Sunday, 25 December 2016

Sakaci 23

    
            💔💘 *SAKACI* 💘💔

                        2⃣3⃣

© *Fatima A Garba*.

Yau ne Farida ta kar6a girki kuma yau ta na da niyar ta kyautatawa yayan nata shiyasa ta wuni gyaran gida, duk da gidan ba wani datti ne dashi ba, amma sanin halin yayan nata da son tsafta yasa ta yi k'ok'arin kimtsa komai.

Ta na gama gyaran gida ta hau na jiki duk ba ta da tabbacin wanda ta keyi dominsa zai yaba, amma dai a ganinta bai kamata wannan ya zama hujjarta na k'in gyarawan ba.

Shiga kitchen ta yi, ta na tunanin mai za ta dafa mai wanda tasan zai yaba, tunowa da ta yi a rayuwar Dr yana son shinkafa da wake da kuma miya, ko bayason cin abinci aka bashi wannan zai ci sosai.

Sannan kuma mutun ne mai son farfesun kayan ciki, ba tare da 6ata lokaci ba ta nemi Isiyaku mai sharan gida da gyaran flawa, ta aikeshi kasuwa ya siyo mata duk abinda ta ke bukata.

Cikin k'ank'anin lokaci gidan ya kaure da k'amshi, daf da magriba ta kammala komai gami da jerasu akan dining table.

Wanka ta shiga, gami da d'auro alwala, ta fito dai-dai an kira sallah don haka kayan da ta ke sallah da shi ta zira had'e da shinfid'a sallaya.

Ko da ta idar da sallah ba ta tashi ba azkar ta cigaba da yi kafin lokacin sallah isha'i ta tashi ta gabatar.

Kwalliya ta yi, wanda rabonta da ta yi irinshi ta manta, tabbas ta san ta yi kyau, material ta d'auko mara nauyi, kasancewar garin akwai zafi.

Doguwar rigace d'inkin fitet, ya kamata sosai dama gata masha Allah, ko'ina ya fito ba'a magana.

Kasancewar ita masoyiyar turare ne yasa ta fesa kusan kala shida ajikinta, gasu masu sanyin k'amshi shi d'in ne kuma ya bada k'amshi mai sanyi ga dad'i.

Kama gashinta ta yi da ribon kafin kuma ta kafa d'auri wanda ya mata kyau matuk'a.

Falo ta fita, zama ta yi akan kujera ta zaman mutun d'aya kafin kuma ta janyo wayarta, Ummi ta kira.

Cikin farin ciki suka gaisa da Ummi, Ummi ta ce "Farida Umar kinsamu
Yayanki kin manta dani ko"

Cike da shagwa6a Farida ta ce "ni na isa na manta da Ummina" Ummi ta ce "toh ba lefi da fatan dai kuna lafiya, ba wata matsala ko?".

Farida ta ce "ba komai Ummina sai kewarki" murmushi Ummi ta yi irin nasu na manya kafin kuma ta ce "karki damu d'iyata da nasamu saukin aiki zanzo naganki"

Ummi ta sa ke cewa "yauwa kafin na manta, kina yawan yin wannan addu'o'in da na baki"

Farida ta ce " wanne daga ciki Ummi" Ummi ta ce " wanda na ce ki dinga yin Istigifari, Salatin annabi da Lahaula wala k'uwata illah billah, na fad'a miki duk wanda ya lazimcesu ba adadi insha Allahu zaiga biyan buk'ata aduk abinda ya sa gaba, don haka ki dage kinji"

Farida ta ce "toh Ummi inayi amma zan k'ara dagewa, Allah ya k'ara girma Ummi"

"Ameen" Ummi ta ce da ga nan sukayi sallama gami da ajiye waya.

Dai-dai wannan lokacin ya shigo, hannuwanshi cikin ajjihun wandonshi, kallonta ya ke baya ko k'ifta ido.

"jibi mutumin nan inda ya samin ido, yanzu da ni ce na ke mai irin wannan kallon da kaji bak'ak'en maganganu" ta fad'a a zuciyarta.

Shima maganar ya ke a zuciyarshi "Wow, Allah na gode maka da ka azurtani da wannan zankad'ed'iyar matar"

"Sannu da dawowa" ta katse mai tunani, cikin basarwa ya ce "ke me yasa baki san kalar kwalliyar da tafi dacewa da zamani bane, haba abu sam ba fasali ya kamata kisan irin kwalliyar da za ta miki kyau, mtsss" ya karashe da jan tsaki.

Shi kanshi yasan abinda ya fad'a ba gaskiya bane, amma gudun karta yi tunanin ta burgeshi yasa yayi haka.

Wani bakin ciki ne ya tokare ma ta mak'oshi, cikin sanyin murya ta ce "na kawo maka abinci ne"

Fitanshi yayi ba tare da ya tanka ma ta ba, ba kuma don baya jin yunwa bane sai kawai don tsare gida irin nashi.

Yau kam ma ta gagara yin kukan saboda bakin ciki, Qur'anin ta ta d'auko domin ta na bukatar abinda zai sanyaya ma ta zuciya.

Ba ta ajiye Qur'anin ba sai da ta ji ta samu sanyi a cikin zuciyarta, abinci ta d'iba dai-dai wanda za taci sauran ta zuba a babban wormer, hijab d'inta ta zura gami da fita.

Mai gadi taje ta bawa abincin, da murnarshi  ya kar6a, bud'ewa yayi yana kallo gami da saka ma ta albarka, juyawa ta yi domin tafiya dai-dai wannan lokacin ya shigo gidan.

"Malam musa don Allah zo ka siyomin biredi" idanunshi ne ya kai kan abincin, atake yaji yawunsa ya tsinke.

"Malam Musa a ina ka siyo wannan abincin" ya jefa mai tambayar, kasancewar bai lura da ita ba yasa bai gane ita ta kawo ba.

"Alhaji ai yanzun nan dakta ta kawo mana" ya fad'a yana washe baki.

"yaufa za'ayita" ya fad'a acikin zuciyarshi.

"Aikuwa Malam Musa zan maka kwad'ayi domin tare zamuci, ban san abinda aka dafa ba kenan, na ce na k'oshi na san kuma babu saura a cikin gidan"

Ya fad'a yana shirin zama akan bencin da Malam Musa yake kai, Malam Musa ya ce,

"Toh Alhaji ai ba komai ni,zubamin nawa ma a murfin kawai" ya fad'a yana yaba irin kyawun halin mai gidan nashi.

Dr ya ce "a'a tare zamuci" "toh ayi haka" Malam Musa ya fad'a cikin farinciki,

Suna cikin ci ta dawo da kwanon farfesu a hannunta, ganin Dr ya na cin abinci da mai gadi abun ya bata dariya kuma da ta mai tayin abincin fa ko kulata baiyi ba, gimtse dariyarta ta yi.

Shikuwa kicin-kicin yayi da fuska ya ma cigaba da cin abincin sa tamkar bai ganta ba.

Itama sharewa ta yi sannan ta ce "Malam Musa ga farfesun kayan ciki nan idan zaka k'ara"

Malam Musa ya ce "ayya dakta kinga ni bana cin kayan ciki wallahi"

"Toh ka ajiye idan kaga almajirai sai ka basu" ta fad'a.

"Hoh yarinyar nan za ta kasheni wai sai ta sa naji kunya" ya fad'a a zuciyarshi.

"Kije ki ajiye a fridge zai yi anfani ko zuwa gobe ne" ya fad'a fuska a murtuke, ita abun ma dariya ya bata, juyawa ta yi cikin gida ta na dariya ciki-ciki.

~Ummu Hanan~

No comments:

Post a Comment