💔💘 *SAKACI* 💘💔
0⃣3⃣
© *Fatima A Garba*
Ba ta sha wuya wurin gane gidan ba, a dai-dai kofar gidan mai keke napep ya ajiyeta bayan ta biyashi kud'inshi ta shiga gidan da sallama don ta ga kofar gidan a bud'e, koda tashiga bata ga kowa a filin gidan ba, hango wata kofa shine ya tabbatar mata da nan ne hanyan da zai sada ta da cikin gidan.
Bubbuga kofar ta yi, ba da jimawa ba wata dattijuwa ta zo ta bud'e, bayan Maryam ta gaisheta ta ansa cikin sakewan fuska kafin daga bisani ta ce " baiwar Allah daga ina, wa kike nema"
Maryam tace " gidan Dr Farida na ke nema da fatan banyi 6atan kai ba" dattijuwan tace "bakiyi 6atan kai ba bismillah ta na ciki"
Bayan ta shiga da ita ciki ta nuna mata wurin zama sannan ta ce "bari naje na sanar da ita zuwanki, au sai dai ban tambayi sunan ba, yi hakuri tsufan ne ya motsa"
murmushi Maryam ta yi, gami da cewa "Maryam ne sunan Baba" "toh har naje na sanar ma ta".
Ba jimawa ta fito sannan ta ce " tana nan zuwa bari na kawo miki ruwa kafin ta fito" "nagode" Maryam ta ce da ita.
****
Fitowanta kenan da ga wanka cikin sakewan fuska ta ce " kawalli yaushe kika shigo" harararta ta yi cikin wasa sannan ta ce " ah toh ba kin shiga kamar mai canja fata ba, na jima da shigowa"
Murmushi Dr Farida ta yi had'e da zama kafin kuma ta d'auko mai tafara shafawa sannan ta fuskanci kawarta da murmushi kwance saman fuskarta ta ce " afwan my Jidda, meye labarin?"
" hmm dole kiyi dariya tunda jiya kin barni cikin damuwa da tashin hankali" Jidda ta fad'a cikin damuwa, a ta ke murmushin da ke kan fuskar Farida ya sauya izuwa damuwa, Jidda tacigaba da cewa " Dr wai mai yasa Dr Umar ya ke miki hakane? Ni yadda yayi jiyan nan agaban jama'a wlh bai min dad'i ba, ba kuma ni kad'ai ba, duk jama'ar da ke wujen.
Kuma na lura wannan bashine na farko ba, wai mai yasa ya ke miki haka ne, shin me yake faruwa ne, a gaskiya ina bukatar na san wani abu dangane da ke k'awata" ta fad'a ta na kallon Farida.
Hawaye da ta ke 6oyewa ne ya zubo akan kuncinta saboda famo mata wani miki da Jidda ta yi, a dai-dai wannan lokacin ne, wannan dattijuwar tashigo don sanar da ita ta yi bak'uwa, Farida ta bata ansa da ta na zuwa.
Farida ta kalli Jidda har wannan lokacin hawaye bai daina zuba daga fuskarta ba, ta ce " kawata kiyi hakuri..."
Bata kai ga k'arasawa ba jidda ta dakatar da ita ta hanya d'aga mata hannu, kafin kuma ta girgiza kai gami da cewa " na lura akwai abinda kike 6oyemin wanda ya shafi rayuwarki"
Ta d'an yi shuru na d'an sakwanni, kafin kuma ta cigaba da ce wa.
Ba zan matsa miki akan dole sai kin sanar da ni ba, sai dai zanyi bak'in ciki, wacce na d'auka aminiyata ita ba haka ta d'aukeni ba" ta k'arasa da cewa "tashi muje".
Kama hannun kawarta ta yi had'e da zama agefenta sannan ta ce " bana nufin na 6oye miki duk abinda ya shafeni sai dai tunowa da tarihin rayuwata shi yafi komi tayarmin da hankali, karki damu kawata na miki alkhawarin baki labarin rayuwata amma mufara zuwa na sallami bak'uwata tukun na".
******
"Lale da maryam" ta fad'a da murmushi kwance saman fuskarta kafin ta zauna agefenta.
Duk'awa ta yi had'e da gaishesu.
Suka ansa cikin sakewan fuska kafin Farida ta ce "kin cika alk'awari, da fatan kuna nan lafiya" "lafiya muke Dr" Maryam ta ansa.
Farida ta ce "Maryam wannan kawata ce sunanta Dr Jidda itama likita ce a asibitin Abubakar Tafawa Balewa University Teaching Hospital (ATBUT) da ke nan Bauchi" ta fad'a ta na nuna Jidda.
sannan ta juya ga Jidda ta ce.
" wannan patience d'ita ce kuma k'anwata Maryam" Jidda ta ce "barka da zuwa k'anwarmu"
"yauwa Dr "
Maryam ta ansa cikin farin ciki, wai yau ita ce ta samu damar zama kusa da manyan likitocin da ake ji da su a wannan jahar, "lalle ita d'in mai sa'a ce" ta fad'a cikin zuciyarta.
Farida ce ta katseta ma ta tunani da ce wa.
"yanzu kafin kifara bani tarihin rayuwarki muje muyi breakfast"
"Dr nikam Alhamdulillah nak'oshi" cewar Maryam
Farida ta girgiza kai gami da cewa "A'a Maryam kar mu fara haka da ke please taso muje"
"Dr dan dai karki ce na miki musu ne amma muje"
"Yauwa ko kefa taso muje" ta fad'a gami da rik'e hannunta, don zuwa kan dining, Jidda ta rufa musu baya, ko wannen su ya samawa kanshi wurin zama.
kana ta k'wallawa wannan dattijuwar kira, cikin hanzari ta k'araso gami da ce wa " gani uwar d'akina" cikin sakewar fuska Farida tace " Iya abinci za ki kawo mana don Allah kiyi da hanzari" cikin girmamawa wacce aka kira da Iya tace "angama uwar d'akina"
***
Bayan sungama cin abinci ne suka koma cikin falon, bayan sun zauna Farida ta d'auki remote d'in TV had'e kashewa, sannan ta ce " malama Maryam ke muke sauraro" gyara zama Maryam ta yi sannan ta fara kamar haka.
****************
Maryam Adamu shi ne sunana, mu asalin yan garin Bauchi ne anan aka haifi kakan ninmu har izuwa kanmu, yanzu haka muna zaune a unguwar bakaro.
Gidanmu gidan yawa ne haka kuma gidan gado ne, domin kakana shi ya gina gidan.
gidan mu ginin k'asa ne mai sassa da dama, kakana ya mutu tun ina da shekara d'aya a duniya, matan kakana hud'u ne, yanzu haka biyu ne suke raye.
uwargidansa Baba Dije watan shi biyar da rasuwa itama ta rasu, yaranta takwas (8), ita kuma ta biyun goggo jummai ta na raye yaranta goma sha uku (13), sai ta ukun yaya uwani ita ce ta rasu wata biyar da suka wuce, tabar yara goma (10) sannan amaryarshi Baba Ladi ita kuma yaranta tara (9) itace kuma ta haifi Babana.
Kakan mu ya rasu yabar yara maza da mata su arba'in (40), maza ashirin da hud'u (24) mata goma sha shida (16), kuma ko wani d'a namiji idan yayi aure nan yake ajiye matarshi, a k'alla a gidan mun fi tamanin (80) badda matan da aka aurar.
Familynmu ba wasu masu arzik'i ba ne hasalima kowa ta kansa ya ke yi.
Mahaifiyata jamila ta taso ne a wurin yayar babanta wato goggonta, kasancewar iyayenta sun rasu, don haka ta taso cikin rashin gata.
Allah bai bawa goggonta haihuwa ba, mahaifiyata ta taso cikin wahala don ba irin azabar da goggonta ba ta gana mata tun ta na k'arama harta girma, talle kuwa na safe daban na rana da na yamma harma da na dare don haka ko lokacin zuwa makaranta bata samu, wannan ne yasa ta tashi ba arabi balle boko.
Unguwarsu d'aya da mahaifina, a yawon tallanta suka had'u da mahaifina soyayya ta kullu a tsakaninsu har ta kaisu ga yin aure.
Mahaifina mutun ne mai zuciyar neman na kansa, sana'ar saida kayan miya ya keyi a kasuwar wunti, yana kuma samun rufin asiri domin ba'a ta6a fashin d'aura tukunya a gidanshi ba koda ba dad'i za'aci, wannan ne yasa dayawa daga cikin matan gidan suke sha'awa dama sune su ke samun wannan rufin asirin, sa6anin ita mahaifiyata.
Mahaifiyata mace ce mai son abin duniya sannan bata da godiyan Allah, ita kullun cikin buri take.
Wannan ne ya sa ta sana'a sosai acikin gidan kuma Allah yasa mata albarka aciki amma bata ganin haka, kullum hangenta sama yake da samun ta.
Mu biyar (5) ta haifa ya Zakariya shine babba sai ya Sani, sai kuma ya mustapha sannan ni saikuma autanmu Habibu daga kanshi mahaifiyata tace bazata sake haihuwa a wannan talaucin ba, amma karku manta babanmu yana matuk'ar k'ok'arinshi.
Dukanmu yayi k'ok'arin sakamu a Islamiya da makarantar boko ta gwamnati, duk abinda aka nema dangane da karatun mu yana k'ok'arin bamu, kuma yana sa ido sosai akan zuwanmu sam baya wasa, wannan yasa dukanmu muna karatu.
Yanzu haka yaya Zakariya da yaya Sani suna level 3 a university yayinda shi yaya mustaph yake shekararshi ta farko a university ni kuma ina SS2 a secondary.
Bayan su yaya Zakariya sunyi wayo saita fara d'aura musu talle randa babanmu ya gani yayi fad'a sosai karshe ya kira su yaya Zakariya ya musu fad'a had'e da nuna musu illar talle, tun daga wannan lokacin suka bijire ma ta, ba yadda ba ta yi dasu ba sukak'i.
Sai kuma ta sa buri akaina ta fara d'auramin talle a 6oye, har ya kasance har makarantar Islamiya ko na boko da abin siyarwa na ke zuwa wannan ne yasa ban fiye maida hankalina akan karatu ba ganin haka wani malamin mu ya samu Baffanmu ya fad'a mai a ranar naga tashin hankalin da banta6a gani ba.
Baffanmu yamin dukan kawo wuk'a har sai da na kasa tashi ya kuma koma ga Innarmu ya ce " daga yau ta sa ke d'auramin talla a bakin aurenta" sanin da ta yi bata da wani gata sama da gidanshi yasa ta hakura ta daina d'auramin talla.
Sai kuma ta tsiro da wani sabon abu, lokacin da alamun budurci suka fara bayyana a tare dani kyawuna ya k'ara fitowa dama ni fara ce, abinda yafi rud'an samari da dama kenan akaina, alokacin kuma samari suka fara turu-ruwa a kofar gidanmu, wasu da nufi mai kyau wasu sa6anin hakan.
Alokacin ne kuma maitar Innata na son kud'i ya dad'a bayyana, a 6oye ta fara barina ina fita hira da samari ba ta re da sanin Baffa ba.
Ba kuma nan ne inda matsalar ta ke ba, idan na fita hira nadawo ta dinga tambaya ta me aka bani idan nace bakomai anan zata yita zage-zage da in raba kaina da matsiyatan samari da dai sauransu, tun ina damuwa da yadda ta ke yi har nima na fara kwad'aituwa da hakan sai kuma na fara wulak'anta duk saurayin da baya bani kud'i, harta kai nakan yarda wasu samarin sud'an tatta6ani sai dai ban ta6a bari ya wuce haka ba.
Har izuwa lokacin da jamilu yazo gareni shi ne ya fara bud'e min ido da kud'i.
Mahaifin jamilu babban d'an kasuwa ne wanda yake da manyan shaguna a central market, yana kuma rik'e da shago d'aya daga cikin shagunan mahaifinshi, wannan yasa yake mana 6arin kud'i.
Shi ne yafara ketamin rigar mutunci na, tun daga wannan lokacin yadinga rud'ana da kalamansa na yaudara.
Lokacin da na fara mai k'orafin ina tsoran shigan ciki, sai ya kawo shawaran kar6an maganin tsarin iyali.
Da farko nak'i yarda amma ya yi ta rud'ana da kalamanshi na yaudara har na yarda, da kanshi ya kaini na fara kar6a.
Da ga wannan lokacin Jamilu ya mai dani tamkar matarshi, ya d'aukeni duk lokacin da ya keso, kuma da sanin Innarmu na ke fita wani lokaci ma har kirari ta keyi min.
Baffanmu ba shi da masaniya a halin da nake ciki domin duk wata hanyar da zai fahimta Inna ta toshe shi.
Tabbas na cuci kaina da na amince shi masoyina ne na gaskiya, lalle kalaman soyayyanshi wanda duk na yaudara ne sune sukayi sanadiyar fad'awata tarkon halaka badan Allah ya kawoki rayuwata ba Dr.
Ta nunfasa sannan ta ce
"Dr kinji tarihin rayuwata"
kukan da suka ga Farida nayi shi yafi basu mamaki da shiga yanayin damuwa, ko ita wacce labarin yashafa batayi wannan kukan ba.
Jidda ce ta matso kusa da ita cikin damuwa ta ce " kawata wannan labarin bai cancanci wannan kukan ba mai yasa zuciyarki ta ke saurin karaya ne?"
"Labarinta ya tunomin da rayuwata a baya ne Jidda"
Ta dubi Jidda sannan ta ce "zan baku tarihin rayuwata amma ba yau ba, sai dai ko gobe"
" Sannan karkiga laifin zuciyata da yawan karaya Jidda wannan zuciyar" ta fad'a ta na nuna k'irjinta da yatsa saitin inda zuciyarta ta ke, cikin kuka ta cigaba da cewa " wannan zuciyar ta dauki abubuwa da dama"
Ta na gama fad'an haka ta tashi tabar wurin ba tare da ta sake magana ba, tana kuma shiga ta rufe kofarta da key.
Dukansu sunshiga damuwa da son jin labarin Dr Farida don dukansu sun shiga wani irin yanayi ganin halin da ta shiga wanda har saida suka zubar da hawaye.
Akarshe basu da za6i illah ko wacce ta kama gabanta, Dr Jidda ce ta kai Maryam har kofar gidansu, bayan ta yi ma ta Nasiha sosai mai kuma shiga jiki.
~Ummu Hanan~
No comments:
Post a Comment