®
✏📖
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
©Khadija Sidi.....✍🏼
1⃣4⃣
Bangaren Gimbiya Kamariyya kuwa, tunda jakadiya ta sheda mata halin da ake ciki ta kasa samin nutsuwa, gaba d’aya ta fita daga hayyacinta. Washegari da safe ta na kwance bisa cinyar Gimbiya Binta ta na ta kuka kamar k’aramar yarinya, Gimbiya Binta ce mai rarrashinta. Wayarta ta shiga k’ara, da sauri ta duba, ganin wanda ke kiranta ya sa tayi sauran danna wayar ta kara bisa kunnenta.
‘’Yerima mun shiga uku, Yerima ya zan yi?’’
Muryar Barde kad’ai ta isa rikita mai sauraro, murya ce mai tattare da kwarjini, k’asaita da kuma nutsuwa. Duk da tashin hankalin da take ciki be hana ta runtse idanunta ba yayin da ta ji ya ambaci sunanta "K'amariyya.....’’ Sannan ya fara magana cike da k’asaita ‘’Ki kwantar da hankalinki, babu wanda ya isa ya auri matata, fad’amin shi wannan da ki ke magana akai wanene shi? Waye ubansa? Dan wani masarauta ne?’’
‘’Fabarusa, amma ba za mu iya jayayya da shi ba Yerima, sawun giwa ya taka na rak’umi....’’ Ta na magana ne cikin shasshek'ar kuka. Hankali kwance Yerima Barde ya ce "Fad’amin sunansa, dan wani gida ne acikin masarautarmu? Shin da me ya ke tak’ama haka ya tsoratar min da Gimbiya?’’
Ta na mai magana a hankali, dakyar ta iya furta ‘’Yerima Mai Mar-ta-ba ne.....’’
‘’Wanene Mai Martaba?’’ Ya tambaya a takaice. Jin haka ta san be gane in da ta dosa taba, ta ce ‘’Mai Martaba sarkin Fabarusa....’’
'Dif ta ji Yareima Barde, shiru kamar wanda ruwa ya shanye har sai da ta duba wayar dan azatan ta wayar ce ta yanke. Ganin be yanke ba, a hankali ta furta ‘’Yarima...’’
Dogon numfashi ya ja kafin ya ce "Akwai kuskure, babu wannan maganar, ki saurari wayata zuwa anjima.’’ Ya na gama fad’in haka ya katse wayar. Wani sabon kuka Gimbiya K’amariyya ta saka. Cike da tausayi Gimbiya Binta ta ke dubanta, cikin ranta kuwa ta k’udiri niyyar ceto rayuwar ‘yar uwarta. Ta na mai murmushi ta ce da Gimbya K'amariyya ‘’Didi kar ki damu, aradu sai na share mi ki hawaye, in har na kasa aratta kashe ni.’’ Sannan ta d'auki hanyar fita bayin ta na biye da ita.
******** *********
FABARUSA
Yarima Abubakar Abdulrahman wanda aka fi sani da Yarima Barde na Fabarusa, shi ake nufi da wannan kalmar kyau, dan buzu jikan buzu, shi ba sarki ba ya fi sarki iko da mulki. Fari ne sol, dogo mai k’irar nan ada ake danganta su da k’irar zaki. Ya na da faffad’ar kafad’a maji k’arfi da kumari. Sam babu alamar muni a tattare da shi, ya na da dogon hanci da ya zo daf da bakinshi, da manyan idanu mai rikita duk mai kallo. Bak’in gashin da ya sauko tun daga sajenshi ya zagaye fuskarsa, har zuwa saman bakinsa. Abun ku da buzu ya na da suma kamar balarabe, baki wanda yayi lub-lub kwance bisa kansa. Yawan sumar ya sa ba ya damuwa da aski, sai dai ya rage, hakan yasa idan aka gan shi akan yi zaton balarabe ne.
Yarima Barde bai da wata sutura da ya wuce farin tufafi, kullum tufafinsa fari ne k'al, haka zalika rawanin ko hularshi. Mutum ne mai tsafta, isa da k’asaita, wanda hakan kan janyo wasu da dama danganta halinsa da mai shegen girman kai. Shi ne na ishirin wajan mahaifinsa, inda ya ke da yayye goma sha tara, goma sha takwas mata duka suna gidajen mazajensu, da namiji d’aya Abdulkarim wanda ake kira Sadauki, tsirar watanni biyar ne tsakaninsu, shekararsu Talatin da biyu da haihuwa. K’annensa goma, mata biyar da maza biyar.
Kasancewar hali da ya bambanta tsakanin Barde da Sadauki, inda Barde ya ke da nutsuwa hankali da sanin yakamata, Saudauki shi ne shaye shaye, rashin tarbiya da bin mata. Hakan ya sa Barde ya zama mafi soyuwa wajen mahafinnasu Mai Martaba Sarkin Fabarusa, duk da kuwa da yawa ana lak’anta soyayyar d’an da mahaifin akan soyayyar da Sarki ya ke yiwa mahafiyar Barde ne ya shafi d’an na ta, duk da dai ba ta cikin fada, ko ince k’asar Nijar baki d’aya.
Cikin lambu ya ke zaune bisa katuwar darduma, tare da dogarawa uku wanda ke tsaye daga gefe guda. Yanayin da iska ke kad’awa da kuma yanda gayayyaki da furanni su ka yi koreshe shi zai tabbatar maka da daminar bana ta yi kyau a masarautar Fabarusa.
Sanye ya ke cikin farar shadda dinkin yar shara, ga farar hular shi da ta sha kari karkace bisa kan sa. Tunda ya aje wayar Gimbiya K’amariyya ya kasa motsawa daga in da ya ke. Dogon numfashi ya saka, ya na mai k'in gasgata abun da ya ji daga Gimbiya K’amariyya, kasancewar ba ya nan sa’in da Sarkin Sa’ayra da tawagarsa su ka ziyarci Fabarusa.
Ganin ya yunk’ura da niyar tashi, Dogarai su ka yo kansa da sauri, yayin da d’aya daga cikin su ya matso gaban Yarima ya aje farin takalmi gaban sa, su na mai fad’in "Hattara dai magajin Sarki, hattara salamun Yarima’’
Cikin k’asaita ya zura k’afafunsa cikin takalmin, Dogarai su ka rufa ma sa baya, ba su fasa fad’in
"Lafiya salamun Yarima, lafiyarka dama da hauni, dama da hauni lafiya, salamun salamun’’
Isar su bakin kofar lambu, da ke kufar ba ta da tsayi sosai, ga Barde da tsayi mashaAllah. Dogarawa su ka ce "Shafi bisa Yarima, sunkuye salamun’’(ma’ana Badde ya dan sunkuya kada ya bugi hular sa).
Da fad’ar haka Barde ya d’an sunkuya, sai gasu sun fito daga cikin lambun. Duk in da su ka gifta sai ka ji ana mik’a gaisuwa. Shi kuwa ko kallo ba su ishe shi ba, Allah Allah ya ke ya isa ga turakar Sarki, sai dogarawan ke amsa masa gaisuwar, haka kuma ba su basa fasu nusar da shi ba ta hanyar kiran lafiya, duk san da su ka yi arba d abin da zai iya tuntu6e da shi, ko wanda zai iya 6ata shi kamar danshi, ko gidan tururuwa ko rami, sai ka ji su na ambaton
‘’Hattara salamun Yerima’’
Haka har su ka kai ga turakar sarki, in da su ka tadda Jakadiya daga bakin kofa. Ganinta Yerima ya tambaya Sarki shi kad’ai ne zai iya ganinsa? Da ke Yerima Barde dan gaban goshin Jakadiya ne nan da nan ta masa iso. Kai tsaye ya shige yayinda sauran dogarawan su ka yi tsaye su na jiran sa daga waje.
Da shigarsa ya tadda Mai martaba hakimce, k’ishingid’e bisa wata k'atuwar dadduma da aka yi da fatar rak’umi, yayiwa hannun sa na hagu majingini bisa wani k’aton tintin mai zanen tambarin masarautar fabarusa, hannunsa na dama rik’e da k’aton jarbi ya na ja.
Kyakkyawan tsoho ne mai kimanin shekara tamanin a duniya, shi kanshi Barde be k’ara ganin tsufar mahaifin na sa ba sai yanzu da ya gansa sanye cikin farar jallabiya, furfura fal bisa kansa, amma ace ya nemi auren yarinya yar shekara ishirin, wanda ya yi jika da ita, kai har tattaba kunne ma! Gaskiya dai maganar nan da kuskure.
Zancen zucin da Barde ke yi kenan yayin da ya zube gaban Mahaifin na sa ya na mai mik’a gaisuwar sa. Amsawa Sarki yayi, tare da fad’in "Barde da wani abu ne?’’
"Barde ya dukar da kai kasa, kana ya ce
‘’Allah ya ja zamanin ka, shin za a taimakawa masarautar S’ayrasa ne?’’
Sarki na mai murmushi ya bashi amsa da
‘’Tabbas za mu taimaka musu, amma fa sai sun ba mu dama’’
Barde bai gushe ba ya k’ara tambayar Sarki
‘’Allah ya taimake ka, tunda su ka zo gare mu, ai sun bada damar kenan, Allah ya taimaki Sabkawa.’’
‘’Ba su ba mu dama ba, kila dai za su bayar, amsar ta su mu ke jira’’
Sarki ya amsa a tak’aice. Jin haka Barde ya rusunar da kai, kana ya ce "Allah ya d’aukake ka ranka shi dad'e shin wata dama ce wannan?’’
Sai da wasu d’an dak’ikai su ka wuce, kafin Sarki ya bud’i baki ya ce
‘’Ba wata dama ba ce, illa kulla aminci ta hanyar kawar da gaba har abada. Mu na son tabbatar da amincin Sa’ayrasa, kafin mu fidda tsagwaran dukiya wajan taimaka musu, don haka mu ka yanke hukuncin auratayya tsakanin masarautarmu da ta su’’
Gaban Barde ne ya fad’i, cikin ransa ya na mai nanata "Dagaske ne kenan, innalillahi wa innailaihi rajiun!’’ Sarki na mai dubanshi, ganin yanayin da ya shiga ya ce
‘’Mu na sauraran Barde, akwai abun da ya kamata mu sani ne?’’
Nan da nan Barde ya nutsu, ya na mai 6oye halin da ya ke ciki ta hanyar yin nauyin baki ya ce
"Babu Allah ya ja da ran Mai martaba, Allah ya tabbatar mana da alkairinsa’’
Cikin nuna jin dad’i Sarki ya ce
‘’D'an mu ya gama magana, mun san a koda yaushe kai mai amincewa da hukuncin mu ne ba tare da ka tsananta bincike ba, shi ya sa ba mu da haufi akanka. Wannan lamari alkhairi ne ga masarautar mu’’
Jikin Barde kamar wanda aka d’aure, zuciya sark’ak’e ya yiwa sarki sallama. Kai tsaye na shi sashen ya nufa, in da ya ji zazza6i na neman rufe shi tsabagen 6acin rai.
******* ********
Sa’ayrasa kuwa, Gimbiya Binta na fita turakar Sarki ta nufa, in da take da tabbacin za ta sami Jakadiya. Ta ko yi sa’a ta same ta ta gama shirya Sarki kenan, ya fita ran gadi. Zaune ta ke farfajiyar turakar sarki, ta na cin goro. Ganin Gimbiya Binta gabanta, ta shiga mata kirarin da ta saba mata
‘’Ture a ga tsiya, a kalla ruwan ido ya tsiyaye, tanka ka lalace, shiga d’aki bakin ciki ya kashe ka, ta Amale(Sarki) kin fi darbejiya d'aci, mai san zama da ke ya tambayi hali.’’
Gimbiya Binta na mai murmushi ta d'agawa bayin da su ka taka mata baya hannu, ma’ana su ba ta waje, nan da nan su ka koma da baya, yayin da Jakadiya ta mata tayin ko za su shiga daga ciki ne? Gimbiya ta ce rariyar ma ba laifi. Sabuwar shifid'a Jakadiya ta mata, In da Gimbiya ta ke tambayar shin ya lafiyar Takawa?
Jakadiya na mai girgiza kai ta ce "Bijimin Duniya ana wani hali, damuwarshi ta kai matuk’a, abinci ma ba sosai ya ke iya ci ba, fari da batun tsohon banza na Fabarusa shi ya sako shi gaba Gimbiya’’
Gimbiya Binta na mai duban Jakadiya ta ce ‘’Jakadiya, halin da mai martaba ya ke ciki zai iya illata shi da ma iyalan sa baki d’aya, kuma watsi da lamarin Fabarusa barazanar rasa rayukan talakawa ne, domin za su ga Takawa ya fi san iyalan sa akan talakawan sa, wanda hakan ka iya kawo rabuwar kai a wannan masarauta ta mu, kuma ko shakka babu k’udirin abokan gaba Masarautar Fabarusa kenan’’
Jakadiya na mai jinjina kai ta ce
"Sadak’ata Gimbiya, wannan batu na ki na yarda da shi’’
Gimbiya Binta ba ta gushe ba, ta nisa sannan ta k’ara da
‘’Masarautarnan kaf, babu wanda ya kai Jakadiya kusanci da sarki, yanda ya yarda da ke babu na biyunki, ke ki kasan Takawa, ke ki kasan cikin Takawa, shi ya sa ake kama k’afa da ke kan lamarin Takawa, gani na zo da shawara da kuma neman taimako daga gare ki, ban sani ba ko Jakadiya za ta amince da ni’’
Jin haka Jakadiya ta jefa kan ta baya, ta saki wani irin dariya mai k’ara kafin ta fara yiwa kan ta kirari kamar haka
‘’Sai ni Hindu Maryamu, jikar Baba Kilishi, jikar Nana, ban fito ba sai da na shirya ko a lahira rago ake duka dan bantan uba, lokacin iska akan ci 'ya'yan tsuntsu, kuci bayan gaban da k’aya’’
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
No comments:
Post a Comment