INA ZE KAI MU
Safiyyah Ummu-Abdoul
7.
Wata rana ina kwance ya shigo, lokacin duk na tsani auren da shi kan shi. Ji nake da za'a bani daman kashe mutum ɗaya toh Mustapha miji na zan kashe.
"Kin bi kin sa damuwa a ranki, ni dai kin ganni nan ko kotun koli za ki kai kara ta ba zan sake ki ba, aurenmu mutu ka raba ne wallahi. Ga wannan ki shak'a zaki manta duk wani damuwa" Ya ce da ni yana mai cusa min faudar da ke rike a hannun sa setin hanci na. Ba musu na ja numfashi na kaɗan don a lokacin ban wani tunanin komi se ta samun mafita ko da hakan na nufin karewar rayuwata ne.
Shak'ar farko na so na k'ware, sai da na gama tari sannan ya ce in sake shak'a. Take na fara ji na sama, ina ganin sa biyu-biyu, ina auno rayuwa mai daɗi. Ban iya tuna komai ba har sai karfe goma na dare.
Ciwon mai sosai na ke, da kyar na kai kaina ɗakin Mustapha, dariya ya sakar min irin dariyar muguntar nan.
"Welcome on board wifey" Ya ce a shakiyance.
"Kaina! Kaina!! Kaina zai fashe, ya min nauyi" Na ce masa ina hawaye.
"Au na manta fa Novice ce, zo ki sha wannan zaki samu barci. In kin saba da er fauda ba abin da zaki na ji sai izza da ganin kowa bai isa ba. Ba na so a na kawo miki wargi ne" Ya ce yana haɗa magungunar tari wajen uku a kofi ɗaya, ya sa cokali ya jujjuya sannan ya bani na sha. Ba musu na kwankwaɗe duka, ban san ya akayi kofin ya bar hannu na ba.
Barcin nan sai da nayi ta na awa 72. Na farka wayam ba tare da wani damuwa ba. Na rama sallolin da ake Bina inda Mustapha ya ce min ai kasaru zan yi saboda ai barci tafiya ce. Ban Musa ba don na tabbatar da shi mai so na ne tun da ya yaye min bakin cikin da ke rai na.
Haka na jero su biyu-biyu, asuba kuma na yi ɗaya duk a ruwayar Mustapha. Na idar da sallolin na zauna cin abincin da ya kawo min nan ne abubuwa su ka fara dawo min ɗai-ɗai, kama Mustapha da nake da mata da kuma tabbatar da shi ɗin ba kowa bane sai celebrity ɗin Facebook amma ko kwalin sakandire din shi ba zai kai shi ko ina ba. Nan fa na shiga cikin doguwar tunani da ban ma san Mustapha ya shigo ba har ya daɗe a tsaye.
"Haba Baby zaki kashe kanki ne? Na sama miki mafita amma duk da haka, ni kin san kalar damuwar da ada nake da, amma yanzu da taimakon Wa'innan duk ya zama tarihi. In ba kya so ne sai in ji, in kin mutu wa yayi asara" Ya ce cikin fushi ya fice daga ɗakin. Ban ɓata lokaci ba na sake kai ma. Ciki na wasu kayayyakin aiki.
Da haka tun ban saba ba har na saba har na k'ware na so na fi Mustapha iyawa ba. Tun da ga lokacin sanwar gidan ya chanza, don Mustapha cewa yayi
"Zulfaa in baki ci mai kyau ba lalacewa zaki yi kuma ba zaki zama kwaruwa ba sai in ana ganin ki fresh kuma yar lukuta. Nan babu shegen da zai raina miki wayau" da kalaman nan yake cika min ciki da kayan daɗi.
Gaba dai har aka zo lokacin zaɓe , nan kuma yan siyasa suka same ni, zan hau saman stage ko gidajen rediyo ko talabijin in zage gwamnati mai ci. Na tara masu mabiya fiye da tunani saboda in na tafi high duk karyar da ya zo min faɗi nake.
Wata rana gwamnati mai ci ta gayyaci Mustapha ta bashi makudan kuɗi akan ya hana ni maganar tun da sun gayyace ni na ki amsar gayyata a cewar bana cin amana. Haka ya zo min da waya a hannu yana mai nuna min alert.
"Kinga zulfaa kuɗin nan ya ishe mu rayuwa, don Allah ki bar abokan hamayya haka nan in ba haka ba wallahi zan sa ki a faifai toh, kin san duk abin ki dai na fi ki mutane na fi ki shahara sannan ke macece abu kaɗan zn fadi a kanki ki tsani kanki, sannan kin san duk matasa zaune gari banza sun fi bibiyan Facebook da sauraran radio ko Yoh ina su ka gani ba" dariya nayi ma ishi sannan nace
"Toh wa zai ga biliyan 200 sannan ya bi ta yan adawa, ka ga ce da su zan fita ga yan jaridu in faɗa ma yan Nijeriya mugun halin ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa. In ce a da ina tare da su yanzu na bari" Na faɗa masa kai tsaye. Bai Musa ba sannan bai yi wata shakka ba, take na sa ya min transfer ta biliyan 50 na ce ya Riki saura.
Cikin sati gwamnati ta sa aka shirya hira da ni a kafafen radio ta kasa da jihohi. Sannan ta min kyautar mota kirar Marsandi da ta fito a shekarar ga makudan kuɗi ta akawu.
Ana gobe za'ayi na tura ma kawata kuɗin nan akawun dinta da ke Kasar Dubai biliyan ashirin, na tura sauran akawun din yaya na da ke Belgium duk a sunan su rike min amana.
Saura sati ɗaya zaɓe na hau kan sifiku da Kasar zasu ji gaba ɗaya, sannan wasu kasashe ma zasu ji. Tun da ga wakilansu masu ɗaukan rahotonsu.
"kamar yanda kuka sani Sunana Zulfaa Zakari da aka fi sanina da sarauniyar yakin zaɓen jam'iyyar adawa, a yau zan fara da faɗa muku dalilin da ya kamata a ce kun zaɓi shugaban kasa mai ci da kuma gwamnonin jam'iyyar su.
Kun san yanda harkan luwaɗi yayi kamari a Kasar nan toh ba komai bane dalili sai don samun goyon bayan wa'inda kuke shirin zaɓa a matsayin shugabanni.
In kuka yi la'akari da wannan hirar zaku ga da sa hannun gwamnati mai ci a yanzu, sun samu miji na bayan kasancewar sa kawali a gare su ban san ɗan daudu bane a gare su sai shekaran jiya inda na kama shi da wani qusa suna luwaɗi yayin da sauran na zaune har da yan qololuwa. Sun bukaci da na yi shiru sannan na fito na bayyana ma duniya bakin halin adali mai son talakawa na jam'iyyar adawa. Sun tura min kuɗi na dukan kuɗi makudai da ya kamata a ciyar da talakawa bayan bugun farko da suka tura ma miji na biliyan ɗari biyu.
Ko da ace sun yi nasarar kashe ni kada ku yarda ku zaɓi azzalumai ba kashe ku kaɗai za su yi ba za su tabbatar da dukkan yaranku maza sun zame masu yan daudu... " ɗauke ni da akayi tun daga kujera ta nan na lura da yan jarida sun fara ja da baya. Wasu na guduwa.
" Wai ke ce? Ya ilahi ko dai fatalwa ce ba an ce an kashe ki ba" cewar Afreen
"Tabbas kuwa haka ne an kashe ni" Ta ce tana share hawaye
No comments:
Post a Comment