Thursday, 14 September 2017

Ina ze kai mu 4

INA ZE KAI MU
Safiyyah Ummu-Abdoul

                 4.
Tun daga ranar ban wani damu da na gaida ta ba, don cikin abin da ake koyar da mu ko mahaifanmu ne su ka k'i gaskiya jininsu ya halatta. Sannu a hankali sai gani tsundum a cikin su don barin gidan mu nayi ban ma kowa sallama ba. Ganin sun same ni da kyau sai aka fara koya min ta'addancin har ya kai ga mu ake turawa kasuwannin kauye mu sato 'yan mata da matan aure don sun saɓa ma addinin musulunci sun fito daga gidajensu ai cewa akai kada su fita a qur'ani wato inda Allah maɗaukakin sarki ya ce "... WALA TABARUJA TABARUJNAL JAHILIYATIL ULA..."

***
Akwai wani fita da za'a yi, sai ameer ya kira ni ya ce

"Kai abu sufyan, dole ka nemo Alkunya, ka ga Joseph da Simon da suka  yi mubaya'a shekaran jiyan nan sun sake suna 'ABU TALHA da ABU YASIR kuma na shigar ma su da sunan su ina ga har kuɗin su ya shiga" jin ya ambaci kuɗi ya sa a ce

"Abul Hussain" Nan ya ɗaga ni sama yana faɗin "ka yi wayau. Don duniya mutane da dama za su so ka ko don Albarkanci Sayyadi Husaini RA" .  Nan ya ja ni wani ɗaki mai cike da kwamfutoci. Mutumin da ke zaune a kan kwamfutar rike ya ke da kwalbar giya, nan na ga ameer ya buɗe firij din ciki ya dauko na sa kwalbar ya kurɓa. Ganin kallon da na ke masa ne ya ce

"Ba abin da Allah ya tsana sai kafurci, sannan sai mata su dinga yawo su na jawo alfasha. Ka ga muna taya shi yakin haka muna da ga jikin mujahidoon wa'inda wuta Sam baya taɓa su. Zamu ji daɗi a duniya sannan a qiyama muna da babban rabo" zancen sa ya shige ni kwarai. Har nake ganin toh da wannan mu ka tsaya ɓata lokaci.

Nan ta ke na saman kwamfutar ya bukaci da in taho, hoto na aka ɗauka sai na ga an sauya an kara min duhu da girman idanu, hakan sai ya sa ba duk wanda ya sanni ba zai gane ni ba.

"Duk sanda bukatar yin faifai na bidiyo ya ta so kada ka yi a ko ina sai ɗakin nan don fuskanka zai rikide zuwa wannan ne" bamu tashi a wajen ba sai da na ji sakon dollars dubu biyar, ban fito daga mamaki ba sai ga wani daga wata kasa. Kafin faduwar rana na samu miliyan ɗari da yan kai.

No comments:

Post a Comment