KARNINMU...
©FIKRA WRITERS ASSOCIATION
BABI NA TARA
Safiyar Litini da wuri su Messi su ka shirya zuwa makaranta kamar da gaske. Kowa mamakin zuwansu makaranta ya ke ba kamar abokansu, Nuhu ya fi kowa murnar ganinsu amma gefe ɗaya kuma tsoro ne ya kama shi kar dai ko wata aika-aikar suka zo aikatawa. Sun isa kafin a fara taron latti don haka ba'a tsaida su a bakin kofar makaranta ba kamar yanda aka saba.
Suna zaune a aji kamar da gaske, duk da ba littafai gare su ba illa guda biyu da memon aure da kowannen su ya mallaka sun yi kokarin rubuta duk darasin da aka musu. Mamaki ya cika yan ajin lokacin da Rabs ya tashi ya tambayi mai mu su geography
"yaa Maalam! Ka ce shi weathering ɗin nan shi ne ke sa dutse ya zama kasa ko? Toh kana nufin cewa Allah bai halicci kasa ba se dai a samu daga dutse ne? "
" A'a Rabiu, Allah ya halicci kasa, sannan ya halicci duwatsu, shi ke saukar da ruwan sama, da karfin ikonsa rana ke fitowa, da qudirarsa mutane ke tafiya hakama dabbobi, don Allah ka fahimce ni, shi weathering Ma'anar sa farfashewar duwatsu, in dutse ya fashe zai bada wasu manya, har ya kai ga marmara, har kananan duwatsu (gravels) har zuwa kasa. Shi kimiyya ko da yaushe fahimtar su suke faɗi ba wai suna jayayya da qudiran Allah bane. Kuma ai gashi na gwada maka hakan ko? " ya faɗi yana murmushi duk don su samu kwarin guiwan zama su yi karatu amma sai suka shayar da shi mamaki sanda Baaba ya ja tsaki ya ce,
" ni Wallahi shi ya sa na ce muku bokon nan duk karya ce da kafurci, ya za'a yi a zauna ana faɗin saɓanin Allah da annabi" ya karasa yana mai mikewa.
"Ba kaji ana joga-joga mugun ciwo ba, Rabs Allah fisshe ka kamuwa da wannan cutar don ba magani gare shi ba" Messi ya faɗi yana bin sawun Baaba ya zuwa kofar ajin.
"A tashi lafiya Yaa Maalaam!" cewar Rabs yana mai bin sawun yan uwansa.
A iya sanin tsagerancinsu ba'a taɓa sanin sun kai ga haka ba, ace duk tsaurin malamin Geography sai da ya kasa ɗaukar mataki don mutuwar tsaye yayi har suka bar ajin, sannan ya dawo ga sauran ɗaliban. "kar ku bari guguwar KARNINMU ya ɗebe ku, Kunga lokaci, kada ku yarda ku yi wasa da ita. Duk lokacin da ya wuce ba ya taɓa dawowa, asarar da kayi kuma ba za ka san kayi asarar ba sai a gaba. Karatu ya kawo ku nan in kun yi hakuri zai wuce, kuma zaku fi kowa morar karatun.
Nima Shekaru goma sha da su ka wuce ina Kamar ku, da na yi hakuri na maida hankali yanzu akwai wanda ke karɓan albashi na? Ni ke cin kuɗi na sai na ga dama zan ba wasu kyauta.
Sannan duk mai son ilimin sa yayi albarka Toh lallai i-lallai sai ya girmama ya kuma daraja Malaman sa. Allah ya baku sa'a ya shi muku albarka " yana gamawa ya fita daga ajin ya bar sauran ɗalibai da maida zancen abinda ya faru.
***
Cike da ɓacin rai Ahmad ya ce
"Da wata a gun bayan ke?na ce wa ya saki aikin nan?waya baki kayan?"
"Eh Hajiya ce...Hajiya ce ta sa ni", faɗin Habi ta na mai zaro idanu. Jinjina kai Ahmad ya yi , kafin ya ce
"Je ki kira min Hajiyar!"
Habi da ta samu daman barin Ahmad tuni ta wuce ɓangaran Hajja Bilkis da sauri, dan gani ta ke Ahmad zai iya mangare ta yanda ta ga ran sa ya ɓaci, haka ta shige ciki ta na mai tunanin ko wanene Ahmad agidan. Gashi dai fuskar sa kamar wanda ta sani.
Ahmad na nan tsaye, jim kaɗan Hajja Bilkis ta fito ta na mai taku ɗai ɗai cikin shigar shadda dokakkiya. Cike da tak'ama ta ce, "Honourable gani,ance ka na kira na?"
Ahmad na duban ta ya ce "Bilkis wannan yarinyar kuma wacece? wacece ki ka ba inner wears ɗina ta wanke?"
"Au! Wai Habi? sabuwar mai aiki na ce ai, Jummai ba lafiya....."
"Mai aiki Bilkis?"
Ahmad ya katse ta ya na mai bayyana ɓacin ransa a fili. Hakan ya sa Bilkis wacce dama a kule ta ke da shi faɗin.
"Da hausa fa na ke magana Honourable ba da wani yaren ba, mai aiki mana....."
"Mai aikin ce ki ka bawa inner wears ɗina ta wanke?dan ba ki san daraja ta ba?"
Cikin tsiwa Hajja Bilkis ta bashi amsa da
"Honourable kenan! ka tara su shirgi guda a ɗaki ba kyan gani, shi ne na ce idan ta gama gyara ɗakin na ka ta fito da su a musu saukar dauɗa"
Idan ran Ahmad yayi dubu ya ɓaci, saboda ɓacin rai har huci ya ke. Ya na mai nuna ta da dan yatsa.
"Ki na nufin hatta ɗakin na wa wannan yarinyar nan ce za ta dinga gyarawa? ba ki da lokacina balle na yaro na Bilkis?"
"Haba dan Allah! Wannan ai shi ne zancen ɓur in ji tusa! Kai ɗin lokacin mu gare ka? Nan ba tun safe ka sa kafa ka fice ba tare da ka ko leko mu ba bare ka san a wani hali mu ke! In dai kayan ka ne da ɗakin ka su sha zaman su,sai a barka ka da dauɗar ka! ni ka ga tafiya ta....."
Ta juya za ta koma ciki, a fusace Ahmad ya shiga kiran sunan ta, amma ina! ko waige ba ta yi ba.
***
Sani ya dage kan ra'ayin saka Lanto makaranta, Nuhu na kara masa kwarin guiwa saboda tun da ya taimaka ya kuɓutar da lanto suka zama abokai, cikin ikon Allah ya sami haɗin kan mahaifinsa cikin kwana biyu ya gama yi ma ta komai ya sa ta a makaranta.
A yau Litini ta shirya cikin kayan makaranta ta wuce makarantar gidan maigari ta boko, in da karatunsu da ga karfe takwas na safe zuwa sha biyu na rana ne kullum, hankalin mama ya tashi don ba karamar asara za ta yi ba tsakanin takwas zuwa sha biyu na ranakun makaranta.
Sai dai su na tasowa ta ɗaukar mata alala da anyi la'asar kuma an wani ce ta sake tattaro kururunta zuwa gida don ta je islamiyya. Mama Hanne takaici ya isheta ta dura ruwan masifa babu wanda ya saurare ta, hakan yasa ta alwashin yin awara da an kira magariba Lanto ta fita suya waje.
Cikin shiganta ta tsaf ta fito riga da skirt na atamfa koriya da ratsin fari, ta yi ɗaurin ture kaga tsiya, saman kanta kuwa farantine cike da gurjiya yayin da fuskarta tasha hoda rabajau. Mayafinta siriri karami dashi makale a kafaɗanta ta yi hanyar soro tana ɗigirgire Baba Dije tabi bayanta tana yi mata kirarin nata,
"jaruma mai kan albarka badai na kwantai ba komai naki daban yake da yan matan Dunotsi, kai ko a cikin Kasar Haurobiya babu kamar ki. An buga an barki diyata mai farin jinin ɗawisu". Tuni kanta ya fasu ta fice tana takama kai tsaye kasuwa ta nufa tana takun kasaita kamar ta wuce gidansu Lanto amma saita kasa ta biya tana shiga ta iske Mama Hanne shirum da dafaffiyar gyaɗa gabanta ta yi turus tana tambayar, "Mama lafiya naga kinyi kashi banga Lanto ba?", Saida ta shaka sannan ta numfasa ta ce,
"hmm! Barni ɗiyar nan wannan ja'irin yaron Sani ya dage ya sa ta makarantar boko uban kuma ya ɗaure musu kugu ga wancan figararran ahalinsu kiɗaɗɗiyar yarinyar nan Lubabatu yana daɗa ingizasu".
Wani kududu ya tasoma Larai ta dubeta gatsetse, "Mama kika yarda?"
"Kaniyarki Larai in ban yarda ba ya zanyi babansu yasa baki?"
Tana shirin magana ne Lanto ta shigo duk ta haɗa zufa alamun anci wuyar tafiya tana hango Larai ta washe baki ta nufeta.
"A 'a Larai yanzu ki ke tafe? Ina makaranta bari in sauya tufafi mu tafi, Mama kin gama?" ta karasa tana mai tambayar mama.
Harara suka watsa mata su duka, bata sauraresu ba ta wuce ɗaki kaya kawai ta sauya ta fito tana tuntuɓe takaici ya kumeta jin yanda take tashi da kaurin rana gashi ba halin yin wanka haka zata fita gudun jafa'in Mamanta.
Sunkutar farantin ta yi, "mu je Larai ba na son makara ina so in uku ta yi zan dawo inyi aikin gida in tafi islamiyya karfe huɗu".
"Ke kinci....." Ta lailayo mata ashar.
"Wa kike tunanin zai ɗaukarmin abincin wallahi maza ki ficemin kibani waje yanzu dai sha biyu ki dawomin nan da karfe ɗaya da rabi ki ɗauki abinci in kin saida kya tafi makarantar kuma akwai suyar awara kofar gida da anyi mangariba!".
Galala ta tsaya tana kallon Mamar tasu, ta buɗe baki zata tofa ta tuna nasihar Malaminsu na ɗazu in da yake tunasar dasu muhimmancin kyautattawa mahaifa musamman uwa saita guntse bakinta ta yi gaba. Zungui-zungui Larai ta bita a baya.
Tafiya suke kowa da abin da yake sakawa cikin ransa, Lanto sauri take burinta takai ta saida saboda ta dawo da wuri bata san rasa karatun islamiyya sossai ta fara jin daɗinsa musamman da Malam ya fara yi musu bayanin sallah ta gano gyarraraki tsaf tare da tata ibadar. Larai ce ta gaji da gum da gum ta dubeta, "baki da wayau Lanto me zaki yi da wata makarantar boko? Arnaku fa ne ke yi".
Ta yi mata duban uku ahu,"inji wa?". Ta tambaya cike da gatse tana dubanta
"in jini". Ta bada amsa kai tsaye tana turo cingum ɗinta da ta yi katon kwai.
"Kinyi kuskure to Larai, ilmi aba ce mai kyau kuma abin takama, ko wane irine karatun ne kuwa, boko kuwa kin jahilceshi ne amma shi ne abin da ya dace a ɓata lokacin nemansa fiye da talen da muke yi ba".
"Hmm! Kedai a bar kaza cikin gashinta, ba Nuhu kike bi ba, zai kai ki ne ya baroki ai nasan ba banza kika fake da karatun ba, Allah kadai yasan abinda kuke aikatawa".
Daidai lokacin suka karaso kasuwar taso tankawa ta waske amma maganar ta cigaba da nukurkusarta.
Zamansu babu wuya cikin ikon Allah Lanto ta soma sayarda gyaɗanta, nan da nan ya zama saura kaɗan ta kare baki ɗaya. Suna nan zaune ta hango shigowar Lado cikin kasuwa abin mamaki yana tafe yana tangaɗawa ya nufosu yana washe baki nan take lanto ta haɗe fuska babu ko fara'a kan fuskarta a haka ya sami waje ya zauna suna taɓa hirarsu shi da Larai, hirar da ta kasance rabi duk batsa ce.
Kamar an jefosu duk su biyun suka faɗo wajan suna zazzare idanu suka zagayeshi Baaba da Messi ne da alamu a buge suke.
"Dilla kai Baaba ka jika masa aiki ya bamu hakkinmu".
Lado ya zaro idanu kamar yaci babu ya dubesu a tsorace ya ce "lafiya?". Ya furta baki na rawa.
"Hakkinmu zaka bamu, aikin da ka samu mu bi wacan kwailar yarinyar". Messi ya karasa furucin yana sauke manyan idanunsa kan Lanto.
Dauke kai ta yi ta tattara kayanta ta matsa can gefe guda.
Basu yi aune ba ya zare wata sharɓeɓiyar wuka ya na nuna Lado da ita ya ce"bani kar in maka aika-aika".
Nan ya kama makyarkyata yana rawar baki ya dubesu" wallahi banda ko taro...".
Kafin ya dire Messi ya burma masa wukar take ya saki kara giggitaciya nan da nan kasuwa ta hargitse kowa na gudun cetan ransa.
***
Muna masu baku hakuri rashin jin mu da kuka yi, hakan ya faru ne saboda wasu hidindimu da suka sha karfin lokutan mu. Amma Insha Allahu mun dawo kenan.
Muna baran addu'ar ku, Allah ya kai rahma zuwa ga Mahaifin yayanmu Hamza Dawaki, Allah ya jikan sa da ɗaukacin musulmai fa suka riga mu gidan gaskiya.
No comments:
Post a Comment