Thursday, 22 December 2016

KIYYAYA CE KO SON ZUCIYA? 4


***
Kwanci tashi asarar mai rai, komai na tafiya yadda ya kamata Ummi rayuwarta take cikin kwanciyar hankali har zuwa lokacin bata sake haɗuwa da Haidar ba shima kuma bai dawo gidan ba. Kwatsam ranar Asabar Baffa ya kawo musu ziyara nan ya samu Ummi ya dinga caccaketa kan bata son zumunci. Jikinta yayi sanyi sossai ta dinga hango rashin kyautawarta a kala tafi shekara rabanta da gidan ko hidima ake sai dai Ummu taje kanta a kasa ta dinga bashi hakuri ta wuce islamiyya zuciyarta cike da tunanin yadda zata sabawa kanta da zuwa gidan.

***
Zaune suke ranar Lahdi Ummu nayi mata tsifar kanta ta muskuta tana son furta abin da ke cizon zuciyarta.
"Ummu ina son zuwa gidan Baffa amma wallahi wulakancine bana so".
"Hmm! Ummyter nafiki gudun wulakanci amma kisani shi zumunci abune mai matukar kyau da tasirin dai-daita lamura. Ki kauda komai ki rungumi kyautattawa musamman ga masu kuntattamiki da sanu zakiga ribar rayuwa".
"To Ummu zan gwada amma wallahi lamarin akwai ɓaccin rai duk juriyarka sai ka gaza".
"A a Ummyter juriya bigirece na cikar  burika".
"Allah ya yi mana jagora Ummu".
"Amin Ummyter kinga gama kaya daya aiko cewar za ayi taro karshan wannan wata, saiki daure kiba mara ɗa kunya kije".
"Ummu taron menene haka?".
"Ummi nima ban sani ba yadai nemi ganinmu baki ɗaya hadda ke".
"Zan je Ummu insha Allahu, me zaki musu ne game da taron".
"Kamar kinsan tunanin da nake kenan Ummi".
"Kimusu kunun ayarki mai daɗin nan".
Ta karashe tana dariya itama dariyar tayi tare da cewa,
"kyalesu kawai tun da ba sanin taron kona menene ba a tari gaba".
"Allah ya nuna mana Ummu".
"Amin".
***
Kwanci tashi babu wuya wajan ubangiji, har kwanakin taron suka karato ana gobe taron da da dare Ummi na ɗakinta tana aikin da aka basu a makaranta wayarta kirar tecno p5 tayi kara ta saki ajiyar zuciya ganin mai kiran ta sa hannu ta ɗauka cikin nutsuwa ta yi sallama.
"Assalamu alaikum".
"Wa alaikisala Aisha!".
Yar! Tsigar jikinta ta motsa saboda yanayin daya kira sunan nata, mamaki fall ranta Khalifa baya kiran sunanta kai tsaye sai zai mata batu mai muhimmanci jikinta ya yi sanyi ta amsa  a dausashe.
"Na am Sadauki".
Sunan da take kiransa kenan lokuta da dama, ya cigaba.
"Zuciyata kullum cikin begenki take, burina auran mace mai tarbiya yau gashi na samu nagartaciya. Karki gujemin duk runtsi!".
Ya ɗan tsagaita,
"Aisha zuciyata ta zaɓeki matsayin wadda zata zamo abokiyar rayuwata, ina fatan kikasance tare dani duk tsanani kamar yadda nake burin kasancewa tare dake har darussalam insha Allahu".
Maganganunsa sun gama kashe gaɓan jikinta, tana zargin Khalifa na cikin fitar hayyaci amma ta kasa gasgata hakan saboda muryarsa ras take babu alamun maye. Tayi saurin fatattakar tunanin daga zuciyarta ta numfasa.
"Sadauki zuciyata ta gama amincewa dakai, ina burin zama mallakinka kullum addu ata ubangiji ya tabbatar da alkhairi cikin rayuwarmu. Ka gama mamaye duk wani gurbi na zuciyata".
Sun jima suna musayar kalaman zahirin kauna daga bisani suka yi sallama cike da kewar juna. Ummi ta dafe kai tare da sakin numfashi tana mamakin kalamansa wanda bai taɓa yi mata kwatankwacinsu ba duk da ita ɗin shaidace kan kaunar da ya ke mata.

Mikewa ta yi ta nufi malallautarsu ta ɗauro alwala, gab da zata gota ɗakin Ummu kunnuwanta suka jiyo mata sautin Abbu yana magana kasa-kasa.
"Maryam magana nake so muyi dake kan batun Ummi".
Muryar Ummunta ta amsa,
"ina jinka Abbun Ummi".
"Yayane yazo da batun yana son haɗata aure da Haidar".
Das! Gaban Ummi ya faɗi cikin sauri ta wuce tabar gun kafaffunta na rawa sun gaza ɗaukarta tana zuwa ta zube yaraf kan katifa. Ta dafe kanta tana furta duk addu ar data zo bakinta kanta ya sara kirjinta ya yi nauyi ta rufe idonta dum! Ji take kamar in ta buɗe zata riski makanta ne ta cije leɓanta tana karanta innalillahi.....zuwa wani lokaci nutsuwarta ta dai-daita ta yi zugudum tana tunanin abin da ya ke shirin faruwa da ita.
Dare aka ce mahutar bawa in ji yan magana, amma ga Ummi abun yazo a hagunce ne kwata-kwata ta rasa nutsuwarta kanta banda zafi babu abin da yake. Ga wani sanyi  daya ke kaɗata tamkar mai rawar mazari cikin kankanin lokaci zazzaɓi mai zafi ya rufeta har haɗa hakora take gab-gab. Zuciyarta tayi tsai wajan tunanin yadda rayuwar Khalifa da tata zata kasance, wani fanin tana nusar da ida kan cewar.
"Haba Ummi yanzu akwai abin da iyayyanki zasu nema ki gaza yi musu? Sun lura dake da rayuwarki tarbiyarki tun kina tsuma har zuwa girmanki ba tare da sun gaza ba dame zaki sakamusu bayan biyyaya?".
Lokacin da tazo nan a zancan zucin saita sami kanta da sakin ɓoyyayar ajiyar zuciya taja zani ta  rufe jikinta saboda sanyin da take ji. Haka ta kwana sake-sake washegari ta tashi sukuku tayi fiyau da ita babu zazzaɓin sai kanta da yake sarawa jefi-jefi.
Haka ta kasance har zuwa tafiyarsu, Ummu na lura da yanayinta sossai saita ta alaka hakan da rashin son zuwa kiran. Karfe sha ɗaya na safiya suka yi wa gidan tsinke kasancewar akwai rashin nisa a kafa suka zo. Tun a harabar jikin Ummi ya yi sanyi ganin uwar dukiyar da aka makare a wajan motocin hawa kansu sun kai goma ta yi mamaki matuka ganin irin gyaran daya sha.
Cikin shakku suka karasa cikin gidan. Abbu ya nufi ɓangaran Baffa su kuma suka wuce ɓangaran matar gidan da sallama suka shiga aka amsa babu yabo ba fallasa. Suka zauna jigum tsayin mintuna goma ko ruwa babu wanda ya basu, Ummi ta gaji tana jin kishirwa ta mike ta nufi hanyar da take tunanin zata kaita _kitchen_ cikin nutsuwa. Gaisawa suka yi da Mama Ladi mai wanke-wanke ta bata ruwa ta juyo, kwatsam suka kiciɓus da Haidar a bakin sirririyar hanyar da zata dawo da ita falo ta haɗe fuska tayi kicin-kicin cikin turo baki ta ce,
"bani hanya in wuce".
Yatsurawa ɗan karamin bakinta ido, wani abu na fizgarsa ya saki murmushin mugunta ya kai hannu ji kake ɗil ya ɗani baki ai kuwa taji zafi ta dafe gun tana jijjiga kai. Bata yi aune ba ya sureta chak! Bai zame ko ina ba sai ɗakinsa dake babu tazara sossai.
Yana direta ta mike ta soma ja da baya tana yi masa kallon tuhuma, bata yi aune ba ya jefa mata tsintsiya a fuska harta karceta ta saki sirirriyar kara ya zare mata ido.
"Sharemin ɗakin nan tas".
Ta murguɗa baki ta hararreshi,
"anki ɗin ai ni ba Baiwarka ba ce".
Zare _belt_ ya yi yana dubanta, fuska tamke babu fara a.
"Ai dama mun saba, kada Allah yasa ki share wallahi mugun duka zan miki!".
Ya faɗa ƴyana huci, ganin babu sarki sai Allah yasa ta soma tattare ɗakin sai da ta kwashe kayan kasa ta sauya _bed sheet_ ta tattare kayan wankinsa ta haɗa masa waje ɗaya. Ta ɗauki mofa ta gyara ɗakin tas tasa _air freshner_ ta zuzzuge labulayan take ɗakin ya yi ɗum ya ɗauki kamshi. Ta gaji sossai ta zauna yaraf! Buɗe firinji ta yi zata sha ruwa saboda bushewar da makogwaranta ya yi dam! Gabanta ya faɗi.

Hannunta ya hau rawa zuciyarta ta hau bugawa cikin sauri ta maida ta rufe. Ta runtse ido tare da fitar da huccin iska mai zafi. Jiki a sanyaye ta mike ta gyaro banɗakin ta fito duk ta yi sakaro da ita. Dai-dai lokacin suka shigo ɗakin su uku Fadila da Ahmad da kuma Haidar. Cikin tuhuma Fadila ta jefa masa wani birkitacan kallo,
"wannan fa?".
Ta nuna Ummin kamar taga kashi. Ya sosa kai yana murmushi,
"mtss! Na manta nasa wannan kwailar ta yi min shara".
Ya dubeta tare da zare ido.
"Ke! Dilla fice ki bani waje, kin tsareni da ido kamar jigar mayyu _get out of my room_ fice min daga ɗaki".
Cikin sauri ta fice har tana tuntuɓe, saida ta saisaita nutsuwarta sannan ta shiga fallon. Ummu ta dubeta,
"ina kika tsaya?".
"Ina wajan Baba Ladi ne".
Ta yi mata karyar kare kai. Fitarta keda wuya ya soma duban tsarin ɗakin gyaran ya yi masa sossai ya faɗa banɗaki ya watso ruwa ya fito ya shirya ya dubesu.
"Zamu amsa kiran Daddyna, ku ɗan jirani".
Cikin murna suka yi masa fatan alkhairi yana fita suka kashewa juna idanu suka hau aikata abin da suke tunanin zai fishesu.
***
Dakin mahaifinsa ya yi wa tsinke, duk sun hallara shi ake jira, yana shiga ya haushi da faɗa Abbu ne ya dakatar dashi suka buɗe taro da addu a daga bisani mahaifinsa  ya fara bayanin nasarorin da aka samu a dukiyarsu na wannan shekarar tare da kammala karatun Haidar har ya gangaro kan makasudin tarasu.

"Alhamdulillah Haidar tun dawowarka karatu nasa ido kan ko zaka fito da MATAR AURE amma shiru hakan yasa muka duba babu cancantar zamanka haka don haka mun yanke haɗaka aure da kanwarka Aisha".
Tashin hankali wanda ba a samasa rana, take wani gumi ya dinga tsattsafowa Haidar duk da sanyin _Air conditioner_ dake sanyayya ɗakin. Ummi kuwa kasa kataɓus ta yi ɗakin yayi ɗif kowa da abin da yake rayawa cikin ransa. Bangare daya Maman Haidar kuwa ji tayi tamkar saukar aradu a kanta amma ganin babu wasa a fuskarsa yasa ta cin laya tace,
"amma ya dace aji ta bakinsu.....".
Ya katseta,
"duk cikinsu babu wanda ban isa dashi ba don haka bana son kanannun maganganu".
Gum tayi da bakinta ya cigaba,
"ga wannan mukulin gidanane na kijikin gidan nan ka ɗauka na baka ga takardun nan, akwai motoci guda biyu a ciki suma naka ne sannan nabuɗe maka shagon saida shadda da atamfa da kuma lessuna ka dinga saidawa shima nakane ka dinga juyawa bana bukatar ko sisi dan gane da riba cikinsa na bakane don ka kula da iyalinka".
Kasa cewa komai yayi don farin ciki sai hawaye dake bin fuskarsa ya yi godiya hakama iyalansa. Mommy daskarewa tayi a wajan tsabar mamaki da takaicin abin da mijinta ya yi taja numfashi da kyar ta mike cikin ci da zuci ta furta,
"dan me zaka yanke hukunci babu shawara, ai nima iyalinka ce ina da hakki akai".
"Dan kina IYALINA dukiyata taki ce?".
"Idan ni ban da hakki akai Haidar fa?".
"Sai ku bari saina mutu saiku sarrafata daga ke harshi ɗin".
"Gaskiya wannan zalluncine.....".
Kafin ta dire ya kaiwa bakinta wani duka da sauri Abbu ya tareshi yana faɗin.
"Haba-haba yaya ba girmanka ba ne a gabanfa yara muke".
Cikin huci ta furta,
"barshi-barshi ya dake ni ya daki auransa, igiya ta ɗaureshi har tayi rara, munafikin banza munafikin wofi ni za a nunawa karyar zumunta?".
Cikin shammata ya kwace rikon da Abbu ya yi masa ya zabga mata mari, ya nunata da yatsa.
"Ni zaki tozarta? Wallahi na shirya wa komai a kan auran nan ciki hadda rabuwa dake wallahi".
Ya nuna Haidar yana huci,
"kai kuma kabi uwarka ka nuna min ita ta isa dakai ba ni ba".
Fuu! Ya bar wajan yana hucci da sauri Abbu ya rufa masa baya. Ta yi tsaye tana mamakin yau ita yake faɗawa magana dangas, ta sauke idonta kan Ummu dake bata hakuri ta wurga mata bahaguwar harara.
"Lallai Maryam kinyi nasara, kinyi nasarar rusa duk wani shirina karo ƙbiyu zuwa uku kenan mijina na marina  sanadiyar 'yarki wallahi wallahi sai kinyi nadama ko zanyi yawo tsirara saina kuntatta rayuwarku keda ira-iranki".
Fuu! Tabar fallon, Ummu ta yi doguwar ajiyar zuciya ta sauke idonta kan Haidar  daya kai karshan fallon ta kasa tantance yanayin daya ke ciki. Tausayin Ummi ya tsirga mata matuka cikin ranta.

Haidar na shiga ɗaki ya riski Ahmad da Fadila na kallo, babu fara a ya zauna ta dawo kusa dashi ta nannike ya tureta ta mike tana muzurai,
"jeki saina nemeki".
Ganin babu wasa yasa ta fice tana gunguni. Tana fitowa ta riski Mommy na bada labarin abin da ya faru hankalinta ya tashi sossai harda hawayenta tana faɗin "wallahi Mommy kusan matakin ɗauka kan batun nan".
Hajiya Karima taja doguwar ajiyar zuciya tace,
"ai duk laifinkine Hajiya Sadiya da anyi magana kice asiri baya cin mijinki ai ga irinta nan zaki rasa tillin ɗanki!".
"To ya zanyi?".
Ta faɗa kamar zata yi kuka, raɗa ta yi mata a kunne suka tafa suna dariya.
***
Abbu ne ya dinga lallashin Baffa har ya sasauto  daga bisani ya zaro wayarsa a aljihu ya kira layin Haidar. Dai-dai lokacin daya tsiyaya ruwan shansa cikin kofi ya zuba mata ido yana tunanin yasha ya samu sassauci wata zuciyar na tuna masa Daddynsa na gida ya gama amincewa shanta ne mafita a yanayin daya ke ciki. Yana kafa _cup_ ɗin a bakinsa ƙkiran mahaifin nasa ya shigo ya dire tare da saisaita muryarsa ya amsa. Umarni ya bashi ya zo ya kai su Abbu gida su soma haɗa kayansu zuwa jibi su tare cikin girmammawa ya amsa tare da ajiye wayar. Mikewa ya yi ya bar Ahmad na kwankwaɗarta ya ratso fallon yana jin sautin Momnynsa na masifa ya yi murmushi,
"Mommy faɗa ba naki bane, Daddy yayi fushi kema kinyi fushi wazai taushi wani. Kibari ya sauko sai musan abin yi, shiyasa Ummu ke burgeni wani........".
Yana furucin yana barin fallo karaf! Suka yi karo da Ummi data kawo kai cikin fallon dukkansu suka yi baya fuskar kowa a tamke,
"kazo in ji Baffa".
"Banza bakauyiyya Daddy ake cewa".
"Anki a faɗa ɗin mara mutunci".
Yana niyyar cafkota mahaifinsa ya karaso,
"zo ka kai su".
"To Daddy".
Ya juya suka rufa masa baya ba magana kowa na sakar zuci.

Har gida ya kaisu ya dawo kai tsaye ɗakinsa ya wuce ya zuciyarsa kwar cike da kunci. Ya buɗe ma adanar sanyi ya hau kwankwaɗa sai da yaji ya yi mankas sannan ya ajiye ya sawa ɗakin mukuli ya kwanta. Bashi ya tashi ba sai tara na dare jinsa ya ke kwakwalwarsa _fresh_ kai tsaye wanka ya yi ya ɗauki _key_ ɗinsa ya nufi _Hauronbiya club_ yana da tabbacin a can zai sami Fadila.......

No comments:

Post a Comment