Tuesday, 19 September 2017

Bintu ɗiyar bayi ce (book 2) 14

®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!(2)
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

GARGA'DI

KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.

1⃣4⃣

Sidiya ce...✍🏼

Barde kuwa a nasa 6angaran komawar sa turakar sa har da amai. Hankanlin sa be kwanta ba sai da ya amayar da dukkanin abun da ke cikin sa. Abun da ya ke bashi mamaki be wuce yanda yaji dan adam ya na wari kamar na mushe ko kuwa ja6a ba, daga ganin shigar ta ya san baiwa ce sai dai ba irin kalar shigar bayin Fabarusa ba ne, ko koma baiwar wata masarauta ce dole ya sa a nemo masa ita a sallame ta daga cikin fada ta je ta nemi magani gyambon da ke jikin ta idan dai ba so ake kar shi har lahira ba. Da wannan ya sami mafakar rashin zuwa ya ga amaryar sa, yayi kwanciyar sa abun sa.

Washagari da sassafe Jakadiya ta je masa da karin kumallo na musammam bisa ga umarnin Sarki Abdulrahman. Wanda Yarima Barde ya san ba komai ba ne illa tambayar
‘’shin ka je wa matar ka?’’
Saboda haka ko da Jakadiya ta tashi tafiya sai Yarima Barde ya bata sak’o zuwa ga Gimbiya Fatima, ya na mai fad’in
‘’a shedawa Gimbiya Fatima, bayan gaisuwa da fatan ta na lafiya, ta saurari zuwan mu bayan fad’uwar rana, kada ta tsawaita buri ba ma buk’atar komai daga gare ta’’

Kalaman da Barde ya k’arasa da su be hana Jakadiya rangwad’a gud’a ba, dan kuwa ta san tabbas idan aka juri kai zuga gabas wata ran ta zo da ruwa. Ai kuwa ko da sak’on ziyarar Barde ya riski su Bintu, nan fa Bintu ta ga ta kan ta dan kuwa tun da safiyar Manman Cangwai ta shiga gyara ta da su turarukan wuta, tsimi ne da cukwid’i kai har da wanda ma ba a sa ta ba, domin fa Maman Cangwai ita ta na da nata manufar na musammam cikin ran ta na game da Bintu, sai dai sa6anin sauran ita kad’ai ke san Bintu da alkhairi.

In dan ban da fad’uwar gaba babu abin da Bintu ta ke, bini bini ta ke duba lokaci ta na mai fargabar fad’uwar rana da abun da za ta zo mata da shi na daga ziyarar Yariman Fabarusa. Haka kuma kaman nin wannan da ta gani cikin lambu be dena mata gizo ba, da za ta sami dama ko shakka babu ta na komawa cikin lambu ko Allah ya sa ya k’ara bayyana a gare ta.
Yarima Barde ma cikin zulumin had'u da k’anwar Gimbiya K’amariyya a matsayin matar shi ya wuni. Rana na fad’uwa ya shirya cikin shigar sa na saraki, biye da shi amintaccan bawan sa ne wanda ake kira Bakar namba, su ka nufi 6angaran su Bintu.

Lifaya fara kyal Bintu ta d’aura bayan ta sha turaruka na hayaki da humra. Ta na daga zaune bisa gado gaban ta na fad’uwa tsabagen fargaba ji ta ke kamar ta zura a guje. Maman Cangwai ce ta sa ta a gaba ta na ta jera mata bayanai tare da kashedi, fad’i ta ke

‘’kin san dai ke d’iyar Sarki ce ba d'iyar bayi ba, ki kasance mai rowar muryar ki a gare shi, ban da yawan surutu in dai ba ya zama dole ba, ki kasance gwanar iya kalamai duk san da zaki bud’i baki ki yi furuci, ki tabbatar kin tauna kin juya kan ta hito daga leban ki.........’’

Daga waje tun isowar Yarima 6angaran na Bintu warin nan da ya ji a lambu ya fara bakuntar hancin sa, hankalin sa ne ya fara tashi yayinda ya ji bugun zuciyar sa na dad’a k'aruwa. Cikin wannan hali ya yi tsaye bakin k’ofar falon Bintu, yayinda bak’ar namba ya shiga kwad'a sallama.
Ladiyo na mai amsa sallamar ta fito, ganin wanda ke gaban ta tsaye ta yi ta na duban sa. Sanye ya ke cikin fara Jabba wanda aka mata ado da koran zare, bisa babban rigar sa ce na dokakkiyar shadda fara kyal sai d'aukan ido ya ke. Haka rawanin da ke bisa kan sa irin na buzaye zuwa huffin da ke sanye cikin k’afafun sa farare ne kyal kai ka ce shirya shi aka yi.
Ganin ta saki la66a da su ga66a ta na duban Barde, ba ta da niyar motsawa bare ta kai gaisuwar ta gare shi, ya sanya Bakar numba fad'in
‘’hattara d’iyar talakawa! Yarima Barden Mahadi shi an gaban ki’’

Tuni Ladiyo ta zu6e k’asa jin buzun nan dai ba kowa ba ne illa mijin Bintu, fad’i ta ke
‘’tuba na ke Yarima, Allah ya huci ran Yarima, babban Barde babban bako’’

Shi kuwa Barde ganin tufar jikin ta ne ya dad’a d’aga masa hankali ba wai yanda ta masa ba, dan kuwa tabbasa wannan baiwar mai wari da yayi arba da ita cikin lambu a daran jiya irin shigar ta kenan. Idan kuwa haka ne to lalle d’aya daga cikin bayin matar da aka aura masa ne ke wannan mugun warin da ke neman halaka shi.
Bakar numba ne ya amsa da
‘’an gaishe ki d’iyar talakawa, ki shedawa Gimbiya Fatima Yarima Barde na neman iso gare ta’’

Da sauri Ladiyo ta tashi har tana hard’ewa, yayinda ta ke fad’in
‘’an gama ran Yarima ya dad’e’’
Ciki ta shige jiki na rawa,  ta tadda bayin da ke hidima cikin falo wanda k'atuwar muryar Bakar numba ya sanar mu su da isowar Barde, kowannan su ya nutsu jere cikin sahu, musammam bayin Fabarusa wanda dama sun fi na Sa’ayrsa sanin darajar Barde. Kai tsaye cikin d’akin Bintu Ladiyo ta shige ta na mai zubewa k’asa gaban Bintu dan kuwa ganin Barde ya sa ta tsorata da sa’a tare da nasarar da ke tattare da d’iyar bayi
‘’ran Gimbiya ya dad’e, Yarima Barde ya iso ya na mai neman iso gare ki Gimbiya’’

🐫🐪🐫🐪🐫🐪

No comments:

Post a Comment