Saturday, 10 December 2016

Mafarkin Abdoul 4th


MAFARKIN ABDOUL
©Safiyyah Ummu Abdoul
                       ٧.

Zaune take tana kwalliya,  murna ne fal a cikinta don grand  frère ɗinta Abdoul zai kawo mata ziyara. Sanye take da riga da skirt na material mai kaloli,  ɗinkin ya fito da surarta  ya bayyana asirtaccen kyawun da Allah ya mata. 
    Feshe jikinta tayi da turaruka fin kala biyar,  duk da kasancewarsu  masu saukin kuɗi sun fitar da kamshi mai daɗi da kwantar da hankali.
    Karfe biyu ya iso,  kiranta yayi a waya cewan ya iso,  yayin da ita kuma ta zura hijabinta purple kasancewar shine kala mafi karanci a kayan.
      Falon su tayi masa iso,  wanda ke fitar da sassanyar kamshin freshener irin na Larabawa.  Lumshe ido yayi sanda ya sa ka fara guda a cikin falon.  Kamshin da ya daki hancinsa ya sa masa nishaɗi,  se da ta kawo masa abin tarba sannan ta samu waje ta zauna.
    "yan mata"  Ya faɗi fuskarsa yalwace  da murmushi.
    "yayan  yan mata"  Ta faɗi tana maida masa da murmushi.
   Tsare ta yayi da ido yana neman abinda zai bambamta ta da halimar  da ke zuwa masa a mafarki,  mafarkinsa na jiya ya dawo masa inda yayi Wai  Halima ta haihu an samu Abubakar suna ce masa saadik .  Hure masa fuska tayi. Nan da nan yayi farka daga duniyar tunanin da ya shiga.
   "lafiya grand  frère"  Ta faɗi cikin yanayin damuwa.
    "Babu komi je  pense  à  ton  avenir (ina tunanin future ɗinki ne) "  Ya faɗi yana murmushi wanda kallo ɗaya zaka masa kasan iyakarsa fatan baki ne.
     "wani abun ya faru ne?"  Ta faɗa a ɗan firgice,  kallonsa  take cikin kwayar idonsa ko zata fahimci wani abun.  Ganin bata fahimci  komi ba yasa ta saukar da idonta.
     "abinda da Hammad  ya miki mana,  aka ce miki baya damuna ne.  Addu'a ta kullum  Allah baki miji na gari,  shekaru ashirin da biyu ai ba a ce da ke yarinya ba"  Ya faɗi ya na basar da damuwar da ta shiga kamar bai san tayi ba.
     "Au da ma Shine,  ai mun shirya kasan  na faɗa maka wancan yarinyar bacin biyan maza da take har da ɗaga wuya tana taɓa wa,  wai karamar yarinyar da aka rabu da ni yar jami'a saboda ita kenan"  Ta faɗi tana dariya kasa kasa.
     "don ta sha giya Shine me?  Ba hakan ya ganta ya ce yana so ba,  in ita giya tasha ke anya beyi gwajin takalmi da ke ba,  wani irin zuciya gare ki,  kina tunanin zai chanza ra'ayinsa ya aureki ne bayan tun farko ya nuna miki shi ba mijin aure bane,  haba Halima da hankalinki da komi kina bari so na sarrafa miki rayuwa,  oh ku ne masu bin na turawa da suke cewa 'everything is fair in love and war' Ko? Toh ki sa ma ranki cewa  rien est juste dans l'amour et la guerre (nothing is fair in love and war)" Ya faɗi a fusace,  tabbas  ta san gaskiya ya faɗi amma ya zatayi da son Hammad.  Kuka take mai hana sukuni ido ya sa mata duk da yana jin kukan har kahon zuciyar sa.  Sai da tayi mai isarta sannan ya fara lallashinta. 
        "Kinsan rayuwarki na da mahimmanci a tattare  dani,  kiyi hakuri kiyi tunani kinfi karfin Hammad in aka dubi halayya da kamala,  ki hakura tun yanzu kafin ya kara miki wani takaicin gaba. Ki kuma cigaba da addu'a Shine maganin komi"  haka yayi ta bata kalaman karfin gwiwa har ta sake.
    "Ana fa fama da zazzaɓin cizon sauro,  da typhoid ga tattalin arzikin duniya na cikin ha'ula'"  Ta faɗi tana mai sauya hiran.
    "Eh wallahi,  ko ina har fa Nijeriya kuma rashin tsaftar  muhalli duk ke kawo hakan fa"  Ya faɗi cikin halin ko in kula.
    "Ta ya kenan?"  Ta tambayeshi don bata fahimce shi ba.
    "sakacin mu yayi yawa,  ba ma gyara gwata a anguwanni,  bola ko ina,  ciyayi sun fito jikin gidaje,  amma son kai irin na mutanen mu yanzu ba'a gyarawa.  Sauraye  sun samu mafaka,  in ka gyara cikin gidan ka ai zaka fira waje,  kinga dole zazzɓin cizon sauro yayi yawa.
   Typhoid  kuwa yanzu kinga damina ne,  muna tara ruwan sama muna sha ba tare da an tafasa shi ba.  Tsakanin sama da inda ka tara ruwa ai akwai germs da zasu shiga.  Ko rijiyoyi  da suka cicciko kinga ai ko alam mutum yasa  dattin  zai kwanta kafin a sha."
     "wai yaushe ka fara aiki da asibiti ban sani ba.  Tunaninka  sak abinda ya ke faruwa.  Allah dai ya kare mu da lafiya".
     "Aameen ya rabbi" 
    Haka suka cigaba da hira yaje yai sallan la'asar ya dawo,  sai wajajen biyar na yamma yai musu sallama suka rabu.

   
MAFARKIN ABDOUL
©Safiyyah Ummu Abdoul
                ٨.
Yanda Abdoul ya tafi haka shawaran da ya bata ya bi ta gefen kunnen ta don kuwa sabon soyayya suka fara da Hammad,  duk tayi masa zancen aure yakan ba ta amsa da cewa "ai kawancenmu yafi soyayya  mahimmanci kar ki bari zugin  kewaye ya zama katangar  biyan bukatar zukatanmu"  a haka yake binta da daɗin baki har ta saduda.
   Ana cikin haka sai ya sauya salon soyayyar su ya zama hiran da suke na batsa ne,  tun bata sakin jiki har ta kware a sarrafa kamai da kan motsa sha'awar su wanda hakan yasa yakan bata kula na musamman. Sukan kashe awanni  suna waya har sai sun kai ga samun natsuwa,  wata rana  suna cikin irin wayar se ya ce mata
       "Baby ina so in na zo Niamey  zaki ɗan min wasu abubuwan da kike kwaɗaita min a waya"  Ya faɗi cikin sigar rarrashi.
      "Anya sweetyna  kana so na kuwa,  kasan dai bazan taɓa yin zina in saɓa ma Mahalicci na ba don faranta ranka"  Ta ce a fusace
    "wa ya ce miki zina za muyi ai kin wuce ayi aron hannu da ke,  wallahi  iyakarmu romance,  ba zan taɓa keta haddinki ba."  haka yai ta faɗa mata kalamai masu nuna aminci da yarda har ta amince.
    Washegari  kuwa sai gashi,  ta shirya da sunan zata shiga makaranta kamar yanda ya raɗa mata ta faɗi sai ga Abdoul  ya iso gidan babu sanarwa ya zo mata sallama za shi karatu Kasar Faransa.
      "haka ba ko ɗan notice"  Ta faɗi a zolayance
     "Na duba ne naga tabbas in ba wani kwakkwaran abu zai kaiki skul ba toh kina gida,  shi yasa kawai na ga gara in zo yau tunda tafiyanmu ta nuna zuwa France"
    "aiko da ka taka zero,  yanzu take shirin  shiga makarantar wai an kira ta"  faɗin haj Mas'ouda da ke shigowa falon.
     Kallonta Abdoul yayi alamun rashin yarda,  murmushin  yake ta sakar masa wanda ya tabbatar masa da zarginsa.
   "shin ina zata je tayi karya da makaranta" Ya samu kansa da tambayar kansa hakan.
    "Sai muje  mu dawo kawai momma" Ya faɗi ma Haj Mas'ouda yana murmushi
    "Toh a dawo lfy,  kaga sai kayi mata faɗan rashin tsaida miji,  ta lake ma Hammad wanda sam ba aurenta  a rayuwarsa."  Ta ce fuskanta na nuna alamun takaici.
     "Momma lokaci ne..."  gwaɓe mata baki da akayi ne yasa ta yin shiru.  Se dai a ranta tai ta surutun an sa mata idanu.
    Fita  sukayi tana tunanin yanda zasuyi da Abdoul don ya sauke ta a inda Hammad ke jiran ta.  Sake-sake kawai takeyi don har sun kai ga gate ɗin makarantar su sai wayarta ta ɗau kara.  Kafin ta ɗauka yai saurin ɗauka ya amsa wayar kana ya sa wayar a handsfree
   "baby ina jiran ki tun ɗazu,  na matsu naji ɗumin  jikinki"  aka faɗi a ɗayan ɓangaren.  Da ace  zata iya nutsewa a kasa da tayi don kunyar da ta shige. 
    "se dai kaji azaban wuta don ubanka,  kai rayuwar da ka zaɓa ma kanka kenan lalata yaran mutane toh Halima  tafi karfin ka kuma ka fita hanyar ta ko in wulakanta maka rayuwa"  bai jira amsar Hammad  ba ya figi motar zuwa gida.
     Haj Mas'ouda  ya zayyana ma komi nan ta fara kuka tana  salalami
  "Halima me yasa zaki ɓata rayuwar ki  haba nayi mamakin abin da yasa kika kasa rabuwa dashi ashe, ancen mahaifiyarki gsky ne da tace an gama kwakule ki.  Tir wallahi  da halinki"  Ta faɗi tana shirin tsallaketa ta wuce.
     Kafafunta ta riko tana rokon ta,  rantsuwa take mata akan ba abinda ya shiga tsakanin su asali ma wannan ne na farko nan dai  ta kwashe yanda sukayi ta fada musu.
     "Toh da kika tashi zuwa ki isko shi aka ce miki haka ne zai sa ya aureki?  Sai ma ya kara tsanar aurenki.  Kinga dai ni namiji ne,  duk macen da na lagudata  ta yarda ta aure ni wahala zata sha,  kuma haka duk wani namiji yake,  uwa uba ya sa ki a ɗiya mace to babu sauran mutunci tsakani.
    Zama ayi ta wayar batsa shi ke kai matasa ga aikata, zina,  kuma da yake ce miki turmi da taɓarya ne kawai zina ina ya bar ayar Allah da yace kada mu kusanci zina,  kinga kenan hatta karatun batsa,  zantuttukan  batsa,  kallon batsa ana iya danganta su da kananun zina,  kuma abin nisantarwa.  Halima ki ji tsoron Allah ki tsoraci kwanciyar kabari,  wuta gsky ne kuma azaban Allah  gaskiya ne.  Momma na wuce sai in na dawo" Ya karasa zancen yana mai da akalar zancen zuwa ga haj Mas'ouda. 
   Godiya ta bishi dashi da albarka da tayi ta sanya masa.  Nan ta bar Halima da bakin ciki da kunya.
  

No comments:

Post a Comment