®
✏📖
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!(2)
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
GARGA'DI
KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.
1⃣0⃣
Sidiya ce....✍🏼
Ana gama wankan amarya Bintu ta ja jik’akken mayafin ta ta rufe fuskar ta tana mai shar6ar kuka. Ba tare da 6ata lokaci ba d’aya bayan d’aya sauran iyalan Sarki su ka dinga zuwa Jakadiya na gabatar da su, har su ka k’are sannan aka rufe taro da addu’a. Da aka gama maimakon a kai Bintu d'akin auren ta, 6angare ne na musammam cikin gidan Sarki, sai wani 6angare aka sake kai ta na daban daga cikin 6angaran Goggon nan wanda ya kunshi d’aki biyu kowanne da bayi sai kuma falo. Nan za ta zauna har sai sanda ta kai budurcin ta d’akin mijin ta. Za6in bawai d’aya daga cikin bayin ta wanda za su na kwana 6angaran ta aka bata. Gwaggo Munari ce ta za6a mata Ladiyo dan kuwa ta fi yabawa da hankalin ta, sauran kuma wuni za su na yi, idan lokacin bacci yayi ko kuwa Bintu ta sallame su sai su koma 6angaran da aka tanadarwa bayi.
Yarima Barde kuwa duk wannan bikin da ake masa ya na daga na sa 6angaran. Su Yarima Jafar da Khalil tun suna iya jure shirun da ya mu su har su ma su ka gaji su ka yi na su gurin. Da ya gaji da zaman ne ya watsa ruwa yayinda ya sanya jallabiya, kai tsaye in da ya saba zuwa duk sanda ran sa ya ke 6ace ya nufa, wato lumbun da yake k’yatare da 6angaran matan Sarki. Nan bisa dutse ya kusa raba dare, sai da ya ji idanun sa sun masa nauyi sosai sannan ya tashi a hankali ya nufi 6angaran sa. Ko da ya zo giftawa ta 6angaran da ya san babu shakka nan aka sauki amaryar da aka aura ma sa, sai ya tsinci kan sa ya na mai mummunar fad’uwar gaba. Hakan ya sa shi wucewa da sauri ya na mai ambaton ubangiji. Bakin kofar sa ya tadda dogarai da bayin sa sun yi jugum jugum kasancewar ya mu su hani da biyo shi, ganin sa su ka fara masa kiran lafiya su na mai fad’in
‘’takawa sannu Yarima Barde, lafiyarka dama da hauni, dama da hauni lafiya, salamun salamun’’
Ganin ya zo daf da shiga kofar da za ta sada shi da 6angaran sa, su ka taka masa baya, har ila yau fad’i su ke
‘’gicciye dama Yarima, gicciye salamun’’
Tsayawa Yarima Barde ya yi, ya d'aga mu su hannun alamar baya buk’ata su biyo shi kafin ya sa kai ya shige ciki. Ya bar su waje su na kallan kallo, dan kuwa sun san lamarin auren Yarima Barde kan su zai k’are duk da dai ba su suka kar zuman ba, rataya aka ba su.
Washagari da sassafe jama’ar Fabarusa, Samari da ‘Yan mata har da tsuffin cikin adon su na burgewa su ka yi dandazo kofar fada domin kallan hawan angonci bisa al’ada. Amma Yarima Barde ya yi k’yememe ya ki fitowa ko da kuwa kofar 6angaran sa ne bare a sa ran zai hau. Ko da su Khalil su ka je da numin bashi baki, a bakin k’ofa dogarawa ma su tsaran kofar Yarima Barde su ka fad’a mu su buk’atar Barde na kada a bawa kowa damar isa gare shi. Dan haka sai hakura su ka yi, Magatakarda ne yayi shela ga jama’a cewar Yarima Barde be shirya yin hawan angoncin shi a ranar ba, su yi hakuri sai zuwa ran da ya shirya za a sheda mu su. Da kyar kamar ba su hakura ba su ka watse, dan ba k'aramin cin burin hawan angoncin Yarima Barde su ka yi ba, kasancewa akwai k’auna tsakanin sa da Talakawa, musammam ‘yan mata da samari, Yarima Barde na su.
"Bayan hayaniyar kofar fada ta lafa, jama’a sun watse su Gwaggo Munari da sauran tawagar Sa’ayrasa su ka yiwa iyalan Sarkin Fabarusa sallama, an had’a mu su koma ta arziki sannan su ka d’auki hanyar komawar su gida S’ayrasa, in da su ka bar Bintu tare da bayin ta, wato Ladiyo, Hansai, lantana da Maman Cangwai a sabon Masarauta. Gwaggo Munari ce ta shedawa Iyalan Sarkin Sa'ayrasa irin tarbar da aka mu su da tarin dukiyar da Bintu ta samu. Gimbiya K’amariyya kuwa sai da ta had’a da kwanciyar asibiti. D’aya daga cikin bayin da su ka juyo ne ta isar da sak’on Lantana ga Yarima Nuhu. Sakon na cewa ta aikata komai yanda ya umarce ta, kuma komai ya tafi daidai. Tsabagen dad’in sak’on na ta har kyautar zani da kallabi ya bawa baiwar domin kuwa in har maganar hakan ta ke babu shakka hakin sa ya cimma ruwa.
Kwanci tashi. Bintu ta cika sati guda Masarautar Fabarusa, amma ko da wasa Yarima Barde be ta6a takowa in da ta ke ba bare ma ta san kalar fuskar sa. Gata kuwa ta na sha gurin matan Sarki, musammam Goggon dole da Uwarsoro ,domin kuwannan su burin su ace amaryar Barde daga ta ta ce, Maman Cangwai ce ke saka Bintu a hanya kasancewar ita ta gane manufar su ba lalle alk’airi ba ne. Ita dai ta bi kowa sannu a hankali. Goggon nan kuwa mulki da jin kan ta kad’ai ya fi k’arfin ta, shi Yarima Barde ba gaban ta ya ke ba, bare uwa uba matar sa.
🐫🐪🐫🐪🐫🐪
Good abu kam yayi naji dadin littafinnan
ReplyDeleteFrom Hausa Ebooks
Litafinan nasiyarwane
ReplyDelete