💫INA DARAJAR TA KE ?💫
KHADIJA SIDI.....✍🏽
4⃣8⃣
Wayar Anty Maijidda Aysha Tafeeda ta nema,ta yi sa’a ta same ta. Jin abun da ke faruwa Anty Maijidda ta shiga kiran Habeebti,amma ta k’i d’agawa. Da sassafe su ka d'auki hanyar Kano,da azahar sai gasu a Bichi,amma su ka tadda gidan Yakumbo a kulle da kwad’o. Wayar Yakumbo ta nema,it ace ta ke sheda mu su suna asibitin tun asuba,Allah ya sauki Habeebti lafiya,kukan jinjirin da ke tashi shi ya tabbatar mu su da ba shakka ta haifo lafiyyan d’a,kwaran gaske.
Jiki sanyaye su ka garzaya asibitin da ke nan cikin Bichi ya ke. D’akin da Yakumbo ta fad’a mu su suka nema. Da shigar su suka tadda Yakumbo d'auke da baby,sai cilara kuka yake ta na ta faman jijjiga shi,sai Hajiya da ta ke ta yiwa Habeebti nasihan da d'au yaron ta bashi nono,amma kamar ana magana da dutse,sai ma juya ma su baya da ta yi kwance bisa gado. Ganin su Yakumbo har da hamdala,ta ce ‘’yauwa gwara da Allah ya kawo ku,ashe kuna tafe dama,kila ganin ku ya sa ta tausayawa yaran nan ta bashi nono,tun asuba ake abu d’aya sai dai a jik’a dabino da zamzam abawa yaro.’’ Tana magana ne yayin da ta ke k’ok’arin mik’awa Anty Maijidda babyn. Ba Anty Maijidda ba,hatta Aysha da ke lek'en yaran da ga nesa sai da ta matso kusa ta na fad’in ‘’Tabarakallau mashaAllah’’ tsabar baiwa na kyau da Allah ya yiwa babyn . Anty Maijidda ce ta k’ara da ‘’ wai wai wai sai ka ce d’an larabawa tibarkallah mashaAllah’’ ‘’Ai uban sa ne sak,idan ki kalli yaran nan ki ka kalli uban shi kadai ya isa mutum tsoran Allah’’ Yakumbo ta fad’a ta na mai tab'e baki. Anty Maijidda na jinjina kai ta d’an matsa kusa da Hajiya su ka gaisa a gaggauce kafin ta dan taba Habeebti,ta na mai magana cikin lallami,ta ce ‘’Aliya taimaka dan Allah ki ceto ran dan jinjirin nan ki bashi nono ya sha,kar kid'au alhakin sa akan laifin da bashi ya aika ta ba….’’ shiru ake ji,ko motsawa ba ta yi ba bare ta nuna ta san da ita ake. Hajiya ce ta fusata ta ce ku barta ta ruk'e nonan na ta,idan ya yi tsami ya fara ma ta ciwo ta san yanda za ta yi da shi. Bari na fita na nema ma sa madara" Ta tashi ta fita fuuu kamar wacce za ta tashi sama. Aysha ce da d'auki yaron ta sa shi a kafad’a yayin da ta fara kai kawo ta na girgiza shi. Yakumbo da Anty Maijidda su ka ci gaba da bawa Habeebti baki amma ta mu su kunne uwar shigo. Har ita ma Yakumbo ta fusata ta k'yale ta.
💫💫💫💫💫
💫INA DARAJAR TA KE ?💫
KHADIJA SIDI.....✍🏽
4⃣9⃣
Har aka sallame su su ka koma gida Habeebti ba ta ko kalli yaran ba bare ta kai ga d'aukan sa ta shayar da shi. Da su ka koma gida ne Alhaji Umar da aka fad'a ma sa an yi haihuwar ya zo tare da matar sa,jin abun da yake faruwa na kin shayar da yaran da Habeebti ta yi ta wajan matar sa ya sa shi shiga har d'akin da Habeebti ta ke ciki ya rufe ta fad’a,ta in da yak e shiga ba ta nan yake fita ba,fad’i ya ke’’ Dan rashin imani kusan awanni bakwai da haihuwa amma kin ki shayar da yaro,da haka sai ki wulgar da shi ki tabbata irin matan nan da basu yadda da kaddara ba su ke kasha ‘yayan su da kan su….minti biyar kar ki k’ara ki tabbatar kin bawa yaro hakkin sa,shi ina ruwan sa?…menene laifin sa?…..’’ da wannan ya juya ya fice a fusace. Yakumbo ce ta d'au yaran ta d'aura mata kan cinya,Habeebti ta yi saurin kau da kan ta gefe,ganin haka ya sa Yakumbo ta ce ‘’ko sai na fitar da Maman da kai na na sa ma sa a baki?’’ jin haka Habeebti ta ce wallahi kar ki tab'a ni Yakumbo,kada wanda ya taba ni". Jan gefe Yakumbo ta yi,dan ta san tabbas Habeebti ba cikin hayyacin ta ta ke ba. Ganin Yakumbo ta ja baya,hannun Habeebti na rawa ta sa cikin riga ta na kokarin fitar da nono ta bawa babyn da bai fasa cillara kuka ba. Sai da ta d'au lokaci sannan ta daure ta iya kallan dan yayin da ta ke kok'arin sa ma sa baki..caraf kuwa ya karb'e ya fara sha yayinda Habeebti ta runtse idanun ta,ta na mai tawassali ga Allah,lalle shi ne zai yaye ma ta wannan bakin cikin da ya addabi rayuwar ta. Su hajiya kuwa ajiyar zuciya su ka saki,atlast Allah ya yi uwa ta shayar da dan ta. Ba ta wani jima ta na bashi nonon ba amma har ya fara bacci ta ciro shi,yaro sai tand'e baki yake da alama be koshi ba. Ta aje shi can gefe ta koma ta kwanta ta na mai gyara rigar ta. Aysha ce ta d'auke shi ta na ‘’Allah sarki wallahi daga gani be k’oshi ba’’ wani harara Habeebti ta watsa mata,tuni ta ja bakin ta ta tsuke. Su Yakumbo kuwa cewa su ka yi ba dai ta bashi ba,hakan ma sai a godewa Allah. Sai da bacci ya kwashe Habeebti Anty Maijidda ke fad'a mu su abun da ya sa suka d'auko hanya. Yakumbo ta tausayawa Habeebti,kana ta ce "shi ya sa ma na ko runtsawa ba ta yi ba,haka na tadda ta shakaf shakaf da gumi da hawaye,tun fa uku na dare da na fito zagawa bayi,duk a zatona ciwan nak'uda ne,ashe da biyu. Na ko fad'awa Karami sai a mayar ma sa da kud'in sa. Allah ya sa haka ya fi alkhairi" su ka amsa "Amin"
A daren ranar Dawud ya zo shi da su Akib da Aunty Salma,wacce ta Umarci Dawud da ya taimaka ya yiwa yaran hud’uba da duk sunan da ya so. Yakumbo ta ce da wani duk sunan da ya so bayan ga sunan uban sa…ai sai ka masa da sunan uban sa kawai ya amsa’’
💫💫💫💫💫
💫INA DARAJAR TA KE ?💫
KHADIJA SIDI......✍🏽
5⃣0⃣
Bayan kwana bakwai Yaro ya ci sunan uban sa Haroun. Babu zancen taron Suna,amma hakan be hana dangi taruwa ba,hatta b'angaran dangin mahaifiyar Habeebti sai da su ka zo,bare kuma su Hajiya da Ummi.
Alhaji Hamisu ne da commissioner Adamu shehu tare da Dawud wanda shi ya ja motar da kuma Akib su ka bak'unci Bichi,inda dama Alhaji Umar ya san da zuwan na su,jin sun karaso ya ce za su iya shigowa zaure,in da su ka tadda shi zaune tare da Baffan Habeebti Alhaji Murtala da kuma mijin Anty Talatu,sai kuma wani Malami da Alhaji Umar ya gayyato a nan Bichi.
Duka bisa tabarma su ka zauna,an fara gaisawa Alhaji Hamisu ya ce da su Dawud da ke shirin shiga cikin gida "ai ba ciki za ku shiga ba,ku ma ya kamata ku zama shedu,maza ku kwaso goro da alawar cikin mota"
"Toh" su ka amsa ma sa,yayinda Dawud ke mamakin rad'in sunan ma sai sun sheda?abun da ya kamata ace tun asuba a yi ma sallacin layi a gama. Da wannan tunanin cikin ran sa su ka kwaso goro da alawa,su kawo cikin soron. Diyar Anty Talatu Asmau,wacce su ke kira Asmee ce mai kimanin shekara bakwai ta zo wucewa,yaro da kwad'ayi,ganin kwalin alewa ga kuma baban ta a wajan ita ma sai ta ja tsaya abun ta.
Su Dawud ba su ankara da abun da ke shirin faruwa ba sai da su ka Alhaji Hamisu ya fidda bandir din kudi,sababbbi k'al yan dari biyar,sannan kwakwalwarsu ta fara aiki.Malam ne ya fara sallama gami da cewa "Toh a gurguje dai bara mu yi abunda ya tara mu anan,dama shi daurin aure ba ya yiyuwa sai abubuwa uku sun cika,waliyai,sadaki da kuma shedu,ina ga kuma duk akwai nan ko?" Aka amsa masa da "kwarai da gaske"
Malam ya ce "Ina waliyin yaro?" "Gani nan" Commissioner Adamu Shehu ne ya amsa ya na mai matsowa gaba. Malam ya ce "ina na yarinya fa?" Baffan Habeebti ya matso gaba ya na mai bayyana kan sa. Malam ya ce "toh bisimillah"
💫💫💫💫💫
💫INA DARAJAR TA KE ?💫
KHADIJA SIDI.....✍🏽
5⃣1⃣
Commissioner Adamu shehu ne wanda ya ke waliyin ango ya dauki kud'in da Alhaji Hamisu ya aje,kana ya ce " Ni Adamu Shehu,ina nemawa dan mu Haroun Shamsu auren d'yar ku Aliya Nasiru bisa ga sunan annabin mu Muhammad salllahu alaihi wasallam,tafarkin addinin musulunci ga sadaki naira dubu hamsin" ya mi ka wa Waliyin Aliya kud'i.
Wanda shi kuma ya amsa tare da fad'in "Ni Murtala Hamza na baiwa Haroun Shamsu auren d'yar mu Aliya Nasiru bisa ga sunan annabin mu Muhammad salllahu alaihi wasallam,tafarkin addinin musulunci ga sadaki naira dubu hamsin,jama'a ku sheda"
Mallam ya dubi waliyin amarya ya ce "kun bayar?" Waliyi ya amsa da " mun bayar" ya dubi na ango ya ce "kun karb'a?" Waliyi ya ce "mun karb'a" Malam ya k'ara da "suturan ta da ci da sha,da kuma bada hakkin ta da k'are hakkin ta sun rataya a wuyan sa,jama'a ku sheda" nan fa aka yi salatin manzo tare da addu'a aka shafa. Aliya ta zama matar Haroun. Wanda idan aka d'auke wanda su ka d'aura da wanda su ka sheda ba wanda ya san da wainar da aka toya.
Cikin gida kuwa kowa na harkar gaban sa. Su Anty Talatu ne su ka sa faifai Al-amin na d'ibar albarka,Habeebti da ke zaune gaban mudubi fitowar ta daga wanna kenan,ta na jin su amma ba ta tanka ba. Can parlour kukan Haroun junior ne ke tashi,wanda ya ke hannun cousins din Habeebti,dan har yau ba nonon arziki ya ke samu daga wajan Habeebti ba,ga shi da tsotso,sai madara ake had'a ma sa da shi.
Asmee ce ta shigo da gudun ta,hannun ta cike da alawa,ta fad'a kan cinyar Maman ta Anty Talatu,sai mai da numfashi ta ke. Anty Talatu na duban ta ta ce "ummm d'iyar arziki ina aka samo swt haka? Allah sa ba kud'in Yakumbo ba ne ya yi ciwo ba?" Asmee na juye juye ta ce Abba na ne ya ban ni ma ya ce na sheda auran Anty Habeebti......"Tsit ka ke ji,daga na d'aki har na parlour da iska ya kai mu su maganar Asmee da dama irin yaran nan ne ma su surutun tsiya,ga murya,ba wanda ya iya tankawa. Kukan Haroun junior kad'ai ke tashi,yayinda kowa idanun sa na kan Habeebti da ta tsaya cak ta na duban Asmee.
Asmee da ba ta damu da canjin yanayin da aka samu a d'akin ba ta k'ara da "har da goro fa,wai angon Anty Habeebti ne ya siyo...Yauwa sunan sa ma d'aya da babyn Anty Habeebti,ya ma sunan Mama?yauwa HAROUN" ta fad'a ta na mai jaddada sunan kamar ta yi abun arziki......
A hankali Habeebti ta tashi,fuskar ta kunshe da murmushin da ya yi kama da na mugunta,ta ja hijabin ta ta zura,hanyar fita ta nufa ta na mai kwallawa Yakumbo kira.
💫💫💫💫💫
No comments:
Post a Comment