Tuesday, 6 December 2016

KARNINMU 7

KARNINMU...

©FIKRA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA BAKWAI

Rai ɓace ta dawo falo ta zauna ta na mai huci. Sallamar Iya Dudu ta ji, amma ɓacin rai ya hana ta amsawa balle  ta ba ta izinin shigowa. Sai da ta jera sallamar har sau uku,ana huɗu ne Hajja Bilkis ta amsa da

"Haba wannan jera sallama haka sai ka ce makahuwa Iya dudu! da Allah ki shigo kawai mana!"
 
Iya dudu da a zaton ta Hajja Bilkis tare ta ke da Ahmad, ta shigo ɗauke da flask, ganin Hajja Bilkis ita kadai ya sa ta sakin jikin ta, in da ta k'arasa ta aje flask ɗin in da Hajja Bilkis ta aje sauran kwanukan abincin, ta juya ta fita. Sai bayan fitar ta Hajja Bilkis ta ja dogon tsaki.

"Lallai Ahmad ya kirawa kan sa ruwa! Har ma ya fice ba tare da ya leko ni ba? Heyyee yaushe na yi sako-sako haka! Dole kuwa na yiwa tufkar hanci!"
  Faɗin Hajja Bilkis kenan azahirance ta na mai jijjiga kafa. A fusace ta tashi, ta fice fuuu ba tare da ta damu da abincin da ta aje ba, haka kuma ba ta damu da ta ce da Iya dudu ta kwashe su ba. Kai tsaye ɗakinta ta koma, in da ta rarubi wayar ta da ke ajiye bisa gadon ta.

Numbar Ahmad ta shiga dannawa,har za ta kira sai kuma ta fasa. Ta shiga neman numbar yayar ta. Bugu uku ta ɗaga. Bayan sun gaisa a tak'aice ta ce

"Yaya ina fatan ki na gida? Dan kuwa zuwa wajan boka na gangare ya kama ni, Ahmad ya fara nema ya suɓuce min!"

"Ah! Ahmad kuwa Bilkis? duk mallakar da ya sha amma kuwa da ya isa mai taurin kai na gaske, menene ma ya faru tukunna?" Faɗin yayar ta daga ɗayan bangaran.
  Nan take Hajja Bilkis ta fayyace mata daga bindi har witsiya yanda ta kasance tsakanin ta da Ahmad. Wanda batun ya sa Yayar ta ta tsaki. Ta k'ara da.

" Aw ashe dan wannan abin ne ya faru shi ne za ki wani tada hankalin ki? Ahmad ɗin har nawa ya ke?"

  Hajja Bilkis ta nisa ta na mai faɗin
"Ah ah fa Yaya, bai taɓa min haka ba sai yau, sannin kanki ne shi fa ice tun ya na ɗanye ake tank'wasa shi, ai a bari ya huce shi ke kawo raban bak'o....."
 
"Ke dalla kar ki damu!" Yaya ta katse ta. Sannan ta k'ara da "Amma tun da kin dage sai ki bari sai gobe da la'asar sakaliya mu je, yau dai ki jira ya dawo ki ga iya gudun ruwan sa."

  Ajiyar zuci Hajja Bilkis ta saki, ta na mai furta. "Allah ya kai mu" Daga ɗayan ɓangaran yaya ta amsa da "Amen. Ina Hanif,an je makaranta ko?"
  Hajja Bilkis da bacin ran ta ya fara raguwa ta ce " Eh fa, ya na can. Yauwa dan Allah ki yiwa wannan mai kawo mi ki yan aikatau magana, idan an sami wata kamar dai Jummai haka ina so"

"Ke dai kam Bilkis kullum cikin sake yan aikatau ki ke, ita Jumman menene aibun ta? me ya same ta?" Yaya ta tambaya.

In da Hajja Bilkis ta mata bayanin rashin lafiyar Jummai. Jin haka Yaya ta amsa ma ta da

"Toh Allah ya sauwake. Kin ci sa'a kuwa anjiman nan mu ka yi da ita za ta kawowa wata k'awata yar aikatau, idan dai na ga ta min zan mi ki waya in ki na gida na turo su kawai in ya so ita sai a kawo mata wata daga baya. Ki kwantar da hankalinki Ahmad dai tafin hannun ki ya ke,sai fa yanda ki ka yi da shi"

   Da haka su ka yi sallama. Sai a sannan ɓacin ran Hajja Bilkis ya ragu. Nan ta tashi ta fara shirin  kutsawa cikin gari yawan da ta saba da sunan kasuwanci.

                     ***
Yayin da su Rabs suka kwasa a guje,  basu tsaya ko ina ba sai ɗakin Baaba kasancewar nan ne mafi kusa dasu.  Dunkulewa suka yi a saman ƙaramin katufarsa,  bayan sun rufe kofar da saka ta sun tura akwatin Baaba suka kara danne kofar.
    "Zanga yanda shegen Aljani zai iya turo kofar da muka danne da garwan chan,  faɗin Rabs cikin maye. 
   " shishshshsh!  Kar fa ya ji mu" cewan Messi yana ɗaura yatsa a leɓe, sai duk suka kwaikwaye shi.
 
   Ba su suka dawo hayyacinsu ba sai sha ɗaya saura,  nan suka ɗun guma teburin mai shayi, anan suka samu labarin abinda ya sa mu lado, kudin indomie  biyu suke da nan suka bada suka ci ba don sun kashi ba,  sannan suka lallaɓa zuwa gidan su Rabs, nan jikin su ya fara tambayarsu kasancewa gari ya ɗau zafi kuma layinsu ne suka hango wutan lantarki. Anan suka kwana suna jinya har garin Allah ya waye.
Ajiyar zuciya Messi yayi bayan ya gama tuna abubuwan da suka faru da su.

                         ***
Cikin nutsuwa Lanto ta fito daga hayin magarya kanta da babban botiki, misalin karfe bakwai da rabi  na safe kamar an ce ɗago idonki ta sauke su kan Nuhu ya haɗe cikin kayan makaranta ya fito tsaf dashi kamar bashi ba sossai ya birgeta amma a wautarta ya yi mata girma da saka uniform duk da tanasan ganinsa ta yi masa godiya kan taimakonta da ya yi sai da gabanta ya faɗi. Zata giftashi ta risina kaɗan sabida nauyin kayan kanta ta furta,

"yaya ina kwana"

Ya yi jim yana dubanta,
"lafiya lau Lanto daga ina?"

"Markaɗan warar yan makaranta  na ɗauko"

"Ke bakya zuwa makarantar?"
Ya tambaya yana tsareta da ido, sai ta diririce duk alamun damuwa sun bayyana a fuskarta bai tanka ba yasa hannu ya sauke bokitin daga kanta ya furta.

"Muje hanyarku zanyi zan ari takardun yaya Sani na waccan shekarar in duba mun kusa fara jarrabawa"

Ta kalleshi tana wasa da warwaronta
"kai waya saka makaranta?"

Tambayar tazo masa a bazata amma ya yi murmushi ya amsa.
"Mahaifina ne ya sani"

"Ka ji daɗin ka, amma in tambayeka?"

"Tambayeni mana kanwata" ya amsa yana tsare ta da idanu.

"Menene amfanin karatun da kake yi?"
Ya yi tsai yana dubanta sosai, can ya nisa ya ce
"Zan faɗa miki in mun sake haɗuwa"

Dai-dai lokacin suka kawo kofar gidansu ta yi kiciɓus da Larai ta kalleta tana dariya.

"Lallai Lanto kin waye"

"Kamar ya Larai?"

"Aha Allah ne ya  tonaki kin ce bakya yin irin abin da nake yi a ɗakin Lado amma meya haɗaki da irin gidansu Gimbiya bayan kowa yasan wacecce ita?"

Lanto ta dubeta da sauri baki buɗe kafin ta yi magana Nuhu ya ajiye markaɗan ya yi gaba yana murmushi yana jadadda mata.

"Lanto kice Baba ya saki makaranta"

Bata tanka ba  iyaka ta bishi da ido tana mamaki shi da yace takarda zai karɓa wajan Sani amma ya yi tafiyarsa. Tsaki ta yi wa Larai ta saɓi botikinta ta shiga gida.
                   ***
Tana dire botikin Maman ta kalleta tare da yin kwafa

"kedai wannan yarinya an yi malallaciya yanzu tun karfe shida na asuba sai yanzu zaki kawomun markaɗan tsabar iya shege?"

Kwalla ta taru cikin idanunta ta dubeta,
"Mamarmu da layi ne fa wajan markaɗan kuma ko sallah ban yi ba kika korani gashi nan rana ta fara fitowa"

Daidai lokacin Sani ya fito ya tsinci hirarsu kaf a kunnuwansa kansa ya ɗaure har takwas yarinya kamar Lanto ace bata yi sallah ba, cikin ci da zuci ya risina ya gaida mahaifiyarsu ta amsa tana harare-hararen iska ya sassauta murya ya ce,

"Mama kina kallon Lanto bata yi sallah ba ƴhar wanan lokacin bafa kyau wasa da sallah"

"Dakata Sani! Nidai ubana ba limami bane balantana in ce wajansa ka gado wa'azi. Nafa soma gajiya da wannan sanaben naka ka gama rainani kamar kashin bayanka"

"Ba haka bane Mama inasan sanar dake ma na yankomata uniform makaranta zan sata sati mai zuwa nagaji d ganinta a matsayin yar talla".

"Jar ubancan! uban kuturuma ya yi kaɗan Sani. Wallahi baka isa ba mudin ina gidan nan talla yanzu Lanto ta fara shi . Kiri kiri zakamin bakin ciki oh ni Hannatu na shiga tara kishiya tara rana ɗaya. Ɗanka na cikinka na yi maka bakin ciki da samunka anya Sani nonona kasha kuwa ? Kai wannan da sake inka guntsa furzarwa kake da kuwa haihuwar asibiti ce da nace musaya akai min wallahi"

Kan Sani ya ɗaure maganganun Mamansu na masa yawo aka, ya juyo ya wurgawa Lanto harara da sauri ta suri buta zuwa kewaye tana kyarma dan tasan halinsa sarai karonsu babu kyau. Jiki a sanyaye ya dubi mahaifiyarsu zai yi magana ta dakatar dashi.

"Fita kabani waje Sani"

Jiki babu kwari ya mike tare da ficewa daga gidan.
                       ***
Bayan an tashi daga karatun safe, almajirai kowa ya kama gaban sa, aka shiga gari neman na rana kafin a zauna karatun rana. Muazze rike da allo ya ja gefe tare da Hamze, in da su ka sami wani ɗan dakali su ka zauna. Muazze ya na mai duban Hamze ya ce.

"Hamze ina so ka buɗe kunnuwanka saurare ni da kyau, ka ga nan ba gida ba ne, Hamze birni ba karkara ba! ka kula ka rage rawan kai"
 
Hamze ya na mai gyaɗa kai ya amsa da "Toh Muazze"

   Muazze be gushe ba ya cigaba da faɗin
"Zancen bara, duk baran da zaka yi kar ka yarda ka yi nisa da makaranta, birni akwai ruɗu, za ka iya ɓata"

  Shiru Muazze yayi ganin wasu almajirai sun zo wucewa. Bayan wucewar su ya k'ara da.

"Kuma zan tambaya ma ka aiki gidan can"

Ya nuna wani gida gefan gidan Mallam Baso.

"Na ji an kawo amarya a daren jiya, Allah ya sa ba'a riga mu ba. Idan ka samu ka ga sai ta na baka abuncin ma ba sai ka yi bara ba,in ka ci sa'a ma har da kuɗin laraba"
  
  Hamze na wasa da saban allon shi ya ce
"Toh,amma yaushe za mu haɗu da Habi? Inna ta ce itama yau za'a taho da ita birni aikatau"

"Ai Hamze sai Allah ya tsaga rabo, domin kuwa haɗuwa abu ne mawuyaci kuma mai sauki, idan anan unguwar za ta yi aikatau d'in sai ka ga Allah ya haɗa fuskokin mu, idan kuma ta yi nisa toh abun da kamar wuya gurguwa da  auran nesa, sai dai fa mun koma karkara idan Allah ya sa ita ma ta dawo"

faɗin Muazze ya na mai duban wasu almajirai da ke kokawa kan gayan tuwo. Ya na mai nuna su da yatsa ya ce.

"Ka ga wasu can su na kokuwa kan tuwo ko? toh ina ma ka gargaɗi da ba ruwanka da harkar kowa bare har kwanan abinci ya haɗa ku. Maza je ka aje allunanmu, ka ɗauko kwano mu je neman na rana"

Da saurin sa Hamze ya karɓi allon Muazze ya haɗa da na shi, ya doshi soran gidan Mallam Baso. Muazze kuwa tashi ya yi ya fara k'ok'arin raban kokawar da almajirai ke yi kan tuwo.

                    ***
A kasalance Gimbiya ta tashi,  tayi sallolinta gami da taya goggo Amarya aikin cikin gida,  sai da ta sallaci la'asar, sannan tayi shirin fita zuwa  kiran da mai girma minista yayi mata don sa hannu a wani kwangila da yayi mata alkawari.
     "Goggo zan tafi amso wani kwangila, in Allah ya sa masa albarka zan samu kuɗi ba ko kaɗan ba,  halaliyata ce ba algus da haram, ki sa min albarka"  ta faɗi tana rungumota ta baya,  tare da kwantar da kanta a bayan ta kamar karamar yarinya.
   "oh ni Luba,  ban san yaushe zaki girma ba,  son jiki kamar kyanwa,  Allah sa albarka,  ya sa mafarin arzikinki kenan ya shirye ki"  ta faɗi fuskanta wadace da murmushi.

    "Goggo baki tambayi wajen wa zan amso ba,  bana jin daɗi in Naga ya kamata ki min faɗa kin kawar da kai,  ko dai kin fara gajiya dani ne"  ta faɗi a marairaice  kamar zata yi kuka.

    "Toh ba dole ba,  yaran da tayi wahalar cikinsu basu sa mata hawan jini ba amma ke kullum cikin sa cikin ku su ya zama baki kirin fiye da bakin gawayi.  Allah wadaran  lalatacciya"  faɗin  matar kawu yaro da take shigowa gidan da tsinkayi maganar Luba.
    "ai gara ni,  ban da aure,  mijin ki fa,  ki koma dai ki bincike shi ko in ce ki jira lokacin da za'a fara biyan bashin da yaci a kan  yaranki mata"  Luba ta faɗi tana dariya mai nuna tsantsan rainin wayau.
   Kafin Goggo ta ce wani abin ta fice daga gidan.  Sannu take tafiya har ta kai daidai majalisar su Kawu,  ta tsuguna ta gaida malam Sadi sannan ta gayar da sauran ta wuce a hankali.
    "Allah de ya la'ance ki Luba,  baki da rabo a lahira wallahi" kawu Yaro ya faɗi yana mai  tsaki.
    Ko ɗaga kai bata yi ba ta shige motar da aka zo ɗaukanta ta tafi ta bar su sun kafa chaptar ta.

                 ***
Bata jira iso ba ta shiga ofishin Minista, babu wanda ya tsayar da ita don umurnin Minista ne kar a yarda a dakatar  da ita.
       Da sallama ta shiga ofishin,  cikin rawan jiki ya taryo ta har zuwa kujerar da zata zauna.  Sam ya manta maganar da suke yi da Ahmad wanda ya suk'u da abinda minista yayi masa.
     "Ba zama na zo yi ba kawai ka bani takardu in cike in tafi,  yau kaɗai ina son Uwata tayi farin ciki a dalili na ko da na dakika ɗaya ne"  ta faɗi tana basar da rawan jikin da ta lura minista keyi na karramawa.
    "Mtswww!  Wai ke har kin san farin cikin iyaye ne?  Kalle ki fa, in dai har farin cikin ba don kin kai mata  kazantaciyyar abin duniya ba Toh tabbas bakin cikin ta zai kar da ke, Allah wadaran macen da bata san darajan kanta ba.  Ka fin in wuce ga shawara ɗaya, ki lallaɓa mutum ɗaya cikin karnukan da ke bibiyanki ki aure ko ta hanyar asiri ne, ya fi miki wannan bazantar da kai din ba" yana kai aya ya tashi ya fice ya barta zaune ido da baki buɗe tana kallon hanyar da ya bi ya wuce.

    

No comments:

Post a Comment