Thursday, 29 December 2016

Dan Adam 5

Wannan karon a kan kujera ta sameta tana amsa waya. Zama tayi har ta kammala sannan tayi magana.
"Gani Hajiya." Ta dubeta a nutse sannan ta soma magana.
  "Yauwa Ummi, dafatan dai Amina ta nunamaki dukkan ayyukan da takeyi? Toh inaso ki zamo mai rike amana, muddin kika ci amanata, bazan kyaleki ba. Yanda zan rik'i amanarki da gaskiya a matsayinki na Amanar a hannuna, haka kema nakeso ki rike, ki kula da dukkan ayyukan da zaki dunga yi."  Ta k'ara karanto mata ayyukan harma da na gyaran sashenta ciki da falonta na biyu, banda wannan da suke ciki don duk cikin aikin Ramma ne. Ta k'ara jaddamata cewar batason k'azanta, hakanan ta kiyaye tsaftar suturunta, duk sadda zatayi wanki, ta tambayi omo zata samu. A dai maganganun Hajiya, Ummi ta fahimci cewa dagaske batason k'azanta kuma tana da kyankyami.
   Ta rausaya kai.
"In sha Allahu Hajiya zan zama mai kula da dukkan abinda kukace, nagode Allah Ya k'ara girma da arziki."
Har a ranta ta ji dad'in maganganun Ummi.
  "Shikenan kina iya tafiya."
                       ☆☆☆
   Tun daga wannan ranar, Ummi ta kama aikinta sosai, Amina na taimakonta. Har ya kasance wani sa'in kafin Amina ta tashi, ta rigata tashi. Tana jin dad'in zama da Amina saboda shawarwarin da take bata, har karatu tana koyamata. Duk da cewar Amina na cin wuya don Ummi ko bak'i bata iya ba. Duk sai ta bata tausayi, haka take lalla6awa ta biyamata, amma ta tabbatar muddin tana wajen Hajiya Madina, bazata ta6a bari ta zauna mata da jahilci ba, duk wadanda suka ta6a zama sukayi aiki awajenta, ba wacce bata sanya a islamiyya ba, boko ne dai ba lallai ka samu ba.
     Saida Ummi tayi sati da zuwa, sannan Amina ta soma shirin tafiya don Hajiya Mama sun dawo. Gaba daya ta ji babu dadi, tana zaune gefe tana duban yanda take ninke kayanta tana sanyawa ciki jaka. Amina ta ankara da duban da takeyi mata, itama sai taji batason rabuwa da ita.
  "Haba Ummi, menene abin damuwa har haka alhalin muna gari d'aya? Karki damu, na tabbata zamu dunga ganin juna. Kedai ki cigaba da hakuri da zama da su tsakaninki da Allah."
   Ummi ta gyad'a kai.
"Toh Anti." Sai yamma suka tafi har Hajiya da su Adnan, gidan ya rage Ummi kad'ai da Ramma. Bayan ta kammala ayyukanta ta fito farfajiyar gidan tayi zamanta. Bata kai mintuna biyar a zaune, budurwar da bazata ta6a mance fuskarta ba wacce suka samu sa6ani da Adnan a farkon ganinta da su, ta fito daga sashensu tare da k'awayenta har su biyu suna dariya.
   Hararar da ta sakarmata ne yasa ta dauke kanta babu shiri ta saddar a k'asa, ta gabanta sukazo wucewa, ai kuwa ta sanya takalminta mai tsini ta take yatsun k'afarta har saida tayi k'ara. Ta juyo ta rankwasheta.
"Munafuka, sharri zakiyimin kina gidan ubana kina cin arziki? Shegiya kawai."
  K'awayen dariya kawai sukayi, d'aya tana fad'in "Kai Iklima baki da kirki."
Iklima ta ta6e baki.
  "Na kaiku?"
Suka fice Ummi ta mike da sauri tabar wajen, saida ta tsaya a lungun ta share kwallah sannan ta k'arasa ciki. Ta zauna a kicin tana kallon yanda Ramma ke faman had'a miya, tana dan jan Ummin da hira har ta share batun Iklima ta saki jikinta.
                      ☆☆☆
 
      Bayan tafiyar Amina, Ummi dole ta sabarwa kanta hira da Ramma, don Ramma mace ce mai abin dariya. Ayyuka ko kusa basu bata wuya sosai don a ganinta ta saba da fin haka acan gidansu. Sau da yawa takan tuna Mahaifinta, tana tunanin ko wane hali yake ciki yanzu, saidai daga zuciyarta ta tunano mata irin tsana da tsangwanar da take sha a wajen shi kansa, sai ta ji tunanin ya kau.
   A d'an zaman da sukayi da Hajiya Madina ta fahimci Ummi lallai bata da wani ilimi da addini, ta lura ko sallolinta akwai gyara ciki, wannan dalilin ne yasa ta sanya Ramma kaita makarantar da yaranta(ita Rammar) ke zuwa, karfe biyu suke zuwa su taso k'arfe biyar na yamma. Babu ruwanta da shiga sashen kowace matar gidan don sosai ta dauki gargadin  Hajiya Madina, hakanan tana rike da nasihar Antinta. 
   Alokacin Hajiya Lubna amaryar gidan sun dawo daga Maiduguri, ta lura yaranta suna da kirki basu da hali irin na yaran Hajiya Binta. Saidai uwarsu ce sai a hankali, mace ce mai shan k'amshi, saika gaisheta sai ta ga dama take amsawa.
  Maigidan ma bai rufe sati biyu ba ya dawo. Ranar da ya kasance Hajiya Madina ce da aiki, sun ci aiki sosai, har da Hajiya Madinar. Ummi banda wanke wannan mik'o wancan babu abinda takeyi. Abinci kusan kala uku ta ga anyi ciki harda suyar kaza bayan an tafasa an tura shinkafa da kayan hadi a k'asanta an toshe bakin da dankali babba guda d'aya. Sai lemun zo6o da taga sun had'a sai kamshin abarba yakeyi. Aka kammala aka zuzzuba, suka ajiye a saman tebur. Ummi da Ramma suka tattara kicin din, can bayan magriba, lokacin Ramma ta tafi, sai ga Hajiya Madina ta fito daga dakinta ta ci ado cikin wani (yellow lace) wanda ya sha adon duwatsu, tayi kyai sai k'amshi kawai ke tashi a jikinta.
  Ummi na  rak'u6e a can gefen kofar kicin tana kallon wani fim na yak'i da su Adnan suka nutsu suna kallo.
  "Wow! Wallahi Mom kinyi kyau."
Cewar Ihsan tana mikewa tsaye, daga ita sai riga iyaka gwuiwa da riga tshirt kanta hula ce ta sanya. Ta isa ga Mamin tana mai sanya hannu ta k'ara gyara mata zaman d'aurin. Murmushi kawai Hajiya Madina tayi.
  "Naji, taho ki kaimin kayannan sashen Abbanku."
  Ihsan tayi dariya.
Tare suke fice ta dauki wasu Ihsan ta dauki sauran. Ummi ta bi Hajiya Madina da kallo cike da sha'awa don kwalliyar ta burgeta. Idan kana da kudi babu abinda ba zakayi ba.
     Har ta gaji da kallon, ta koma daki ta hau duba karatunta, a karshe da ta gaji, kwanciya tayi abinta wani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita don bata ta6a aikatuwa irin na yau ba saboda girkin dawowar Alhaji da ta taimaka da shi.
        Bayan kwanaki biyu da dawowar Alhajin, ranar juma'a bayan ta je ta gaida Hajiya. Hajiya ta dubeta a nutse. Doguwar bakar abaya ce jikinta na wajen Amina.
  "Wai ke baki da kaya ne sai wadannan guda ukun? Yau idan kin saka doguwar riga bak'a, gobe sai jan atamfa kodadde, jibi ma haka? Bakizo da kaya bane ba?"
   Ummi ta sunkuyar da kai gaba daya jikinta yayi sanyi, cikin rawar murya tace.
"Eh su kadai ne masu d'an dama-dama Hajiya."
   Hajiya tayi shiru da mamaki, kafin tace. "Daukomin duka kayanki nagani."
  Ta mik'e da sauri ta cika umarninta, Hajiya ta sanyata ta zazzagesu. Kayan duk ba wani na kirki kam da gaskiyar Ummin.
  "Kwashesu ki maida ledar, kada su koma wannan d'akin. Fita kimin kiran Ramma."
  Ta amsa da toh, ta mayarda kayan jaka sannan ta fita ta kira Ramma. Tana ji Hajiya tace idan ta kammala tayi magana zata bata kudade gobe ta shiga kasuwa ta siyo mata kananun atamfofi guda hud'u sai dogayen riguna yan kanti su kuma guda uku sai wanduna da vest guda shida-shida. Ramma ta amsa da toh, zata mike Hajiya ta dakatar da ita.
  "Tafi da wannan ledar a zubar don Allah." Ramma na dariya ta dauka tayi gaba tana fadin toh.
    A washegarin kuwa Ramma bata zo da wuri ba sai wajen sha d'aya na safe. Sai gata da kayan da Hajiya ta umarceta. Hajiya ta duba sannan ta bata atamfofin ta kai dinki, tayi kiran Ummi ta mik'a mata ledar kayan ta kara jaddada mata cewa ta kula da tsaftar jiki da dakin da take kwana. Ummi ta amsa tayi godiya ranta fari k'al ta zubawa Hajiya ruwan addua wanda hakan ba k'aramin faranta Hajiya Madina yakeyi ba. Saida ta shiga ta zazzage kayan tana duba, ai kuwa dai abinda Hajiya ta karanto shi d'in aka sissiyo harma da k'arin man shafawa da turare (Lovilla) na roba. Har wani tsalle tayi na murna, ko babu komai a makaranta yan ajinsu zasu dinga jin tana k'amshi kamar yanda ta ga yan babban aji a makarantar suna yi idan sunzo giftasu ko kuma monitoci.
                    ☆☆☆
   A wani yammacin Alhamis, Ummi na zaune a tsakar gida tana taya Ramma goge ku6ewa, Hajiya ta fita zuwa asibiti, k'aramar 'yarta wacce ta aurar a karshe tana nak'uda, wato Aisha.  Ihsan da Adnan suka sanyo kai, Adnan na daga gaba a guje yayinda Ihsan ke binshi a baya itama a guje tana rok'on ya ara mata wayarsa. Dariya yakeyi ya juya gareta.
   "Ai baki isa ba, sai na rigaki jin kukan bebin."
  Su dai kallonsu kawai sukeyi. Ramma tayi dariya.
  "Oh, wai kada dai kucemin har Aisha ta haihu?"
   Adnan na dariya alokacin da yake danno lambar Maminsa, ya bata amsa.
  "Ta haifi d'anta namiji yanzu Mami ke gayamin."
  Ai sai Ramma ta kara washe baki.
"Kai Alhamdulillah."
  Ummi dai na kallonsu, ita har mamakin Ihsan takeyi, fara'arta ga yan uwanta ne kawai amma ba dai ga ita ba. Batasan meyasa  take d'asawa da Ramma ba, sune dai bata ta tasu.
  Adnan bayan ya yiwa yar uwarsa murna, ya bawa Ihsan don ta dameshi da rok'o. Nan fa ta cika musu kunne da ihun murna, ya warce wayarsa.
  "Kingani ko? Ai ke wata shashasha ce wallahi, a komai bakya yin na hankali shiyasa ma nak'i baki."
  Tayi mishi gwalo bayan ta saita kafarta zuwa hanyar falo.
  "Oho dai ka bani." A guje tayi ciki, ya bita. Ummi da Ramma abin sai ya basu dariya. Ta fahimci Aisha dai d'iyar Hajiya wacce Amina ta gayamata itace ake nufin ta haihu.
   Ranar suna tayi mamaki da Hajiya tayi mata iznin ta shirya har ita zasu tafi. Ai kuwa tayi murna ba kad'an ba don tunda tazo bata ketare layinnan ba bare har ta hau mota zuwa wani wajen, murnarta ta dad'u, burinta bai ta ga Antinta ba, don ba karamin ganin girman Amina takeyi ba.
    Ta sanya d'aya cikin atamfar da aka dinka mata, kasancewar ba dauri ta iya ba, kawai sai ta kulleshi a baya kamar yanda takeyiwa kayan islamiyyarsu. Ta sanya hijabin islamiyyarsu wanda ya kasance fari tas. Silifas dinta na roba wanda Amima ta barta ta zura ta fito. Ba jimawa suma iyalan gidan suka fito banda Ihsan wacce tun haihuwar da kwana hud'u ta tattara ta koma can.
  "A'a, kaga iyalan Mami." Cewar Adnan cikin tsokana yana duban Ummi. Ita dai murmushi kawai tayi ta sunkuyar da kanta, Mami kanta shigar Ummi ya burgeta sai ya fito da kyan fuskarta. Tana rike da hannun Fahad suka shiga mota.
   Suna tafe a mota, idanunta na kan hanya tana ta kallon manyan titunan garin Kano masu cike da motoci iri daban-daban. Wani motar idan ta gani saidai ta bud'e baki tana kallo. Har suka iso gidan sunan bata ji ta gaji da kalle-kalle ba.
  Acan suka tarar da dukkan yayyun Ihsan duk da lokacin rana ce don ba'a soma cika sosai ba.
  Haka ta zauna jugum a gefe tana kallon yanda suke hira da dariya abinsu babu abinda ya damesu, sai daukar hoto sukeyi da bebi. Ba jimawa sai ga Hajiya Mama da su Amina, batasan Hajiya Mamar ba, amma ganin da tayiwa Amina tare da ita yasa ta fahimci itace. Ai kuwa ta washe baki ganin Antinta. Amina itama riko hannunta tayi fuskarta a sake.
  "Wai kanwata ce ta koma haka? Lallai Ummi Hajiya ta gyaramin ke." Ummi dai dariya tayi ta gaisheta. Amina ta amsa sannan tace bari ta shiga ta gaida mutanen ciki ta dawo gareta don lokacin Ummi ta gaji ta fito 'yar barandar kofar falon.
  Nan fa sukayita hira, Ummi ta sanarmata an sanyata makaranta, Amina na murmushi mai bayyana hak'ora ta dubeta.
  "Ban gayamaki cewa Hajiya bata zama da marar ilimi ba? Kedai ki dage sosai, zakiyi ilimi fiye da zatonki in har Allah Ya so. Kada ki gaji da bada himma."
   Ummi ranta fari k'al hakoranta a waje sun k'i rufuwa ta gyada kai.
  "Toh Anti."

Suna ta hira har Amina na sanar mata batun taron family da su Hajiya sukeyi duk bayan wata uku.
  "Gaba d'aya wanda ke nesa suna zuwa."
  Ummi ta jefomata tambaya.
"Yaushe zasuyi kuma Anti?"
Amina har lokacin da murmushi saman fuskarta ta amsa.
  "Asabar mai zuwa, nan zuwa jibi."
Ummi ta dan ta6e baki kadan.
"Toh ai ba inda zasu zo da mu ko?"
"Eh mana."
  Haka sukayita hirarsu, Amina na sanarmata cewa mamanta tace ta gaisheta. Har aka kammala aka watse batasan sunan yaro ba, sai a mota ta ji Hajiya Mama na waya tana fad'a, sunan yaron Tahir. Suma kishiyoyin Hajiya Madina sun leko saidai ko awa basu cika ba sukayi sallama suka tafi, babu wacce ta zo da yaro cikinsu sai wani shan k'amshi sukeyi.
                      ☆☆☆ 

A gajiye likis Ummi take, suna zuwa sallolin dake kanta kawai tayi ta kwanta. Bata kara sanin abinda ke faruwa ba a duniyar sai bayan farkawarta da Asuba. Bayan ta idar da sallah ta zauna anan addu'o'i har garin Allah Ya waye, kasancewar babu makarantar boko ballantana ta tashi had'e-had'en karin yaran yasa ta komawa tayi kwanciyarta, baccin da tayi har ya fiye mata na farko dadi, ta jima tana bacci kafin kuma ta soma jin ana bubbuga kafarta ana kiran sunanta. Farkawa tayi a firgice tana salati, ganin Fahad yasa ta sauke ajiyar zuciya. Kira ne daga Maminsa akan ta soya mishi kwai ta had'a da biredi da shayi. Dole ta mike ba don baccin ya isheta ba ta fad'a bandaki ta wanko bakinta da fuska sannan ta bi bayansa.
  Saida ta kammala komai sannan ta fad'a d'akinsu, ganin Ihsan bata farka ba yasa ta fitowa batare da tayi abinda ya kaita ba(wato gyaran daki). Tana gudun ta shiga bandakin don wankewa Ihsan ta yi mata rashin mutunci tace ta hanata bacci.
   Misalin karfe biyun rana, kowannensu yayi shirin Islamiyya, kai tsaye yaran wajen mahaifinsu suka nufa sanin da sukayi cewar yana garin suka kwashi gaisuwa ya sallamesu da abin kashewa bayan makaranta sannan suka d'uru cikin mota, suka tafi. Sai lokacin ne Ummi ta samu sararin yin nata shirin na makaranta tana ta zabga uban sauri adalilin lattin da ta so yi, haka ta fito cikin shiri ta yiwa Mami sallama. Mami ta amsa gami da yi mata fatan alheri, har ranta ta ji dadi don abu ne da sam Mamin bata saba ba, alamun Mami gaba daya a yau sun nuna tana cike da nishadi wanda babu damar tambayar dalilinsa. Ta sanya kai ta fice daga gidan.
  A makaranta nan dinma ta ji dadi sosai don kuwa ta kai haddarta saidai ta sha gyara duk da baikai yawan yanda a baya Malamin nasu ke cin gyaranta ba, ta lura yana yi mata uzuri ganin ko bak'i bata iya had'awa ba, wannan dalilin yasa ya ware mata lokacinta daban yake koyar da ita wasula da bak'ak'e.
   Koda suka tashi, cike da nishadi ta dawo haka kawai a yau batasan farincikin ko menene takeyi ba, ta godewa Allah yafi sau biyar a zuciyarta. A farfajiyar gidan ta iske motar Danliti, hakan ya bata tabbacin cewar Ihsan sun dawo. Hajiya Binta ta gani tare da wata wacce ba yau ta soma ganinta ba ga dukkan alamu kuma kawarta ce. Ta gaishesu a ladabce, suka amsa ciki-ciki suna karemata kallo. Bata kai ga karasawa ba ta ji suna maganarta, inda matar ke cewa.
"Ina mamakin Hajiya Madina, ko a ina ta kwaso wannan mai ruwan buzayen? Wannan ko Alhajinku ya gani mai yiwuwa yayi ta hud'u da ita."
  Ta karashe tana dariyar zolaya. Hajiya Binta ta ja tsaki.
"Ai kuwa da anyi girman kwabo, ballantana kuma sanin kanki ne Alhaji banda waccan shegiyar babu mai fad'amasa ya ji acikinmu, abin na kona raina."
  "Ai ku kukayi sake, ki bada hadin kai kika yanda komai zai chanja mana."

 
  Iyakar abinda Ummi ta tsinkaya kenan cikin zantukansu kafin kuma ta ta6e baki kawai, a kasan ranta kuwa tana tsoron ranar da Mami zata gaji ta korata daga gidan, watakil shikenan kuma dukkan gatan da ta soma samu na ilimi ya rushe. Saidai kuma tayi mamakin yanda Hajiya Binta take kula kawaye irin haka, da ace sun saba kwarai, da babu abinda zai hanata yin shishshigi wajen bata shawarar watsi da zantukan wannan mata. Da sallama ta nufi shiga falon, saidai kuma tayi turus ganin takalman maza har sawu hud'u da kuma na mata a bakin kofar, haka kawai ta ji gabanta ya fad'i, koda ta shiga bata ga kowa ba a wannan falon, ta numfasa ta karasa ciki, har ta chanja sutura tana cike da tunanin wadanda suka zo, sai kuma ta tunano da su Yaya Haidar, watakila su d'inne suka zo. Ta shirya cikin atamfa riga da zani da dankwali bayan tayi wanka sannan ta d'auro alwala ganin Magriba na dab da yi, fitowa tayi falo, tana son zuwa sanarwa Mami cewa ta dawo saidai kuma batason iske bak'in gaba d'aya nauyinsu take ji.
  A kicin ta had'u da Ramma, ta gaisheta. Ramma ta amsa tana fad'in.
  "Yanzu kuwa Hajiyar ke tambayarki, ta ji shiru nace kin dawo kina ciki. Kije tana nemanki."
  Gaba daya ta ji tsoro ya kamata har yanayin fuskarta ya nunawa Ramma.
  "To ai naga tana tare da bak'i yanzu."
Ramma ta kama baki. "Su waye bak'in? Ai 'yan gida ne, Hajiya Babba ce fa da yaranta."
  Ta gyada kai sannan ta juya ta nufi hanyar falon Mami gabanta na dukan tara-tara, ita da ba don ance Mami ke nemanta ba da babu inda zata. Har ta kai kofar shiga sai kuma ta juya da sauri don ji tayi ba zata iya ba. Muryoyin da ta jiyo daga bayanta na matasan yasa dole ta juyo. Gaba daya mazan ne suka fito da alamu dai masallaci suka nufa sakamakon kiraye-kirayen sallar da aka soma. Kallo d'aya tayi musu ta durkusa da sauri ta gaishesu. Suka amsa sannan ta basu wuri don su wuce. D'ago idon da zata yi sukayi ido hud'u da Faruk wanda dagaske kallonta yakeyi, ta gwammace ace bai kalleta din ba domin kuwa kallo ne ba na arziki ba face kallon raini, fuskarsa babu wata alamar fara'a; ta sadda kanta da sauri.
  "Ai kuwa Mami na ta cigiyarki da alama kin mata wani gagarumin laifi Ummi." Cewar Adnan ya karashe da dariyar zolaya.
  "Um." Shine abinda ta furta kawai da murmushi dauke saman fuskarta. Bayan sun wuceta ta bi bayansu da kallo. Wannan karon, Yaya Usman ne kadai ya sanya manyan kaya, gaba daya su ukun k'ananun kaya ne jikinsu. Hajiya Babba Allah Ya bata arziki na zaratan maza wadanda dukkansu basuyi kama da ragwaye ba a komai da ya shafi gwagwarmayar rayuwa da sauransu. Saidai da ace za'a bata za6in wanda yafi kyau da burgewa a fuska acikinsu, toh fa babu abinda zai hanata nuna Yaya Haidar bisa hujjarta na ganin duk ya fisu fara'a. Koda kuwa tasan da yawa cikin wasu matasan yanmata irinta, zasu iya bugun kirji su za6i Yaya Faruk, ita kam banda ita. Tsakani da Allah ta ji haushin kallon da ya bita da shi tamkar wanda ya ci karo da kashi, ta numfasa don tuni sun jima da kauracewa ganinta ta juya, gabanta ya fad'i ganin Ihsan tsaye ta harde hannuwa a kirji ta zubamata na mujiya fuskarta dauke da wani mugun murmushi. Ummi ta kauda kai ta bi ta gefenta zata wuce saidai maganganun da ya soma fitowa daga bakin Ihsan ya tsayar da ita cak!
   "Mutum dai ya tsaya iyakar matsayinsa, ko kusa kada yayi tunanin zai iya da Babban Goro, duk cikinsu babu sa'an aurenki, don haka ki maida maitarki, kurwar kaf dinsu, ta fi karfinki."
   Daga wannan ta sanya kai ta fita tana kwalawa Ramma kira. Iyakar radadi da bacin rai, Ummi ta ji shi a ranta, batasan sadda idanunta suka ciko da kwalla ba, wannan cin zarafi har ina? Kai tsaye an yankemata mummunan hukuncin da ko a mafarki bata yi zaton koda mak'iyinta zai shaideta da aikatawa ba, toh daman ina ita ina ire-iren wadannan mazan? Yaudarar kai ne, koda ta auna cewa Ihsan batasan irin zargin da ya kamata tayi mata  ba, yasa ta yin murmushi mai ciwo, da alama Ihsan bata gama sanin bambancin matsayinta da su ba, tabbas ta cucesu tunda har ta had'asu da ita, watakil da zasu ji da sai sun had'a da kai mata bugu don haushin abinda tayi musu. Ta share batun gami da goge fuskarta sannan ta juya ta koma don ta tabbatar a yanzun Mami ta shiga sallah. Dakinta ta koma itama ta tayar da nata sallar, saida ta idar ta kaiwa Allah kukanta akan Ya ji6anci lamuranta. Bata da kowa sai Shi, Shi ne gatanta. Yayi rahma ga Mahaifiyarta. Haka tayita kwararo addu'o'i har tana fidda ruwan hawaye kafin kuma ta shafa. Bata kai ga mikewa daga wurin ba ta ji Fahad na kwala mata kira adaidai sadda ya murd'a kofar dakin nata.
  "Ummi! Kizo inji Mami."
  Ta mike batare da ta cire hijabin ba ta bi bayansa.

No comments:

Post a Comment