Monday, 19 December 2016

Yar Ajinmu 2nd

'YAR AJINMU CE

PART 4,5,6

   4=
Bayan zufa ta gama karye man na
kalleta nace, Bintu menene ya
maidaki haka? Wasu hawaye naga
sun yima idanuwanta fitar burgi
sannan naga ta kara matsowa kusa
dani tana kallon idanuna kamar tana
nazartar wani abu a cikinsu. Kafin
bintu ta bani amsa na fara tunanin
rayuwarmu ta baya kadan
MARIAYAMOH AJIRI INTERNATIONAL
SCHOOL Itace makarantarmu kamar
yadda na fada tun farko, kamar kuma
yadda kowa ya sani wannan
makarantar ta kudi ce, makaranta ce
dake da hazikan malamai da kuma
dalibai. Ranar da mahaifina ya
kawoni aji daya a secondry din
makarantar ranar ne mahaifin bintu
ya kawota aji daya itama bazan ta6a
mancewa ba duk da muna yara
amma nafi bintu shekaru ko yaya ne!.
Ko a waccan lokacin nakai shekara
goma sha biyu bintu kuma zata kai
goma daidai hannunta rike da robar
swan water, ta rataya katuwar school
bag dinta kamar wadda zata koma
wani gari da zama tasha 'yar fingilar
hijabinta kayanta fes gogaggu, duk
da muna yara a waccan lokacin ban
mance wannan rana ba. Bintu itace
mutum ta farko da muka fara magana
da'ita a fadin makarantar lokacin tazo
neman ajinsu nima nazo neman
ajinmu muka tambayi juna?. Tun
kafin mu ba junanmu amsa wani
malami ya kiramu ya nuna mana ajin
da zamu zauna Daga nan labarin ya
fara Zanci gaba
     5=
Tun daga wannan lokacin da an fito
tara zamu haðu da bintu muna kashe
kudinmu tare na tara. har gidansu
aka san da abokinta wato ni. Muna
matukar kaunar junanmu duk da
kasancewarmu yara kanana a waccan
lokacin, Gidansu bintu masu hali ne
kamar yadda na fada a baya,
mahaifinta alkali ne mai zaman kansa
mutum ne mai gaskiya da sanin ya
kamata, Wannan yasa ya fuskanci
kalubale sosai a rayuwarsa
sanadiyyar aikinsa. Ba wannan ke
gabana ba dan kar na gundurar da
mai karatu, Haka-haka har muka
kawo Aji biyar a wannan lokacin ne
aka maida Jarabawa sai an bada kudi,
gidanmu babu kudin da za'a bada
nayi jarabawa wannan yasa na shiga
halin tunani da hanyar da zan nemi
kudin har tasa na fara fashin zuwa
makaranta. Ni mai mutane ne kuma
mai son karatu wannan yasa 'yan
ajinmu ke yawan zuwa gidanmu
kuma suna tambayata lafiya akan
abinda ke hanani zuwa makaranta
nakan ce musu mahaifiyata ce ke
batada lafiya amma zandawo zuwa.
Da wannan hujjar na rike dukkan
wanda zai tambayeni dalilin rashin
zuwana makaranta, amma sam ba
hakan bane!. Ba nida wanda zanje
wajansa ya taimakaman da kudi duk
cikin 'yan uwan namu. Bintu ce kawai
na fada ma matsalata ganin itama
bata 6oye man sirrin gidansu duk
wuya, Mahaifinta ta samu da
maganata akan tanaso ya biya man
kudin jarabawa kamar wasa tun yana
sharewa yana daukar zancenta na
kurciya har dai ya sa ta ta kirani
Zuwana gidansu bintu ne yai man
maganin matsala ta mahaifinta ya
biyaman kudin jarabawa nan take ya
dauki nauyin dukkan biyan kudin duk
wata dawainiya tawa, Ina kawowa
nan a tunani na sai naji hawaye
nabin fuskata Zuciyata ta yiman zafi
sosai bintu ce gabana tana bara
kyakjyawar bintu dana sani itace ta
koma baka hatta kayan jikinta sun
yayyage wani wajan ZANCI GABA
      6=
Na kara kallon bintu sannan na juya
na kalli waðancan sauran mabaratan
dake zazzaune suna jiran wanda zai
zo ya basu. Na juyo da dubana gareta
sannan na cigaba da tuna na
baya-"-"-" Tun bayan sa'adda
mahaifin bintu ya dauki nauyin biya
man kudin makaranta da duk
dawainiya ta sai na zama kamar dan
gidansu bintu kullum muna gidan
muna karatu, malami na musamman
mahaifinta ya samar mana a gida
yana kara koyar damu, musamman
ma da yaga lokacin fara jarabawar
fita yayi. Sannu-sannu kwana nesa
har muka gama makaranta tun daga
wannan rana ban kara ganin bintu
ba! Sa'adda nazo gidan mutanan
unguwar ke ce man ai sun tashi
sakamakon transfer da akai ma
mahaifinta zuwa garin Kaduna daga
abuja Shikenan rabuwarmu. Bintu ta
tafi bamuyi bankwana ba, a waccan
lokacin banida waya haka ma bintu
bata da waya,wannan ne sakacin
farko da mukayi mu duka nida ita!
Sun tafi sun barni da ciwo da
magagin da bazan sake ganinsu ba,
sune gatana na biyu bayan iyayena
mahaifiyar bintu ta daukeni tamkar
dan da ta haifa da cikinta. Kullum
mahaifan bintu kokarinsu su ga
matsalata su gyaraman Alkali mutum
ne da ya gama man komai a rayuwa,
A dan zaman mu dashi na fahimci
abubuwa da yawa game dashi,
mutum ne mai son karatu da mutum
mai kokari yana son yaga kana maida
himma akan duk abinda kasa a
gabanka Wannan yasa ban zama
raggo ba na mike ina jajircewa
saboda alkali yayi alfahari dani koda
wata rana, yasan baiyi kiwon banza
ba, akwai shakuwa da mutunta juna
tsakanin 'yan gidanmu da 'yan
gidansu bintu! Mahaifina shima
bayada waya balantana ace yana da
lambar wayar mahaifin bintu alkali
shikenan mun rabu da bintu na faða
a zuciyata Na kalli gidansu bintu ina
tuna dan zaman mu dasu hawaye
suka wanke fuskata shikenan bazan
kara ganinku ba, kun tafi bamuyi
bankwana ba idanuw

No comments:

Post a Comment