Friday, 23 December 2016

MATAR SADDIK 7

"Miyasa kike fargaba to?".
"Hmm!".
"Hmm? Ban gamsu da hakan ba MATAR SADDIK".
"Saddik!".
"Na'am".
"I love you".
"Na gode, amma na fahimci damuwa tatrare da kuzarinki da idanunki da kuma fuskarki. Kisawa zuciyarki hakuri dan Allah ki kauda kai abisa duk abinda Mommy....".
Cikin hanzari tasa hannu ta rufemasa baki tana girgiza masa kai tare da jefa masa kallon gargaɗi. Tare suka fito Hajja da Jiddah da Baba mai aikinta duk sun shirya suka dunguma sai Dala gidansu Saddik.
***
Cikin ikon Allah suka isa gidan lafiya, tun daga harabar gidan suka fahimci cikar da gidan ya yi ga maroka sai wasa jarirai suke. Suna yin parking ya buɗe suka fito Jiddah ta ɗauki jakar Safiyyah ta kama hannun Hajja suka shiga ciki. Tana ganin mahaifiyarta ta saki Hajja ta nufeta tana tsalan murna da ganinta. Cikin wasa ta ce,
"tafi can kin sakarmin Kaka kin tawo kina washemin baki".
Gaba ɗaya aka ɗauki shewa, daidai lokacin Safiyyah ta shigo idon Mommy a kanta das! Gabansu ya faɗi su dukan ba kamar Mommy data lura da turowar cikinta daya kara mata kyau. Hakama Mommyn Lubnah suka kali juna sukai kwafa, Hajiya Mardiyya kuwa murmushi tayi har ga Allah tausayin yariyar ke zirgamata zuciya. Bata taɓa ganin mace irin Mommy ba mai son ƙkanta. Kwata-kwata ta rufe ido muradin zuciyarta kawai take nema. Cikin nutsuwa ta kamo Hajja ta karasa da ita tana faɗi,
"Jiddona saiki bar mana Kakus kinga Mommy ko?".
Dariya tayi tana sune kai, sossai Aunty taji daɗin ganin Jiddah da alama tana samun kulawa saɓanin abinda Mommy take faɗa.
"Mommy ina yini, barka an sami karuwa".
A ɗararre ta amsa fuska babu annuri hakan bai dameta ba tagaishe da su Aunty Zahra ta wuce sashin masu jego. Matasan mata duk sun hallara kowa da abinda yake , tana shiga ido yayo kanta yuuu ta sada kai ta wuce tsakiyar Teemah da Sanah ta zauna tana murmushi suka sha kunu tasa hannu ta ɗago haɓarsu,
"in kukai fushi bakwa kyau amaran karni".
Tureta sukai,
"sai yanzu kika ga damar zuwa?".
"Kuimin uzuri aminaina".
"Mun miki to MATAR SADDIK".
Hannu tasa ta ɗauki yaron Sanah,
"ya sunansa?".
Teemah ta yi karaf,
"Sunansa Abubakar Saddik".
Ta zare ido,
"are you sure?".
Ta faɗa tana tsare Sanah da ido kai kawai ta ɗaga mata a hankali ta saukeshi tana karemasa kallo ta rungumeshi wata kaunar yaron na ratsata. Duk suka sata gaba suna tafa hannu suna dariya. Shigowar Ummu Abdoul yasa ta saukeshi tana lumshe ido suka shiga tsokanarta tilas tayi gum. Diyar Teemah kuwa Maryam aka sanya mata. Kafin kace kwabo gidan suna ya ɗauki harami kowa sai shige da fice yake. Duk yadda Mommy taso tada fitina Safiyyah kaucewa hakan take, komai tasata sai tace to Mommy ba tare da nuna ko alamun fushi ba. Karfe huɗu suka saka ankon da sukai suka fito ras taurari huɗu har Jiddah cikon ta biyar ko ina suka bi ƙkallonsu ake sunyi kyau sossai aka shiga ɗaukar hotuna. Aunty Zahra taita yi musu tsiya wai sun musu yan ubanci.
Duk kai komon da Safiyyah ke yi idon Mommy  a kanta, babban abinda ya tsare mata gaba dan kareriyar sarkar dake wuyan Safiyya kirar Dubai wadda a iya kintattarta a kala ba a kasara ba ta yi kimanin dubu ɗari biyu da hamsin. Bata ko tantama kuɗin ɗantane yayi kuka wajan mallakarta. Taja numfashi Hajiya Mardiya na kula da yanayinta daidai lokacin Safiyyah ta ratso fallon gaba ɗaya annurinta ya haske wajen tayiwa mazauna wajan wani irin kwarjini ta gifta su Mommy da kaɗan muryarta ta sauka kan dodon kunnanta.
"'Yar matsiyata zo nan".
Sarai tasan da ita take, amma hakan baisa ta juyo ba zuciyarta na tuna mata girma da matsayin mahaifa. Take wani karsashi ya harbi zuciyarta ta cigaba da tafiya bata ko juyo ba. A kufule Mommy ta mike zata fincikota, Hajiya Mardiyya ta mike ta tareta,
"ba girmanki bane Hajiya Kundum inda girma da arziki MATAR SADDIK ya ce a wajanki".
Cikin takaici take kallonta kallon uku kwabo ta ja wani mugun tsaki kamar zata tsinke harshanta.
"Mtsss! Hajiya Mardiyya in rasa wazan haifa sai wannan munasirar?".
"Koma me ne ne kisawa ranki hakuri hidima ake kina gani gashi ta kwafsamiki ta wuce. Waya gari ya waya?".
Kaɗa kai kawai Mommy ta yi tana bakin cikin tareta da Hajiya Mardiya ta yi, aranta tana ayyana yadda zata tozarta Safiyya cikin taron. Bata kara mintina goma ba tabar wajan take Hajiya Kilima ta bita ɗaki sukai kus-kus. Can Mommy ta fito ta kira mai aikin Safiyyah Baba dan ta lura akwaita da shishigi ɗaki tajata suna shiga ta dubeta.
"Baba aiki zamu saki fatan zaki mana?".
"Sossaima kuwa Hajiya",
Ta faɗa tana washe baki suka haɗa ido sukai murmushi.
"Ungo wannan kisan yadda ki kai kika saka a jakar uwar ɗakinki".
"ƁBan gane ba wai nufinku Aunty?".
"Ke! MATAR SADDIK nake nufi".
"Au to to na gane, amma bazan iya ba gaskiya".
"Hajiya Kundum yi mata da yaran da zata gane, wato yaran talaka".
Aikuwa take ta ɗoramata dubu ɗari,
"ga dubu ɗari in kin gama akwai wata ɗarin".
Da hanzari ta wawura ta yi gaba, cikin sanɗa da kiyayya ta tsaya ta cusa kuɗinta a lallitarta ta sikafa ta rike abinda aka bata katam ta nufi ɗakin su Teemah. Tana shiga kuwa bata sami kowa ba ta aikata abinda aka sata ta fito wajan fitane sukai kiciɓus da Jiddah ta yi dururu alamar rashin gaskiya ta wuce Jiddah ta rakata da ido tana taɓe baki. Da murnarta ta dawo tana sanar da ta aikata suka cika mata hamsin. Hamsin ɗin saisun bincika ta tafi tanata tsalanta. Mommy ta dawo tanata hidimarta, babu alamar takaicin Safiyyah har hakan ya bawa Hajiya Mardiya mamaki.

Hidima ake sossai kowa na abinda ya dameshi nan da nan Mommy tayi bakam, can Aunty Zahra ta fito kamar zata yi kuka.
"Mommy an takaitani".
"Lafiya Yayarsu?".
"Sarkata Mommy babbar bangantaba".
Cikin mamaki Mommy ta mike tana salallami nan da nan zance ya game gida kowa na jimantawa. Safiyyah ta dubi Sanah,
"wai sata a gidan suna Allah kyauta".
"Amin kedai Aunty".
Muryar Mommy ta katsesu,
"kowa ce ta ɗaukomin jakarta ba sani ba sabo".
Nan da nan aka rufe kofa aka taramata jakunkunan a gabanta, tanason ta fara da jakar Safiyyah karta sha wuyar caje amma ta rasa wacece jakar ciki domin da jakar Safiyya da Sanah da Teemah da kuma Ummu Abdoul duk iri ɗaya ce. Cikin ranta ta furta Allah yasa kar dara taci gida.

***
Gaba ɗaya Mommy gumi take saboda rikicewa a hankali ta ke caje jakunkunan har takai ƙan jerun gwanon kakunkuna huɗun masu kamancecceniya. Cikin murmushi tasa hannu ta ɗauko ta farko ta zazzage babu sarka ciki a yatsine ta ɗagata,
"tawa ye?".
"Tawa ce, cewar Ummu Abdoul".
Ta kuma janyo guda ta duba ta ɗagata,
"tawa ye?".
"Tawa ce Mommy", ta amsa tana sakin ɓoyayyar ajiyar zuciya gefe ɗaya Baba itama ta saki tata ajiyar zuciyar tana yiwa Mommy dariyar mugunta. Saidai gabanta ya tsananta faɗuwa wajan rarrabe jakar Sanah ta saka kota Teemah. Kafin ta gama tunani ta riski muryar Sanah na amsa,
"tawa ce".
Aka mika mata tuni jikin Mommy ya gama sanyi ganin dara taci gida. Da sanyin jiki ta janyo jakar ta duba ilai saiga sarka take kowa ya yi salati su Safiyyah sukai tsili-tsili Teemah kuwa ko a jikinta saima murmushi da tayi tabar wajan. Cikin mutuwar jiki Mommy ta rakata da ido, sai kuma ta haɗe fuska tana murmushi ta dubi Hajiya Kilimaht,
"ke dama kanwarki kika bawa ajiya kika wahalshemu?".
"Mantawa nayi Mommy".
Daga haka tabar wajan, nan da nan aka bar batun sarka. Suna shiga ɗaki Safiyyah ta tsare Teemah da ido.
"Sis ya haka?".
"Hmmm! Safiyyah tunda dai ke kin kuɓuta ai anyi mai wuyar Allah shirya Mommy".
Da mamaki suke kallonta,
"kamar ƴya?".
Ta yi murmushi ta ce,
"lokacin da muka fita gaba ɗaya zuwa harabar baya a gabanku na bawa Safiyyah rikon Saddik. Ina shigowa na nufi banɗakin cikin ɗakina ko minti biyar banba naji an shigo da zanyi magana saina fahimci mai shigowar cikin sanɗa yake saina leko ta kafar kofar. Ina ganin Baba tanata bincika jakunkunanmu harta gano ta Safiyya tana  buɗe jakar Safiyya kuwa na fito. Sai tayi duru-duru. Na tsareta da tambaya zataimin inda-inda nace zan mata ihun ɓarauniya aikuwa saigata tana warwaremin yadda sukai da Mommy. Jikina yayi sanyi tsohuwar tabani haushi sossai, domin na lura san kuɗinta ya yi yawa ai TALAUCI BA HAUKA BANE. Nan naita yimata faɗa hada kwalarta tana nunamin sharin shaiɗane. Na girgirmata kai ina faɗi aa Baba hada son zuciyarki menene Safiyya bata yi miki cinki shanki karatun jikokinki biyu duk ta ɗauka hada abinda huruminta ba. Sai tasa kuka tana nunamin kuɗin hayarsune ya kare bata da halin biya tana jin nauyin tambayarki shiyasa ta amincewa bukatar Mommy amma yanzu zata mayar mata. Nasan halin Mommy sarai saina hanata na ɗauko jakata nace tasa a ciki, ta nuna bazata saka ba saida mukai ja inja sannan ta saka ta dubeni da mamaki,
"me yasa kikace insa ataki?".
Kai tsaye na bata amsa,
"idan a jakata aka gani Mommy baza ta yi hunkuci ba koda zatai bazataimin kwatankwacin na Safiyya ba".
Jikinta a mace ta saka ta tafi tana waige wannan shi ne abinda ya faru".
"Allah ya rufa miki asiri kamar yadda kika rufawa Safiyyah Fatima".
Muryar Aunty Zahra ta ratsa kunnuwansu a hankali ta karaso ta rungume Safiyya idonta jajjir ganin yadda hawaye kebin kuncinta. Tausayin yarinyar ya cika mata zuciya sossai ta rasa wace irin tsana Mommy tai mata haka. Sossai suka lallasheta tare da nuna mata komai lokacine. Haka taro ya tashi kowa na saka da warwara cikin ranshi. Da yamma Saddik yazo ɗaukarsu, amma still babu walwala tare da Safiyya yaso sharewa suje gida amma ya gaza shi kansa taku yi masa dariya. Ya yi shahadar kuda ya ce,
"Jiddona waya taɓa miki Mommynki?".
Ai kuwa Jiddah ta yi karaf tiryan-tiryan ta wasafa masa abinda ya faru, cikin hargagi Safiyya ta tareta.
"Jiddah gidanku ina kika ji?".
"Mommynmu naji tana bawa Mommynsu Mama labari".
"Kin koyi gulma ko Jiddah tarbiyar da nai miki kenan?".
"A'a Aunty wallahi ba gulma nai ba tambayata fa yayi".
Jikinsu yayi sanyi sossai Saddik da kyar yake tukin Hajja kuwa mamakin halin Kundum take tana zagin Baba ba tare da duban tsufanta ba dukda ta girmi Baban sossai. Karshe tace sai Saddik ya koreta, nan fa Baba taita furuwa tana bada hakuri ba wanda ya tanka mata cikinsu har suka isa gida. Kowa ya nufi ɓangaransa, da abinda yake sakawa cikin ransa. Safiyyah na shiga ɗaki ta watsa ruwa tayi sallahr isha i ta saka doguwar riga mara nauyi mai hannun shimi amma ta kamata sosaai ta zauna bakin gado tare da yin tagumi tana tuna abinda ya faru idonta taf hawaye. Saddik ya watsa ruwa ya fito amma jinsa yake sakaf babu taimakon Safiyyah kai tsaye ɗakinta ya wuce harya shigo bata san da zuwansa ba ya zauna tare da ɗora kansa kan kafaɗunta yana shishinar gashinta mai daɗin kamshi bata katseshi ba amma ta zame masa kamar dutse. Ya birkitota suna jin numfashin juna,
"Safiyyah!".
Shiru babu amsa ya sake kiranta har sau uku saita zuba masa idanu kawai kamar warkewar makanta,
"kiyi hakuri Safiyyah....".
"Shiiiii! Bana bukata alfarma ɗaya kawai zakai min".
Bata jira cewarsa ba ta cigaba,
"karka kori Baba kamar yadda Hajja take tunzuraka".
"Dalili?".
"Saboda mace ce mai rauni mai cike da bukatuwa matsi yasata aikata hakan, tunda nake da ita daidai da gishiri ban taɓa kamata ta ɗaukarmun ba".
"Wannan ce hujjarki?".
"Ita ce Saddik in dai nice nai mata afuwa".
"Shikenan ubangiji ya yafe mana baki ɗaya".
"Yauwa nawan".
Ya harareta da sigar wasa,
"naki kona Lubnah?".
"Namu to baki ɗaya".
"Kai kin cucce ni amma".
"A haba kaifa jarumin maza ne".
Dariya sukai baki ɗaya ya janyota ya soma wasa da gashin kanta tuni salon ya sauya. ASUBA TAGARI SAFDEEQ.
***
Washegari haka suka tashi cike da farin ciki, bayan fitar Saddik ta dawo ta duba sashin Baba sama da kasa babu ita babu dalilinta ranta ya sosu tana tausayin matar sossai haka ta cigaba da zaman falon saida Hajja ta fito sannan take gaya mata ai tun daran ta fice ta bar gidan. Bata so hakan ba amma saita share tace,
"Allahsa hakan ne yafi alkhairi".
Koda Saddik ya dawo ya sami labari bai wani nuna damuwa ba dama shi matar ta fice masa cikin rai. Jiddah kuwa tasha faɗa wajan Safiyyah ta nuna mata kada ta sake irin wannan katoɓarar.
                                                     ***
Kwanci tashi cikin Safiyyah wata biyar cif aka tada maganar auran Saddik hidima aka shiga yi sossai. Mommy da kanta ta fita Dubai ta haɗowa Lubnah lefe akwati goma. Saddik dai ya zuba mata ido ganin bata haɗawa Safiyya ba kuma ko maganar ƴhakan bata yin. Ya rage saura sati biyu bikin ya kasa jurewa ya tarita da batun lefan Safiyya. Ai kuwa kamar jira take inda take shiga ba nan take fitawa ana cikin hakan Daddy ya shigo nan ya hau tambayar abinda ya faru kan Saddik a kasa ya kasa cew komai sai Mommyn ce tayi bayani aikuwa Daddya ya raba rigima inda ya ce shi zaiwa Safiyya nata kayan. Ai kuwa Mommy ta shaka domin dai tasan Daddy baya k'aranta. Aikuwa yadda akaiwa Lubnah dozin haka Daddy ya yi mata. Ya rage saura sati biyu biki Safiyya ta aika aka karɓo mata kuɗinta wajan Abbƴ dubu ɗari uku Sanah ta kawo mata dubu ɗari kyauta hakama Teemah Aunty Zahra kuwa da Aunty Halima dubu ɗari biyu suka bata babu shawarar Saddik ta sauya komai na ɗakinta ya fita aiki ya dawo sai iskewa ya yi ana haɗa mata kaya. Ai kuwa nan ya dunga faɗa kan me zata shigo masa da maza gida a zuciya itama ta hayayyako masa dama cike take da haushinsa gani take rawar kafa yake kan auran kawai munasirancine yanason Lubnan. Ransa ya ɓaci sossai ganin ta dage tana yarfa masa magana batai auneba ya yarfa mata marin daya gigitata sai kuma yabi ƴhannun nasa da kallo da sauri ya barmata gidan yana hucci. Ita kuwa bata hango lefinta ba saima ta ɗauki fushi da shi. Sossai ɗakinta ya yi kyau dan kayan ɗakinta ta suyar musu dubu ɗari uku ta cika ɗari biyar suka haɗa mata saiti. Tsayin kwanaki suna takun saka da juna, yana tausayinta amma ya kasa kai kanshi gareta yana san nuna mata kuskuranta. Babban takaicinsa kayan da ta sauya da kanta bayan tasan hakkinsa ne wannan kasa jurewa ya yi ranar monday da safe da zai fita ya tambayeta nawa ta kashe kuɗin gyaran amma buɗar bakinta sai cewa tayi,
"ina ruwanka?".
Bai bi takanta ba ya wuce aiki daya taso ya biya gidan Saubahn ya tsare Sanah saida ta gaya masa kuɗin data kashe, ba jinkiri kuwa a gabanta ya yi wa Safiyyah transfer na one m accont ɗinta ya yi musu sallama ya wuce gaida su Abbu.

Tana zaune sakon ya sameta mamaki ya kasheta to wai sakarya ya maida ita ne? Tana nan zaune shaiɗan na mata huɗubar tsiya ya yi sallama ya shigo laɓɓanta da suka motsane kawai suke nuna alamun amsawarta ya wuce ɗakinsa ta bishi da harara. Shuɗewar muntuna talatin ta nufi ɗakin yana zaune yana aiki cikin kwamfuta ta shiga da sallama ya amsa ya ɗauke kai.
"Naga sakon kuɗi bansan na menene ba?".
Ya kalleta kawai yayi murmushi ya kauda kai kwata-kwata faɗanma kara mata kyau yayi a idonsa. Fuu! Ta mike da niyyar barmasa ɗakin batai aune ba ta tsinci kanta a faffaɗan kirjinsa saita sakuka mai cin rai. Bai lallasheta ba saida tayi ta gama ya sassauta murya,
"haba Safiyya ya kike so inyi? Saddik na kine bashi da buri sai naki bashi da walwala sai taki duk kin bi kin rikitashi ki duba yadda ya rame duk dan saboda ke. Haba MATAR SADDIK kefa kika dage saina bi umarnin Mommy kuma anzo gangara ki birkicemin hakan ya dace?".
Jikinta ya yi sanyi sossai so da kauna da kuma tausayinsa suka haɗu sukai wa zuciyarta rubdugu ta kwantar da kanta cikin sanyin murya ta ce,
"ka yafemin damuwar dana asassa maka Saddik kasa tankwara zuciyata nayi musamman idan na tuna wata rana itama Lubnah za a kirata da MATAR SADDIK hakan na min ciwo".
"Safiyyah duk wadda za a kira da MATAR SADDIK bayanki ce, kin yarda?".
"Na yarda MIJIN SAFIYYA".
Dariya sukai gaba ɗaya daran dai sun rayashi da walwala da kuma farin ciki.
***
Kwanci tashi biki saura sati guda duk wani shirye shirye sun kammala. Sai jiran lokaci sai dai Safiyya duk rame ta kaɗe harga Allah tausayin ƙanta take na yin kishi da Lubnah. Kamar kodayaushe sunfito lacture tana zaune tana jimamin rashin zuwan Ummu Abdoul yau har akai first lacture can ta hango Raliya wata makiciyarsu  a gun zama ta nufota hakan nan jininsu sam bai haɗu da ita ba. Tana karasowa ta zauna batan taso ba ta amsa mata sallama suna zaune jefi-jefi suna taɓa hira saiga Ummu ta karaso suka saki murmushi tare ta furta.

No comments:

Post a Comment