Saturday, 10 December 2016

ANA KUKAN TARGAƊE 6

ANA KUKAN TARGADE...
Part 6⃣
Avva omar yaro
(Prince av)
09032724001

"A ina shi kuma yake sa'ada" ya fada tareda juyowa yana kallon vocal, nan ta labarta masa labarin chuchu da Kwalisa baki daya.
Kai Kawai yake gyadawa tareda tuna wani shudadden lamari a tasa rayuwar da sauri ya kauda tunanin tareda cewa "zan binciki lamarin"
  Karfe 5:10 vocal ta koma Gida, tareda bawa kukunsu umarnin yin girkin da marasa lafiya zai iya ci.
   Yayansu abdoul shiyai driving dinsu itada ummanta suka koma asibitin, lokacin da sukaje ana kiran sallar magariba dan haka abdoul din A.A yabi suka nufi masallacin dake Cikin asibitin, vocal kuma ta ajiye hijabinta a gefen gadon da h.deejah ke kwance ta fada toilet dan dauro alwala.
   Ummu abdoul ta dafa gadon da h.deejan ke Kwance, wani irin tausayi dayake a zuciyar ko wace mace na nasanin ciwon juna shiya hado da jimamin halin dataga h.deejah suka samar mata da kwalla a ido, gefen mayafinta tasa tana gogewa, harga allah duk yadda vocal tabata labarin halin da h.deejah ke ciki saita tarar daya fice haka, tana tofa mata addu'a vocal ta fito daga toilet din
"Ummu na fito" ta fada tana karasa shimfida sallaya, gyada kai kawai ummu abdoul tayi batareda tanka mata ba, ganin hakan yasa itama vocal din bata kuma cewa komai ba ta tada sallah.
Saida ummu abdoul ta idar ta addu'ar datake shekama h.deejah sannan ta nufi toilet din cikin sanyi jiki, tana cikin sallah A.A da abdoul suka shigo, vocal ta kara gaida A.A tareda yi masa ya mai jiki ta dubi yayanta "ya abdus salam dan bani key na manto hand bag dina a mota"
Kallonta yai tareda tsare gida "inkin daukko amfanin mai zatai miki yanzu a nan" ya fada cikin gatse.
Vocal tai kasa da kanta kawai dan tasan halin yayan nata akwai zuciya a makoshi, ummu abdoul ce data idar da sallah ta tanka masa "kai dadina dakai bature akwai son nuna isa wallahi, toni nace ta daukko jakartata saboda wayarta na ciki, zan kira abbanku na fada mishi inda muke, danni tsabar rudewa na manta ko kiranshi banyi ba, gashi kuma tawa wayar ba chaji"   keya ya hau sosawa  cike da kunyar yarfin da umman tai mishi ya mikawa vocal key din.
     *        *        *
Yau satin chuchu 2 kenan a halin coma (dogon suma) wanda har zuwa lokacin ba wanda keda tabbacin ranar dazata farfado, sunan dai kawai chuchu batada lafiya ne amma alamomin ciwon sunfi bayyana akan rayuka uku A.A , h.deejah da vocal yadda suka rame sukai duhu ba wanda zaice basu ke ciwon ba, tundaga ranar da abin ya faru vocal bata kara zuwa school ba a nan asibitin take wuni.
        *        *        *
Zaune suke kan kujera 3seater a dakin md suna kallon wani film din india BAHUBALI, tsakiyarsu dan karamin bowl ne dauke da popcorn dayasha hadi da vanilla.
"Ni wallahi film dinnan harna gaji da ganinsa kai kullum inka zo bakada abin kalla sai shi, sina sinan cikinsa ba bawanda ban haddace shiba a kwanyar kaina, kuma duk saboda nacin kallonsa da kake son farillanta min nima dankai naga ka wajabawa kanka, wallahi allah ne ya rufa maka asiri shekaran jiya bayan ka tafi gida har zan hullashi a dustbin bansan meya katse azancina ba harka dawo yau ka sameshi a 'yance" md ke fada tareda dibar popcorn din ya zuba a baki, bai mamaki ba dan yaji kwalisan yabar zancensa yabi ruwa yasan halinsa inyana kallon film din hatta wayarsa kasheta yake dankar a nemeshi, baya kaunar duk wani shamaki dazai sa ya dauke idonsa daga majigin dai-dai da sakon daya, kiftawar ido ma a ganinsa dandai ya zama dole ne.
Md bai kuma tanka masa ba ya jawo littafin long walk to freedom yaci gaba da karantawa, har film din ya kare aka fara rubutu sunaye baiji motsin kwalisa ba, ya gane karewar film dinne ta taken karshe da suka sa a end of the film din, ya kifa littafin akan center table bayan ya duba shafin daya tsaya, akwatin majigin yafara bi da kallo kafin ya dire idanuwansa akan fuskar abokin nashi "subhannallahi" ya ambata a rikice ganin halin yake ciki wanda da alama ya shure mintinoni a hakan ture bowl din popcorn din yayi tareda matsawa kusa dashi yana dafa kafadarsa "abokina lafiyarka kuwa?"
  A zabure kwalisa yaja baya yana kallonsa da alama baima ji salatin da md din yaja ba, kawai ya dawo daga duniyar tunanine sanadiyya feeling din daya ji a jikinsa, maida kansa yai jikin kujera ya kwanta tareda lumshe ido a hankali wata kwalla ta gangaro kuma tunsa "chuchu" ya ambata batare daya bude ido ba.
Cikin sarkewar harshe md ya furta "mutuwa tayi?"
     Girgiza kansa kawai yai batareda ya amsa tambayar da aka mako masa ba, md yaci gaba dabinshi da kallo cikin nazartar inda yasa gaba, mikewa tareda nufar fridge din dake dakin gorar ruwan c'estbon ya dauko tareda murde kanta, ya kafawa kwalisa a bakinshi, bai musu ba shima ya bude bakin tareda dago da kansa yana kur6ar ruwan, dan a dai-dai lokacin shima yana bukatar abu mai sanyi dazai rage masa zafi da zugin da zuciyarsa keyi.
     Saida ya shanye gorar ruwan tas sannan ya saki wata ajiyar zuciya mai karfi tareda jijjiga kansa, md bai zauna saida ya farasa gorar a dustbin tukunna sannan ya dawo dan neman karin hasken ambatar sunan chuchu da kwalisa yai.
  Kwalisa ya kura masa ido tsayin lokaci kafin ya dauke kansa "md ranar wanka ba'a voyen cibi, dan naga alama hakan bazai haifar min da da mai ido ba, tun daga lokacin da hajiya tabani labarin bukhar da yayarta hankalina ya gaza kwanciya, nai alkawarin ba chuchu ba kowacce bata kaita bace bazan kara wulakantawa ba akan ta furtamin kalmar so, naso kwarai na gyara alakata da ita amma sai nake ganin kamar inna koma chuchu bazata dubeni ba, ganin yadda rabuwarmu da ita ta karshe ta kasance, kalamanta keta amsa min kuwwa inna tuna lokacin "bawanda na tsana yanzu a rayuwata irinka" md tabbas lokacin na hango tsanar da chuchu ta fada a cikin idanuwanta, hakika yanzu nayi nadama mutuka ina kuma yunkurin gyara kurena na baya, amma rashin ganin chuchu ko kawarta ya tayarmin da hankali mutuka, md a yanzu haka zuciyata na dab da buguwa idan harba haduwa nayi da chuchu na nemi yafiyarta ba kuma na mallakamata tawa boyayyiyar kaunar danake mata saboda....."
A kagauce md ya tare shi "wai chuchun dai dana sani kwalisa? Koko wata chuchular kaima ka samu?"
      Harara kwalisa ya fara bin md da ita, kafin ya bude baki cikin gatse yace "su chuchun ruwansu ake yowa ko noma su ake, dahar zaka ringa yimata kishiya" md hannu yasa a kunnensa ya karkade dan gani yake kamar sai yaje anmasa wash & set din kunnen saboda baya jiyo masa maganganu dai-dai, amma kuma yanayin da kwalisan ya nuna na nufin daga wajenshi maganar ta fito tun daga kolin zuciyarsa, danya kuma tabbatarwa saiya karyar da kai "yi hakuri abokina kenan chuchu A.A ko?" Kada kai kwalisa yai cike da nuna gamsuwa da marainiyar murya yaci gaba "md naga yarinyar na ganin kima da mutuncinka mezai hana ka shigemin gaba wajen tattaki har gidansu na nemeta, danna tabbata inni kadai naje ta hadani da karnuka, intaimin mutunci kenan batare datasa sojojin gidan sun tilasmin yin tsallen kwado ba"
   Maganar taso bawa md dariya amma kawai saiya kanne ya wayence da tari wajen fidda dariyar "ka ta6a zuwa gidansu ne kaga sojojin?" Kwalisa ya kawar da kai "koba'a fada maka ba kasan gidan babban mutum kamar A.A zaka sami abinda yafi sojoji ma a matsayin masu gadinsa da iyalansa"
      "Hakane" kawai md yace tareda mikewa ya juyawa kwalisa baya cikin fushi ya fara magana "indai akan labarin da hajiya tabamu ne bai kamata kaji kaunar chuchu ta dalilinsa ba saboda na tabbatar akwai randa labarin zai 6ace daga memoryn ka, kaga kenan duk randa ka manta labarin hakan na nufin ka yasar da rayuwar chuchu?" Ya karashe maganar da salon tambaya.
  Zumbur kwalisa ya mike baki na rawa "wallahi abokina ba akan labarin da hajiya ta bamu bane kawai dai......."
Md bai bari ya karasa ba ya tari numfashinsa "kawai dai kana son cimma wata mummunar manufarka akanta ko? Nina sani kwalisa banza bata kai zomo kasuwa ba yadda za'ai ka kaunaci chuchu tsakani da allah, kawai dai kace surar jikinta na fusgarka, nikuma wallahi bazan ta6a baka kofa ka cuci 'yar mutane ba" cakumar kwallar rigar md yai cikin karaji yake cewa "uban wayace sha'awarta nake, inda sha'awarta nake dabanyi amfani da damarmakin data bani ba saina zo na gayyatoka, ka gayamin gsky md kodai kaima ka fara sonta ne?" Md kam idanuwansa na waje yaji matsa shi kwalisan ma tsoro ya fara vashi ganin yadda yake gabatar da acting dinsa kamar zararre, dakyar ya dage wajen hada furucin "sakeni haka muyi magana ta nutsuwa abokina, na fuskanci inda kasa gaba"
Ba musu ya sakeshi aiko md ya fada kan kujera yana maida numfashi, kwalisan ma zama yai jiki a sanyaye ganin halin dayasa abokin nasa, shikansa baisan garin yaya hakan ta faru ba.
        "Yakamata koma menene kwalisa yanzu mu fara neman chuchu tukunna dan nidai jikina yana bani daskiya ba lafiya ganin yadda suka daukewa skull kafa itada kawarta"
"Kasan gidansu ne" cewar kwalisa.
Md ya dan daga kansa "ummmm nasan dai a nan wajejen forestry take, amma muje kawai ai gidan babban mutum kamar A.A baxai 6uya ba" mikewa sukai su biyun suka fito farfajiyar gidan, md ya karbi mukullin motar kwalisa a cewarsa shizai driving dinsu dan kwalisan yafi samun relief kafin suje, shima kwalisan bai musa masa ba yabashi dan shima yana bukatar hutun jiki dana zuciya.
      Maigadi ya wangale musu get, dasauri md ya taka birki sakamakon karo dasuka kusa yi da wata katotuwar mota KLASSEIN baka ita kuma tasawo kai tana shirin shiga cikin gidan, su sukayi ribos suka koma ciki yayinda hakan yabawa na motar damar shiga farfajiyar gidan, bai tsaya gyara parking ba kawai ya kashe motar ya fito, sanye yake da yadin filtex blue mai haske wanda hakan yasa ana iya hango vest dinshi ta ciki, kamala da kwarjininsa ne yasa kwalisa da md fitowa daga motar batare dasun shirya ba, kobasu ga kamarsu da chuchu ba sun san shi a ido kasancewar yadda fuskatar tasa tazama ba bakuwa ba a gidan television da masu news paper.
      Durkushewa kawai sukai a gabansa suna gaida shi cikin nuna ladabi da girmamawa, A.A ya bisu da kallo cikin so da kaunar su daya darsu a ransa lokaci daya, hakika kowaye kwalisan a cikinsu baiga laifin 'yarsa ba danta fada soyayya dashi, ya kare musu kallo su biyun kafin ya tsaida fuskarsa akan kwalisa daya fuskanci yafi takurewa da rawar dari, hakan yasa ya dora masa karan dori cewa daga gani shine kwalisan, gyaran murya yai kawai tareda kama kafadarsu ya mikar daya bayan daya, dukfa hakan basu sake ba saida suka sake dan rankwafa masa.
Hannu ya mika musu da nufin su gaisa amma inaaa ko wannensu ya kasa miko hannunsa, murmushi kawai yai kafin yai gyaran murya "wanene mukthar kwalisa a cikinku?" Ya tambaya da tausasawa "gashi nan" md ya fada yana nuna shi, A.A yai murmushi kadan ganin wanda ya zata din shiya gani "mukhtar nasan koban maka bayanin ni waye ba ka ganeni a yadda yanayinka ya nunan, amma dai duk haka bayanin yanada dadi" yai shiru kafin ya cigaba "nine ABUBAKAR AUYO mahaifin AYEESHER CHUCHU yarinyar dake sonka a makaranta, nazo ne takanas gareka mukhtar danna roki alfarma a wajenka, wanda nasan kudina ko martabata bazasu bani ba, saidai kawai taimako da tausayi dazakai amfani dashi, mukhtar badan halina ba ina rokonka ka taimaka ka cheto rayuwar 'yata kwalli daya dana mallaka"
A rude kwalisa ya dago tareda cewa "abba meya sami chuchu" A.A yai taku daya biyu tareda basu baya cikin rawar murya yake labarta musu halin da chuchu ke ciki, tun kafin ya karasa md ke jijjiga kai cikin tsananin tausayin chuchu, yayinda kwalisa keta faman share kwalla da fadin a fili "chuchu ce a halin coma, chuchuna ce a halin bugun zuciya, chuchu keda hawan jini duk sanadina, dan allah abba ka taimakeni ka kaini wajen chuchu na nemi yafiyarta wallahi ina son rayuwarta fiyeda tawa" ya rike kafar A.A yana fada.
           *         *         *
A mota md ke labartawa A.A yadda sukayi da kwalisa da cewa fitowar dasukai ma gidanshi zasu allah ya kawo shi.
Kwalisa shidai yana gidan baya allah allah yake kawai yake ya ganshi a gaban chuchu yaga halin datake ciki ko hankalinsa ya kwanta, md ke jan motar yayinda A.A ke wajen mai zaman banza yana godiya ga allah a zuciyarsa ganin yadda ya kawo masa lamarin a saukake.
Suna tafe yana nunawa md hanya har suka karaso asibitin, md yai parking suka firfito A.A ne ya wuce gaba suka bishi har zuwa dakin da chuchu ke kwance, lokacin dasukaje vocal na gefe tana karatun alkur'ani suna shigowa ta mike tana binsu da kallo cikin tsananin mamaki, direct kwalisa gadon da chuchu ke kwance ya nufa batare daya amsa sannu da zuwan  da h.deejah ke musu ba, kallon mamaki kawai take binsu dashi na tunanin daga ina A.A ya samo wadannan kuma? Tunaninta ya katse lokacin dataji vocal na cewa KWALISA? cikin tsananin mamaki ta ambaci sunan da sauri h.deejah ta Juya dan ganin waye kwalisan, amma cikin matasan biyu tarasa gane wannene?.
      Kwalisa shikam fargabarsa anya kuwa in chuchu ta farka zata so shi kamar yadda yake fata, dan a yanzu ma kalamanta ne suka ci gaba da amsa masa kuwwa "bawanda na tsana yanzu a rayuwata irinka..." Ya toshe kunnuwansa kawai jin yadda sautin zancen ya dume masa dodon kunnuwa.......

😳Tofa!!!! Mu jirayi farkawar chuchun muga mezata yanke tsakanin alakarta da kwalisa?
Mu tara a ANA KUKAN TARGADE... 7
           naku prince av
           09032724001

Inason amfani da wanna damar wajen bawa masoyana hakuri masu bibiyar novel din TURN BACK TO BYGONE, aimin uzurin rashin fitowar part 4 akan kari, labarin ne true life kuma precious dake bada labarin na kwance ba lafiya, dan haka kuyimin uziri zuwa samun saukinta danta karashen min labarin nima na sambado muku.
Dukda nasamu korafin mutane akan cewa ina amfani da #-word dayawa hakan ma ina kara bawa masoyana hakuri zan gyara ana gaba insha allahu, ga full meaning din wasu word din :- d/f - different
B/t - between
Coz - because
Lyf -life
5rn - friend
6ter - sister
Lyk - like
   Zan ringa rubuta full name dinsu a gaba insha allahu.
Prince av

No comments:

Post a Comment