®
✏📖
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
©Khadija Sidi.....✍🏼
0⃣7⃣
Babu shiri Bintu ta tashi da sauri, jin Mary na maganar sauko da ita ta ka ta san muguntar Mary za ta aika. Hanyar fita ta nufa ta na jera adduoi iri-iri, ta kama wannan ta saki, wani ma ko k’arshen shi ma ba ta iya kai wa. Su Gimbiya ma ba su yi k’asa a gwiwa ba, biye su ke da ita, ita dai burin Gimbiya ta ji shin da wa Bintu ta ke6e, idan kuwa Aisar ne sai na lahira ya fita jin dad’i, dan kuwa a daren ranar kwanan Sa’ayrasa ne ya kama ta.
Ganin Bintu ba ta jira ta k’arasa gabanta ba, ta na haki kamar zakanya ta fizgo ta, ta hard’e kafar ta sai ga Bintu zube gabanta cikin ca6al6alin ruwan sama "Rage tsinannan tsayin naki dan ubanki, shiyasa ki ke tunanin kin balaga kin isa ke6ewa da malamai." Fad’in Mary ta na mai shararawa Bintu mari. Bintu durkushe bisa gwiwowinta, hannunta bisa kuncinta inda hawaye ke gangarowa daga idanunta, fad’i ta ke ‘’Ina tuba Anty Marry, ki gafarce ni, kimin rai’’
Fili ya cika maki’il da d’alibai, kowa na fad’in albarkacin bakinsa, da masu tausayawa Bintu musammam da su ka san ita ba ‘yar kowa ba ce ta shiga hannun Marry, da ma dai ita d’iyar masu mulki ko sarauta ce da duk jarabar Marry sai ta saurara mata gudun abun da zai je ya dawo. Sai kuma masu mata Allah shi k’ara. Wani wawan mari da Marry ta dad’a kaiwa Bintu, sai ga Bintu a k’asa, sunkuyawa Marry ta yi, hannu bisa kan Bintu ta kama gashinta, ta fisgo ta cikin zafin nama, sai da Bintu ta runtse ido tsabagen azaba. Cikin rad'a ta ce "Ke da wani Malami ki ka ke6e a sashen karatu?’’
Idanun Bintu runtse, da kyar ta iya furta ‘’Ina tuba Anty Marry’’ Cike da mugunta Marry ta fizgi gashin Bintu kamar mai shirin raba gashin da fatar kan Bintu, wani kuka Bintu ta saki, sai ga kallabin ta hannun Marry, inda gashin da dama nad’e shi ta yi cikin kallabi ya warware, sai gashi ya sauka har gadon bayan ta. Ba Marry da su shedigyal ba, hatta sauran d'alibai sai da su ka yi mamakin kyawun gashin Bintu, da ke kullum kanta d’aure ya ke da kallabi, idan ba tsautsayi ba, babu wanda ta ke bari ya gani.
Sikanti ba ta san sanda ta ce ‘’Car uban nan, gide akwai mai irin wannan gashin cikin makarantar nanniya?” Shedigyal da wani bakin kishi ya rufe ta ganin gashin Bintu cewa ta yi ‘’Wannan har wani gashin azo a gani ne?’’
Marry kuwa da tuni ta yi mutuwar tsaye, hannun ta rik’e da kallabin Bintu, murmushin mugunta ta saki, ta na mai jinjina kai ta ce ‘’Sikanti ba ni aran almakashina ki.’’ Gaban Bintu ne yayi mummunar fad’uwa, ta d’ago idanunta da su ka yi jajur ta na mai duban Marry. Marry na murmushi ta gyad’a mata kai ta ce "Gashinki zan yanke muddin ba ki fad'a min da wanda mu ka ganki ba, bayan kuma kin fad’amin na kai bayin k’asa ki lashe kashin yan aji d'aya da su ka yi da harshen ki.’’
Wani sabon kuka Bintu ta saki, musamman jin Sikanta ta tura wata yar aji d’aya ta d’auko mu su almakashi. ‘Dalibai ta bi da kallo cikin neman d’auki, amma sam ba ta ga mai niyar taimakon ta ba, kowa na tsoran sa baki kada gobe idan an je wajan matemakiyar shugaban makaranta wacce ta ke mace ce, a ce har da su, suna ji suna gani a had’a da su. Idanunta ya sauka kan Gimbiya, ta watsa mata harara dan ita ko a jikin ta, Ita so ta ke ma a zo a yanke gashin Bintu ko ta samu ta ji wani Malami ne aka gan shi da Bintu, dan kuwa ta san tun da Bintu ba ta musa ba ko shakka babu da gaske an gan ta d’in ne.
Hankalin Bintu be dad’a tashi ba sai da ta ga an mik’awa Marry almakashi, yayinda ta tsugunna, ta sa hannu ta tattare gashin Bintu cikin hannun ta, wanda rabi kad’ai ta iya kamawa tsabar cikar gashin Bintu, tsakiyar gashin ta sai ta almakashin na ta, ta na mai fad’in ‘’Gide da wani Malami mu ka gan ki?’’
Bintu da ta za6i masifar da hukuncin Marry akan na Gimbiya, ta kasa bud'ar baki ta furta sunan Aisar, sai ta tsinci kan ta ta na mai fad’in ‘’Ki yi hakuri, ina tuba, ba zan k’ara ba.....’’
Jin sautin almakashi ya na ratsawa cikin gashin ta, da kuma sautin mamaki da ya fito daga bakin d’alibai ne ya katse amsar da ta ke bata, idanu runtse yayinda zafafan hawaye su ka zubo daga idanun ta, jin saukar jelar rabin gashin ta k’asa.
‘’Lah'ilaha'illallahu’’ Fad’in Iya Dije wacce dawowar ta kenan ta shigo dan ganin ko Bintu ta koma d’akin ta, ta tadda d’alibai sun yu da'ira, ta na kutsawa ciki Marry na yanke jelar rabin gashin Bintu. Da saurin ta k'arasa in da Bintu ke tsugunne gaban Marry, Shedigyal da Sikanti, ta yi saurin d’ago Bintu ta na mai fad’in ‘’Yo menene zan gani ni Dije?!! Gide wannan wani irin rashin hankali da zalinci ku ke yiwa yarinyar nan?!!! Gide akan wani dalili?!!! Gide wa ya ba ku wannan lasisin?!!’’ Ta shiga jera mu su tambayoyi kamar mai shirin taya Bintu kuka ta na mai duban gashin Bintu da su ka yanke.
Ba tare da nuna nadamar abun da ta yi ba Marry ta amsa mata da ‘’Kama ta mu ka yi ta ke6e da Malam Aisar....’’ Waje ya kaure da hayaniyar d'alibai, Gimbiya kuwa kukan kura ne kad’ai ba ta yi ba ta je ta shak’o wuyar Bintu.
Ran Iya Dije idan yayi dubu ya 6aci, kallabin Bintu ta fizge daga hannun Marry yayinda ta mik’awa Bintu ta na mai fad’in ‘’Gide daura ki koma d’aki, kar ki damu ni Dije sai na bi mi ki hakkin ki, aradu ma kuwa" A sanyaye Bintu ta karbi kallabin, har lokacin kuka ta ke, gaba d’aya kayan ta ya b’aci da ta6on ruwan sama da ta kwaso, kan ta sun kuye ta shige ciki. Bayan tafiyar ta Iya Dije ta mayar da kallan ta ga su Marry kana ta ce ‘’Ni Dije ni na ce Malam Aisar ya bar min sak’o wajan Bintu kasancewar ba zai same ni ba, kuma sak’on ba na kowa ba ne face sak’on Malam Hashim.’’
Wato daga Marry, har shedigyal da Sikanti babu wanda bai tsorata ba cikinsu, dan tabbas sun san matsayin Iya Dije gun Malam Hashim, da sun san da sa hannunta da ba su yiwa Bintu abun da su ka yi mata ba. Tuni idanunsu ya raina fata, cikin kame-kame Shedigyal ta ce ‘’Yetto Allah shi an sheda na hallau daliban nanniya su assheda na, yatsa ban kai ga jikin yarinyar ga ba, idan k’arya na kai aratta kashe ni."
Ko da jin haka Sikanti ma ta yi saurin d’age hannu sama ta na mai fa’d’in ‘’Balanta ni hallau Marry na rako’’ Marry kuwa da ta san k’iri-k’iri Iya Dije ta ganta tana yanke sumar Bintu, jikin ta ne ya hau b’ari, kana ta yi k’ok’arin jan Iya Dije gefe domin bata wani abu dan kuwa kowa ya san Iya Dije da san abun duniya. Amma Iya Dije ta yi kyememe ta k’i sauraronta, sai ma barin ta ta yi awajan ta yi tafiyar ta. Tuni makaranta ta d’auka gobe Marry za ta sha horo, har da masu shagali dan murna. Gimbiya kuwa duk da jin Iya Dije ce ta tura Bintu gun Aisar ba ta fasa mata bambamin wai akan me ya sa ba ta fad’a mata ba ita je a madadin ta tun da ta san ta na san shi, ko damuwa da abun da Marry ta yiwa Bintu ba ta yi ba bare ta saurara mata.
Da daddare Iya Dije ta kira Bintu ta na mai jaddada mata kar ta damu, ita za ta tsaya har sai an bi mata hakkin ta, ita dai duk abun da Iya Dije ta ce gaban Malam Hashim ta amsa mata da eh. Da ke Bintu mace ce mai yafiya sai cewa ta yi ‘’Dan Allah Iya Dije ki bar ta kawai ba sai kin wani bi min hakkina ba, Inna ta tace kowa yayi na gari dan kan sa’’
Iya Dije na mai girgiza kai ta ce ‘’Wagga gaskiya d’aita, amma wannan maganar ban barin ta ko dan rufin asirin kai na, aradu ma kuwa! Yo ki na tunanin idan shi Malam Aisar d’in ya ji bari zai yi? Abun da dai ya fi sauki ki yi yanda na ce kin ji ya?'’
Da wannan su ka yi sallama. Daren ranar Marry kuwa kasa bacci ta yi tsabagen fargaba, gashi ta cire wa d'iyar mutane suna, gashi duk abun nan da ta yi a banza tun da da sanin Iya Dije, babban tashin hankalin ta shi ne matakin da Malam Aisar zai d'auka idan ya ji abin da ta aikata. "Kar dai fa ace ita d’in sai an yanki rabin gashin kan ta!'’ Abin da zuciyar ta ke raya mata kenan, yayinda ta ke kwance bisa gadan ta, kowa yayi bacci ya bar ta. Sai shafa d’an gajeran gashin da be ma kai kamu d'aya ba ta ke, ta san lalle idan da za a cire shi duka ko kwatan wanda ta cirewa Bintu ba zai kai ba. Girman kai ya hana ta iya zuwa ta bawa Bintu hakuri ko ta sami rangwame, "Ni Marry gide tawa ta same ni kishiya tara rana d’aya’’ Ta fad’a a fili yayinda ta tashi zaune ta na mai d'aura hannu aka.
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
No comments:
Post a Comment