💔💘 *SAKACI* 💘💔
3⃣0⃣
© *Fatima A Garba*
Komawa gefe yayi ba tare da ya iya yin komai ba, bargo ya janyo gami da rufesu, kafin kuma yace.
"Kwanta kiyi baccin ki kinji"
Wani irin bakinciki taji ya taso mata, cikin dashewar murya tace "ya Umar mai yasa kakeyi min hakane, nagaji, nagaji hakurina ya k'are wallahi bariki zan shiga"
Tashi yayi cike da tashin hankali ya kunnan wuta, k'ok'arin bud'e kofa ta ke, daga ita sai tawul ajikinta.
Zuwa yayi da sauri yasha gabanta gami da cewa.
"Ina zakije daddaran nan" "bazan iya ba Dr zanje na nemi wani tunda kai kasa yimin" cikin damuwa yace
"Farida anya kinada lafiya kuwa, kodai kinsha wani abu ne" fad'awa jikinshi ta yi gami da k'ank'ameshi, ta na cewa
"Ban san me yake damuna ba, nidai ka taimakeni Ya Umar idan ba haka ba wallahi ko wurin su Baba maigadi sai naje sunyi mun, wallah idan ba'ayi min ba mutuwa zanyi"
"Kar na sake jin haka a bakin ki Farida ba kyau haramun ne, muje na miki"
Sam ya kasa aikata komai, cikin damuwa yace Farida na kasa wai shin me yake faruwa damu ne, nakasa yin komai me yasa"
Tureshi ta yi gami da tashi da sauri ya kamota yana kiyi hakuri zan nemi mafita, "wallahi bazan iya ba ni ayau nakeso amin, kuma sai naje anyi min"
Tabbas da gaske ta ke zata aikata abinda ta fad'a, to me yake damunta ne, zare key d'in d'akin yayi ya 6oye.
Tabbas ranar basu rintsa ba, yayi tunanin Faridan shi ta samu ta6in hankali ne, sunga tashi hankali ba karami ba.
Da asubar fari ya jata suka shiga mota Jos suka nufa ba wanda yayi sallah acikinsu balle wanka.
Karfe shida da rabi na safe suka isa, kai tsaye gidan Ummi suka nufa.
Daga Ummi har Alhaji hankalinsu yayi muguntashi cikin yanayin da suka ga yaran nasu, cike da damuwa suke tambayar yaran nasu.
Dr ne yace "Alhaji akwai damuwa" Alhaji yace "me yake faruwa ku sanar damu hankalinmu atashe yake"
Nan take Dr ya sanar dasu komai, cikin 6acin rai Ummi tace "wato har yanzu bakabar bakin kishin nan naka ba, tabbas yau saika sauwak'ewa yarinyar nan"
"Ummi ki rok'a min shi yazo yayi" Farida ta fad'a kafin kuma taje ga Dr ta ne kamashi ta ne cewa, "Ya Umar ka taimakeni badan halina ba"
Hawaye ne ya fito daga idanuwanshi yace "Ummi wallahi na rantse miki da Allah ba kishi bane nima ban san me yake damuna ba, kinji yanzu abinda ta ke fad'a ni kuma na kasa Ummi"
Alhaji ne yace "Ummi rik'e hannunta ku shiga ciki, zanyi magaba da Umar"
Bayan su Ummi sun shiga ciki, Alhaji ya juyo ga Umar yace.
"Umar yaushe ne ka samu wannan matsalar domin nasan da kanada lafiya tunda gaka da yara" Alhaji ya fad'a.
"Wallahi Alhaji har yanzu lafiyata kalau, idan ina tare da Mariya hakan baya faruwa amma da nazo wurin Farida komai sai ya sauya kuyi mana addu'a Alhaji bana so Farida ta jefa kanta a hatsari"
"Tashi muje" Alhaji yace da Dr, kafin kuma yayiwa Ummi waya da ta d'auko gyalanta su taho da Farida.
**** ****
Wurin babban malami sukaje, kuma babban limamin ne a wani babban masallaci, masani ne sosai a harkar addini.
Zaune suke agaban Sheik Muslim Anas, sannu ahankali Alhaji ya fayyace mai komai.
Kallonsu yayi sosai kafin ya juyo ga Alhaji yace "a gaskiya Alhaji wannan al'amari akwai d'aure kai, amma fa ina tunanin sammu akayiwa yaran nan, sai dai kasan sanin gaibu sai Allah, yanzu kuje gida karku bari yaran nan su aikata komai ita kuma ku bata kyakkyawan kulawa, domin komai na iya faruwa"
Zanyi istihara duk abinda ake ciki zan nemeku da safe, amma zan dad'a jaddada muku ku kula dasu sosai kuma karku fad'awa kowa abinda ake ciki"
Godiya sosai Alhaji yayiwa malam, kafin suka tafi.
**** ****
Da safe wurin karfe sha daya, kiran sheik ya shigo wayar Alhaji yace mai za yana kiransu da gaggawa.
~Ummu Hanan~
No comments:
Post a Comment