Tuesday, 19 September 2017

Bintu ɗiyar bayi ce 16

®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

GARGA'DI

KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.

©Khadija Sidi.....✍🏼

1⃣6⃣

Washagari kan Sarki ya zauna fadanci, yayi kiran Waziri da Hadiman sa guda hud’u, dan kuwa tun zantawar sa da Jakadiya, har ta kai shi ga d’akin Inna Salti Sarki be runtsa ba, shawarar Jakadiya ke masa yawo aka. Ai kuwa dai Waziri ma na’am yayi da shawara, a fad’ar sa ‘’karan ban shi an maganin zoman bana’’

Biyu daga cikin Mahadin Sarki su ne su ka banbanta batu, ana su zai fi ga kyau Sarki ya tsaya tsayin daka kan lamarin sa na gaskiya, dan ko da ba su ji ba, wanga magana hallo maganar mata ce. A wannan sanadin ne Sarki ya ce in su na biye da shi za su iya zama fada, in kuwa ba haka ba ya na mai d’aure su har sai hakin masarauta ya cimma ruwa, dan babu damar korar su daga fada su na amintattun Hadiman sarki, surrin fada babu wanda ba su sani. Da wannan su ka ja bakin su su ka yi shiru, su na mai Allah wadar da wanda ya bawa Sarki wanga shawara, dan kuwa Sarki idanu ya rufe madafa kawai ya ke nima, ya kuma sami bahaguwar madafa mai wuyar 6ullewa sai dai fa Allah shi kyauta da aikin dana sani.

Bintu na gyaran gadon Gimbiya Binta, ita kuma Gimbiyar na daga kishingid’e bisa tin tin ana mata danna. Sai ga Jakadiya ta shigo jiki na rawa daga gani kasan da magana a bakin ta. Bayi na ta gaishe ta, haka ma Bintu wacce tun shigowar Jakadiya ta ga ta kafe ta ido. Jakadiya na mai duban Bintu ta ce "ko da ban sani ba ke an Bintu’’

Gaban Bintu ne ya fad’i yayinda ta zube k’asa ta na mai fad’in ‘’Allah ya huci zuciyar Jadiya, Bintu na ke ba ki 6ata ba’’
Kallan ta ta ke cikin nazari, kafin ta juya ta dubi Gimbiya Binta, gudun kar sauran bayi su gane sakon da za ta fad'wa Gimbiya, sai cewa ta yi
‘’ta kan kwaba, ta kan kan ta, ta kan akwati mai taya, sai sid’if ta fad’a, sai sid’if na d’auka’’

Jin haka Gimbiya Binta ta saki k'awataccen murmushi, dama abun da ta ke jira kenan, kana ta ce
"zannuwa ishirin sun yi kad’an, aradu na k’ara mi ki goma har da kallabi goma’’
Jin haka Jakadiya ta rangwad’a gud'a ta na mai fad’in ‘’yaro wake tab'a mai uwa? Ba zai ci ba kayan kasuwa, sai ni Hindu jikar Baba Kilishi Jikar Nana, godiya na ke Gimbiya’’
Kana ta kai kallan ta ga Bintu ta ce "biyo ni yarinya’’

Gaba Bintu na fad’uwa duk dai ba ta fahimci zancen na Gimbiya da Jakadiya ba, ta bi bayan Jakadiya. Ganin haka wata Baiwa mai kaiwa Yerima Nuhu duk wani labari na game da lamarin Bintu ita ma ta ja kafar ta zuwa neman Yarima Nuhu, dan kuwa dai ita ma ba ta gamsu da wannan lamari ba.

Bintu na tafe bayan Jakadiya, ganin in da su ka dosa gaban ta sai faduwa ya ke, musammam da ta ga sun doshi turakar Sarki gadan gadan. Nan su ka tadda Sarki tare da Waziri da Hadimai, bayan su babu wani mahalik’i da ke wajan face amintaccen bawan sarki wanda ake kira Nahana. A bakin kofar turaka Bintu ta kasa d’aga k’afa ta shiga dan tsoro da kwarjini, tun da aka haife ta ko harabar wajan ba ta tab’a shiga ba, bare ace turakar sarki, ga ta ga sarki. Sai da Jakadiya ta d’an jawo ta, na mai mai mata shune da baki ta shiga.

Ganin ta gaban Sarki tuni ta zube k'asa ta na mai kwasar gaisuwa. Yau ga Bintu ga Sarki da waziri har da Hadimai, ko shakka babu dole k'awarta Cangwai ta ji wannan labarin.

Sarki zaune ya hakimce cikin rawani, ya dubi Jakadiya ya ce ‘’ba mu tarihin wanga d’iya’’

Zama Jakadiya ta gyara, kafin ta ce ‘’Allah ya ja daran Babban bijimi, wanga d’iya sunan marigayiya Baba Kilishi ta ci, hakan tsirar haihuwar ta da Gimbiya k’arama kwana d’ai ta, tare su ka tasa da Gimbiya k’ara, dad'in dad’awa makarantar su d’aya, bambacin su d’aya, wanga dai baiwa ce, kuma d’yar bayi, diya ce gun uwar bayi da kuma wannan bawa da ake kira Bala, eh Mahuta ba ,aradu ma kuwa’’

Waziri ya dubi Jakadiya ce ‘’ai fad'uwa ya zo daidai da zama, uban ta shi an babban bawa nai, ya ta ke da suna?’’

‘’Fatima, amma Bintu aka ce mata, kamar yanda ake kiran Gimbiya k'arama Binta’’ ta bashi amsa a takaice. Ita dai Bintu ta na nan kai durkushe daga can gefe amma daga tsakiya da ke ba shakka turakar ba dai girma ba, na gaske ma kuwa. Ko kwakkwaran motsi ba ta iyawa, bare ta d’an d’aga ido gudun kar ta had’a ido da Sarki, dan karshen kwarjini ya mata a yau da ta ke ga ta gashi.

‘’Fatima’’ muryar Sarki ta ji ya daki kunnan, tuni ta k’ara nutsuwa ta na mai rusunar da kai kamar wacce za ta shige k’ark’ashin k’asa. Ba mafarki ta ke ba, sarki da kan sa ya kira sunan ta, ina ma Cangwai ta na nan ta gani da idon ta, dan Idan ta ba ta labari sai ta ce k’arya ta yi.....tunanin da ta ke cikin ran ta kenan, jin Sarki ya ce
‘’a matsayin ki na baiwa a gare mu, shin akwai umarnin da za mu ba ki ki bi?’’
Bintu ta yi saurin duk’ar da kai ta ce "tir da bawan da bai bin maganar uban gidan sa, zan bi umarnin Mai martaba, ko da kuwa hakan zai zama sanadin rasa rai na, kwankwatsi ma kuwa’’

Kwalla na kad’ai Hadiman nan biyu ba su zibdawa Bintu ba, shi kuwa Waziri kai ya shiga kad’awa cike da gamsuwa, bare Jakadiya da ta ke ji kamar ta sab’a Bintu a baya tai ta rawa, Allah dai ya kawo mata tsuntsu daga sama gashesshe. Sarki na mai nazarin Bintu na wani d’an lokaci, daga bisani ya ce za ta iya tafiya. Ta na mai godiya ba tare da ta san abun da ake kullawaba ta fita.

Bayan tafiyar ta Sarki ya ce ya gamsu da komai na ta, amma ya na so Jakadiya ta sa ido kan ta na wani d'an lokaci kafin su gama zartar da hukunci. Da haka da haka har su ka wuce zaman fada.

Da yammacin ranar gaba d’aya walwalar Gimbiya K’amariyya ya dawo. Bintu na zaune gaban ta tana yanke mata farce wayar gida da ke aje d’akin ta ya fara k’ara. Cikin farin ciki ta d’aga, ganin haka Bintu ta tashi da niyar ba ta waje, amma Gimbiya K’amariyya ta d’aga mata hannu alamar ta yi zaman ta.

Maganar da Gimbiya ke fad’awa Yarima Barde ne ya bawa Bintu mamaki, ji ta yi ta na fad’in ‘’Takawa dai ya yanke hukumcin aurar da kauna ta Binta ga Mai Martaba Sarki na Fabarusa...’’

Gaba d’aya jikin Bintu yayi sanyi, cikin ran ta tausayin Gimbiya Binta ta ne ya kama ta, har fad’i ta ke
"Allah sarki Gimbiya ta ceto rayuwar ‘yar uwar ta, yanzu na gane dalilin maganar da sarki ya min, wato ina d'aya daga cikin bayin da za’a tura tare da Gimbiya Binta, kaiconi Bintu karatun mu kuma shikenan’’

Tausayin Gimbiya da ita kan ta shi ya gajiyar da ita ranar, ta kasa ta6uka komai har dare yayi ta koma gida.

Suna cin abinci da Inna, yau sun sami sauran biski daga gidan Sarki. Baba ya shigo babu sallama sai surutai ya ke kamar mahaukaci saban kamu, fad’i ya ke
‘’ta na ina ne wai ma?’’ ganin su a tsakar gida ya ja ya tsaya ya na mai fad’in
'’yo to ashe ku nan kusa ma’’

Inna ta yi kasake kafin ta ce ‘’Hallo Malam Lifiya? Yau ko sallamar babu?’’
‘’sallamar kenan ai uwar matar sarkin Fabarusa’’ cewar Baba ya na mai duban Bintu da sai saka lomar biski ta ke, hannu baka hannu kwarya. Inna na murmushin jin maganar Baba, ta ce ‘’Malam yau kuma raha a ke ji?’’

Cikin jadadawa Baba ya ce ‘’yo to wani raha bayan yanzu waziri ke sheda min, nan da d’an kwanaki za a tura a tsaida ranar bikin Gimbiya Bintu’’ ya k’arasa maganar ya na mai washe baki wanda daga Inna har Bintu sun kasa gane manufar dariyar ta sa.

Inna ce ta ce ‘’ayyo,  Gimbiya Binta ko? Ai yanzu haka maganar da mu ke kenan, Wallahi yanzu ta ke sheda min’’

Baba na mai duban Bintu ya kai mata dak’uwa ‘’ungo nan yar jakar uba!’’ baki cike da biski Bintu ta tsaya ta na duban Baba. Ganin haka Inna ta ce "Allah sarki, aradu ba munahinci ta yi ba, hira ce ta kawo maganar....’’

Cikin k’ulewa Baba ya ce ‘’yo to na gaji da wannan rashin fahimta ta ki Yagana, gide ina nuna mi ki annabi hallo ki na runtse ido, wannan(ya nuna Bintu da yatsa) ita za a amrar ga Sarki Abdulrahman na Fabarusa a matsayin d’iyar Sarki....’’ tuni Bintu ta kwarai, ta wanke Inna da biskin bakin ta tsabagen tari.

🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

No comments:

Post a Comment