Sunday, 25 December 2016

Sakaci 26

          💔💘 *SAKACI* 💘💔

                       2⃣6⃣

© *Fatima A Garba*

Farida da Ummi na zaune a falo suna hira, duk rabin hiran ya ta'allaka ne akan nasiha wanda Ummi ta ke yi ma ta.

Dr Umar ne ya shigo falon, idanunshi na kan Farida, addu'a yake Allah yasa ba ta sanar da Ummi ba, domin sam Ummi ba ta d'aga ido ta kalleshi ba, balle ya sa ran za'amai magana.

Tashi ta yi had'e da barin wajen, har sai da ta shige d'akin Ummi kafin ya d'auke idanunshi daga kallon da yake mata.

Zama yayi a gefen Ummi gami da cewa "wash nagaji" yaji ba ta tanka mishi ba, ya sa ke cewa "Ummi Alhaji bai dawo ba ne"

"Ka ganshi ne anan" ta fad'a a hasale, tun daga nan ya sha jinin jikinsa, murya a raunane yace "Ummi wani laifi na yi ne"

Cikin fad'a ta ce "ban sani ba, na ce bansani ba, yau wai ni ce zaka ci amana Umar, wallahi kaban mamaki, bansan haka kake ba"

Murya a raunane yace "Ummi ki yafe min, wani abun akace miki na yi ne, kiyi hakuri ki sanar dani kar Allah yayi fushi dani"

Rai 6ace tace "na yi zaton kai mai rik'e Farida ne bisa amana, Umar na yi zaton ko wani kaga yana k'unta ta ma ta sai inda karfin ka ya k'are, mai yasa ka aureta kasan baza ka iya rik'eta ba"

"Ba komai bazan so Allah ya kama ka saboda hakkin baiwar Allah nan ba, tabbas saki ba abu ne mai kyau ba sai dai ina maka tsoron kamuwar ubangiji"

"Domin haka ina shawartarka da kaji tsoron Allah ka saiwak'e ma ta Umar"

Ummi na gama fad'an haka ta juya gami da cigaba da duba wasu takardu.

"Ummi wallahi ina sonta, ina sonta, Ummi kiyi min addu'a ban san mai ya ke damuna ba, na kasa mancewa"

Rabonta da ta ganshi yana kuka ta manta, tabbas ya na bukatar kulawarta, ya zama lalle ta taimaka musu.

Murya mai tattare da lallami Ummi ta yi magana "toh kai wace irin zuciya ce da kai da ka kasa yafe ma ta, yarinyar nan ta nemi gafararka, Umar karka zamar da kanka jahilin karfi da yaji mana"

"Ummi ban san mai yake damuna ba wallahi hoton yaron ya kasa fita a cikin zuciyata, Ummi Faridana ce fa"

Murmushi Ummi ta yi irin nasu na manya, lalle ba wani abu ba ne ya ke damun Umar sai kishi.

"Yayan Farida" Ummi ta kira sunanshi.

"Na jima da fahimtar kai da k'anwarka kuna tsananin k'aunar junanku, amma ku kanku kun kasa fahimtar hakan"

"Lokacin da kuka kawo girma na yi tunanin zaku fayyace wa juna halin da ko wannenku yake ciki, amma naga ba kuyi hakan ba"

"Sannan ko da Alhaji yayi maka maganar Mariya nan ma na yi tunanin zaka fito da buk'atar zuciyarka, har zuwa randa ka kawo kaya, da farko na yi farinciki dana ga akwatuna biyu amma jin bayaninka ya sakarmin da gwuwa"

"Har izuwa lokacin da yaron na Adamu ya fito, fad'an da naga kanayi nasan tabbas akwai dalili, sosai naji haushinka lokacin domin kak'i ka fitar da sirrin zuciyarka"

"Bayan kunyi wanna tashin hankalin da ita sai na fara k'aryata tunani na, amma randa ka taho daga Bauchi ba shiri, tafiyar da baka ta6a irinta ba, nasan akwai damuwa, na yi k'ok'arin tambayarka, amma kace ba komai"

"Ni nasan damuwarka ba zata wuce saka ranar auren Farida da Ahmad ba"

"Hankalina ya tashi matuk'a, wannan ne yasa bacci ya k'auracewa idona, a daren naji ina buk'atar na sameka dan mu tattauna, kai tsaye na shigo d'akinka a wannan daran.

Na yi sallama kafin na shigo amma naji shuru, kuma inajin kukanka da surutanka, wannan ne yasa na shigo, na lura a wannan lokacin sam baka cikin hayyacinka"

"Hankalina yayi mak'ar tashi da jin kalaman da suke fitowa daga bakinka, anan na tabbatar da kana k'aunarta k'auna kuma mai tsanani"

"Ban bari ka ganni ba na koma d'akina, hankalina ya tashi a ranar na samu Alhaji na fayyace mai komai nan fa muka dukufa addu'a"

"Allah ya ansa addu'ar mu, tun daga wannan lokacin hankalina ya kwanta, duk a tunani na Farida ta samu kwanciyar hankali, Umar ba zanso Ku rabu da juna ba domin kuna son junanku"

"Sai dai ba zan lamunci ganin Farida a damuwa ba, domin haka nake rok'onka da ka sauwak'e ma ta, saboda ka kasa rage kishinka, wanda hakan cutarwa ne a gareku"

Tamkar k'aramin yaro haka ya rik'e hanun Ummi ya na cewa "Ummi dan girman Allah karki rabani da Farida wallahi ina sonta, zan iya mutuwa akanta ki taimakeni"

Cikin hikima Ummi ta ce "ni kaina bana so na rabaku, sai dai maslaha nake nema muku domin wannan kishin naka yana cutar daku"

"Addu'a zakimin Ummi na rasa yadda zanyi ki rok'a min Allah" sosai taji tausayinshi, itama dama ba taso su rabu domin ba wanda zai rike mata Farida da amana sai shi.

"Zan yarda ku koma amma da sharad'i" "Ummi please banda sharad'i mai tsauri" ya fad'a yana rok'onta.

"Toh ai shikenan sai kaba ni takardar ta" Ummi ta fad'a ta na k'ok'arin tashi, da sauri ya sha gabanta gami da sunkuyawa gwuwowi biyu a kasa kafin kuma ya ce "wallahi na yarda da sharad'in"

"Da safe ka rarrasheta idan ta yarda, ta amince zata bika, to sharud'in zai biyo baya"

Ummi ta fad'a gami da tafiya d'akinta, daren ranar Ummi ta rayashi ne da addu'o'i, ta rok'a musu Allah sosai wanda ta ke sa ran addu'arta ta kar6u.

~Ummu Hanan~

No comments:

Post a Comment