KARNINMU..
©FIKRA WRITERS ASSOCIATION
BABI NA HUƊU
Da sallama ciki-ciki ya shiga falon yana mazurai da cin magani dan kar a kawo mishi wargi, don yasan tuni labarin abinda ya aikata na goya Gimbiya a gadon bayanshi ya iske ta, shi kuma bai shirya ma wani dogon turanci ba.
Tana hakimce akan daya daga cikin luntsuma lumtsumar kujerun da sukayi wa falon k'awanya, Kyakkyawar mace mai siffar kamala da kwarjini, hannunta rike da rimot din tv tana juya duk tashar da take so, Yaranta biyu wanda kallo ɗaya zaka musu ka san yan biyu ne saboda tsabagen kama, zaune suke a saitin kafarta.
A hankali ta dago dara-daran fararen idanuwanta biyu ta saukesu a kan shi, sun ɗauki tsawon wasu dakiku suna musayar kallo sannan ta ba banza ajiyar shi ta cigaba da canza tashoshi.
"sannu da shigowa Dady" yaran biyu suka faɗi suna masu mikewa.
"Yauwa twins, Kunga na manta jiya mun yi alkawari zan dawo da wuri yau, ku cigaba da hakuri dani kunsan hakkin talakawa" ya faɗi yana rungumarsu a tare.
Ji tayi inama ta iya ashar ta sakar masa wanda zai mutu bai manta da shi ba, har zata ce talakawa su gimbiya ba tunawa da video da Haj Balkisu ta turo mata haɗe da shagube. Amma ina sai ta sami harshenta da yi mata nauyi, kawar da fuska kawai ta yi.
Tsawon minti daya yana kallonta sannan ya karkaɗe babban rigar sa ya nufi saman bene inda karamin falonshi yake.
Kallo ta bishi dashi gamida taɓe baki
"Ga doki har doki amma kafar na sakaina"
Ta fadi hakan a zuciyarta, dukda tasan mijin nata tantiri ne a gurin neman mata amma bata zaci zai iya mantawa da daraja da matsayinsa na Babban Minista a birnin da ake ji dashi a kasar Haurobiya goya karuwa ba tare da jin kunyar 'yan rakiyarsa da 'yan jarida ya wuce da ita cikin hotel ba, a saninta duk tantirancin shugaba yakan maida Al'amura irin haka su zama SIRRIN ƁOYE ga al'ummarsa. Duk irin bala'in da ta tanadar ma zuwan shi ta gagara aiwatarwa, asali ma nauyin baki ta tsinci kanta a ciki shi yasa tai iskar kare dashi.
Ta kebe baki haɗe da jan tsaki, zuciyarta cike fal da zallar takaicin wannan mummunar hali na mijinta.
***
Tun da ya shiga falon ya kasa zama, sai kai wa bango mari yake yana safa da marwa, nadama ce fal a zuciyar sa duk da matarsa bata ce da shi uffan ba haka a wajen taron da suka yi. Nan take abubuwan da suka faru ya dawo masa kamar yana kallon film;
Tun bayan da ya sauke wayar amininsa Ahmad ya gagara motsawa, can dai yai kokari yaja wata zazzafar iska ya fesar zuciyarsa cunkushe da damuwa, yasan halin 'yan adawa, kuskure kaɗan suke jira sukai mutum kasa war-was!!!
"Kai ni wai wani karen haukan ne ya cijeni na aikata wannan rashin hankalin?"
Ya tambayi kansa yana dukan kansa da hannun hagu, yaja wata zazzafar iska ya fesar, wani tsantsar dana sani ne ya kara mamaye zuciya da gabban jikinsa.
Duk tunanin da yake yi ya rasa wakar farawa, dan haka ya janyo daya daga cikin wayoyinsa da tun dazu ya danna su a silent saboda kiraye-kirayen da ake ta mishi kan abin kunyar da ya aikata.
Baibi ta kan rututun miscalls din da ya gani ba ya kara lalubo lambar Ahmad ya danna kira.
Saida ya katse sau uku sannan Ahmad din ya daga a karo na hudu.
"Ya akayi?"
Ahmad din ya furta daga can bangaren murya a cunkushe.
"Miye ma ba'a yi ba Ahmad? Tuntuni nake tufka da warwara amma har yanzu na rasa wakar farawa wallahi..."
"Sau nawa nake fada maka Sadisu? Su mata da kake ganinsu idan ka biye ta tasu sai su kaika su baro"
Ahmad ya fadi hakan zuciyar shi fal da takaicin ministan.
"Mai afkuwa ta riga ta afku Ahmad, mafita ya kamata mu nema kawai"
"Ka kira Malam din?"
Sai a sannan ya tuna da abinda ya manta, dan haka ya katse wayar da sauri.
Amintaccen direbanshi ya kira don dashi kawai yake irin wannan tafiya, zuwa da kai yafi sako, dan haka da kanshi zaije ba sako ba,
Yana isowa ya ja shi suka fice.
***** *****
Ko da ya isa wajen ya iske malamin ya sallami kowa don haka ka'idar zuwan su yake. Tun bayan da suka yi waya ya sallami duk Sauran kwastamominsa ya tsaya jiran sa.
Bayan shigarsa zama yayi ya tankwashe da kafafu a gaban Malam, lokaci zuwa lokaci yana saɓa gefen babbar rigarsa ya share zufar da ke tsiyayo masa.
Hankali tashe ya gama korawa Malam duk abinda ya faru sannan ya kara da cewa.
"Malam babban tashin hankalina shine, muna da miting nanda awa rabin awa , nasan ana nan ana jira a tada maganar a gurin, shiyasa na tako da kaina, dan Allah a rufe bakin duk masu niyyar tada zancen a gurin"
"Ashsha!! Abu bayyi dadi ba Ranka ya daɗe , amma babu abinda zai gagara in Allah ya yarda"
Malam Baso ya fadi haka, sannan ya maida hankali kan farantin dake gabanshi wanda ke shake da kasa, ya cigaba da zane yana gogewa.
Tsawon minti biyu sannan ya dago kanshi yana kallon minista, ya haskeshi da murmushi da jajayen hakoransa waɗanda suka dafe da ruwan goro.
Hannunshi ya zura can cikin wasu tsummokara da suke nade a gefe, ya ciro wata kwalba mai kama da ta fiya-fiya ya mikawa minista
"Ga wannan, turare ne, ka tabbatar ka bade lungu da sako na kayan da zaka saka ka halarci gurin taron, nima anan zan cigaba da aiki, babu wanda ya isa yai maka ko kallon banza balle har a iya tunkarar ka da Zancen, kai ba ma su kaɗai ba, har ilahirin Haurobiyawa ba zasu sake ɗauko maganar ba"
Wata wawuyar ajiyar zuciya minista ya sauke, a cikin kashi dari na damuwarshi kashi sittin sun zube, ya yarda da aikin Malam, bai taba cewa 'eh' yaga akasin haka ba.
Da haka sukai sallama bayan ya zube mishi dauri biyar na bandir din naira dubu dubu.
***** *****
Malam baso shararren malami ne da ya shahara a koyar da almajirai, daga gari-gari ake kawo su a yankin birnin Dunotsi, harkan shi da yan siyasa ya sa ya mallaki babbar tsangaya a ɗaya daga cikin anguwanin da ke wajen babban birnin, inda yake karantarwa, a Dalilin hakan sunan anguwar ya tashi daga hayin tuntura zuwa zawiyar malam Boso.
Asalinsa gardi ne yai gardama daga gurin malamin shi, da yake yanada sa'a a duk al'amarin dayasa gaba lokaci kadan da kafa tsangayarshi yai fice a babban birnin haurobiya, boyayyar sana'arshi itace tsubbu da duba ga jama'a, saboda sa'arshi yasa har manyan mutane ke ziyartarshi, cikinsu harda babban minista.
*** ***
Ko da ya dawo, hakan su ka yi meeting ɗin cikin kwanciyar hankali da tarin nasarori, domin babu wanda yai masa ko kallon banza balle a tayar da Zancen aika-aikar da ya aikata. Nan suka baro tare da Ahmad suna masu farin cikin aikin malam.
"His excellency! Na faɗa maka malaman nan sun yi sai kace kai wane wane, da baka je ba na tabbatar da yanzu sai Allah" Faɗin Ahmad suna mai kara musabaha
"Hmmmn! Nagode Aminini Allah bar zumunci" minista ya faɗi cikin sanyin jiki.
***
Ajiyar zuciya yayi da ya kawo nan ya tashi ya ɗauko ruwan gora mai sanyi ya kora, wani sashi na zuciyar sa na dana sanin zuwa wajen malam yayin da ɗayan sashin ke nusar da shi siyasa sai da malamai, hakan yake kasancewa duk lokacin da ya ziyarci malam, nan kuma YANDA YA FARA BIN MALAMAI ya dawo masa...
***
Bayan sallan isha'i Gimbiya ta sulale daga gidansu ba tare da tayi ma kowa sallama ba, bata tsaya ko ina ba sai gidan malam Sadi. Da sallama ta shiga ta gaida iyalinsa sannan ta tambaya ko yana nan.
Sunyi mamakin bakuwar don a iya saninsu Malam sadi mutumin kirki ne, to mai zai kawo Lubabatu wajen sa. Cikin sanyin jiki matarsa ta uku ta je ta sanar masa da zuwan bakuwar.
Da murnar sa ya fito da tabarma ya shimfaɗa mata a gaban ɗakinsa inda duk wanda ke gidan zai iya hango su gudun zargi.
"sannu Lubabatu zauna, mairamu kawo mata ruwa"
Ya faɗi yana mai zama a tabarman.
"baba ina so ka kira matan gidan don su ma zasu amfana da labarin" ta ce bayan ta sake gaishe shi. Nan take ya kira su suka zauna sannan ta fara.
"A iya sani na da wayo na kuka dawo hayin nan, zan fara muku daga asalinmu yanda za ku fahimci komi. " ta faɗi a sanyaye.
LUBABATU MUSA (GIMBIYA LUBY)
Asalinsu yan garin MESIRA ne da ke chan arewa maso gabashin k'asar Haurobiya, Malam Sambo shine mahaifin Malam Musa tare da matarsa Inna Talatu, su biyar suka haifa.
Jamila itace babba sai Mardiyya sannan mal Musa da k'annensa su biyu Misbahu da autarsu Sabirah.
Malam Sambo ba wani mai arziki ba ne sai dai godiyan Allah domin wani lokacin abinda zasu ci ma ga-gararsu ya ke musamman in kasuwa ya ja baya Kasancewar sa ɗan kasuwa mai siyar da kayan masarufi.
Allah bai yi yaran za su yi karatu mai zurfi ba, tun daga makarartar gaba da primary, su ka tsaya, ba su k'ara gaba ba, suka cigaba da sana'ar siyar da kayan masarufi kasancewar shine sana'ar babansu, yayin da matan kuma aka aurar da su. Ana cikin haka ne Malam Musa yayi kaura zuwa Dunotsi anan ne ya haɗu da Juma, suka kulla soyayyar da ta kai su ga aure.
Farkon aurenshi duk bayan wata uku ya kan ɗauke ta zuwa Mesira dan gaida iyayensa, ganin sun shekara biyar bata yi ko ɓatan wata ba nan danginsa suka matsa masa ya kara aure.
Juma ta goyi bayan hakan don ta riga ta yanke kaunar samun ciki balle haihuwa, son da Musa ke mata yasa ya kekyashe ido ya ki amincewa a karshe ma ya yanke zumunci tsakanin sa da yan uwansa bayan rasuwan iyayensa.
A shekaransu na bakwai da aure Allah ya azurta su da ciki, murna a wajensu babu kama hannun yaro, sun gode Allah da baiwan da ya musu.
Sannu a hankali suka yi ta renon cikin har ya kai wata tara. Ranar wata talata nakuda ya taso ma Juma, da taimakon Addu'a Allah ya sauke ta lafiya, ta haife yarinya sak mai kama da ita. Ranar suna yan uwa da abokan arziki sun zo anyi biki inda yarinya ta ci suna LUBABATU.
LUBABATU ta taso cikin gata da kulawar iyayenta, tana da shekara uku gidan da ke kallon gidansu wato malam Sani ya kama da wuta, duk ahlin gidan sun rasa rai sakamakon gobaranbanda yar budurwar gidan Saliha da Kaninta yaro. Malam Musa ya ji mutuwan makocinsa saboda tunda ya zo garin Malam Sani ya ke rikon sa a matsayin kaninsa.
Bayan an gama makoki dangin mahaifinta suka ce basu san da Zancen ɗaukan nauyin ta ba, nan suka ba ta kwanaki ta fitar da miji ko su aurar da ita ga wanda suka so.
Nan hankalin Juma ya tashi don shakuwar da ke tsakanin ta da Saliha, tunanin ta taya zata taimaka wajen ceto Saliha daga bakin ciki, a karshe ta tsai da tunani ɗaya.
"Malam don Allah Alfarma nake so" ta faɗi bayan ya dawo daga kasuwa, ya ci abinci suna yar hira tsakaninsu
"Maman luba faɗi bukatar ki in Allah ya yarda za'a cika miki" ya bata amsa yana mai kashe mata idanu. Sunkuyar da kai tayi tana murmushi.
"don Allah yanda Allah ya rufa maka asiri ka taimaka ka auri Saliha, Kaga ga ciwon da ke damu na wanda zai iya zama ajali na duk da ciwo ba mutuwa bane, amma kayi ma Allah ka auro ta." ta karasa tana tsugunawa.
"Zan yi tunani, amma kin san banda wani wadata ko, amma Hmm..." ya yi shiru ya bar ma cikinsa saura.
Juma kuwa ta kasa ta tsare har ta shawo kan Malam Musa ya aure Saliha ya fake da Juma na fama da ciwon zuciya (cardiovascular infarction).
Anyi biki lafiya amarya ta tare da Kaninta Yaro a gidan malam Musa inda shi aka gyara masa ɗaki zaure.
Zaman lafiya da kaunar juna ke wanzuwa a gidan, Malam Musa kan ja Yaro zuwa kasuwa don shi ma ya goge a harkan, shekara ɗaya da auren Saliha ta haifi ɗan ta na farko wanda ya ci suna Nuhu, bayan shekara biyu ta sake haifan Aisha.
Lokacin shekaran LUBABATU tara a duniya, a shekaran ne kuma mahaifiyarta ta sake samun wani cikin.
***
Wata rana Luba ta dawo daga makaranta sai ta shiga ɗakin Yaro wanda akwai shakuwa sosai a tsakanin su don har aka tsokane ta da "Luban kawu Yaro" duka ta dawo makaranta nan take fara yada zango don amsar adawa yau ɗin ma haka ne. Nan ta same shi yana kallon film ɗin turawa bata ɓata lokaci ba ta samu wuri ta zauna ba tare da ta ce dashi uffan ba ganin hankalinsa na kan bidiyon da ya ke kallo.
"ya ta in sa miki mai daɗi?" ya tambaye ta yana mai murmushi
"eh! Kawu, mai wakan Indiya don Allah" ta faɗi da murna ta don duniya babu film din da take so sama da Indiya.
Bai sake cewa komi ba ya sa wani wanda a lokacin ba ta san abinda ake yi ba tana kallo a tsorace ta gagara ta shi.
" kwantar da hankalinki wasa suke yi mai daɗi, ko mu zamu iyayi" ya faɗi yana rungumo ta jikinshi.
Shiru ya sake ratsa wajen, suna kallon baɗalan da ake yi a ciki. Sannu a hankali ya fara aiwatar da wasannin gare ta, bayan ya samu natsuwa ya bata balangon ɗan majaja da tafi so sannan ya sallame ta yana mai kwaɓa mata akan tayi shiru.
Wasa wasa Duk ta dawo makaranta sai sunyi wannan wasa har lokacin haihuwan mahaifiyarta Juma ya tsaya, addu'a suke Allah ya sauke ta lafiya amma haihuwan sai ya zo da gardama Allah yai mata rasuwa.
Ba karamin rashi suka yi ba, sunyi kewa da makoki suna masu zubar kwalla saboda kaunar da ke tsakaninsu, ta samu shaidan kwarai daga makota da yan uwa, Saliha tayi kuka sosai don ji tayi kamar ta rasa yar uwarta ta jini.
A hankali suka cigaba da al'amuransu ba don sun manta da ita ba sai don sun san damuwa ba zai dawo da ita ba.
No comments:
Post a Comment