Tuesday, 19 September 2017

Bintu ɗiyar bayi ce 11

®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

©Khadija Sidi.....✍🏼

1⃣1⃣

Bayan Bintu ta ci abinci, ta watsa ruwa, Inna ta shiga ta same ta kwance ta na hutawa. Ganin Inna ya sa ta tashi zaune, Inna na murmushi ta ce "Gide na aza kwana ki ke(na zaci bacci ki ke)’’

Kai Bintu ta girgiza mata, cike da farin cikin yau ga ta da Innarta, ta ce ‘’A falke na ke Inna (ido na biyu Inna)’’ Nan ta zauna kusa da ita in da ta fara mata tambayoyi game da makaranta kamar dai yanda ta saba. Jin Bintu ta ce komai lahiya lau, bai hana Inna fad’in ‘’Ki dai k’ara hakuri da takwarar ta ki, na ce dai lafiya lau ku ke zaune ko?’’
Da har Bintu za ta fad’a mata halin da ake ciki, sai ta fasa don kuwa ta san halin Inna da sa abu a rai, sai cewa ta yi ‘’Lahiya lumi.”

"Ngla zauro, Ala barraaz3( da kyau Allah ya yi albarka)" Fadin Inna ta na mai dafa kan Bintu. Bintu ba ta gushe ba ta yiwa Inna tambayar da ya tsaya cikin ranta, ta ce
‘’Inna me ke faruwa ne?’’ Kai Inna ta girgiza sannan ta ce ‘’Wannan annobar ta duk shekara ita ta sake bayyana Bintu.’’

Gaban Bintu ya fad’i ta na mai dafe k'irji ta ce ‘’Fari?’’(Annobar yunwa, sanadiyar k'arancin ruwan sama)

‘’Aradu ma kuwa, wanga ma ai tafi ta kowacce shekara, talakawa mu na cikin wani hali, dussa ma da za a bawwa awaki gagaran mu yake, hatsin da ki ka ga ina tankad’ewa na gidan sarki ne, Allah ya sa ya shigo ta hannuna, na sami dussar ko ba komai ma sami na karin kumallo, na dare kuma ma ci ragowar babban gida.’’ Cewar Inna.

‘’Innalillahi wainna ilaihi rajiun’’ Fad'in Bintu kenan yayinda zufa ya shiga keto mata. Inna na mai girgiza kai ta ce ‘’Abunda mu ke ta fad’a kenan ‘yar nan’’
kana Bintu ta ce ‘’Yo to Inna me zai hana mu nemi taimako wajan sauran masarautar? Ai na ga ba laifi k’asar mu dai akwai abinci ga taimakon juna’’

Inna ta ce ‘’Uhum ina ne ba a nema ba? Su ma ai sun gaji, yau da gobe ya wuce gaban wasa ai, ridda karya kuka tatsa’’ Zuciyar Bintu d’aya ta furta ‘’Fabarusa fa.....’’

Da sauri Inna ta doke bakinta, hannun Bintu bisa bakinta, Inna na mai zare ido ta ce ‘’Kul ashirni zanne(rufa min asiri), shiga uku takabar sarakuwa!(sirika) Kar ki sake ambatan yankin ga dan Allah, kin manta bakar gabar da ke tsakanin mu, ahir ba da ni ba saka lallen kaza!’’

Ajiyar zuci Bintu ta saki tare da fad'in "Yo to Inna ai dalili ne ke sa a kama kaluluwar sarakuwa...(Dalili ke sa a kama kaluluwar sirika)"

Inna na girgiza kai ta ce "Na ce ki bar maganar ga Bintu, ba na kwawarniya shiga rumbum k'ore."

Ta na mai jinjina kai ta bar maganar, fatanta Allah ya kawo musu d'auki, Inna ta amsa mata da amin. Ranar har Bintu ta kwanta ba ta ga dawowar mahaifinta ba, dama dai idan ana cikin fari har kwana ya kan yi can fada.

***** ******
Washegari da sassafe, Bintu na bacci wata baiwa daga babban gida ta yiwa Inna sallama. Inna da ta yi  zatan kiran na ta ne ta ce ‘’Allah sarki, hallau kun ji ni shiru ko?’’

Jin haka baiwa ta ce ‘’Gide kiran ga ba na ki ba Uwar bayi, wannan kira na Bintu ne daga Gimbiya Binta’’

Kafin Inna ta bata amsa, mahaifin Bintu ya fito a fusace, in da ya hau Inna da fad’a ‘’Yanzu ki na nuhin(nufin)  wanga d’iya ta na nan ta na kwana(bacci) har k’arfe bakwai na safe ba ki tashe ta ba tsabagen lalacewa! Yagana anya kuwa?’’

Cikin sanyin murya Inna ta furta ‘’Ayi hakuri na ga jiya ta dawo shi ya sa...’’

‘’Yo to da hakurin ya mutu nawa ki ka biya kud’in sadaka?’’ Jin haka Inna ta ja bakinta ta yi shiru, ba ta ankara ba sai ganin Baba ta yi ya shige d’akin, haka kuma be fasa fad’an da ya ke ba, har ya iske Bintu ta yi d’ai-d’ai ta na baccin ta cikin kwanciyar hankali. Be yi la’akari da rabon da ya sa ta a ido watanni uku kenan ba, ya rufe ta da fad’a da zagi. Ita kuwa Bintu kamar a mafarki ta ke jin muryarsa, a hankali ta bud’e ido, ko da su ka had’a ido cikin magagin bacci ta furta ‘’Baba?’’

A fusace ya yi mata dak’uwa ‘’Baban ubanki! Hegiya kin saki la66a da su k'a66a ki na ta kwanan asara! Tashi maza ki wanke ido ki tahi babban gida!"

Nan da nan Bintu ta wartsake, ta na mai raribar hijabinta, ta ce ‘’Yi hakuri Baba, jiya na dawo ban ganka ba.....’
‘’Yo to ai gashi kin ganni, yar tselan uwa mai kama da kuliya’’

Ko a jikin Bintu haka ta fito Baba na biye da ita, dan kuwa idan da sabo ta saba, dan ba dan Baba shi ya haifeta ba da sai ta ce ya ma tsane ta ne gaba d’aya. Har yanzu mita Baba ya ke, ita dai Inna d’auke kan ta ta yi, ta shiga wasu sabgogin gaban ta. Baba ne ya ce da baiwa mai jiran Bintu ta je ta ce ga Bintun nan ta tafe. Ta na fad’in ‘’Madallah’’ ta kama hanyar ta tafi.

Buta Bintu ta d’auka ta kewaya bayi, da ta fito ta sa dakakken gawayi da gishiri ta wanke hakoran ta, sannan ta wanke fuska. Baba da ke tsaye gefe ya na jira ya ce ‘’Maza kama hanya ki yi gaba’’

‘’Malam na ce a bari ta yi karin kumallo ko?’’ Fad’in Inna cike da nuna damuwa’
‘’Kayya! Wani kari kuma Gimbiya ta yi kira? Ke rabu da ita, idan kin dawo kya yi karin, wuce ki tafi’’ Cyewar Baba.
Silifa ruwan d’orawa ta sanya a k’afar ta, har za ta fita Inna ta ce ta tsaya su tafi tare. Amma Baba ya ce babu wannan maganar, karshen ta ma ya yanke hukuncin raka Bintu da kan sa. Haka ya sa ta ta gaba, ya na biye da ita, duk wanda su ka gani a hanya sai ta tsaya sun gaisa da Baba, a haka har ya kai ta ga  filin sukuwa, sanna ya juya ya koma gida.

Tafiyar Baba ke da wuya Bintu ta hangi Yerima Nuhu tare da tawagar sa bisa doki, ganin su ya sa Bintu d'aga k’afa ta na mai adduar Allah Ya sa kar su cimma ta, amma ina Allah bai amsa addu'arta ba, domin kuwa ganinta ya sa Yerima dukan bayan dokinsa da dorinar hannun sa a hankali, hakan ya sa dokin k’ara sauri haka tawagar ta shi wanda ya kunshi abokan sa guda hud’u, nan da nan sai ga su gaban Bintu su na mai tada k’ura yayinda su ke jan linzamin dawakan dan su sami su tsaya.

🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

No comments:

Post a Comment