Saturday, 10 December 2016

ANA KUKAN TARGAƊE 4

ANA KUKAN TARGADE...
part 4⃣
Avva omar yaro
(Prince av)
09032724001

"....abinda kake son aikatawa mukhtar" taja numfashi hade da ajiyar zuciya tana goge hawaye amma kamar kara gayyatarsu take, bukhar yai mata abinda bazata ta6a yafe masa ba a rayu.
        *        *        *
"Yan jigawa ne mu, anan muka tashi mukaga iyayenmu da kakanninmu, nida takwarar haihuwata MAIMUNA mune na biyu a wajen iyayenmu, bayan babban wanmu abdoul.
  Kamar mu daya nida maimuna wacce muke kira da beli kamar an tsaga kara, banbancin mu kawai a halayya, beli nada sanyin hali da zurfin ciki, sa6anin ni dakeda tsiwa da rashin tsoro.
Muna tsanin son junanmu fiye da kwatance, abu daya zance muku kowannenmu yana san dan uwansa fiye da kansa, wanda in daya zai samu daya ya gwammace ya rasa..." H.iyami ta dakata tana kallonsu, sukuwa kwalisa da md sun nutsu suna saurarenta jin tayi shirune yasasu kallonta a tare, murmushi tai mai ciwo tareda ci gaba "inai muku matashiya da wannan ne danku fuskanci yadda muke  son juna bada wasa ba.
Yauma kamar kullum mun fito break a makaranta a lokacin muna j.s 2 (mune 'yan mata a zamanin) dan wasu sa'anninmu ma anyi musu aure, maimuna ta kalleni "iyami yau mai zamu siya ne?" 
    "Nidai beli koma menene mu siya amma banda dan marere kinga jiya shi muka sha, kuma naji kamar daxamu fito daxu umma na cewa shi zatai da rana"
    Beli tai murmushi kamar dama hakan take so taji daga gareta da sauri ta amshe "to ko muje gidan tsaiba mai waina"
Iyami ta kalleta tana mamakin meyasa kwana 2 take son suje gidan mai wainar, bayan da ta tsani zuwa gidan hakan yasa duk soyayyar da iyami kewa waina take hakura tunda zuwa siya bai kwantawa 'yar uwarta ba, amma bata san kwanan nan maganidisun dayake fusgar 'yar uwarta da gidan ba.... Bata gama tunani ba beli ta katseta "inkuma bai miki ba allah saimu sake, naga kamar hankalinki bai kwanta da gidan ba" ta karashe da sanyin murya da hakan ke nuna tsantsar karfin hali da tilasta kai a ciki.
Itama iyamin da sauri ta tareta "bahaka bane 'yar uwa kawai ina tunanin in mukaje gidan tsaiba ne kamar zamu samu layi ke kuma naga yunwa kike ji"
    Da fara'a beli ta amshe "laaaa ba wani layi kinga ai yanzu aka fito break" iyami bata kara cewa komai ba suka kama hanya suka tafi, kamar kurame haka suke tafiya kowacce da abinda take sakawa a ranta.
A farfajiyar gidan suka taradda samarin makarantarsu suna jiran wainar suma, dansu basa shiga saidai 'yar mai wainar taringa kar6o kudinsu in an soya ta kawo musu.
Duk iya kare musu kallon da beli tayi bataga wanda take son gani ba, dazasu shiga gidan har kara waiwayen su take amma badai ya nan din, batai aune ba taji tai karo da mutum da sauri ta dago tareda ja da baya tana zare ido, ta juye masa wainar daya riko tsaf a farar rigar uniform dinsa, gaban rigar duk ya rine da kalar manja, jikinta sai 6ari yake dan tasan itace batada gaskiya ta shigo da waiwaye bata kallon gabanta.
    Shikuwa ya kame gaba daya yama rasa mai zai mata ya huce, in ransa yai dubu ya 6aci, ba zubewar wainar ya bashi haushi ba illa bacin rigarsa dakuma shirun datai tana kallonsa kamar bataga aika aikar datai masa ba.
    Itakuwa beli harga allah bata iya sarrafa kanta inta ganshi ko daga nesa bare yau dasuke kusa da kusa, kuma ga laifin datai masa dan haka saita makure a jikin Bango kawai jikinta kamar ana kada mata gangi, fuskar datake waiwaye yanzu gata a gabanta amma ta kasa tsayawa ta kalleta koda da wutsiyar ido ne.
      "Waike dabbar ina ce ne ko kwakwalwar kifi gareki bakya ganin irin ta'asar dakikai min amma tsabar iskanci kika ja baki kika kulle uban me kike takama dashi" bukhar keyin furucin cikin tsananin fushi da 6acin rai, shirun dai takuma yi tareda runtse idonta tana jiran taji saukar dukansa a jikinta, ganin yadda tai hakan ba karamin fusata shi yaiba yaci gaba da zazzaga mata masifa daya gaji ya 6alle ma6allen rigar daga shi sai singlet ya wurga mata waccen kanta "gashi nan kuma wallahi saikin wanke" rigar ta sauka kan farin hijabinta shima ya samu nasa tabarrikin manjan, batai yunkurin sauke rigar daga jikinta ba dukda lurar datai itama nata kayan na 6aci.
           Daga cikin gidan suka ji hayaniya tai yawa hakan yasa suka fara lekowa dan ganin meke faruwa, daga cikin 'yan ajinsu wata ke cema iyami da bata leka ba "iyami da beli fa ake fada..." Aitun kafin ta karasa ta ajiye yarinyar hannunta datakewa wasa tai hanyar zauren gidan, adaidai lkcn bukhar ke hankada beli dacewa saita wanke mishi kayansa, mazan dake farfajiyar gidan duk sun taru suna bashi hkr, amma inaaa  shi abinda yake kona masa har ynz beli taki budar baki ta bashi hkr.
      "Na rantse d allah in yarinyar nan tai wasa saina tsundumata a cikin kwata na fanshe 6atamin rigar datai" bukhar ke fada Cikin tsananin fushi
"Haba bukhar ba'ayi haka ba dan allah kabi komai a sannu" cewar wani abokinsa dake rirrikeshi.
       "Kubarshi dan kutumar ubanshi y hullata" gaba daya suka juya dan ganin mai maganar, iyami ce taci damara da hijabinta, ta tattare kafar wandon ta maidashi three quarter da alama ta shiryawa koma da wane bala'i bukhar yazo.
   Ta karasa gurin tareda dauke rigar dake yarfe a jikin beli, yarda ita tayi a kasa tareda sa kafa ta mutstsikata "idanka haifi d jini kazo ka ta6ata k gani"
Ta fada tana girgiza kugu.
Tsalle bukhar keyi yana cewa "a sake shi ya karairaya iyami" amma inaaa abokanansa sun rikeshi sunata bashi baki.
  A haka iyami tagama zage-zagenta tareda jan hannun beli suka bar farfajiyar gidan "waiya dakeki ne" iyami ta tambayi beli ganin yadda take kuka bilhakki.
  "Bai dakeni ba iyami amma dai kinsan nice banida gsky ko tunda tun farko....."
      Bata karasa ba ta katseta a fusace "na rantse da allah ko kece laifin gaba daya bazan zauna ina gani ana ci miki kashi haka ba, ni wallahi sonayi ma anbarshi ko hakora 2 ne in zubar masa"  shiru beli tayi dan masifa da fadan iyami ba bakon abu bane a duniyarta
         *        *        *
Tun daga lkcn iyami tace sun daina zuwa gidan wainar, ita kam beli bata so hakan ba, dan harga allah ba siyan waina ke kaita gidan ba, tsananin azabar datake ji a ranta akan kaunarsa yasa kullum takanso suje gidan, dan tasan a nan majalisar su take indai an fito break.
       *         *        *
Kwanci tashi ba wuya a gurin allah, dan yau gashi su iyami na shirin fita daga j.s.s 3 Suna tsaka da zana jarrabawar su ta placement.
     Yauma suna hanyar dawowa gida beli ke cewa da iyami "kinji maganar da baba yai jiya ko" ta karashe zancen a kasalance.
Da dariya iyami tace "ke wallahi dadina dake bakya rabuwa da abin haushi, menene abin damuwa dan yace mu fito da mazajen aure, nidama jamilu ya takuramin wallahi"
    "Inke kinada jamilu iyami niwa nake dashi"
     "Kiyiwa kanki adalci mana beli maza nawa ke sonki, wallahi ko jiya saida ayuba dan zaki yaimin magana akanki, nibanga abnd kike so a gun namiji da ayuban baida shi ba, inai miki sha'awar aurensa beli koba komai yana sonki fiye da sauran samarinki"
   Shiru beli tai tana sauraron kalaman 'yar uwarta, hakika tasan iyakar gsky take gaya mata, amma ina ita zuciyarta tuni tayi nisan da bata jin kira, a sanyaye tace "allah ya za6a abinda yafi alkhairi"
"Ameen" kawai iyami tace danta lura belin bataso hirar tayi tsayi.
         *         *          *
"Maimunatu wato kedai bakya jin magana ko, to wannan shine karo na karshe dazan miki magana, gashinan kanwarki yau sati 2 kenan dakawo kudin aurenta amma ke kin tsaya ruwan ido da kwakwar tsiya, nabaki kwana 4 nan gaba ki fiddo mijin aure cikin manemanki, inko bahaka ba nizan za6o miki da kaina, tunda ke allah yayi ki mai kunnen kashi ce, tashi ki bani wuri konai ball dake " yana fadar haka ta mike da sauri dan tasan kadan daga aikin baban nasu ne yai ball din da ita.
  A dakinsu ta riski iyami tasa abinci a gaba tana jiranta, a salube tai sallama tana goge kwallar idonta, kan katifa ta fada tareda ci gaba da rera wani irin marayan kuka.
Iyami ce ta ringa lallashinta da bata baki akan taci abincin, dakyar ta daure tayi loma 4 tace ta koshi, jijiyoyin kanta sunyi rudu-rudu alamar ciwon kai ke dawainiya d ita, dan haka bayan iyami ta dan tsakuri abncin ta debo mata ruwa tareda bata panadol, jikinta yai zafi sosai tana 6arin jiki ta kar6a ta sha "nagode" tacema iyamin tareda jan bargon ta kuma rufe jikinta.
Bayan tayi bacci ta farka ne iyamin ta tsirata da tambayar wa takeso a samarinta, shiru tayi dan ita harga allah babu wanda zcyr t keso a cikinsu, idonta duk ya ciko d kwalla "iyami ranar wanka ba'a 6oyon cibi, n gaji nima da 6oyon abin a cikin raina, inaji kmr inban fadawa waniba zcyt zata iya bugawa" ta tsagaita tana shashsheka, iyami tai zugum kawai tana kallonta batare d tace komai b belin t cigaba "tun shekara 2 baya zcyt takamu da tsanani kaunar bukhar wanda har nakejin inbashi ba bazan iya zaman aure da kowane namiji ba, amma ni kaina nasan d wuya bukhar y amshi soyayyata sbd takun sakar dake tsakaninmu dashi, dukda haka zcyt bataimin adalci wajen daina sonsa ba, saima karuwa dayai, 'yar uwata ki taimakeni na samo soyayyar bukhar wlh inna rasa shi zcyt zata iya bugawa" ta karasa tana dafe kirjinta
     Cikin tausayawa iyami tace "karki damu insha allahu nai miki alkawari bakida miji sai bukhar,xan gwada tawa basirar akansa" rungumeta beli tayi tana kukan farin ciki.
          *         *          *
Iyami kam tasha kai ruwa rana tsakaninta d bukhar kafin y kar6i soyayyar beli, saida kyar da karfin addu'a tasamu damar hadasu, wanda iyanzu haka harshima ya turo nasa magabatan nema masa auren beli, an tsaida rana daya dai-dai dana iyami wato saura sati 3.
         "Karki damu kwana 2 kawai zanyi na dawo bawani dadewa zanba, kuma tafiyar nan danke zanyi maimuna, sonake n hado miki laifen  d ba'a ta6a yiwa wata 'ya ba a garin nan" bukhar ke wannan furucin bayan yaje suyi sallama da beli d nufin zashi cikin garin kano hado kayan lefen aurensu.
Murmushi tayi kawai ganin yadda kullum bukhar keson fifita a cikin 'yan matan garin "nikam daka barshi ma ko a nan k hado inaso, kai nake so ba lefe ba"  ta karashe d muryar shagwaba.
"Nasani maimuna sanin yadda kike sona yasa nima nake son n dage wajen nuna miki tawa soyayyar d karfin tuwo dana aljihu dan wani abinma saikin shigo daga ciki" ya fada yana kashe mata ido, rufe idonta tai dan kunya ma ita y bata dan haka tace masa "k ganka ko"
           "Na ganni me? Ai gsky n fada dan ranar d aka kawo ki gidana....."  Aibata bari ya karasa b ta juya gida d gudu tana ce masa "saika dawo" murmushi yai kawai dan kunyar beli b bakuwa bace a gurinsa, daga nan tasha ya nufa dan hawa motar kano inda zai hado lefen nasa a can.
           *          *          *
Tun ana kirga kwanakin tafiyar bukhar d jiran dawowarsa har an gaji d jiran tsammani dan yau satinsa 2 kenan d tafiya, wanda daya dawo d tuni bikin saura sati 1, iya tashin hankali beli t shiga wanda sanadin haka yasa t kwanta rashin lfy, ganin halin datake ciki yasa iyami itama cewa a dage nata bikin sai bukhar din y dawo dan bazata iya tafiya tabar 'yar uwarta a wannan halin ba.
Kimanin wata 2 kenan yau d tafiyar tasa, wanda yasan beli inya ganta bazai ganeta b, dan gaba daya tayi wani irin baki ta rame yau d lfy gobe babu, a haka ta takurawa iyami d cewa tai aurenta karta tsaya jiranta dan itakam jikinta n bata d kyar in bukhar zai dawo, suna cikin takaddamar abule kaninsu y fado dakin dasuke a guje kafarsa tayi bututu d kasa alamar yaci gudu, iyami ta kalleshi a fusace "ban hanaka shigo mana daki b sallama b, kuma karin iskanci ma yau harda wani shigowa a guje kamar filin sukuwa"
Yaron yana haki yake cewa "yi hkr yaya iyami dama lbr zan baku ynz muna wasa a wajen gdn mai gari wata mota mai kyau tazo ta wuce, muka bita d gudu muna ruge-rugen Ta6awa, koda t tsaya sai mukaga ashe bukhar ne y dawo a cikinta......" Aibai karasa ba beli t mike zaune "da gske kake abule? Yana ina ynz" take tmbyr sa d karfi.
Abule n cin gefen rigarsa yace "yana gidansu harda wata..." Bai karasa b ta figi zani a jikin kyaure tai hanyar waje d gudu, tana kaiwa kofar fita daga gdn t dakata ganin babanta d yayansu abdul na magana kmr d hargagi, suna jin motsi suka juya d sauri gaba dayansu wani irin kallon tausayi suke binta dashi, babanta ne yai karfin halin cewa "lafiya maimunatu ina zaki haka" d sauri t karaso batare d wata kunya b tace "baba ynz abule ke bani lbr wai bukhar y dawo, shine zani inji y zancen aurenmu" Baba kam tsabar tausayi har kwalla ya faki idonta y goge kafin yace "mushiga daga ciki maimuna akwai batun dazamu tattauna dake" jiki a sanyaye t juya sukai cikin gida.
"Ina babarku" ya fada yana kallon iyami d tafito itama d nufin bin bayan beli "tana madafi bari nai kiranta" ta nufi kicin dan kiran babar tasu.
            Tare suka karaso a lokacin harsun shimfida tabarma sun zauna, dan haka suma nemar guri sukai suka zauna, malam ne yai gyaran murya da cewa "inaso ku bani duk hankalinku d nutsuwarku dan hakan shi zaisa ku kalli abin a matsayin wata jarrabawa d ubangiji yai mana" y tsagaita yana kallonsu daya bayan daya saida y tabbatar d nutsuwar kowanensu sannan yci gaba "dazu mlm madu mahaifin bukhar y sameni a rumfar kasuwa yake bani hakuri d cewa wai bayan bukhar y tafi hado lefe birni anan y hadu d 'yar abokin mlm madun suka fara soyayya, ynz dai in takaice muku zance har sunyi aure shine suka zo gida gaida iyayensa".
        "Na shiga uku" beli tace tareda mikewa zumbur tana kallon kowa d kowa, iyami ma mikewa tai tareda dafa kafadarta tana tana bata baki, kawai sai ganinta sukai ta fadi kasa tana aman jini, gaba daya sukayo kanta cikin tashin hnkli, malam d abdul masu karfin halin yimata sannu, yayinda iyami da innarsu banda kuka b abnd suke.
"Lailaha illallahu muhammadur rasulillahi sallallahu alaihi wasallam" iya abinda beli tace kenan tareda fadowar wani katon gudan jini daga bakinta.
Kuka muka barke dashi wannan karon harsu malam d abdul kukan suke, a haka aka hada beli aka kaita gidanta n gsky, fadar tashin hnklin dana shiga ma bazai misaltu b, dan saida aka hadamun d rubutun dangana tukunna n fara warwarewa.
Randa akai sadakar arba'in din beli a ranar aka daura aurena d jamilu Nafseen, watanmu 4 a jigawa muka dawo cikin kano d zama sbd aiki daya samu a nan, bukhar kuwa tun daga lkcn ban kara jin duriyarsa b, ko yana raye koya mutu oho, abu daya na sani shine bazan ta6a yafewa bukhar abinda yaiwa beli ba........"
H.iyami n kaiwa nan t kuma sakin wani kukan mai cike d kewa d tausayin kai, kwalisa d md suma kukan suke dan harga allah labarin y ta6a zuciyoyinsu mutuka, musamman Kwalisa dayake ganin kmr shima inbai bi a hankali b soyayyar sa zata iya sheke chuchu kmr yadda t bukhar ta sheke yayar mamansa beli.
Da sauri ya nufi gurin h.iyami tareda rike kafafunta yana kuka "hajiya na tuba nayi kuskure ki yafemin insha allahu nai miki alkawarin saina nemo chuchu duk inda take na aureta......"

😳tofa ko Kwalisa zaici nasarar samo chuchu kamar yadda y ambata? Har ynz dai bamu kuma jin lbrn A.A ba damuka bari a bandaki rungume d gawar 'yarsa d matarsa.
Ina vocal ne?

Duk wadannan amsoshi dama wasu na cikin
ANA KUKAN TARGADE... 5⃣
Naku
Prince av
09032724001

Inason amfani d wannan damar wajen mika ta'aziyyata a wajen al'ummar musulmi bisa rashin 'yar uwarmu da mukayi ZAHRA'U BABA YAKASAI  allah y jikanki da rahama yasa kin huta, intamu tazo mukuma allah yasa mu cika da imani, ameen, ina barar salatin annabi 10 ga duk wanda y krnt lbrn nan allah y kaiwa anty zahra'u haske kabarinta dan girman najamul huda.fa! 1

No comments:

Post a Comment