'YAR AJINMU CE
Part 9,10
9==
Jamilu wannan ranar ne bakar rana
gareni a dukkan tarihin rayuwata,
Ranar ne da daddare aka zo gabana
aka yima mahaifina yankan rago Suka
halbe mahaifiyata Nan take wani
daga cikinsu ya haqe ma kanwata
Nabila Yayi mata raping Ni kaðai ce
na tsira, tun daga wannan lokaci sai
muka rasa yadda zamuyi bamu san
kowa ba balantana muje mu zauna
wajansa, mu uku ne daga nabila sai
Fatima shikenan sai zamansu ya
dawo gareni nice uwarsu nice
ubansu. Akwai lokuta da dama da
suke sakani a gaba suna kuka nice
mai rarrashinsu, mai basu hakuri
akan su dangana suyi shiru, Fatima ce
nafi tausayawa koba komai itace
karama cikinmu yarinya. Shikenan
Karatuna da nasu ya watse Nida nake
aji Uku level 300 shikenan karatuna
ya lalace babu mai daukar nauyin
karatunmu Nasan zakace ina
gadonmu? Bayan jana'izar
mahaifinmu ba wanda muka sani a
garin, muna cikin gidan akace mu
tashi inji mai gidan, Wannan ne ya
ðaga hankalina matuka na rasa yadda
zanyi da rayuwata. Haka muka tashi
daga gidan dani da kannena Nabila
da fatima Nan muka samu gidan wata
tsohuwa muka zauna itace ke kula
damu tana bamu abinci, Tana dauke
mana kananun matsalolinmu , itama
abinda yasa ta taimaka mana saboda
mahaifiyata suna mutunci da,ita.
Zamanmu gidan wannan tsohuwa
ba'a daðe ba itama rai yayi halinsa
sanadiyyar accident, nan ma aka
tadamu daga gidan wannan
tsohuwa, shikenan gatanmu ya kare
gaba daya. Haka muka dinga yawo
babu abinci, duk wanda zai taimaka
mana sai yace, sai yayi amfani damu
naki yarda na kare mutuncin
kannena basuda wani gata da ya
wuce ni, dan haka na miqe tsaye
wajan ganin na kare mutuncinsu.
Haka muka samu gidan wata
tsohuwar muka zauna nan ne abinci
ya fara yi mana wahala hatta kayan
sawa suka gagaremu, sai kaya kala
daya su yi satia jikinmu bamu canza
ba, gaba daya kayanmu sun tsufa har
sun fara yayyagewa, wannan rasa
dole na miqe ina bara domin na
samu abinda su fatima da Nabila zasu
sa a bakinsu. Wani lokacin da kyar
nake samun abincin da zamuci duk
wanda ya ganni maganar banza yake
man, ina kyalesu na dangana
al'amurana duka ga Allah buwayi
gagara misali nasan shine zai man
maganin komai.
10==
Bintu ta gama bani labarinta mai
cike da tausayi da alhini ba karamin
girgiza nayi ba sanadiyyar mutuwar
mahaifinta alkali gaskiya ne da
hausawa ke cewa yanzu rayuwa
marar gaskiya yafi mai gaskiya a cikin
al'umma, duk ma wadanda sukayi
wannan aika-aikar can su da
ubangijinsu. Bintu! Na kira sunanta
idanuwanta sharkaf da hawaye nace
insha Allah kukanki ya kare Bintu
rayuwar da kikayi a baya insha Allahu
ta zama tarihi yanzu zamuje gidanmu
sannan mu dawo mu dauki Fatima da
Nabila su ma su koma can. Wani
hawaye naga yana bin fuskarta gaba
daya ta canza kalar tausayi, dauða
tasa fuskarta har wani sheki takeyi,
Nagode jamilu dama nasan Allah zai
kawo man karshen wannan
jarabawar, Na tada mashin ðin nace
mata hau mu tafi. Ta hau tana waigen
wadancan sauran mabaratan dake
zazzaune bata masu sukeyi ba, Komai
yai farko zai yi karshe. Zuwansu
gidan Su jamilu Alhaji ibrahim
Garbati yayi alhinin abinda ya faru da
mahaifinta matuka yayi Allah wa dai
da mutane masu irin wannan
rayuwar, Motarsa ya dauka da kansa
ya dauki bintu da Jamilu dan zuwa
daukarsu Fatima da Nabila acan inda
suke zaune. Ba karamin daði bintu
taji ba sai take jin gaba daya
maraicinta ya kare, rabonta da dariya
harta manta sai gashi yau tana
washewa har tana kin boye farin
cikinta, Wani yanayi takeji a cikin
zuciyarta mai sanyi, kamar bata ta6a
jin dadi kamar haka ba tunda take,
Har jamilu dake zaune gefenta ya
lura da haka yayinda ya dinga jin
daðin shima cikin ransa yana
hamdala da Allah ya sake hadasu da
bintu. Zuwansu gidan ne abinda ya
kara baiwa jamilu mamaki gidane ko
rufin kirki babu, babu banma san
yadda sukeyi da damina ba ko idan
ana iska mai karfi, Nan take bintu ta
ruga ta rungumi yan'uwanta tana ce
masu, Bakin cikinmu ya kare, mun
bar rayuwar tashin hankali da
barazana zamuyi rayuwarmu kamar
kowa they life happily zamuji dadi
naga yan'uwana ku taso mu tafi.
Dariya suka dinga yi suna godewa
sarki Allah SAURA DAYA
Monday, 19 December 2016
Yar Ajinmu 4th
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment