Sunday, 25 December 2016

Sakaci 22

            💔💘 *SAKACI* 💘💔

        

                      2⃣2⃣

© *Fatima A Garba*.

A tsaye ta sameshi ya kasa tsaye ya kasa zaune, sai safar da marwa ya ke  a cikin office d'in, fuskarnan a murtuke, gaggawan sauke idanunta ta yi saboda wani kallo da ya ke jifanta da shi.

A ta ke zuciyarta ta fara bugawa da sauri-sauri, rawa jikinta yake tamkar mazari.

"Mene ne hujjarki ta zuwa ki zauna a tsakiyar wa'encan garadan"

Ba ta iya d'agowa ta kalleshi ba, bare kuma ta bashi ansa, "magana na ke miki" ya daka ma ta tsawar da har sai da taji ta har tsakiyar kanta.

Ba ta iya d'aga kanta ba ma balle ta ba shi ansa, cikin maganarshi ta k'asaita ya ce!

"Kinyi na farko sannan kinyi na k'arshe, ya kamata ace kinsan ke matar aure ce, ni kuma da kika ganni nan ba sakaren namiji ba ne, don haka idan kika sa ke mai-maita makamancin hakan, ke da aiki sai dai kiga anayi, da fatan kin fahimci abinda na ke nufi"

"Kayi hakuri, hakan ba zai sa ke faruwa ba" ta ce da shi, har cikin ranshi ta bashi tausayi, amma tunowa da abinda ya hana zuciyarshi sakat yasa shi shiga wani irin yanayi, lokaci guda kuma zuciyarshi ta yi bak'i.

Idan ba darajar iyaye ba yaushe hakan zai faru, Allah ya gani bai ta6a aikata zina ba, yana mugun kyamarta, sannan bai ta6a gajiyawa ba wurin rok'on Allah akan ya had'ashi da salihar mace.

"Kai Farida kin cuceni na jima ina inganta rayuwarki lokaci guda ki wargaza komai, mai wannan yaron ya rud'eki a wannan lokacin kika bashi kanki"

Ko zan hana kaina abu ke zan baki kawai don bana so wani ya sake rud'anki a karo na biyu, amma kin rusa min komai.

Kujera ya samu ya zauna ya fuzar wata iska mai zafi daga cikin bakinshi.

"Ki zauna na kammala wani aiki kafin mu shiga tiyatan" Ya fad'a ya na janyo jakar laptop d'inshi.

Zama ta yi gami da takurewa wuri d'aya domi ita sam yanzu ba ta sa kewa muddin yana wuri.

Ya kai kusan awa guda (1hr) kafin ya umarceta da su tashi su je dan gudanar da aikin da ke gabansu.

   
                     ****

Basu suka bar asibitin ba sai karfe sha biyu (12) na dare, Mariya ta cika ta yi fal, saboda a ranar ta kar6i girki, sannan ta ga fitar Farida da ga gida, don haka ta kasa tsaye ta kasa zaune, zuciyarta fal kishi.

"Don Allah AC bedroom d'ina da na falo ba sa yi ga zafi, ko zaka taimaka ka dubamin" Farida ta fad'a cikin sanyi muryarta.

"Tun yaushe ne ya daina yi" ya tambaye ta.

"Dama tunda nazo gidan bai ta6a yi ba" ta ansa mai, tsaki ya ja gami da cewa, 

"Amma kullun ina tambayarki inda wata matsalar sai kice babu"

Ita dai ba ta ce komai ba, bud'e murfin k'ofar yayi yana shirin fita, ita d'inma fitar ta yi, ta na aiyana irin zafin da zata sha yau, domin zafin yau yafi na kullun.

Ga mamakinta taji ya na binta a baya, ko ba komai taji dad'i.

Ta na tsaye ta na kallon ikon Allah, ranta bai gama 6aci ba sai da taga ya na bin Farida shashinta, tabbas tasan tunda Farida ta shigo gidan k'arshenta yazo, ba ta shigo bama sai da ta kusa korarta, eh toh korarta mana.

Sam basu lura da ta wurin ba, koda suka shiga kai tsaye d'akin baccinta ta bud'e mai ya shiga, wata y'ar stool ta mik'o mai akan ya hau kai.

"Wannan sai marasa tsayi irin ku" ji ta yi tamkar a mafarki, idan kuwa ba mafarki ba ne, toh babu tantama kunnenta baiji ma ta dai-dai ba.

"Wai tunanin me kike ina miki magana hankalinki baya nan" ya fad'a da muryar da baza ta iya tantance wa da fad'a yayi maganar ko akasinta ba.

"Banji mai ka ce bane" kafin ya kai ga magana sukaji ta banko k'ofar, lokaci guda suka kalleta.

"Toh maciya amana ranar kwanan nawa ma sai anci amanata ko tsoron Allah bakyaji, toh wallahi na gaji da ganin bakin ciki, a cuceni a hanani kuka ba zai yuwu ba"

"Ba ta re da ya tanka ma ta ba ya ratsa ta gefenta yayi ficewarshi, tabbas ta kula, kuma ta san hakan gargad'ine ya ma ta.

Juyowa wurin Farida ta yi hannunta a k'ugun  kafin kuma ta ce " wallahi dani kikeyi na miki alkhawarin sai kin fita kinbar gidan nan, zanje na sa meshi sai dai ya za6a tsakanin ni da ke, munafuka"

Daga haka ta fice, Farida ko kallo Mariya bata isheta ba, ita tasan ko giyar wake Mariya tasha baza ta tunkari Dr da wannan maganar ba, idan kuwa ta yi gangancin fad'a zai bata mamaki, domin shi ba'a mai gatse.

               ****    ****

Washegari da safe ya shigo lokacin ta yi wanka har ta gama gyaran gidan, ta shiga kitchen ta na had'a tea.

A tsaye ta sameshi sanye cikin light brown d'in riga mai gajeren hannu, wandon kuma dark brown, kalar kayan sun kar6eshi matuk'a, kasancewar kalar fatarshi ne.

Sumar kanshi a gyare, ya kwanta luf gwanin sha'awa, kai gayen ya had'u ta ko'ina.

Idan ka kalleshi za ka d'auka matashi ne d'an shekara talatin, ba zaka ta6a cewa ya kai shekara arba'in da biyar ba.

Dr akwai iya d'aukan wanka, kuma duk kayan da ya saka zaka ga ya k'ar6e shi.

Sannan shi mutun ne mai tsafta shi yasa kafin ka ganshi k'amshin shi ne zai fara yimaka sallama.

Tsugunawa ta yi gami da gaisheshi, ansawa yayi fuskar nan kamar ko yaushe.

"AC jiya yayi" ya tambaya a tak'aice "eh yayi" ta bashi ansa, kafin ya sa ke cewa,

"Ni zan fita ki shirya anjima zanzo na d'auke ki"  "toh, Allah ya tsare" ta fad'a, "ba wani abunda kike buk'ata"

Ya sake tambayarta, da sanyin murya ta ce " eh babu" ta ansa.

Juyawa yayi yana wannan tafiyar nan tashi.

Zama ta yi ta rasa me ya ke ma ta dad'i a rayuwa, sam ba ta kaunar wannan hali na ko inkula da yayanta yake nuna ma ta, k'arshe tea d'in da bata sha ba kenan.

~Ummu Hanan~

No comments:

Post a Comment