INA ZAI KAI MU
Saura za su zo a comments, Saura kuma a sace ko a ciren suna
DAGA ALK'ALAMIN SAFIYYAH Ummu Abdoul
safiyyahjibril@gmail.com
Kowane k’arni kan zo da cigaba, yana d’aya daga cikin cigaban da muka samu a namu k’arnin hanyar sada zumunta, a karnonin da su ka gabata mutum kan yi tafiyar kwanaki, makwanni, watanni har wani sa’in shekara don kawai ya sada zumunci da wani makusancinsa, a hankali aka samu motar hawa, zuwa jirgin kasa har aka k’era jirgin sama duk don sassauta hanyar zumunci, fatauci, neman ilimi da sauransu.
Karni na Ashirin da d’aya ya sassauta hanyar sada zumunta inda ya kawar da sauran hanyoyin kamar su wasika, garmaho, da sauransu ta hanyar kawo mana kafofin sadarwa da zaka yi Magana da makusancinka ko da kowannenku na kowane ‘bari na bangon duniya ne. Cikin dak’ik’u zaka isar da sak’onka kuma a aiko maka da martini, hakan ya kawo saukin harkan kasuwanci, da kuma yad’a ilimi ko da kuwa ilimin na banza ne.
***
Sunana Afreen Aliyu, ina da shekaru goma sha takwas a duniya, na kasance ‘yar auta a gidan Sheikh Aliyu Yasin, gidanmu kasancewarsa gidan Malanta ya kara sa muka taso cikin tarbiyya da ilimin Addini don kuwa kaf a yayyi na goma babu wanda bai yi haddan Alkur’ani ba kuwa. Ina da shekara goma sha hud’u na haddace Alkur’ani sannan na d’aura Tafsirin Jalalyn cikin ikon Allah a cikin shekaru biyu dai dai da kammala karatun sakadare na sauke wanda hakan ya sa ina d’aya daga cikin ‘ya’yan mahaifinmu da suka sauke littafan tafsiri fiye da Uku. Farincikin hakan ya sa Mahaifi nay a siya min waya kirar Samsung Galaxy.
“Afreen kinga shar abinki, zan ce a saka ki a shafukan k’aruwa” Fad’in Fadila. Fadila kawata ce da muka kammala karatun sakandare tare da ita, ta mallaki waya tun muna aji hud’u a sakandare kuma tun a lokacin mukan shig shafukan sada zumunta kamar su Facebook, Instagram, da Whatsapp. Duk a wayarta muka bud’e shafi a Facebook da Instagram amma gudun kar a gane mu a gida muka bud’e da sunaye mabanbanta da sunayenmu na asali.
“Ina na Facebook ai, kinsan murnar da na ke yi yanzu shine ba zan dinga tsallake fatawowin mutane akan magungunar da suka siya ba, kin san in mun tashi aure ba wanda zai fad’a mana gara mu ji daga garesu” nace ina juya idanu na.
“Ai Kawas whatsapp nake nufi, Jiya Hajiya Maryam Mallaka ta kar’bi lambobinmu ta bud’e wani zaura a whatsapp wai Matsalolin mata (Matan Aure only) kuma na bada lamba har an saka ni, in gaya miki ce musu nayi ina da aure da ‘ya’ya hud’u a wajen gabatarwa” Ta karasa nuna kashewa. Ba tate da ‘bata lokaci ba na yi rajista da Whatsapp, nan fa Fadila ta dinga rok’an masu kula da zauren da take son saka ni akan a saka ‘yar uwarta, hakan kuwa akayi.
***
Wata uku da fara Whatsapp d’ina na kula na rage ibadu na, sallah har sai an idar a masallacin gidanmu ban yi alwala ba, don sam bana so darussan da mata ke yi akan rayuwar aure da kuma koyar da kwanciyar aure su wuce ni. Da dare kuwa sai in kai karfe d’aya, don akwai wasu da basa fitowa sai cikin dare, wasu kuma sai sun fito daga turaka zasu bada labarin abin da ya faru sannan suyi sallama.
A kwana a tashi na ji duniya babu wanda nake so sama da mijin Hajiya Yalwa, saboda irin yanda yake tafiyar da ita da kuma bayanin surar sa da take mana wani lokacin har turo hotunansu tare takeyi
No comments:
Post a Comment