💔💘 *SAKACI* 💘💔
3⃣1⃣
© *Fatima A Garba*
Alhaji abin da na gani ya tsorata ni, tabbas anyi wa yarinyar nan sammi, shi kuwa yaron nan 'karfin addu'a ne ya ku'butar da shi, yanzu zanyi k'ok'ari na karya wanda zan iya sauran kuwa dole se munje gidan domin anyi birne-birne da yawa a cikin gidan"
Cewar Sheikh Muslim.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" abinda su Alhaji suke mai-maitawa kenan,
"Malam toh a gidan mijin nata ne akayi birne-birnen, kokuwa a ina ne?" Ummi ta tambayeshi.
"A'a agidan mahaifinta ne, yanzu ga wannan, ganyen magarya ne da addu'o'in karya sihiri, ku shiga cikin gida zan sanar dasu yanzu kije ki ma ta wanka dashi sannan ki bata tasha, sauran kuma sai kun gama"
Farida na gama sha bayan an mata wanka ta fara wani irin bak'in amai, lokaci guda zazza6i ya rufeta.
Koda Sheik ya ganta yace ba damuwa hakan yana nuna sihirin ya karye kenan.
Alhaji yace "Shiek naji kace anyi birne-birne acan gidan mahaifinta yanzu meye abin yi"
Sheik yace "haka ne amma fa dole sai naje gidan da kaina sanna za'a tone su gami da karya dafin su"
Alhaji ne ya rok'eshi akan don Allah ya sallami iyalanshi suje bauchin haka kuwa akayi.
Sunyi k'ok'arin kiran Baba amma wayarshi akashe, na Aunty kuma bata d'auka ba.
Don haka kai tsaye gidan suka zarce.
Tun daga waje suke jiyo murya Aunty tana fad'a, ko sallamarsu bata ji ba, abinda suka gani bayan sun shiga yayi mugun d'aga musu hankali, shin dagaske ne ko kuwa gizo idanuwan su suke musu.
Baba ne zaune akasa Aunty ta na ta surfamai bala'i, kanshi a kasa tamkar yaron gida da ubangidanshi.
Shigowansu yayi dai-dai da kwara mai miyan da ta yi akanshi, cikin gi-gicewa yake cewa.
"wayyo Allah idona bana gani Aunty ki taimake ni" da gudu sukayi kanshi cikin tausayawa.
Cike da 6acin rai Farida tace "mai ya miki" ba ta re da ta bata ansa ba, ta yi hanyar fita cike da rashin gaskiya.
Sheik ne yace."Karku barta ta fita" da hanzari Dr yaje ya rufe kofar da key.
Sheik yace baiwar Allah zo ki zauna kifad'a mana duk wani sharri da kulla-kullen da kika yi"
Cike da rashin gaskiya tace "wani kulle-kulle kuma na yi, kokuma kunzo ne kumin sharri har gidana, toh wallahi bazan yarda ba"
"Akan me zaku zo har gida kuce zaku ritsa min mata ta wallahi ku fita min daga gida munafukai" Baba ya fad'a cikin hargagi.
Alhaji zaiyi magana ya katse shi da cewa "nasan kai kashirya komai kuma wa ma ka d'auko nake jin muryashi kuka shigo min gida, to ka kwashesu kubarmin gida"
Duk wannan maganar da yakeyi idanunshi basu bud'e ba, ga kuma rand'ad'in da suke mai.
Ran Alhaji idan yayi dubu ya 6aci zai sa ke yin magana.
Shiek ya sake katseshi da cewa "karka ga laifinshi ba cikin hayyacinshi yake komai ba"
Wannan ya fad'a ne cikin rad'a wanda Alhajin ne kawai yaji abinda yace d'in.
Sheik Muslim ne ya d'auko wani ruwa ya mik'awa Alhaji yace " maza bashi ya kur6a sannan ka shafamai ajiki zai rage mai rad'ad'i"
Shidai Alhaji yaga irin ruwan da akaba wa Farida ne amma sai yabi umarnin Sheik ya aikata abinda yace d'in.
Kasancewar shi Baba azaba ta dameshi a idanunshi har kuma baya iya bud'esu yasa ya yarda.
Cikin hanzari Aunty ta taso da niyar kwa6ar da maganin, amma kafin takai ga hakan Sheik da yake ankare da ita yasa mata kafa, ba ta re da ta idar da nufinta ba ta jita a kasa.
Sannan ya bita da wata gigitacciyar tsawa wanda ta sata nutsuwa ba tare da ta yi niya ba.
Hannu biyu ta ke rokon kar azubawa Baba wallahi zasu kasheta, ba ta re da 6ata lokaci ba kuwa Alhaji yaba Baba yasha, Baba yana cewa
"Kwantar da hankalinki Aunty da zaran idanuna sun bud'e zanyi maganin........" Bai kai ga k'arasawa ba ya fara kwara wani bakin amai tamkar zai fitar da hanjin cikinshi, Alhaji da Umar ne suka rik'eshi.
Sai da aman ya lafa tukunna Sheik Muslim ya juyo ga Aunty yace "za ki je ki tone abinda kika birne kokuwa saina yi maganinki.
"Kana tunanin zan bi umarninka ne, toh wallahi kayi karya sai naga bayansu"
"mutanan da suka rik'eki amana kike ikirarin sai kinga bayansu, anya akwai zuciya a k'irjinki kuwa, mai suka miki, mai suka tsare miki" cike da damuwa Ummi ta ke tambayarta.
"Tabbas da zuciya a kirjina ita d'ince ma ta shawarce ni da abinda nakeyi"
"Sun rabani da farincikina, suna tunanin zan barsu da nasu ne, kokuma suna tunani zan aureshi ne, na zauna dashi tsawon wannan shekarun ba ta re da na sa ke haihuwa ba, kuma ace ban damu ba"
Ta k'ara da cewa "toh bari kuji na zauna dasu ne dan d'aukan fansa"
"Mai muka miki, na rik'eki tankar uwa mai yasa haka" Farida ta fad'a
"Idan ku kun manta bari na tuna muku, bayan auran mu dashi na yi k'ok'arin kawo yarana gidan nan saboda tarbiyarsu da ta fara lalacewa inaso na kawosu gabana domin na kula da su"
"amma sam yak'i amincewa yace yana tsoron kar asake 6ata miki rayuwa, tunda yarana mazane kuma sun kawo girma"
"Na yi magiyar amma yaki amincewa k'arshe yace sai dai na nemi yardarki, koda muka miki maganar fashewa da kuka kikayi, nan kuma mahaifinki yace sam baisan zancen ba"
"Kuna tunanin hakan yamin dad'i ne, sai kuma bayan an kwana biyu sai ga Umar ya dawo gidan nan da zama, sai nace toh ko shi ba namiji bane"
"Abun yamin zafi ba kad'an ba, daganan na k'udiri aniyar d'aukan fansa ta dabara, na mallake Alhaji ba ta re da kowa ya sani ba, sannan na yi k'ok'arin yiwa Umar asiri akan ya afkawa Farida"
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" abinda su Alhaji suke fad'a kenan.
"Sai dai duk lokacin da malamina ya yi aiki akan shi sai muga haske ya baibaye shi, sam sihirin yakiyin tasiri a kanshi"
"ak'arshe na farrak'a tsakaninsu, sannan aka tura musu sha-shatau a harkar ibadar su, ta yadda asiri zai yi saurin kama su".
"Domin inaso na tozarta Farida ta yadda bakin ciki zai zama silar mutuwar mahaifinta, lokacin da kuka munafurceni kuka had'a aurensu, shi ne na tashi tsaye"
"Tabbas da Umar ya sake ya kusanceta da shida mazantarkarsa sunyi hannun riga, ita kuma alokacin zata bak'unci lahira"
"Toh amma sai yayi taurin kai, koda malamina ya duba sai yaga addu'ar da kuke mai ne ta hana sihirin yin tasiri akanshi"
"A wannan lokacin ba dan naso ba dole na 'kyale shi, randa tazo gidan nan na k'arshe na bata maganin da idan tasha dole ne taje ta nemi wani namijin.
"Na tabbata da zaran ta mutu shima dole ya bakunci lahira, kuma ko ayau kuka kashe ni na rama bakincikin da suka cusamin"
"Domin sai abinda naga dama yakeyi a rayuwarshi, abinci da magani sai naso yake anfanuwa dasu"
Kuka sosai Baba yake yi yana cewa "kije na sa keki, tabbas nasan kin bani wahala iyakar wahala, amma me yasa kika nemi ki cutar da Farida me yasa baki tsaya akaina ba, ni nasan alhakin Sakinatu ne yake bina, amma mai yasa Farida"
"D'aga hannu sama yayi yana cewa "Allah na tuba ka yafemin tabbas naga rayuwa ina neman yafiyanka ya Allah"
Ummi ce tace " tabbas kin cika muguwa, mai yasa za ki cutar da yarinyar nan, bayan kin san duk irin abubuwan da ta fuskanta arayuwarta, Allah ya isa tsakaninmu da ke"
Aunty ko kallonsu batayi ba taje ta fito da akwatinanta gami da cewa "sauran kayan nawa na aiko a kwashe mun" ta na gama fad'ar haka ta fice.
Dr yace baza ta fita ba dole a mik'ata ga hukuma, Baba yace "barta Umar wallahi na yi imani duniya zata koya mata darasi"
Daga Ummi, Farida har Baba kuka sukeyi sosai Sheik Muslim da Alhaji da Dr su suka tono duk wani sihirin da aka birne agidan, d'akinta ma basu bari ba nan magungunan da aka samu ba'a cewa komai.
"Kai mutun mugun ice ne" cewar Alhaji, nan fa Alhaji da kanshi yaba Sheik Muslim labarin irin gwagwarmayan da bayin Allah nan suka shiga, ya tausaya musu matuk'a.
Bayan sun zauna ne Sheik Muslim ya fara magana kamar haka.
"Zan fara ta kanki Farida lalle kin fuskanci jarabawa arayuwa kuma kin jure, wanda muke miki zaton rahmar Allah a rayuwarki"
"Allah subhanahu wata alah yana jarrabar bawanshi yadda yaso da kuma lokacin da yaso, ba kuma domin baya son ka bane, a'a yana sonka, sai dai yana gwada imaninka ne"
"Tabbas kin jure irin jarabawar da kika tsinci kanki aciki, kuma ladanki na wurin Allah kuma za kiga irin sakamakon da zai miki imma ki fara gani tun aduniya kokuma sai anje lahira"
"Alhaji Sulaiman tabbas kayi *SAKACI* da amanar da Allah ya damk'a maka na iyalinka, ka kuma ga irin kamun da Allah ya maka.
Wannan na duniya kenan Allah kad'ai yasan na lahira, kaga ahaka ma ka tuba ne da badan haka ba Allah kad'ai yasan a ina abun zai tsaya"
"Yan uwa ina muku nasiha da duk wanda Allah ya dam'ka muku amanarsu toh fa ku rik'esu hannu biyu, domin akwai ranar da za'a titsiyeka a tambayeka irin rik'on da ka musu"
"Don haka sai mun jajirce, abu k'ank'ani shi zai zama silar shigar da mu aljannah haka kuma abu k'ak'ani na zunubi zai kai mu ga shiga wuta"
"Alhaji Muhammad kai da iyalinka kun birgeni matuk'a, duk iyaye nagari ya kamata ace su kasance masu addu'a ga y'ayansu kunga k'arfin addu'a ko, toh Allah ya shige mana gaba"
"Kai Umar ka d'auki iyalinka ku tafi, ka kuma rik'eta da amana kekuma ki cigaba da kare hakk'okin Allah, Allah yasa muku albarka azamanta kewarku"
Addu'a sosai akayi a gidan kafin kowa ya kama gabanshi.
~Ummu Hanan~
No comments:
Post a Comment