Thursday, 1 December 2016

KARNINMU 5


KARNINMU...

© FIKRA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA BIYAR

Bayan shekaru uku da rasuwan Juma malam Musa ya buge ɗakin ta ya haɗa da ɗakin zaure aka fitar da kofa ta cikin gida, don auren Yaro ya tashi, anyi shagali sosai amarya ta tare a ɗakinta,  duk da haka wasanni tsakanin da Luba bai chanza zani ba.

Haka Abubuwan sukai ta tafiya har lubabatu ta kai shekara goma sha huɗu a duniya, tun tana fargaban irin wasan da suke yi har ta fara sanin garɗinsa  ya zo in basu samu damar yi ba har kewa take yi.  A shekaran ne  yayi  nasaran shiganta,  ba ta wani sha wahala ba don ya daɗe yana kwak'ulanta, ranar ta dawo makaranta shi kaɗai ne a gida saliha da suke kira goggo Amarya da matarsa inna fatu sun tafi Mesira Kasancewar am aiko da rasuwan yayan Malam Musa da sukan taɓa zumunci dashi.
  Shi ya taimaka mata ta gyara jikinta sannan ya tsoratar da ita da cewa in ta  faɗi ko ta bari aka sani  za'a jefe ta ne har ta mutu. Tunawa da tayi da anyi ma matar Sale mafarauci yasa ta yarda.
    Duk da Auren da yayi Yaro kan biya bukatarsa sau biyu ko uku a sati biyu,  tun abin baya burge ta har ta zo ta saba,  sannu a hankali har yazo ya kan gayyato abokansa su kunna kallon batsa suna kwatanta abinda suka gani a ciki. Duk in sun gama yakan bata kwayoyin hana ɗaukan ciki.

Shiganta aji uku na sakandare ne ta gano cutar da ya ke mata,   tun daga lokacin ta dena bashi haɗin kai a daɗi,  wani lokaci yai amfani  da karfi, wani lokaci ya kuma da kanta take bashi haɗin kai yayin da jikin ta ke bukatar haka .
                   ***
  
Bayan ta kammala karatun sakandare ne ta shiga makarantar horar da malamai, a lokacin ne kuma wata irin natsuwa ta shige ta,  girma ya zauna mata ba abinda ta sa a gaba se karatunta na addini da boko. Yayin da shi ma Yaro matarsa ta sa masa ido sosai don neman matansa ya zarce har an fara kukan yana tare yara kwararo-kwararo. Malam Musa yai faɗa yai nasiha amma inaa sai yaro ya maida shi makiyin shi na sahun farko,  ba dai aji alkhairin sa a bakinshi ba.

Haka dai luba ta maida hankali har ta kammala karatun ta zama cikakkiyar malama, a hutun zaman jiran aiki ne ta maida waya abokin hiranta ta shiga dukkan  kafofin sada zumunta na waya,  amma ta fi jin daɗin WhatsApp kasancewar ya fi sirri da bayanai masu kayatarwa. Tun goggo Amarya na faɗa har ta gaji don kullum abin nata gaba gaba ya ke yi.

"Lubabatu ! Lubabatu"

Tun daga falo goggo ke k'wala mata kira, shiru har sai da ta shigo ɗakin  ta same ta cikin bargo. Filo ta ɗauko ta jefa mata, gami da zare bargon da ta rufe jiki dashi.

     Tashi ta yi haɗe da yin mik'a kafin daga bisani ta katse wayar da ta ke amsawa. Na wani sabon saurayin da ta haɗu dashi a Facebook

" Haba goggo na,  uwar da bata da Part two, mai kuma na miki kika kwaɗa min filo" ta  faɗa cikin shagwaɓa.

Girgiza kai goggo  ta yi haɗe da cewa

  "Kai yarinyar nan Allah ya shiryeki baki da aiki da ga ansa waya sai latse-latsen waya, nifa abin naki wallahi har mamaki yake bani ko gajiya ba kya yi, to ni ba wannan ba zan wuce makaranta don Allah kije ki ɗaurawa babanki abin kari, karki tsaya yin chating ɗin nan har ya tashi don Allah "

Murmushi ta yi sannan ta ce" Toh goggo na yanzu sallah zanyi sai na fita na je na ɗaura "

Rik'e baki ta yi haɗe da faɗin

" kina nufin 7:30 kina zaune ko sallah asuba bakiyi ba? Anya luba kin ɗau hanya madai-daiciya kuwa? gaskiya kiyiwa kanki faɗa wallahi"

Kunnenta duka biyu ta rik'e gami da cewa
"zan gyara insha Allahu goggona"

"Da dai yafi" ta bata ansa haɗe da buɗe kofa domin tafiya.

Wayarta ce ta yi k'ara alamar shigowan sak'o da ga whatsapp, da kamar bazata duba ba sai kuma zuciyarta ta umarceta da ta duba, umarnin zuciyarta tabi ta hanyan buɗewa, k'aramin ihun ta yi haɗe da fad'awa kan katifarta,

"kai wannan ɗinkin yayi, ai dole sweety ta haɗani da telan nan, hohoho za'a yak'esu wallahi, har na ganni a cikin d'inkin nan ho ni Luby" ta faɗa a fili.

Ta ɗauki tsawon lokaci ta na chating da kawarta, akarshe dai kawar ta ma ta alk'awarin had'ata da telan.

Sai kusan tara (9) saura ta ajiye wayar a gurguje ta shiga bayi ta yi wanka haɗe da ɗauro alwala, a gurguje ta yi sallah, tana idar da sallah ko addu'a bata tsaya yi ba ta wuce gaban madubi haɗe da tsara kwalliya, wasu kaya riga da wandon, ta ɗauko.

Rigar pink wandon kuma bak'i, ya matseta irin leggings  ɗin nan, kayan sun kamata k'warai, kuma sun amshi jikinta.

Taje gashin kanta ta yi haɗe da kamashi da ribbon sannan ta saka wani takalmi mai tsini, sai da ta feshe jikinta da turare masu k'amshi, kafin ta isa ga madubin da ke jikin bangon ɗakin na ta.

kallon kanta ta yi a madubi, juyi ta yi haɗe da ɗan sakin k'aramin k'ara, ita kanta tasan wankan ya amsheta.

Fita ta yi haɗe da janyo kofar  ɗakinta. Tafiya ta ke ta na girgiza duk wata sassan jikinta, cikin ɗan k'ankanin lokaci ta kammala haɗa abinda zasuyi kari da shi. Wainar fulawa tayi musu da kunun tsamiya.

Sai da ta tabbatar da kowa ya samu nashi kafin ta koma ɗaki. Faɗawa kan katifarta ta yi gami da janyo wayarta, a lokacin ta tuna jiya fa mijin Hajiya Aminan group ɗinsu na  MANYAN MATA ya dawo tabbas yau zasu sha labarin yadda abubuwa suka kasance tsakanin ma'auratan adaran jiya.

K'aran shigowan sak'on da ta dinga ji ne yasa ta ce
"na shiga uku an fara ba ni"

Ba tare da 6ata lokaci ba ta buɗe whatsapp ɗinta, kai tsaye group ɗin ta shiga wanda mafi yawancin y'an group ɗin matan aure ne.

   Natsuwa tayi tana karantawa har ta kai karshe,  duk hirarrakin akan yanda suka raya dararensu  ne,  da kuma bayanai akan salo salon kwanciyar aure da sauransu. Kiran da ya shigo wayarta ne ya dawo da ita duniya daga mafarkin ido biyu da ta fara wai gashi Mijinta na mata abubuwan da ta karanta.

   "sweety kin yi waya da telan ne?"  ta tambaye ta daga  ɗaga wayar.
  
    "Kinga luby tunda auren nan yaki yiwuwa ni fa zan bada kai ne,  wannan dadi da suke bamu labari kar ya wuce mu"  surayya  ta faɗi a ɗaya ɓangaren.

"kinga!  Ban ki shawaranki ba amma Zancen gaskiya ko ni da na rasa budurci na ban jin zan iya ba, ki yi hakuri aure lokaci ne"  Lubabatu ta faɗi a sanyaye.
Haka dai tayi ta bata kalaman kwantar da hankali.

Surayya kawar lubabatu ce da suka hadu a wani Group, sun amince da juna sosai har wasu da basu a Group din sanda suka haɗu ke musu kallon yan uwa.
Surayya yar Kasar Sarma ce dake makotaka  da Haurobiya , karatu ya kawo mahaifinta Haurobiya daga nan aka ɗauke shi aiki a nan cikin birnin Dunotsi.

Amma a kwana a tashi sai gashi surayya ta ci galaba akan lubabatu saboda yawan abubuwan da suke karantawa a groups na kuma koyar da su abubuwa da sunan kula da miji.
    Surayya tai amfani da muryan da Allah ya bata da surarta  ta ja hankalin mijin hajiya Amina, shi ya fara saninta ƊIYA MACE  hakan yasa ya zuba mata dukiya ba ko kaɗan ba. Duk ababen da Haj Amina ke koyar dasu a Manyan mata shi take kwatantawa Alhaji Nasiru. Nan da nan ya buɗe mata ido da kuɗi da manyan kyaututtuka.
     A ɓangaren Luba kuwa bata yarda gida an ɗago takunta ba har sai da tayi  zurfi don bata yarda ta zama karuwa kamar kowacce  ba, ta sha faɗa ma Surayya cewa "Nifa Kingani nan sai dai na zama sophisticated prostitute wacce zata zama yar rakiya (escort)"
   Surayya kan dauki Zancen ta a matsayin shirme har sai da ta ga yanda take juya manyan shuwagabannin  Haurobiya....

                 ***
"Hmmmmn!" lubabatu ta saukar da ajiyar zuciya tana kallon Malam Sadi,
      "Sanda mahaifi na ya tabbatar da abinda nake aikatawa har kwanciyar asibiti yayi, ban taɓa faɗa masa komi akan mafarin lalacewa na ba,  bai taɓa zagi na ba sai dai yana yawan min nasiha da addu'a kuma Insha Allah na kusa dainawa. Ku taya ni da addu'a sannan kada ku amince ma kowa da yayanku mata. Shi kawu Yaro da ya lalata ni ya fi kowa zagi na da aibanta ni" ta faɗi tana rushewa da sabon kuka.

"kiyi hakuri Lubabatu,  Allah miki Albarka ya shirye ki da Sauran zuria baki ɗaya. Allah ya jikan Juma ya saka ma Saliha da Aljanna, yanda Yaro ke Faɗin labarin gidan Mal Musa abin ba kyan ji, ashe halinsa yake faɗi tashi na raka ki lubabatu " Mal sadi ya faɗi yana share hawaye.

    Tare suka gangara zuwa gidan su lubabatu, ya sa tayi masa sallama da Malam Musa.  Nan din ma hakuri ya bashi da nasiha sannan ya nemi gafaransa don an sha zagin sa da shi.

Wannan shi ne mafarin zumuncinsu da Malam Musa.

               ***

Washegari da safe, Babban rumfar da ke bakin k'ofar gidan Malam Baso cike ya ke fam da almajirai, kowannan su rike da da allo sai kwala karatu su ke iya k'arfin su. Malam Boso na zaune a tsakiyar su.

Mota ce kirar taxi ta zo ta tsaya a gaban rumfar.  Malam Tanko ya fito ya na lalubar aljihun sa, ya na Faɗin

"Maza ku fito mana Muazze, Hamze a fito maza"

   Muazze da Hamze su ka fito a tare cikin hanzari su na mai mayar da kofar motar domin rufewa. Malam Tanko ya fiddo  kuɗi ya biya direba da tuni shima ya fito domin sauke kayan su Muazze da ke cikin but.

Ganin su Malam Baso ya taso da sauri ya na mai washe baki, dan kuwa Malam Tanko mutumin shi ne.

Malam Tanko na mai Faɗin "An zo birne Hamze, birnin Dunotsi kenan Hamze"

K'arasowar Malam  Baso yayi dai-dai da tashin direba, da fara'arsa ya k'arasa ya na mai mik'awa Malam Tanko hannu ya na fad'in

"Salama'alaikum,Malam Tanko an k'araso? an zo lafiya?"

  "Eh mun karaso lafiya lau sai godiyar Allah" fad'in Malam Tanko ya na mai yin musabaha da Malam Baso.

Ya k'ara da
"Ga Muazze an dawo makaranta, ga kuma Hamze ma wannan karan shi ma zai fara"

Malam Baso ya ce "Kai madallah, ai haka ya kamata, sunnun ku yara, Muazze an yi noma lafiya?"
     Sai a sannan Muazze ya durk'usa ya gaida Malam Baso, ganin haka Hamze shi ma ya yi yanda ya ga Muazze yayi.

Malam Baso ya amsa a takaice, sannan ya umarce su da su kai kayan su zaure in da su ka saba ajiyewa. Hakan kuwa aka yi.

Bayan shigan su Malam Tanko ya ce

"Na ce ya batun tsarin zaman karatu? ya nan yanda ya dai ke ko? Dan a hak'ik'anin gaskiya muna jin daɗin yanda Muazze ke samun ilimi, yaro har ya kusa sauka"

"Eh Toh! Malam Tanko mu koma daga inuwar can ko? sai mu yi maganar"

Faɗin Malam Baso ya na mai nuni da  wata bishiya da ta samar da yalwataccen inuwa can daga  gefan rumfar almajirai. Malam Tanko ya ce

"Toh bisimillah" duka su ka ɗunguma zuwa rumfar.

No comments:

Post a Comment