ANA KUKAN TARGADE...
Part 1⃣
Avva omar yaro
(Prince av)
09032724001
Sadaukarwa!
Wannan littafi sadaukarwa ce kacokam ga duk wata kungiya ko group na MARUBUTA dake social network musamman :-
RUBUTU DA MARUBUTA
GIDAN MARUBUTA
AMINCHI WRITERS DBT
KAINUWA WRITERS ASS
allah yabar zumuci ameen
* * *
B.U.K 2016
Dalleliyar motar kirar land rover baka wuluk tai parking a wajen da aka tanada dan ajiye motoci, daga cikin motar sautin muryar fitaccen mawakin nan korede bello ke tashi cikin wakarsa romantic, ta dau lokaci kafin ta bude kofar motar a hankali ta ziro da kafarta dake rufe cikin takalmi mai uban tsini kalarsa launin baki, wandon jikinta skin tied ne bakin ne shima daga cikin motar ta bude clutch bag dinta tare da zaro waya 'yar karama kirar (baby nokia) contact ta shiga laluba har tazo kan number datake nema ta danna dialling, ringin daya biyu aka daga tare da cewa
"Chuchun gayu kin iso ne"
Da dariya ta amsa "wlh vocal, kina ina ne"
"Nima shigowata kenan nayyo wajen cafteria saboda ciroma da cikina yaketa kira yasin" takarasa dauke da dariya itama chuchun da dariya ta tare "yanzu dai kina cafteria kawai"
"A,a ix not kawai, nadai kusa karasawa ina daf da bishiyar resberry dinnan"
"To amini dan allah bani 2 minute na karaso yanzu"
"Nabaki ma morethen 2 but gsky karki dade" da wani murmushi chuchu tace "yawwa luvly vocal" ta sauke wayar batare data jira jin mai vocal din zata ce ba.
Da azama ta dauki babbar wayarta ipad dake ajiye a mazaunin mai zaman banza tare da karasa ficewa daga cikin motar tai mata key kafin ta juyo taci gaba da tafiya, sanye take da riga top girl iya cinya kalar pink mai gajeran hannu, rigar matsetstsiya ce daga sama yayinda daga wajen kugun ta bude kamar raper, kanta ba dan kwali saidai tayi rolling da karamin mayafi, idonta saye cikin wani makeken space daya mamaye kusan rabin fuskarta, hakan bai hana siririn dogon hancinta bayyana ba wanda yasha ado da stud ta gwal, kana ganinta kaga kanuri amma tsanani hutun datake ciki yasa bakar fatar ta rikide daga baka ta kanurin asali zuwa farar mai dan duhu, daga gaban goshinta gashi ne ya kwanta yala yala irin na kanurin asali, duk wanda zai ganta a wannan lokacin bazaice kanuri bace, tafi kama da fitacciyar mawakiyar nan ta ethopia SONA.
Duk inda ta gifta maza da mata ke daga mata hannu da cewa "chuchu" ko "A.A" itama da murmushi take maida musu martani da daga hannu dan wasu dayawa batasan sunansu ba, inkuma suna kusa saita karasa su gaisa ta wuce gaba.
Wannan al'ada ta chuchu itace ta siyo mata soyayya a zuciyoyin mutane da dama maza da mata, sam batada girman kai ko dagawa kamar sauran 'ya 'yan masu kudi, ga kyauta kullum hannunta a sake yake dayin abin alkhairi.
Ita datace vocal tabata minti 2 bata karasa wajen ba sai bayan minti 11 da sassarfa ta karasa ta rungumota ta baya "yi hakuri sa'adena wallahi bada son raina na jima haka ba" vocal da da niyyarta tafara zazzagawa chuchu kwandon bala'i amma jin tace "sa'ade" sai hakan yabata dariya tama manta da fadan datai niyyar yi mata saita 6ige da cewa "allah chuchu kin 6ata min rai, kin shanyani a kasan bishiya kinje kinata fama yakarewa mutane hakora dan nasan wallahi abinda ya tsaida ke kenan" chuchu ta kyalkyale da dariya tare da sakinta daga rikon datai mata "na gode allah ma daba gatson hakora gareni ba, da sharrin naki saiya fi haka" itama vocal da murmushi a fuskarta tace "yooo a juri zuwa rafi... Kullum kina yankarewa ai wata ran sai sun zama gatso yasin" gaba dayansu sukai dariyar wannan karan kafin vocal ta kama hannunta "ni dan allah mu wuce cafteria nan karki karasa kasheni da yunwa" ba musu chuchun tabita da cewa "eh ai nike kwashe miki abincin cikin naki, shi yasa kika ce zan kasheki da yunwa".
CHUCHU
Ayeesher abubakar auyo shine cikakken sunanta, chuchu ya samo asali ne tun daga yarintarta irin sunayen ajebo dinnan da ake sawa (kmr tamu chuchun rubutu & marubuta) itace 'ya daya tak wajen alhaji abubakar auyo (A.A) fitaccen dan kasuwa ne a kano da nigeria gaba daya, harma sauran kasashen dake ketare A.A nada kamfanoni da hannayen jari a nan, cikakken kanurin mai duguri ne mai mata daya wadda ta kasance 'yar abokinsa babansa ce deejah, ayeesh (chuchu) ita ce tsoka daya a miyar da A.A baya hada soyayyarta data kowa a zuciyarsa, yana son chuchu fiye da tunani banda mahaifiyarta deejah ta tsaya tsayin daka wajen gyaran tarbiyyar 'yarta ta daba karamin lalacewa zatai ba, tayi primary da secondry dinta gaba daya a Nigerian turkish dake tarauni, bayan tayi candy ne ta nemi dadyn ta daya kaita Qatar danta karasa karatunta a can, amma sai mahaifiyarta ta nuna rashin amincewar akan hakan, dama shima A.A din ko kadan baya so 'yar tashi tayi nesa dashi, hakan yasa ya fakaice da hanin da deejah tai wajen lalla6a chuchu akan tai karatun ta kawai a nigeria, bada wani ja ba tai amanna da hakan, aka fara nema mata bayero university dake kano, ba'a wani ja lokaci ba admission dinta ya fito inda ta za6i mass communication, sa'adatu kabir anka (vocal) ita kadaice shakikiyar kawarta kuma aminiyarta a skull, dukda tarin masoya datake dasu maxa da mata, hakan baisa ta zama mai kawaye rututu ba, saidai mutunci kawai dake hada su, yanzu haka tana first semester ne a level 100, duk da wannan gata da masoya da chuchu keda su, hakan bai hana zuciyarta fadawa soyayya ba, soyayya ma kuwa mai wahalarwa, tunda wanda take so din baisan tanayi ba, ko ince ba santa yake ba, dalibi ne shima a nan cikin b.u.k din, saidai shi yana cikin shekararsa ta karshe ne, MUKTHAR KWALISA kamar yadda ake kiransa saboda tsananin kwalliya da ado irin nasa, saurayi ne dan kimanin shekara 29, irin giant dinnan ne masu saurin tafiyar da zuciyar mace, fari ne kal mai dogon hanci da oily eyes, ya tsaida dan karamin gashi a habarsa irin wanda kewa samarin yanzu wahalar samu (quarter million), sumar kansa a kwance take baka sidik irinta fulanin adamawa, saidai shi baida siranta irinta fulanin hutu da jin dadi yasa ya rikede zuwa saffa saffa, gymin da yawan excise ya maidashi murdadde tamkar matashin ba'indiyan nan SUNIL SHEKTY , digon bakin tabon sallar dake goshinsa ya kara samar masa da wani kwarjini da kamala, miskili ne na ajin karshe, shiga harkar maxa 'yan uwansa ma bata dameshi ba, bare mata, ba chuchu ce ta fara cewa tana sonsa ba a matan duniya, amma zai iya cewa yafi tsanarta a ransa fiyeda sauran matan, dan yanaiwa chuchu kallo da fuskoki masu yawa.
Yana mata kallon 'yar iska da batada kaya sai matsatstsu
Yana mata kallon ballagaza dabata kunyar shaking din hannu da namiji ko a gaban waye
Yana mata kallon mai son karya da fafa ganin yadda takewa mutane wadaka da kudi tamkar ba daga jikinta suke fita ba
Yana mata kallon...... Kallo kallo dayawa kwalisa kewa chuchu, hakan yasa ko sunanta ya tsani ji bare ya ganta.
Abinda kwalisa bai sani ba sa kananun kaya shine attitude na chuchu, it her favourite bazata iya dainawa ba, shaking with males ix not bad in her character, tana kallon maza da mata da ido daya, wato duk friends ne.
Bari mubi chuchu da kwalisanta muga.
* * *
Suna hira suka karasa cafteria, hannunsu sakale dana juna a haka suka shiga cikin wajen.
Kamar ance dago haka kwalisa ya dago kanshi yana shirin kai lomar chips bakinsa daya cako da fork, karaf suka hada ido da chuchu dake janjo kujera zata zauna, wani irin kallo yake aika mata na tsana da kyankyami zallah tamkar yaga wani mugun abu, lura da hakan datai yasa duk taji ta muzanta walwalar data shigo tana yi ta koma ciki, meye laifinta dan ta so kwalisa abinda ba ita ta dorawa kanta ba, ita kanta inda son yai shawara da ita bazata ta6a bari ya shigeta ba, duk dumbin masoyan dake gareta takasa damkawa kowa zuciyarta sai wanda keta moli da ita, ya maida zuciyar kamar wata kasa takata yake ya wuce batare da tunanin cewa abu mai rai yake takawa ba.
Ta share kwalla da gefen gyalenta batare data so vocal ta gani ba, amma ta makara abinda bata so dinne ya faru, wato vocal taga hawayenta, da sauri takai kallonta zuwa inda chuchun ta kurama.
Ganin kwalisa da Abokinsa MD ASNANIC yasa ta girgiza kai kawai tareda tafa hannunta a wajen idon chuchu.
Da firgici ta kalleta tareda tsiyayowar ragowar kwallar "chuchu lafiyarki kuwa? Subhanallahi kukan me kike" cewar vocal data mike a rikice tana tambayar chuchu.
Yake tayi kawai tare da zama "kwaro ne ya fadamin ido" iya abinda tace kenan ta zauna, batare da vocal ta yadda ba ta nemi guri ta zauna itama da son sanya kawartata barkwanci tace "da alama jakar hajiyata yau ba kudi naga batace kar a kar6i kudin abincin kowa ba" cikin dariya kuwa tace "ayya sa'adena gara dakika tuna min na sha'afa ne allah" ta yafito wata ma'aikaciyar gurin da hannu "ki kawo mana irin abinda wancan ke ci (ta nuna kwalisa da hannunta) sannan kiyo total din kudin abinci kowa na nan kar a kar6a" da sauri tace "ok ma" tareda juyawa kawo abinda aka umarceta dan halin chuchu ba bako bane a wajenta inda sabo ta saba indai ta zo cin abinci sai hakan ta faru.
Bata jima da kawo musu ba kwalisa da md suka mike, kwalisan ke mikawa cashier kudinsu amma saiya ki kar6a da cewa "yar gidan A.A ta biyawa dukkanku" a fusace kwalisa ya watsa masa kudin a teburin gabansa "gashi nan inka so ka watsa a kwandon shara, ba 'yar iskar daxata ci dani wallahi danba gagarata yai ba" hankalin kowa yai kansu dan kwalisa da karfi yake maganar dan chuchu ta jiyo, aiko ta jiyo din zubo musu fararen idonta tai tana kallo.
Shima cashier din a fusace ya watsama kwalisan kudin da cewa "wallahi vazai kar6a" md ne ya shiga tsakiyar ganin ana naiman bawa hammata iska "kayi hakuri kawai mukhtar tunda tariga ta biya, muje kawai kowa yaji abin nan kaizai bawa rashin gaskiya" a fusacen shima yace "wallahi danaci abincin nan gara nai amansa na gwammace na zauna da yunwa" kafin su farga ya fizge hannunsa dake rike a wajen md ya nufi sink gadan gadan, hannunsa ya ringa turawa a can cikin bakinsa, aiko nan da nan ya fara kyalayar da duk abinda ya ci harma abinda yake ba hakkin chuchu ba, shi kansa cashier ya tausaya masa ganin yadda yake aman bilhakki, bayan ya gama ya kunna famfo gamida kurkure baki ya kalli md da fuskar shanu "kazo mu tafi malam" iya abinda yace kenan ya juya fara tafiya, ba musu md din ya rufa masa baya.
Chuchu da a gabanta aka gama komai ta mike idonta taf kwalla ta tare kofar dasu kwalisa zasu wuce "wallahi saika gayamin abinda nai maka kake min wannan zazzafar kiyayya dako a mafarki bana jin za'a samu wanda akewa kamarta saboda....." Bata karasa ba kuka yaci karfinta.
Wani mitsiyacin kallo yabita dashi kafin ya dire da tsaki "kinsan allah inbaki matsa kin ba kin bani hanya saina karairayaki na wuce" ya karasa yana hucin dake nuna da gaske zai iya aikata abinda ya fada
A zafafe itama tace " kwalisa yau ko kasheni zakai bazan kauce ba bare karairayawa, ka karyani! Ka karyani nace!!!" Idonsa ya kada yai jajir ko kadan kalamanta basu sanyayyar masa da gwaiwa ba, saima kaimi da kuzari daya ji an kara masa bisa mugun nufin daya kulla mata, gadan gadan yai kanta yana huci.....
Tofa 😳 wannan shine ana kukan targade kuma saiga karaya.
Mu tara a kashi na biyu
Prince av
09032724001
No comments:
Post a Comment