💔💘 *SAKACI* 💘💔
3⃣2⃣
© *Fatima A Garba*
Rayuwa kenan, Aunty dai sai labarin rasuwarta sukaji, a hanyarta tafiya ne, ta yi hatsari, adalilin shigewa 'kar'kashin babban mota da ta yi, a ta Allah yayi ikonshi akanta, ko shurawa bata yi ba.
Lokacin da Baba ya samu labarin cewa yayi a wuce da gawarta gidan iyayenta, ba yadda ba'ayiba yace ya yafe mata duk abinda tamai, sai dai bazai yafe mata cutar da Farida da taso ta yi ba.
**** ****
"Rungumeta yayi sosai ajikinshi yana cewa "Faridana kinga yadda Allah ku6utar damu ko"
Kafin ta yi magana Mariya ta shigo fuskar nan tasha kuka.
"Dr ina buk'atar ka sauwak'a min, please ka bani takardata nagaji, gwara na barka da ita kafin hawan jini ya kamani"
Sa ke Farida yayi daga rungumar da ya mata, kafin kuma yaje ga Mariya, hannunta ya kama suka fita, bai sa ke hannun nata ba saida ya sadasu da falonta.
Zama yayi akan kejera kafin kuma ya zaunar da ita agefenshi, bai kai ga magana ba ta fashe da kuka.
Rungumeta yayi yana rarrashinta har ta yi shuru kafin yace "na miki laifi Mariya amma ina rok'onki da kiyi hakuri"
"Dr ni nasan baka sona kana zaune dani ne dan dole, kawai mu hakura da juna"
"Wa ya fad'a miki ina zaune dake ne dan dole, abinda nakeso kisani ba'ayiwa namiji dole, kuma da zaran namiji ya gaji da mace bazai zauna da ita ba"
"Zan can kuma kice bana sonki idan bana sonki da tuni kinbar gidan nan, Mariya kece matata ta farko kuma uwar yarana, bana rok'on Allah yabani ikon cutar da ke"
"Please ki kwantar da hankalinki, Farida kanwata ce, Mariya tun Farida na 'karama muke ta re, bani da wata 'kanwa bayan ita, na sha'ku da ita fiye da tunaninki"
"Farida mace ce mai kyawun halaye, Mariya, don Allah ki rungumeta da hannu biyu bazan bari d'aya ya cutar da d'an uwanshi ba, Mariya kizo muzama y'an uwanjuna"
"Please ki cire komai a ranki, ki kwantar da hankalinki"
Tabbas maganganu da ya fad'a sun shige ta kuma sun mata da'di, dama kishi ne ya mata yawa amma Dr bai ta6a nuna mata wani abu ba, haka kuma Farida hasalima duk abinda ta ke yi Farida bata ta6a tanka mata ba.
Gaskiyan Dr ne Farida mace ce mai kyan hali, don haka dole ta zubar da makamanta, ta rungumi mijin ta gami da zama lafiya da abokiyar zamanta.
**** ****
Bacci ya fara d'aukanta taji tamkar hannun mutun ajikinta, farkawa ta yi a firgice gami da kunna wuta, shi ta gani yana mata wannan murmushin nashi mai tafiya da hankalinta.
"Kai Ya Umar bafa haka ake ba, kawai sai kazo ka firgitani" ta fad'a cikin shagwa6a.
"Oya zo ki koyamin yadda akeyi"ya fad'a yana janyota jikinshi.
"wai meye haka nifa ka tafi d'akinka" ta fad'a ta na ja da baya.
Rungumota yayi sosai har tanaji k'aran bugun k'irjinshi, cikin wata irin murya mai cike da kasala yace.
"Please Farida kizo kimin wallahi inbakiyi min ba mutuwa zanyi" kunya sosai taji, kai amma wallahi Aunty ta cuceta.
Rufe fuskarta ta yi da k'irjishi shima 'kan'kameta yayi a jikinshi yana ra'da mata wasu manya-manyan kalamai a kunnanta wanda suka rikita mata tunani, nan fa salo ya canja.
**** ****
Masoyan nan rayuwa suke mai cike da k'auna gami da tattalin juna, idan kaga yadda suke tafiyar da rayuwarsu abin sai ya baka sha'awa.
Mariya da Farida sun d'inke sosai ba mai jin kansu, mutunci da girmama juna ne a tsakaninsu, basu da buri sai na kyautatawa mijinsu, gami da tattalin yaransu, sosai Farida ta janyosu ajiki dama kuma sun saba da ita.
**** ****
Dr ne ya shigo d'akin ganin bata falo yasa ya zarce d'akin kwananta kai tsaye, ta na cikin bargo, yaye bargon yayi gami da cewa.
"My Farida kar dai kice min baki shirya ba" murya canciki tace "Ya Umar kaina kamar zai tsage"
Subhanallah tun yaushe" ya fad'a gami da zuwa kusa da ita, kafin kuma yakai hannunshi jikinta, jikinta yayi zafi sosai, hankalinshi yayi matuk'ar tashi.
Baya son duk wani abinda zai damu Faridarshi.
"Faridana kinji jikin ki kuwa mai yasa baki sanar dani tun wuri ba"
Kayan aikinshi ya d'auko ya fara gwada ta, kafin kuma yace.
"kina da sirinji na d'ebi jininki ya kamata naje agwada dan na tabbatar da abinda yake damunki, zafin jikin naki yayi yawa"
Nuni tamai da hannu inda ta ke ajiye kayan aikinta, ba ta re da 6ata lokaci ba ya d'ebi jininta gami da cewa "bari na turo miki Mariya sai na dawo, zan taho miki da magunguna".
Duk irin gwaje-gwajen da ya kamata amata anyimata amma ba'asamu wata cuta a ta re da ita ba, malaria ne ma aka samu kad'an.
Farida na jinjiki an kuma rasa gane ainihin abinda ke damunta takamai-mai, idan kaga Dr awannan lokacin sai ka tausaya mai, Mariya ita ta ke kulawa da ita.
Tun ta na iya tashi har takai sai an kwantar an tayar, gashi sai kunbura ta keyi daga bayan nan, hankalin kowa ya tashi, dole Ummi ta dawo Bauchi suka cigaba da jinyarta.
Baba kanshi kullun yana hanyar gidan hankali tashe, ranar da Alhaji yazo dubata ya shiga damuwa matuk'a har ya ke cewa Dr.
"Umar rashin lafiyan Faridan nan ya dameni matuk'a anya baza ka fita da ita waje aduba zuciyarta ba dubi fa yadda ta ke kumbura gaskiya abun ya dameni"
Kuka sosai Dr yake tamkar 'karamin yaro, yana cewa "Alhaji bana so na rasa Farida, wallahi bazan iya rayuwa ba ita ba"
Alhaji yace "Umar karkayi sa6o fa, Allah baya barin wani dan wani, zan cen ba zaka iya rayuwa ba ka daina, Allah zai iya d'auketa yaga yadda za kayi don haka addu'a zakayi sannan ka nemi kud'i kayi k'ok'arin fitar da ita k'asar waje ta na buk'atar taimako gaskiya"
Ya juya ga Farida da ta ke kwance da robar ruwa mak'ale a hannunta, yace "sannu Farida, yanzu me yake miki ciwo"
Dafe kanta ta yi da hannu alamar kan ne yake damunta, Ummi ce tace "wannan ciwon kan na rasa irinshi wallahi, sam baya jin magani"
"Allah ya baki lafiya, ya tashi kafad'unki" ficewa Dr yayi daga d'akin domin sosai wa'dan nan addu'o'in suke kashe mai jiki.
**** ****
Acikin kwanaki k'alilan Dr ya kammala shirye-shiryen fita da Farida India, shi da ita ne kawai zasu tafi kasancewar yadda ake fama da rashin kud'i.
Ranar lahadi jirginsu ya d'aga, sai addu'ar dacewa daga masoya.
**** ****
Kasancewar Dr yasan likitoci sosai acan yasa basu wani sha wahala ba, sun samu kulawa sosai.
Dr Shamsudeen, babba likita ne kuma k'wararre a fannin jikin d'an adam, ana matu'kar ji dashi a 'kasar India, shi ne kuma yake duba Farida.
Tun bayan zuwan su jikin Farida ya matsa fiye da tunani har takai idan ka ganta sai ka tausaya mata.
Sosai likitoci suke bincike akanta amma har wannan lokacin ba'a samu wata cuta a ta re da ita ba.
Idan kaga Dr za kayi tunanin shima bashi da lafiya ne, ya rame sosai.
Dr Shamsudeen ya gama duba file 'din Farida, gami da tatta6a jikinta, kana ya juya ga Dr Umar.
Yace "Dr Umar maganar gaskiya bazan yaudareka ba, munyi ikar 'ko'karin mu amma mun kasa gano ainihin abinda yake damunta, kana gani a idonka akayi komai"
Ya cigaba da magana da harshen nasara, "agaskiya shawara d'aya zan baka a matsayinka na 'dan'uwana musulmi, ku dage da addu'a"
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" kawai Dr Umar yake mai-maitawa cikin matsanancin tashin hankali.
Dr Shamsudden ya d'anyi shiru alamar tunani kafin kuma yace "amma inazuwa"
Ma'akatan lafiya yayi wa umarni da sukai Farida wani d'akin gwaje-gwaje.
Yafi awa guda yana aunata cikin gwanancewa.
Dr Umar yana gefe ya kasa ta6uka komai, damuwa tamai yawa, wai me yake faruwa ne ya kasa gane komai.
" *Allahu Akbar, Allahu Akbar* " abinda Dr Shamsudeen yake fad'a kenan, cikin farinciki, muryarshi har rawa ta ke.
Dr Umar ne ya taso cikin gaggawa yana cewa "me yafaru Dr, mene ne don Allah ka sanar dani"
Kamo hannunshi kawai Dr shamsudeen yayi ba ta re da yayi magana ba.
~Ummu Hanan~
No comments:
Post a Comment