Tuesday, 19 September 2017

Bintu ɗiyar bayi ce (book 2) 15

®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!(2)
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

GARGA'DI

KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.

1⃣5⃣

Sidiya ce...✍🏼

Jin haka hankalin Bintu ya tashi, cike da fargaba ta kai duban ta ga Maman Cangwai, wacce ta gane halin da Bintu ta ke ciki kana ta ce

‘’ki nuna masa hanya ya iso gare ta, ni da sauran bayi za mu tsaya daga wancan d’aki, ke kuma Ladiyo da ke  ku tsaya daga wajen kofa kafin Gimbiya ta sallame ki’’

Cikin rawan jiki Ladiyo ta tashi ta na mai fad’in
‘’an gama ran gimbiya shi dad’e’’
Ko da ta koma gun su Yarima Barde, Maman Cangwai ce ta fito da kan ta ta sallami sauran bayi zuwa ga d'ayan d’akin, duk da kuwa bayin Sa'ayrasa ba haka su ka so ba, su ma dai so suke su ga Yarima Barden nan da jama’a ke yawan ambaton sa wajan kyawu. Ladiyo a gaba, biye da Ita Yarima Barde ne in da shi kuma Bakar numb ya tsaya daga waje, su ka shigo falon Bintu.
Warin nan da ke d’aga masa hankali shi ya ke bunk’asa ya na dad’a bakuntar hancin shi duk sanda ya d'aga k’afa ya sauke a falon. Isar su tsakiyar falon Yarima Barde ya tsaya cak, ga mamakin Ladiyo ji ta ya furta

‘’gide bayi masu shiga irin ta ki nawa ne cikin wanga turaka?’’
Ladiyo na mai susa k’yeya yayinda ta shiga kame kame ta cikin fargabar kar dai ya gane ita ce mai bin bayan sa cikin lambu ta yi saurin fad’in
‘’iye na’am? Mu na da d’an dama ran Yarima Barde ya dad’e, wagga shiga ita an shigar bayin Sa’ayrasa, dukkanin mu wagga shiga mu ka yi Allah shi da ran Yarima’’
Yarima Barde na mai duban ta ya ke d’an tuntuntuni, dan kuwa ko shakka babu ya san wagga baiwa ta gaban sa ba ita ce mai warin da ya gani a lambu jiya ba, duk da dai be ga fuskar waccan da kyau ba amma ya san a jiki waccan tafi domin kuwa Ladiyo irin k’ananan matan nan ne. Shi kuma a yanzu be da buri da ya wuce ya gano baiwar nan da ke wari ko ya sami lafiya domin kuwa muddun ta na nan ba zai iya zama ko da na minti hud’u a turakar amaryar ta sa ba, abun mamaki shi ne ta yaya bayin Gimbiya kamar Fatima za su na zama da wari har haka ba tare da ta d'auki mataki ba? Hakan ke tabbatar masa da k'azantar da ke tattare da ita.
Juyawa yayi ba tare da ya sake tankawa Ladiyo ba, wacce ta yi kasake ta na duban sa ta rasa yanda za ta yi da ran ta, ganin dai da gaske ficewar ya ke ta bi bayan sa da sauri, amma ina kan ta cima su tuni ya d’au hanya, Bakar numba biye da shi. Da gudun ta ta dawo d’akin Bintu in da ta zu6e k’asa ta na kuka fad’i ta ke
‘’ki min rai Gimbiya, kwankwatsi ban san shi an Yarima Barde ba, aradu da na san shi na da ban bi bayan shi ba, in k’arya na ka yi aratta kashe ni’’

Cike da mamaki Bintu ta yane lifaya da ta rufe fuskar ta, tambaya ta ke

‘’gide lafiya? Yo to minana? Mi Yariman yay mi ki da har ya sanya ki kuka Ladiyo? Ina Yariman ya ke?’’

Ladiyo wacce duk a zatan ta Yarima Barde ya gano ta ne ran sa ya 6aci har ya juya ya fasa ganin Bintu ta ce

‘’ Yarima Barde ya juya ya koma, ki min rai kar ya sa a tsire ni, ina ni ina lek’en surrun Yarima Barde, ki taimaka ki min rai, wayyo ni Ladiyo sai kuma yanda aka yi da ni d’an daudu a kabari’’

Ganin dai Ladiyo ba ta da niyar bata cikakkiyar amsa ya sanya Bintu tashi ta fita da kan ta, ita ma Ladiyo bayan ta ta biyo wanda kukan ta ya sa sauran bayi fitowa. Maman Cangwai na mai tambayar ko lafiya? Ina Yariman ya ke? shin me ya fito da Bintu daga uwar d’aka ita kuma Ladiyo kukan me ta ke?
Kasa amsa mu su Ladiyo ta yi har sai da Maman Cangwai ta daka mata tsawa sannan ta iya labarta mu su yanda ta bi bayan Yarima Barde zuwa Lambu ba tare da ta fad’i jan  Bintu zuwa lambu da ta yi ba, yanzu haka ya gano ita ta ke lek’en asirin sa.

Cikin jimami kowa ya ke duban Ladiyo wacce ta had’a zufa, hawaye da majina. Ita kuwa Bintu waje ta samu ta zauna cikin neman mafita, dan kuwa muddin abun da Ladiyo ta fad’a gaskiya ne, ko shakka babu dole sai an hukun ta ta, lek’en asirin Yarima ba k’aramin laifi ba ne, za a iya amfani da wannan ace so ta ke ta idda wani mugun nufi kan sa ko kuwa dai ta ha’d’a baki da abokan gaba ta na san halaka shi.

Yarima Barde kuwa da fitar sa kai tsaye gun Jakadiya ya nufa. Ya tadda ta bisa sallaya tana lazumi kan ta zo ta shiryawa sarki sauwar dare. Ganin Barde ta san da matsala wanda shi ma be 6oye mata ba ya sheda mata cikin azanci ba tare da ya fayyace mata komai ba.
‘’ya Jakadiya, a had’a fanteka na turaruka, na jiki zuwa na kaya, a aika ga Gimbiyar Sa’ayrasa, a kuma sheda mata Yarima Barde ma’abocin k’amshi da tsafta ne, ta gaggauta sauya gimshikin kusurwar ta’’

Cewar Yarima Barde, wanda ya juya ya tafi ba tare da ya tsaya amsa tambayoyin da Jakadiya ke shirin jera masa ba. Abun da kuwa ya fi d'aure mata kai shi ne fantekar turaren da za a kai, ga kuma batun na Barde na Bintu ta gaggauta sauya gimshikin kusuwar ta, ko shakka babu Barde ya ji wari daga wani 6angare na Bintu ko kuwa bayin da ke tattare da ita.

Ba tare da 6ata lokaci ba Jakadiya ta aikata yanda Barde ya ce. Cikin baitul mali ta shiga, daga cikin daular iyalan Sarki Abdulrahman ta jido turarurruka fanteka guda, cikin bayi ta za6i wacce ta fi tsana sannan ta d'aura mata fanteka ta tere da bata sakon Barde zuwa ga Bintu. Jin sak'on da aka bata sai ga baiwa a k'asa ta na yiwa Jakadiya magiya da kada ta tura ta da wannan mugun aike, amma ina sai ma tafiyar ta yi ta barta ta na share hawaye dan kuwa dai ta ta ce ta same ta kishiya tara  rana d’aya.

🐫🐪🐫🐪🐫🐪

No comments:

Post a Comment