®
✏📖
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
GARGA'DI
KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.
©Khadija Sidi.....✍🏼
1⃣5⃣
Ko da Jakadiya ta kai ga aya a kirarin ta, ta na mai duban Gimbiya Binta ta ce fad’i in ji, in dai cigaban Babban biji ne sha yanzu magani yanzu. Jin haka Gimbiya Binta ta waiga kudu da arewa, gabas da yamma sannan ta dubi Jakadiya ta ce
‘’bangon gidan ga kunnuwa gare shi Jakadiya’’
Jin haka Jakadiya ta matsawo kusa da Gimbiya Binta, ta amsa da ‘’oh toh toh, bari na matso kusa kar iska ta kwasa ta kai d’akin o o da o o yan bantan uba’’ kunnan ta tafitar daga lullub’in ta, nan Gimbiya Binta ta shiga zayyana mata buk’atun ta, ko da Gimbiya ta gama, Jadiya ta ja da baya ta na mai fad’in
‘’Timirin katauje ba sai da kwandala ba, da kwandalar ne da yafi dama dama, haihuwa babu ciwo sai ka ce fitsari? Gwara ma fitsarin kayi yau da gobe, haihuwar da babu ciwo sai kace ruwan famfo? Gwara ma ruwan famfo ka yi murd’e murd’e’’
Gimbiya da ta gano in da Jakadiya ta dosa, ta na mai kallan gefe da gefe, kusurwa kusurwa gudun kar a jiyo Jakadiya, ta ce ‘’ kar ki ji komai Jakadiya, ina mai tabbatar mi ki idan har ki ka fad’awa Takawa wannan shawara sai ya mi ki babban kyauta, dadin dad’awa kuma ni ma mai mi ki kyautan zannuwa shirin ce, kuma hajjin bana har da ke, aradu ma kuwa’’
Jin haka Jadiya ta ce ‘’yo to menene, dan dai d’an wannan lamarin da be taka kara ya karya ba? An gama ran ki shi dad’e, yau d’in nan ma kuwa’’
Gimbiya na mai jin dad’i, babu shakka tarkon ta ya kama tsuntsuwa ta yiwa Jakadiya sallama, ta bar Jakadiya ta na Allah Allah ta ga dawowar sarki, dan kuwa dai bana kakar ta ta yanke sak’a in dai batun Gimbiya Binta mai yiyuwa ne, ga zannuwa da zuwa hajja, wannan shekara dai ta zo mata da kyau.
******
Bayan an idar da sallar Ishai, kamar kullum Bintu tare da su Innar ta zaune tsakar gida bisa tabarma su na shan iska. Tun da su ka zauna Bintu ta tsurawa zoben hannun ta ido, gaba d’aya ta rasa kwanciyar hankali.
Inna ce ta ta6o ta tana fad’in ‘’ba da ke ake magana ba Bintu?’’ Bintu ta yi firgita ta dawo cikin hayyacin ta "eyee? Na’am?’’ cewar Bintu ta na mai duban Inna da Habibu da su ka kafe ta da ido suna kallan ikon Allah. Inna na buga hannu a iska ta ce ‘’yo to ba na fad’a ma ba, ba ta san ka na yi ba Habibu’’
Habibu na duban Bintu da ta sunkuyar da kai, har lokacin hannun ta be bar kan zuben ba, ya ce ‘’Inna kin sa halin ta, akwai damuwa da damuwar wasu, yanzu haka babu mamaki lamarin Babban gida ke damun ta, ko ta ce rashin lafiyar shugaban k’asa.
‘’mtsw wahalar da rai fushi da makwafci’’ cewar Inna ta na mai nuna Bintu da yatsa ‘’ki je ki d'aurawa kan ki ciwo akan wanda ba su san da ke ba bare su san ki na yi’’
Bintu ta dai ba ta ce komai ba, ita kad'ai ta san irin fad’uwar gaban da ta ke fama da shi. Ita dai adduar ta Allah ya sa alkahiri ne yanayin da ta ke ji.
***** ****
Babban gida kuwa, Jakadiya ba ta yi k’asa a gwiwa ba, bayan ta gama shirya sarki cikin shirin bacci, Sarki na daga shingid’e, kafin ta raka shi wajan matar da ta za6a ma sarki kwana gurin ta ne ta ke bawa Sarki shawara akan lamarin da Gimbiya Binta ta sheda mata, ta k’are maganar na ta da
‘’watsi da al’amarin Sarki Abdulrahman barazanar rasa rayukan talakawa ne, sake dabara a nemi taimako wata masarautar talakawa za su ga kamar an fi san iyalan sarki akan lamarin rayuwar su, hakan ka iya kawo rabuwar kai cikin wanga masarauta wanda dama k'udirin Masarautar kenan. Tun da Sarki Abdulrahman be ji kunyar yada girman sa ba, da saka rayuwar mu cikin kunci, mu kuwa ba za mu kasa masa bita da kulle ba, dukan kabarin kishiya’’ shiru ta yi dan shan nufashi kafin ta k’ara da
‘’wannan dalili ya sa na yi bincike ta hannnun Gimbiya Binta, ta kuma amince da wannan batu, Allah ya ja da ran sa, idan na yi kuskure a yi min rai, ina tuba’’
Shiru ka je, Sarki na mai juya maganar cikin ran sa, in akwai abun da ya dame shi duk fad’in duniyar nan baya ya ke da farin da alumar shi ke ciki, idan kuma akwai abun da ya fi soyiwa a rayuwar sa, to ya bi bayan iyalin sa, musammam ma yaran sa mata guda biyu, hakan ya sa duk duniya babu wanda ya tsana, ya ke matsayin babban abokin gama kamar Sarki Abdulrahman na Fabarusa. Duk da batun Jakadiya lamari ne mai girma, ya tsinci kan sa ya na mai san yin tuntuntini akai.
Ya na duban Jakadiya ya gyara murya ya ce ‘’Jakadiya mun ji wannan batu na ki, duk dai ba mu gamsu ba, za mu yi tunani akai’’
Jin haka Jakadiya ta duk’a ta na mai d’unkule tafin hannun ta na dama yayinda ta d’aga sama ta na mai jinjina ga Sarki, fad’i ta ke
‘’Sukukun bakaka Jatau, mashin da wuta Jatau, idan mai sa6o bai daina ba mai horon ma ba zai fasa ba!lafiya Barden mahadi! Lagiya Sukukun bakaka! Lafiya Darzaza amalen sarakuna’’
********
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
No comments:
Post a Comment