasance ta har abada fitar da bai sake dawowa ba sai gawarshi da aka kawo mana.

Tabbas munshiga tashin hankali mara misaltuwa lokacin da aka shigo mana da gawar Ya Abdallah mota ta bigeshi, ruwan wankan juma'a dana saka mai a murhu shi ne aka yimai wankan gawa.

Ba wanda baiji tsoron tashin ciwon Mama ba a wannan lokacin kasancewar ba wanda bai san irin k'aunar da Mama ta ke yimai ba.

Amma ga mamakin kowa shi ne Mama ko kuka batayi ba hasalima ita ta ke bawa jama'a hakuri.

Hakan da ta yi mutane da dama sunji dadi kuma sun yaba ma ta amma badda Ummi da Ya Umar domin sun san cewa ta na kukan zuci ne.

Ranar da Ya Abdallah ya cika kwana bakwai da rasuwa Baba ya dawo, wanda rabonmu da shi wata biyar kenan, shi ne kuma yayi dai-dai da watan Ya Hamid hud'u da sati biyu da rasuwa, sam Baba bai san da rasuwar Ya Hamid ba balle kuma na Ya Abdallah.

Aranar munsha mamaki irin kukan da Baba ya ke yi yana da yasani, tabbas a ranar mun tausaya mai ban ta6a sanin Baba ya damu damu ba sai ranar, yana kuka yana cewa!

"Ku yafemin yarana, na cutar da ku cutarwa kuwa mai yawa, ban ta6a yarda kun ra6eni ba, sam bakusan dad'in uba ba, na kasa d'aukan nauyinku da Allah ya d'auramin bayan kuma Allah bai hane ni ba"

Kama hannun Mama yayi, ni kuma ya janyoni jikinshi, wannan itace rana ta farko da mahaifina ya yafara rik'eni cikin kulawa, kuka mukeyi mai ban tausayi, Mama idonta a bushe har wannan lokacin bata zubar da hawaye ba.

Cikin kuka Baba yake cewa " Sakinatu na yi asara, ina tsoron gamuwata da Allah, naci amanar da Lamido ya bani, na zalince ku, ku yafemin ko zan sami sauki"

A ranar da daddare Mama ta sanarwa da Baba irin 6ata min rayuwa da Hassan yayi, Baba yayi kuka yayi bak'in ciki gami da danasani, haka yayita rok'on gafarar mu, a ranar dai Baba bai runtsa ba.

Washegari ya zowa Mama da maganar yanaso mu bishi zuwa Bauchi, domin shi yanzu baya so yayi nesa damu dad'in dad'a kuma mutanen unguwa sun sani agaba akan abinda ya faru ban isa fita ba.

Mama sam tak'i amincewa haka Baba yayi magiyanshi har ya gama amma tak'i amincewa ta ce ita tafiso ya barmu anan, kasancewar baya son ya kuma yin abinda zai shiga hakk'inta yasa ya hakura amma badan yaso ba, sai dai yace dole zai canja mana gida wannan Mama bata hanashi ba.

Kwanan Baba biyu da dawowa amma sam baya zama yana cuku-cukun nema mana gida, Ummi ce kullun ta ke shigowa domin ta d'ebewa Mama kewa sai kuwa Ya Umar da yana dawowa daga aiki mu yake fara lek'owa kuma har wannan lokacin bai daina yi mana hidima ba baranma ni.

A ranar wata laraba ne, na tashi da wani azababban ciwon ciki, Mama ta d'auka period zanyi shiyasa taje da kanta ta siyomin peldine, nasha amma ciwon cikin k'aruwa ya keyi, haka na wuni ina abu d'aya.

Ranar sam ba wanda ya rintsa a cikin mu ukun, da safe ne kuma abun yayi tsanani domin jini ya fara zuba (bleeding) fiye da tunani, ba abinda ba'asa ba don tare jinin amma ina harda guda-guda ya ke fita.

Kan kace meye wannan na galabaita, ba shiri Baba ya je gidan Ummi Ya Umar baya nan amma anci sa'an Alhajinsu na gari, shi ya kaini asibitin a galabaice.

Dak'yar likitoci suka tsayar da jinin na zubar da jini sosai amma sunce ba sai a k'aramin ba, wunin ranar haka likitoci suka dukufa dubo abinda yake damuna.

Abinda suka gani a sakamakon gwajin nawa shi ne silar komai, lokacin wani Dr ya shigo d'akin da nake da sakamakon, a sannan na farka ina kwance jiki ba kwari, ya kalli su Baba hankali tashe yace .

"Kune iyayenta " su Baba da Alhaji sukace "eh likita don Allah sanar damu, abinda yake damunta"

Dr ya gyara gilashin idonshi sannan yace "ina mijinta?" "Ras" gabana ya bada, cikin damuwa "Baba yace bata da miji a yanzu don Allah ka sanar damu meye matsalar"

Dr yace "toh ina fargabar sanar daku akwai wani tsarin iyali da y'arku ta keyi wanda ya janyo ma ta matsala babba, kuma ina tsoron sanar daku mahaifanta ya samu matsala bazata ta6a haihuwa ba, kuma ba lalle ne ta sa keyin al'ada (period) ba koma ta sa keyi toh fa ciki bazai ta6a shiga ba, saboda yin wannan tsarin iyalin wanda ya wuce k'a'ida, a yanzu dai munyi k'ok'arin tsayar da jinin"

Abinda likita ya fad'a shi yayi sanadiyar fad'uwan Mama, cikin gaggawa akayi d'akin emergency da ita, adai-dai wannan lokacin Ya Umar ya shigo asibitin koda yaji dalilin fad'uwar Mama, zama yayi a kasa tamkar zaman y'an bori yana cewa mai yasa aka fad'awa Mama, ba wanda ya iya bashi ansa.

Munga tashin hankali ranar ba yadda ba'ayi dani na kwanta ba nak'i nace dole naga Mamana haka aka barni.

Likitoci sun kai awa biyu a d'akin da Mama take kafin, babban likitan ya fito yace "wai waye Farida" ban iya magana ba illah d'aga hannuna da na yi, yace "toh ma za kije tana son ganinki" ya juya gasu Baba yace sujira na fito.

Halin da naje na iske Mama ya kusan zautar dani, bazan ta6a manta wannan ranar ba.

Farida ta dakata saboda kukan da yasha  k'arfinta, su Dr Jidda ma kukan sukeyi sosai.

~Ummu Hanan~

No comments:

Post a Comment