💫INA DARAJAR TA KE ?💫
KHADIJA SIDI......
8⃣6⃣
Ya na dariya ya tashi ya jawo ta. Da kyar ta yarda ta zauna kusa da shi. Hannun ta cikin na shi ya ce "Komai ki ka ga ya faru da dan Adam muk'addari ne daga Allah,mummna ko kyakkyawa,dama Allah ya rubuta tun randa aka busa ma na rai. Kawai dai ba ki yi koyo da hadisin manzo(SAW) ba inda yake fad'in kafad'i alkhairi ko kai yi shiru,bare ni da na ke mijin ki Habeebti,duk da laifin da na miki a baya na san kin san aure ya fi gaban wasa ko kina sona ko ba kya son,yanzun da na yi accident d'in bayan ni da naji a jiki na waya ji abun fiye da ke? Babu,so kar ki damu,na ji dad'i kin gane kin yi ba daidai ba,kuma kin iya ba da hukuri. My Habeebti ta na da kunya,mai godiya ce idan an kyautata mata,me kuma ba da hakuri ce idan ta san ta yi ba daidai ba,am very proud am ur husband wlh"
Dadi da kunya ya sa Habeebti rufe fuska. Haroun na dariya ya ce,maza a je a yi wanka a kwanta gobe da sahur. Wankan ta yi,kan ta fito Mai Junior yayi bacci. Ko da ta zo kwanciya sai da ta k'are masa kallo tas,sannan ta kwanta ta na mai alfahari da samin miji kamar Mai Junior. Ta na jin shi ya tashi wajan ukun dare,ya ja bargo ya rufa mata da ke daren ranar an tsala ruwan sama. Ga mamakin ta sai ga shi ya d'auro alwala,ya zo ya shimfid'a sallaya ya shiga jera nafila. Cikin ran ta tace " kai Haroun duk duniyancin sa ashe ya na tab'a ibada?ko da yake ai watan ramadan ne,ko kuma dan ya ji ya kusa gangarawa Allah ya taimake shi" da wannan tunanin bacci ya sake d'auke ta.
Washagari bayan sun yi sahur shi ya ja su sallar asuba. Bayan sun idar,ya ga Habeebti na shirin komawa bacci ya hanata,ta na hamma ta ce " Ayya mana Mai junior me zan yi toh?" Hannun sa ruk'e da tasbah ya ce "ki yi zikiri ko ki karanta qur'ani,amma ke da bacci sai gari ya waye,duhu ya gushe,baki san Manzo sallahu alaihiwasalam ya ce ladan wanda yayi haka kamar wanda yayi hajji da umara ba ne?baki san cewa wannan lokacin,da tsakanin sallar magariba da ish'i,da tsakanin la'asar da magariba,da kuma silisin dare lokutan k'arbar addua bane? ko ba ki san la'asar da kuma wannan lokaci na asuba malaiku su ke rufe ayyukan dan Adam,suna masu kai kawo a tsakanin mu da daddare,da kuma malaikun wuni suna masu had'uwa da sallah la'asar da kuma sallar asuba,sannan wanda su ka kwana tare da mu sai su koma sama,sai Allah ya tambaye su ya ku ka bar bayani? alhalin kuma Allah shine mafi sannin su,sai malaiku su ce mun same su suna sallah,mun kuma bar suna sallah. Bukari da Musulimu su ka rawaito" Da wannan jawabin na sa Habeebti ta d'auko qur'ani,tana jingine jikin Mai Junior ta shiga karantawa a hankali,yanda ya ke jiyo sautin karatun na ta cikin jindad'i. Sai da gari yayi haske sannan su ka kwanta.
💫💫💫💫💫
💫INA DARAJAR TA KE ?💫
KHADIJA SIDI......✍🏽
8⃣7⃣
Da yamma sai ga Mama Eze ta zo musu sallama za tafi garin su bikin birne Emeka,kuma ba za ta dawo ba. Daga ita har Habeebti sai da su ka yi kuka su ka k'oshi. Haroun ya ce idan an brine Emeka ta dawo ta yi zaman ta,ai ba mai korarta. Ta ce garin su zai fi mata kwanciyar hankalin ta. Kud'i mai yawa ya kawo ya bata sannan su ka yi sallama. Rabuwar ba dadi.
Ana saura kwana goma sallah,wajan goma na safe Mai Junior ya shigo d'akin Habeebti d'auke da kaya,ya tadda ta na sallah. Aje kayan yayi gefe,sannan ya zauna bakin gado ya na jira ta idar. Alhamdulillah jiki yayi kyau,musammam hannun sa da hatta bandage din ma an cire.
Bayan ta yi sallama ta d'ago su ka had'a ido,murmushi ta yi tare da fad'in " Sannu da zuwa" Mai Haroun ya amsa,tare da mata nuni da kusa da shi. Sai ta cire jikan d'in ta sannan ta taso ta zauna. Ya na mai wasa da awarwarayen hanunnun ta ya ce "Kullum ki na sallar walha,kin ji dad'in" Habeebti ta murmusa tare da fad'in "ai ya na da falala da yawa,cikin shi kuwa harda duk mutumin da ya dawwama ya na mai sallar walha toh Allah zai kiyaye masa gabb'an sa,ma'ana har ya koma ga mahaliccin sa ba zai rasa wani b'angare daga cikin sa ba. Ka ga yanzu ga accident sai ka ga hannu ko k'afa ya cire,ka ga dai Emeka ko da ya rayu dama ya rasa k'afa d'aya,ga wannan masifar ta bomb da ake fama,ga cutuka da su ka addabi alumma,musammam mata,yanzu ka ji ance breast cancer..." Ta dan yi shiru,ya janyo ta jikin ss ya ce "uhum?ina ji,tell me more" kai ta girgiza sannan ta k'ara da "An karb'o daga Anas Allah ya k'ara yarda a gare shi,Manzo(S.A.W)ya ce duk wanda ya yi sallar walha Allah zai gina masa gidan bene a gidan aljannah. Hadisi ne 420 a cikin littafin bulugulmaram. A wata riwaya,an karb'o daga Abu Zarril Gifari Allah ya k'ara yarda a gare shi,cewa Manzo(SAW) yana cewa kowace gab'a na daga na daga jikin ku tana wayar gari akwai aikin sadak'a da ke kan ta,ko wani tasbihi sadak'a ne,ko wani hamdala sadak'a ne,ko wace hailala sadak'a ne,ko wani kabbara sadak'a ne,umarni da kyakkyawa sadak'a ne,hani ga mummunar aiki sadak'a ne. Zai wadatar da su gaba d'aya rakao'i da za su sallace su guda biyu na ga sallar walha ya isar masa. Muslim,Abu Dawud da Ahmad su ka rawaito." kan sa bisa wuyar ta,ya na shinshinar kamshin humran da ta shafa,ya ce "InshaAllah ni ma daga yau zan fara..." Ganin abun da ya ke ta tura shi gefe a tsorace,sai gashi kwance kan gado ya na dariya, ta na hararar shi ta ce " Malam azumi fa ake!"
Ya na dariya ya ce "Me na miki toh! Kun ji mu da mata! Daga dan shinshinar kamshi?" Sai a sannan ta dan ji kunyar yanda ta yi,ta yi saurin kawo wata maganar ta hanyar tambayar sa "kayan menene wannan?" Tashi yayi ya zawo ledar. Kaya ne masu kyau da tsada d'inkakku guda uku,Atamfa,leshi da shadda. ,ya mik'awa Habeebti tare da fad'in ni dai na yi da ka,Allah ya sa su yi mi ki,kayyan sallar ki ne. Cike da farin ciki ta na godiya ta karb'a. Ta ci sa'a duk sun mata kyau,kayan sun zauna a jikin ta kamar dan ita kad'ai aka yi su. Shi kan sa Mai Junior cewa ya yi "lalle ido ba mudu ba ya san kima"
Haka ya had'a mata da mayafai da hijab,sai takalma da jakukkuna da Sark'a da d'ankunne. Haroun Junior ma har da na shi,har kuma anko Mai Junior ya sa aka mu su. Da ke tun zuwan shi Kano ashe ya siyo kayan bayan ya bawa Anty Salma na su Hajiya da Mama,da kuma kud'in kayan azumin da za ta siyo mu su ta kai gida,nan Kaduna ya bada d'inkin na Habeebti,sauran kuma ya aje gun sa. Ya kuma ce da Habeebti ana gobe sallah za su Kano. Murna gun Habeebti ba a magana. Dan kamar k'aramar yarinya ta koma.
💫💫💫💫💫
💫INA DARAJAR TA KE ?💫
KHADIJA SIDI......✍🏽
8⃣8⃣
Ana gobe sallah su ka d'au hanya a motar abokin Mai Junior, da ke tashi motar ta tashi daga aiki,amma ya na sa ran compensation kwana kusa. Shigar su Kano rigima ta tashi tsakanin Mama Junior da Mai Junior,ba kunya ya kalle ta ya ce " Malama b'angaran Mama fa zaki sauka,ina ji ina gani ba zai yiyu sai ina kame-kame ba kan na ga mata ta!". Habeebti da ke zaune bayan mota sai cewa ta yi" Ba wannan maganar fa Oga Mai Junior,ga in da na saba sauka haka kawai Hajiya ba za ta ga na mata tawaye ba,ai ba ma zai yiyu ba,in dai haka ne sai dai na wuce Bichi abun na" Shiru yayi kafin daga bisani ya ce " Toh sai mu sauka tsohon d'aki na kawai...." Baki ta bud'e,dan takaici ma kasa magana ta yi,ta ma sa shiru. Abokin sa sai dariya ya ke mu su.
Suna isa gida,ta d'au yar jakar ta ta yiwa abokin sallama ta shige bangaran Hajiya abun ta. Ta na ji ya na kiranta ta masa banza. Hajiya ta yi murnar ganin Habeebti,musammam yanda ta ga ta yi kyau sosai ta yi bulbul kamar ba watan ramadan ba ne. Sai da ta ji Habeebti ta nemi ruwa Hajiya ta ce "no wonder ashe ke kin dad'e da yin sallar ki" Habeebti ta yi dariya.
Sai da ta huta ta je ta gaida Mama. Yanda ta k'arbe ta ba yabo ba fallasa,amma sam babu sakewa bare a yi hirar kirki. Dan haka Habeebti na bata atamfar da ta siya mata ita da Hajiya,ta mata sallama ta dawo gun Hajiya abun ta. Sai daga baya Aysha ta biyo ta da Junior wanda dawowar su daga gidan Anty Salma kenan,shi ma an kawo sa sallah. Ganin Habeebti gaba d'aya ya kalallame ta da shagwab'a da rigimar wata d'ayan da be gan ta ba. Mai Junior kuwa be sake neman Habeebti ba,har ta je aka mata kitso da kunshin sallah,wai hakan fushi ya ke da ita.kuma har ta kwanta ko waya be mata ba,hakan kuma ba k'aramin sosawa Habeebti rai yayi ba tsabar missing d'in shi da take da k'yar ta iya bacci ba tare da ta k'ira shi ba.
Yau take sallah. Bayan an sakko daga idi,gida ya cika da jama'ar gida. Falon Hajiya Dawud ne tare da Akib da Ayub,duk sanye da fararan shadda. Suna cin tuwan sallah. Hajiya da ta yi adon sallah zaune tsakiyar 'ya'yanta abun sha'awa. Dawud ne da tun da ya zauna ya ke tsimayin ganin Habeebti,amma shiru ka ke ji sai ma Junior da ya baro a waje suna wasa da yaran Anty Salma. Gajiya yayi da sa rai ya ce " Hajiya ina Habeebti ne?" Hajiya ta ce ta nan d'aki ina ga wanka ta ke" Sallamar Mai Junior su ka ji kafin ya shigo sanye cikin shaddar sa fara d'inkin ta zarce,gashi ta sha aiki da shud'in zare,yaci hular sa wacce ta sha kari karkace bisa kan sa. Ga takalmin sa sau ciki shi ma kalar zaren da aka masa aikin da shi. Yayi wani irin kyau mai k'ayatarwa,sai kamshin turaren tomford ke tashi daga jikin sa.
Har k'asa ya tsugunna ya gaida Hajiya tare da mata barka da sallah,Allah ya maimata mu su. Hajiya ta amsa sama sama. Kafin Akib da Ayub su gaishe shi tare da yiwa juna barka da sallah,shi kuma ya gaida Dawud da ya amsa masa fuska murtuke. Mai Junior be damu ba dan yanzu kam har ya saba da yanda Dawud ya ke masa. Ya tambayi Ayub Habeebti,Ayub ya ce ta na ciki. Be tsaya neman iso ba ya sa kai sai gashi ya shige ciki. Nan fa Dawud ya k'ule tare da fad'in "Hajiya ya za ki bari ya shige mata d'aki bayan bata san da zuwan sa ba!" Baki bud'e Hajiya ta ce " Na bar shi kamar yaya?gidan uban sa ne kuma matar shi ce,ita tace ma ba ta san da zuwan shi ba?ku ji mu da ikon Allah!" Tsaki ya ja tare da aje kwanan abuncin ya ma tashi ya fice,in da duka su bishi da kallon mamaki.
💫💫💫💫💫
💫INA DARAJAR TA KE ?💫
KHADIJA SIDI......✍🏽
8⃣9⃣
Habeebti kuwa zaune take gaban madubi,d'aya daga cikin kayan da Mai Junior ya siya mata,leshi sea green nd cream colour ne sanye jikin ta. Ta yi kyau sosai musammam da ta yi kwalliya ta yi kitso ga kunshin sallah. Hannun ta rik'e da dankwali da ta ke k'ok'arin d'aurawa amma masifar mitar da take ya hana ta ta nutsu ta d'aura. " wannan mutumin zai gane kuren sa! Wato har ni zai share ko! Kai tun jiya fa! Ko da yake ma wa ya damu,after ol dama na tsane shi! Arrrggh amma ko barka da sallah dai ya kamata responsible miji yayiwa matar sa...." Duk wannan surutan da take ya shigo ba ta sani ba,sai jin kamshin turaren sa ta yi,kan ta ankara ta ji an dauke ta tsam daga kan stool d'in da take. Har da dan k'arar ta dan kuwa ya mata bazata,farin ciki ya mamaye ranta,ganin ta hannun Mai Junior,ya zauna kan stool din tare da aje ta bisa cinyar sa yana fad'in "I miss you too my stubborn woman"
Sai a sannan ta tuna ashe fa fushi ta ke da shi,ganin sa ya sa ta manta. Nan ta fara k'ok'arin tashi. Ya ruk'e ta gam. Cike da fushi ta ce "wai ma manene ya kawo ka?" Yana wasa da kitson sallar ta ya ce " Na zo na ga kwalliyar sallar mata ta na mata bata barka da sallah kamar responsible miji dat i am,and steal a kiss...) Kan ta ankara yayi kissing din ta. Ganin zai wuce gona da iri ta masa wayo ta tashi da saurin tana fad'in "ka rufa min asiri kar Hajiya ta shigo,gida ne fa ba gidan kaba" dan kishingid'a yayi sannan ya ce " kin tuna min ainihin abun da ya kawo ni,k'arasa shiryawa mu je wajan Mama,na san ba ki mata barka da sallah ba.
Ba mu su ta d'au d'an kwalin ta ta d'aura. Haroun na daga kishingid'e ya ke kallan ta. Mayafi ta d'auka cream ta yafa bayan ta sa Sark'a da dankunne. Ajiyar zuciya ya saki tare da fad'in " Kin gan ki kuwa kamar amarya,dama an kawo min ke haka sanda kina amarya,munci amarcin mu" shiru ta masa kafin daga bisani ta ce" kai ka hanani samin wannan damar a rayuwa ta,ta hanyar min fyad'e har na haifa ma d'a....da ba ka min haka ba da nima naci amarci kamar yanda kowace d'iya mace." "Aliya....." Ya kira sunan ta yayinda ya tashi tsaye. Hannu ta d'aga masa,irin kar ma ka zo kusa da ni,kafin ta yi saurin yin gaba ta fice abun ta" sai da yayi dan jim sannan ya bi bayan ta. In da ya tadda ta tana yiwa Hajiya bayanin za ta gaida Mama. Hajiya ta ce adawo lafiya.
Suna fita kuwa ya ruk'o hannun ta,tayi tayi ya sake ta,ya k'i,har ta hakura. A haka su ka gifta Dawud ko lura da shi ba su yi ba. Ya bi su da kallan takaici.
Sai da suka shiga falon Mama ya sake ta,bayan sun gaisa da Mama tare da mata barka da sallah Haroun ya ce a kawo musu tuwan sallah. Habeebti na girgiza masa kai amma ya d'auke idanun sa. Babbar d'iyar Anty Salmah ce ta shigo da gudu ta na kuka ta na fad'in mota ta buge Junior. Daga Habeebti har Haroun tashi su ka yi da sauri,Habeebti ko takalmi ba ta sa ba suka fice Mama da Aysha na biye da su.
Waje su ka tadda su Hajiya,ga Junior hannun Dawud,gaba d'aya jinin Junior ya b'ata masa gaban farar shaddar sa,dan kan sa ya fashe jini ke zuba sosai. Abun taikaici wanda ya buge shi ya gudu ganin ba kowa a wajan,sun zo za su tsallaka titi zuwa gidan Huda ya buge shi. Da gudu Haroun ya k'arasa wajan Dawud ya na k'ok'arin karbar Junior,amma sai ya hana shi,fad'i ya ke " ka bar shi malam asibiti zan kai shi!" Gaba d'aya ya rud'e,har sai da Hajiya ta ce " Dawud sakar masa d'an sa mana,Haroun maza k'arbe shi mu je asibiti" da kyar ya yarda ya sake shi. Nan su ka shiga mota,Habeebti da ke faman sharbar kuka,sai Haroun da ke ruke da Junior da ke sume,sai Hajiya da Aysha da kuma Dawud da ke jan motar.
💫💫💫💫💫
💫INA DARAJAR TA KE ?💫
KHADIJA SIDI......✍🏽
8⃣9⃣
Habeebti kuwa zaune take gaban madubi,d'aya daga cikin kayan da Mai Junior ya siya mata,leshi sea green nd cream colour ne sanye jikin ta. Ta yi kyau sosai musammam da ta yi kwalliya ta yi kitso ga kunshin sallah. Hannun ta rik'e da dankwali da ta ke k'ok'arin d'aurawa amma masifar mitar da take ya hana ta ta nutsu ta d'aura. " wannan mutumin zai gane kuren sa! Wato har ni zai share ko! Kai tun jiya fa! Ko da yake ma wa ya damu,after ol dama na tsane shi! Arrrggh amma ko barka da sallah dai ya kamata responsible miji yayiwa matar sa...." Duk wannan surutan da take ya shigo ba ta sani ba,sai jin kamshin turaren sa ta yi,kan ta ankara ta ji an dauke ta tsam daga kan stool d'in da take. Har da dan k'arar ta dan kuwa ya mata bazata,farin ciki ya mamaye ranta,ganin ta hannun Mai Junior,ya zauna kan stool din tare da aje ta bisa cinyar sa yana fad'in "I miss you too my stubborn woman"
Sai a sannan ta tuna ashe fa fushi ta ke da shi,ganin sa ya sa ta manta. Nan ta fara k'ok'arin tashi. Ya ruk'e ta gam. Cike da fushi ta ce "wai ma manene ya kawo ka?" Yana wasa da kitson sallar ta ya ce " Na zo na ga kwalliyar sallar mata ta na mata bata barka da sallah kamar responsible miji dat i am,and steal a kiss...) Kan ta ankara yayi kissing din ta. Ganin zai wuce gona da iri ta masa wayo ta tashi da saurin tana fad'in "ka rufa min asiri kar Hajiya ta shigo,gida ne fa ba gidan kaba" dan kishingid'a yayi sannan ya ce " kin tuna min ainihin abun da ya kawo ni,k'arasa shiryawa mu je wajan Mama,na san ba ki mata barka da sallah ba.
Ba mu su ta d'au d'an kwalin ta ta d'aura. Haroun na daga kishingid'e ya ke kallan ta. Mayafi ta d'auka cream ta yafa bayan ta sa Sark'a da dankunne. Ajiyar zuciya ya saki tare da fad'in " Kin gan ki kuwa kamar amarya,dama an kawo min ke haka sanda kina amarya,munci amarcin mu" shiru ta masa kafin daga bisani ta ce" kai ka hanani samin wannan damar a rayuwa ta,ta hanyar min fyad'e har na haifa ma d'a....da ba ka min haka ba da nima naci amarci kamar yanda kowace d'iya mace." "Aliya....." Ya kira sunan ta yayinda ya tashi tsaye. Hannu ta d'aga masa,irin kar ma ka zo kusa da ni,kafin ta yi saurin yin gaba ta fice abun ta" sai da yayi dan jim sannan ya bi bayan ta. In da ya tadda ta tana yiwa Hajiya bayanin za ta gaida Mama. Hajiya ta ce adawo lafiya.
Suna fita kuwa ya ruk'o hannun ta,tayi tayi ya sake ta,ya k'i,har ta hakura. A haka su ka gifta Dawud ko lura da shi ba su yi ba. Ya bi su da kallan takaici.
Sai da suka shiga falon Mama ya sake ta,bayan sun gaisa da Mama tare da mata barka da sallah Haroun ya ce a kawo musu tuwan sallah. Habeebti na girgiza masa kai amma ya d'auke idanun sa. Babbar d'iyar Anty Salmah ce ta shigo da gudu ta na kuka ta na fad'in mota ta buge Junior. Daga Habeebti har Haroun tashi su ka yi da sauri,Habeebti ko takalmi ba ta sa ba suka fice Mama da Aysha na biye da su.
Waje su ka tadda su Hajiya,ga Junior hannun Dawud,gaba d'aya jinin Junior ya b'ata masa gaban farar shaddar sa,dan kan sa ya fashe jini ke zuba sosai. Abun taikaici wanda ya buge shi ya gudu ganin ba kowa a wajan,sun zo za su tsallaka titi zuwa gidan Huda ya buge shi. Da gudu Haroun ya k'arasa wajan Dawud ya na k'ok'arin karbar Junior,amma sai ya hana shi,fad'i ya ke " ka bar shi malam asibiti zan kai shi!" Gaba d'aya ya rud'e,har sai da Hajiya ta ce " Dawud sakar masa d'an sa mana,Haroun maza k'arbe shi mu je asibiti" da kyar ya yarda ya sake shi. Nan su ka shiga mota,Habeebti da ke faman sharbar kuka,sai Haroun da ke ruke da Junior da ke sume,sai Hajiya da Aysha da kuma Dawud da ke jan motar.
💫💫💫💫💫
💫INA DARAJAR TA KE ?💫
KHADIJA SIDI......✍🏽
9⃣0⃣
Suna isa asibiti nan aka shiga bawa Junior taimakon gaggawa. Doctor ne yace "Saboda jinin da ya rasa yana buk'atar jini da gaggawa,wanene su ke of same blood grp da yaran?,ina iyayen shi?" Ganin Haroun be ko motsa daga in da ya ke tsaye ba ya sa Habeebti kulewa, ta ce " Ni ce Maman sa,wlh ban san menene blood grp din sa ba,amma ba mamaki mu zo d'aya,na wa A ne" Doctor ya ce "Owk bara mu gwada na shi,idan kun zo d'aya shikenan" ya koma ciki da sauri. Habeebti saban tsana ta ji ta na yiwa Haroun,ashe Junior zai nemi taimako sanda ya ke siratsi amma yayi mirsisi haka? Su kan su su Hajiya da Aysha abun ya d'aure mu su kai.
Bayan wani d'an lokaci Doctor ya dawo ya ce jinin Habeebti da na Junior be zo daya ba,blood group din Junior AB ne,ina baban sa definitely na shi zai zo d'aya,ya na magana ne ya na mai kallan Dawud,dan duk a lissafin sa Dawud be Uban Junior ganin yanda ya fita hayyacin sa.
Ganin Haroun be tanka ba ya sa Habeebti girgiza hannun sa tana fad'in "Haroun ka na ji fa,nawa ba zai yi ba sai na ka,ka taimakawa d'an ka" kai ya shiga girgiza mata kafin ya ce " Kamar yanda na ki ba zai iya taimakawa Junior ba,haka ni ma nawa Aliya,ni da ke blood grp d'in mu d'aya,ni ma A ne"
Shock ta saki hannun sa baki bud'e,ta ma kasa magana kawai ta sami waje ta zauna dan za ta iya fad'uwa. Hajiya ce ta iya furta " Toh ni Mairo wannan abu da me yayi kama?" Ganin haka Doctor ya ce "Bari kawai aje blood bank a siyi jinin a can in kuma akwai O+ wato universal donor jikin ku pls a taimakawa yaro..." "Ba da gaggawa ya ke buk'atar jinin ba Doctor?" Dawud ne ya katse Doctor da tambaya. In da Doctor ya amsa ma sa " Da gaggawa ma kuwa dan komai zai iya faruwa..." Dawud ya ce "toh d'auki jinana Doctor,shi zai masa....." Doctor ya ce "Yauwa kai O+ ne ko?" Dawud ya girgiza masa kai" Ni ma AB ne kamar yaran" Tas Hajiya ta d'auke shi da mari tare da fad'in " Shashashan banza! Na uwar yaro be yi ba,na uban sa be yi ba sai na ka kai da ka ke yayan uban sa?" Maimakon ya bawa Hajiya amsa,sai jan hannun Doctor yayi ya ce " Mu je a ceto ran yaran nan dan Allah" Doctor yayi gaba Dawud biye da shi. Hajiya kuwa firgita ta yi dan ta kasa gane komai! Bare Habeebti da ta yi mutuwar zaune,rayuwa ta tsaya mata,tunani kala kala ta ke cikin ranta,idan jinin ta be zo d'aya da na Junior ba ita da take uwar sa,na Haroun be zo d'aya da na Junior ba me zai sa na Dawud ya zo d'aya?kai wannan maganar almarace! Ko dai Dawud karya ya ke? Kai Dawud ba zai yi k'arya ba,sai dai Haroun ke karya dan kar ya bawa Junior jini so yake ya mutu ya huta tunda ba dan halas ba ne,shi ya sa sati d'aya kacal ya iya yi gida d'aya da Junior ya dawo da shi kamo...." Da wannan tunanin ta sauke idanun ta kan Haroun. Shi kuwa Haroun abun da ya ke fad'a cikin zuciyar shi shine.." I knw it wasn't me,amma ban tab'a tunanin kai ne ba,of all people Dawud!!!!!"
💫💫💫💫💫
💫INA DARAJAR TA KE ?💫
KHADIJA SIDI......✍🏽
RECAP
Bayan wani d'an lokaci Doctor ya dawo ya ce jinin Habeebti da na Junior be zo daya ba,blood group din Junior B ne,ina baban sa definitely na shi zai zo d'aya,ya na magana ne ya na mai kallan Dawud,dan duk a lissafin sa Dawud be Uban Junior ganin yanda ya fita hayyacin sa.
Ganin Haroun be tanka ba ya sa Habeebti girgiza hannun sa tana fad'in "Haroun ka na ji fa,nawa ba zai yi ba sai na ka,ka taimakawa d'an ka" kai ya shiga girgiza mata kafin ya ce " Kamar yanda na ki ba zai iya taimakawa Junior ba,haka ni ma nawa Aliya,ni da ke blood grp d'in mu d'aya,ni ma A ne"
Shock ta saki hannun sa baki bud'e,ta ma kasa magana kawai ta sami waje ta zauna dan za ta iya fad'uwa. Hajiya ce ta iya furta " Toh ni Mairo wannan abu da me yayi kama?" Ganin haka Doctor ya ce "Bari kawai aje blood bank a siyi jinin a can in kuma akwai O+ wato universal donor jikin ku pls a taimakawa yaro..." "Ba da gaggawa ya ke buk'atar jinin ba Doctor?" Dawud ne ya katse Doctor da tambaya. In da Doctor ya amsa ma sa " Da gaggawa ma kuwa dan komai zai iya faruwa..." Dawud ya ce "toh d'auki jinana Doctor,shi zai masa....." Doctor ya ce "Yauwa kai O+ ne ko?" Dawud ya girgiza masa kai" Ni ma B ne kamar yaran" Tas Hajiya ta d'auke shi da mari tare da fad'in " Shashashan banza! Na uwar yaro be yi ba,na uban sa be yi ba sai na ka kai da ka ke yayan uban sa?" Maimakon ya bawa Hajiya amsa,sai jan hannun Doctor yayi ya ce " Mu je a ceto ran yaran nan dan Allah" Doctor yayi gaba Dawud biye da shi. Hajiya kuwa firgita ta yi dan ta kasa gane komai! Bare Habeebti da ta yi mutuwar zaune,rayuwa ta tsaya mata,tunani kala kala ta ke cikin ranta,idan jinin ta be zo d'aya da na Junior ba ita da take uwar sa,na Haroun be zo d'aya da na Junior ba me zai sa na Dawud ya zo d'aya?kai wannan maganar almarace! Ko dai Dawud karya ya ke? Kai Dawud ba zai yi k'arya ba,sai dai Haroun ke karya dan kar ya bawa Junior jini so yake ya mutu ya huta tunda ba dan halas ba ne,shi ya sa sati d'aya kacal ya iya yi gida d'aya da Junior ya dawo da shi kamo...." Da wannan tunanin ta sauke idanun ta kan Haroun. Shi kuwa Haroun abun da ya ke fad'a cikin zuciyar shi shine.." I knw it wasn't me,amma ban tab'a tunanin kai ne ba,of all people Dawud!!!!!"
💫💫💫💫💫
💫INA DARAJAR TA KE ?💫
KHADIJA SIDI......✍🏽
9⃣1⃣
"Ba gaskiya ba ne Haroun!" Maganar Habeebti ce ta daki kunnan sa,yayi saurin kallan ta tare da fad'in "Ba gaskiya ba ne?" Kai ta gyad'a mai,cikin jaddadawa ta ce "Yes daidai ka ji,ba gaskiya ba ne,k'arya ne ace ba blood group d'in d'aya da Haroun Junior ba,ka na uban sa,wanda ya yi wa uwar sa fyad'e! Bayan nawa da na shi be zo d'aya ba" Idanun Haroun tuni su ka kad'a sun fara canza kala,ya kalli Habeebti ya ce "K'arya na ke Aliya?ki na tunanin k'arya na ke akan blood group d'ina?saboda me ya sa?" "Saboda burin ka ya cika Junior ya mutu ka huta,idan ba ka san ace kana da d'an shege ba you shouldn't have raped an innocent girl! Za ka wani bar Ya Dawud da bawa d'an ka jini,ka ji kunya wlh,na yi dana sanin zaman da na yi da kai iya kwanakin nan Haroun"
Murmushin takaici yayi kafin ya ce "Ashe dama ba ki yarda da ni ba?ki na tunanin zan so Junior ya rasa ran sa,God all dis while ashe babu yarda tsakanin mu?....." Cike da tsana ta ce "Na kusa yarda da macuci kamar ka,sai yau Allah ya k'ara nuna min kalar ka!" Hular kan sa ya cire ya shafa kan,can ya mayar,ya sami waje ya zauna,sai kuma ya tashi gaba d'aya ya rasa me ke masa dad'i. Ita dai Hajiya ta na gefe,gaba d'aya lamarin ya sha kan ta,jiran fitowar Dawud kawai ta ke. Ita kuwa Aysha lamarin ne sam ba ya mata dad'i,ji ta ke dama ba ta zo ba.
Dawowar Dawud ya sa Hajiya tashi da sauri,haka ma Habeebti,Hajiya na tambayar yaya jinin sa ya zo d'aya da na Junior?kan ya tanka Habeebti ta ce "Saboda blood group d'in sa d'aya da na k'anin sa,wanda ba ya so ya taimakawa d'an sa ba na halas ba,Hajiya Haroun ba gaskiya ya fad'a ba,shi ma B ne,kamar Junior..". " "ALIYA!" A fusace Haroun ya daka mata tsawar da sai da wajan ya amsa. Ita ma a fusace ta ce " Prove it! A yanzu a gwada jinin ka!" Matsowa yayi dab da ita,ya ce "Idan aka gwada,duk abun da ya biyo baya,ki kuka da kan ki Aliya...." Ya fizgo hannun ta,Hajiya na magana ya mata banza,Dawud ya yi kok'arin shiga tsakanin sa da Habeebti,ta hanyar sa hannu zai ruk'o hannun ta,Haroun ya bige hannun tare da hankad'a shi gefe sai ga Dawud na shirin fad'uwa,abun da Aysha ba ta tab'a gani ba bare Mama,wai Haroun ya d'aga hannun sa kan Dawud. Fuu ya ja ta. Dawud ya tashi zai bi su Hajiya ta hana shi. Ba su zame ko ina ba sai lab d'in asibiti.
Suna shiga Haroun ya saki hannun Habeebti,sai haki ta ke ta na maida numfashi tsabagen yanda Haroun ya ja ta. Ita kan ta ta tsorata da fushin Haroun dan ba ta tab'a ganin shi haka ba,shi da ba ya fushi ko da an b'ata masa rai. Lab attendants d'in mamaki su ka sha,ganin yanda Habeebti ke haki,ya zo ya tsaya gaban su,ya na huci ya ce "ku ba ni sabon sirinji!" Ai kuwa ba musu su ka d'auko su ka mik'a ma sa dan kuwa a sojan sa ya zo musu duk da babu kaki jikin sa.
💫💫💫💫💫
💫INA DARAJAR TA KE ?💫
KHADIJA SIDI......✍🏽
9⃣2⃣
Ga mamakin kowa,hatta Habeebti sai da ta kau da kai ganin ya caka sirinjin a hannun sa,ya zuk'o jini har ya na d'an d'iga,inda ya fitar da sirijin jini ya d'an biyo kad'an saboda yanda ya sa ba bisa k'aida ba,ya direwa lab attendant gaban ta,da muryar umarni ya ce" Tell her my blood group!" Babban wajen ne ya ce "Malam ba haka mu ke aiki ba" wani kallo da Haroun ya bashi ya sa shi shanye maganar sa,ya fita ya na surutan Allah ya raba su da rude patients. Ai kuwa ba mu su yarinya ta sa hand gloves ta dau sirinjin ta shiga aikin ta. Haroun sai kai kawo yake in da Habeebti ta sami waje ta zauna. Maganin k'arya dai hallara,ya gama cika da batsewar shi ba firgita ta ya ke ba.
Bayan wani lokaci yarinya ta dawo d'auke da yar takarda,ta mik'awa Haroun,amma sai ya k'i karb'a,ya ce "Bawa waccar matar!" Jin haka yasa Habeebti kallan Haroun da sauri,idanun ta sun ciko da kwalla,hannu na rawa ta karb'a ta bud'e,"A" Haroun be yi k'arya ba blood group d'in sa A ne,A+.tuni hawaye d'aya na bin d'aya su ka shiga gangarowa daga idanun ta. D'aga idon da za ta yi babu Haroun babu alamar sa,ya aje ma su lab kud'i ya tafi abun sa.
A reception ya tadda su Hajiya su na shirun zuwa wajan Junior da aka ce za su iya gani. Ganin sa su ka tsaya suna tunanin in da ya baro Habeebti. Dawud ne me tambayar "Ina ka baro ta?" Maimakon ya bashi amsa hannu ya dunk'ule,ji ka ke "TAU" ya kai masa naushi a baki,Hajiya ta yi kan sa ta na mai salati,sai ga Dawud durkushe a k'asa baki na jini,Haroun ya fusge mukullin motar hannun sa. A fusace ya ce da Aysha wuce mu tafi gida!
Ya juya,jikin Aysha na rawa ta bi bayan sa,dama fushin Haroun tashin hankali ne,kowa ya sheda wannan. Hajiya na salati ta ke k'ok'arin duba bakin Dawud,Allah ya taimaka ba kowa gun da tabbas Haroun ya tara mu su jama'a,dan har an fara taruwa Hajiya ta ja Dawud da ya fara zama kamar Haroun sanda aka ma Habeebti fyad'e,zuwa d'akin da Junior ya ke kwance. Da shigar su sai ga Habeebti ta biyo bayan su.surutai ta ke kamar mahaukaciya sabon kamu. Ko ta kan Junior da ke kan gado ya na k'arbar jinin Dawud ba ta yi ba. Gaban Hajiya da Dawud ta zube gwiwowin ta biyu a k'asa ta ke duban Dawud ta na fad'in " Yi min bayani Ya Dawud,ta yaya jinin Haroun ya banbanta da na Haroun Junior na ka ya zo d'aya...." Baki na rawa ya kasa magana da k'yar ya iya furta "ki yafe min Aliya..." "Innalillahi wainnailaihi rajiun..." Fad'in Hajiya kenan ta na mai tafa hannun. Yayinda Habeebti ta tashi da sauri ta fice ba tare da ta san in da ta nufa ba.
💫💫💫💫💫
💫INA DARAJAR TA KE ?💫
KHADIJA SIDI......✍🏽
9⃣3⃣
Shi kuwa Haroun kai tsaye gida ya je ya aje Aysha wacce ke ta hamdala,Allah ya karb'i adduar ta sun dawo gida lafiya. Har za ta fita ya ce "Dawo nan!" Ta dawo da sauri ta zauna jiki na rawa. Ya ce " Abun da ki ka ji kuma ki ka gani wlh ko da wasa na ji kin furtawa Mama ke ba Mama kad'ai ba ko da wasa na ji maganar sai na lahira ya fi ki jin dad'i" da rawar jiki ta ce "Toh". Sannan ta fice. Shi kan sa ya san zance ya ke,Aysha ba za ta iya barin maganar cikin ran ta ba. Shi dai fatan sa Allah ya ara masa lokaci kar Mama ta ji kafin ya sami mafita. Da wannan tunanin ya d'au hanyar gidan Anty Salma.
Ganin yanda ya zo mata afujajan ta san ba lafiya. Bayan sun zauna ya ke fad'a mata abun da ya sami Junior. Ta yi jimami sosai,ta ce "Ga sallah ga tashin hankali,Allah sarki Habeebti" Haroun ya ce "jinin Aliya da na Junior be zo d'aya ba" Sai da Anty Salma ta d'an yi jim kad'an kafin ta ce " Har jini aka k'ara masa,ai wannan ba mamaki,ka san dama ko dai na ta da shi ya zo d'aya ko na ka da shi ya zo d'aya,na ka ne ya zo d'aya kenan,shi ma A ne? Ya girgiza mata kai " Aliya ce A,Junior B ne,kamar Dawud"
Jin haka ta maimaita sunan Dawud ya fi a d'irga,ta ce " Kai Dawud fa?,me ka ke nufi,ban yarda ba,ranar ba shi ya kawo su mama biki ba! Har fa gaisawa mu ka yi,Dawud fa Haroun?duk kamalar sa da ilimin sa?me zai ka masa sharri?abun da magana ta riga ta wuce duk da dai idan maye ya ci ya manta uwar d'a ba za ta manta ba,amma ai na ga kuna zaman ku lafiya ko?"
Ganin yanda Anty Salma ta rud'e Haroun ya ce " Na san ba ni ba ne,tun randa abun ya faru,idan za ki tuna ban bud'e baki na furta na aikata ko ban aikata abun da ake zargina akai ba,ki yi hakuri Anty Salma amma sam ban ga alama ko na k'ank'ani na ce wata mu'amala ta had'ani da mace ba,ko da d'igon spam ne....."
Shiru Anty Salma ta yi kafin ta ce "Me ya sa ka yi shiru idan kasan da haka Haroun?God kasan halin da ka sa mu ciki kuwa Haroun?menene ribar ka in dai haka ne? Haroun ya nisa cike da bakin ciki ya ce " ke kin sani da zan shekara d'ari ina cewa ba ni ba ne ba yarda za ku yi ba,ko kun yarda Hajiya da Alhaji ba za su yarda ba,saboda duk masifar da ta fad'a kan Habeebti ni na jawo,ni na bata kwaya kamar yanda Dawud ya ce,dan ni ba zan iya tunawa ba,kin ga kenan ni na sa ta fita hayyacin ta,har ko ma waye ya zo ya ci galaba akan ta. Wannan abun ba karamin damuna yayi ba. Bayan haka ki tuna shedar da Ayub ya bayar na yanda ya same ni kwance da Habeebti. Ko ni ma da ya tada ni na yi zaton na aikata wani abu kan ta,sai bayan da na nutsu na duba kai na na rasa wata alama na da za ta nuna mu'amalata da mace na tabbatar da duk wanda yayi wannan aikin ya na sane yayi priming d'ina,kuma na shiga ban d'auka ba ba ta fidda barawo. Sai kuma na yi zatan d'aya daga cikin abokai na ne,musammam wanda ya dawo da ni gida shi ya aikatawa Habeebti haka,sai da na yi baram baram da shi,na yi iyakan k'ok'ari na amma na kasa gano gaskiyar abun,hakan ya sa na yanke dukkan huld'a da su ya sama ban da aboki ko guda d'aya...."
"Idan ka amshi laifin da ba ka aika ta ba saboda k'aramin laifin da ka aikata wanda ba cikin hayyacin ka kake ba,wato bawa Aliya kwaya,me zai sa ka yarda a aura ma ka ita?" Dan murmushin taikaici yayi,sannan ya ce " Wannan wani abu ne daban,ina san Aliya Anty Salma,ina san ta tun randa na fara sa ido kan ta,wallahil-azim ina san Aliya fiye da yanda na ke son kai na" Hawaye ne su ka shiga zuba daga idanun sa "Toh amma ban san da maganar ciki da haihuwa ko auren ta ba sai bayan da aka riga aka d'aura mana aure,lokacin ina NDA,bazan b'oye mi ki ba na ji kishi da takaicin haihuwar Junior,na ji bakin cikin zuwan Junior duniya,kuma na ji tausayin Aliya yanda ba kya zato,shi ya sa na yanke hukuncin zama da ita,na kuma zama uban d'an ta duk da kuwa na san halin da na ke sa kai na,for her i risked it all,na san ba ta da mak'iyi cikin zuciyar ta kamar ni,a hankali zan sa to soni. Amma ganin Junior ya sauya min tunanina,kammanin Junior ya tabbatar min da wanda yayi raping Aliya dan gida ne,abun ya dame ni ya dami rayuwata. Har da haka ya sa na dawo da shi Kano,ganin sa tayar min da hankali ya ke,ya na sani jin bak'in kishi duk sanda na tuna d'an Aliya be amma ba d'ana ba. washagarin ranar da na fara kusantar Aliya a matsayin mijin ta ranar mu ka tafi Abuja. Tunanin abun ya sa ko tuk'i kasawa na yi sai marigayi Emeka ne ya ja mu,damuwa ta shi ne shin waye uban Junior?a wannan halin har mu ka yi hatsarri.,amma sam ban tab'a kawo Dawud cikin rai na ba....." Hawaye ya ke sosai d'aya na bin d'aya,ya dubi Anty Salmah da ita ma d'in kuka ta ke,murya na Sark'ewa ya ce " Ki duba lamarin nan Anty Salmah,Yaya na ne Dawud,Aliya mata ta ce....Yaya na ne uban d'an mata ta,ba auren ne ya had'a su ta haife shi ba,fyad'e ya mata....Yaya na shi ya tab'a yiwa matar da na ke aure fyad'e har ta haihu,ina daraja anan?INA DARAJAR TA KE? Zafin da na ke ji a ayau yafi wanda na ji ranar da aka yiwa Aliya fyad'e aka d'aura min"
Kuka Anty Salma ta ke,tausayin Haroun ne ya rufe ta,ta na share hawaye ta ce "Gaskiya Haroun ka yi jarumin k'ok'ari,Aliya ba ta da masoyi da ya wuce kai,in dai haka ne Dawud ya isa munafiki azzalumi,ya isa mahainci,shi ya fi kowa kumfar baki akan an cuci 'yar uwar sa,ya na kallan yanda ka wulak'anta,Alhaji har sallama ka yayi,ba dan Commissioner ba da rayuwar ka ta lalace har abada,duka laifin sa ne dan zalunci da mugunta irin na Dawud,munafiki mai ci da addini. Amma abun mamaki shin ya aka yi har hakan ya faru bayan ranar ya na tare da su Hajiya da Mama?
💫💫💫💫💫
💫INA DARAJAR TA KE ?💫
KHADIJA SIDI......✍🏽
9⃣4⃣
Wannan tambayar na Anty Salmah shi ne tambayar da Hajiya ta ke yiwa Dawud,wanda tun fitar Habeebti in ban da neman gafarar Hajiya babu abun da ya ke. Cike da b'acin rai Hajiya ke duban Dawud da ke d'urk'ushe gaban ta,ya kasa d'aga ido bare ya iya kallan,ta na kuka ta ce "K'arya ne ba ka da sa hannu cikin abun da ya faru da Aliya,duk cikin yaran Alhaji babu nutsattse,mai kamala,ladabi da biyayya da kuma rik'on addini kamar kai Dawud,ka fad'a min gaskiya tun kan na rasa rai na......"Ganin Hajiya na shirin durkusawa yayin da ta ke fad'in " Ka taimaka ka wayar min da kai kafin na rasa rai na" Yayi saurin rik'o ta kan ta k'arasa k'asa,ya zaunar da ita kan kujera,ya zauna gaban ta kai sunkuye ya na hawaye ya furta "Ki yafe min Hajiya,a yau na kasance Dawud daban da wanda ki ka sani a matsayin d'anki.." Tas ta kwashe shi da mari kafin ta ce "Ka na nufin ka na da sa hannu?yar uwar ka?jinin ka?shin ya aka yi har hakan ya faru bayan ranar ka kai mu biki? Karya ka ke dan uban ka!"
Murya na rawa ya shiga ba ta labari kamar haka. " Bayan na sauke su Huda,na fito nemawa Habeebti magani,dab da zan shiga Lamco na amsa kiran ta,na sheda mata gashi na fita samo maganin in da ita kuma ta ke fad'a min an kawo mata wanda na sa akai mata. Ganin na sami maganin a Lamco kuma ba nisa da gida ya sa ni yanke hukuncin fara kai mata kafin na dawo gare ku...." Shirun da yayi Hajiya da gaban ta ke dukan uku uku ta ce ina jin ka. Da kyar ya cigaba da fad'in" Komawa ta gida na tadda su a falo, daga Haroun har Habeebti ba wanda ke cikin hayyacin sa,har gwara Habeebti ita tana iya furta sunan Haroun,in da take neman taimako gun sa,shi kuma Haroun kwakkwaran motsi be iyayi,sunan ta kawai ya ke iya ambata. Ganin halin da Aliya ta ke ciki ya sa na yi k'ok'arin cire mata hijabin jikin ta ko zata samu ta d'an sha iska dan zufa ta ke sosai.....ko sanda na ke cire mata hijabin Haroun ta ke ambata ba ni ba,hakan ya tabbatar min ba ta san da zaman kowa a falon ba in ba Haroun ba,shi kuma tuni ya gama fita daga hayyacin sa,be ma san da shigowa ta ba. A sannan ne shed'an ya min hud'uba mai muni,har na kai ga aikata abun da na aikata....."
"Innalillahi wainnailaihirajiun! Abun da Hajiya ta ke maimaitawa kenan. Dawud na kuka ya k'ara da "Sai bayan da bakin alkalami ya bushe sannan na farga da abun da na yi,bayan na tabbatar da na yi abun da ba wanda zai tab'a kawo tunanin kowa cikin ran sa in ba Haroun ba a matsayin wanda ya aikata laifin,na baro gida. A hanya ne ki ka kira ni na ce mi ki ina tafe....Hajiya ki yafe min sharrin shaidan ne" Hannu biyu Hajiya ta sa ta rufe shi da duka ta na fad'in "sharrin ka ne Dawud,babu shaid'anin da ya wuce kai kan ka Dawud,anya kuwa kai mutum ne? Ka cuce ni,ka zalunce ni ka cuci Aliya ka zalunci Aliya ka d'au hakkin Haroun! Da yanda ka yi ba gwara ka d'au wuk'a ka dab'a min ba Dawud,yanzu fi sabilillahi da wani ido zan kalli Hajja Fadi da Alhaji?da wani ido zan kalli Haroun?da wani ido zan kalli Yakumbo?da wani ido zan kalli dangin mahaifiyar Aliya?da wani baki zan furta mu su d'ana Dawud,d'an da sunkuya na haifa shi yayiwa Aliya fyad'e ya d'aurawa d'an uwan sa laifi?da wani ido zan kalli duniya?Dawud ka zubar da min da mutunci,kima da daraja ta a duniya,Dawud ina darajar ta ka ta ke?ina tawa?ina ta yar uwar ka da ta haifa ma d'an cikin shege,ina darajar d'an yaron can da ke kwance,wanda be ji ya gani ba,bare mahaifiyar sa wacce ba ta ma laifin komai ba,Dawud INA DARAJAR TA KE?
Bud'ar bakin Dawud sai cewa yayi " Hajiya shi ya sa na ke so a raba auren na su,ni na aure ta in ya so na gyara kuskuren da na yi a baya......" Jin maganar Dawud Hajiya ta ruk'e k'irjin ta,ta yanke jiki za ta fad'i,Dawud ya yi saurin rik'o ta,jikin shi ta fad'i sumammiya.
💫💫💫💫💫
No comments:
Post a Comment