Monday, 19 December 2016

Yar Ajinmu 5th

'YAR AJINMU CE

Part 11 last

Kayansu Nabila ta dauko dan
tafiya dasu yayinda alh ibrahim yace,
su bar waðannan kayan nan karsu
dauki komai, kai tsaye banki ya wuce
ya zaro kudi ya nufi super market,
akayi masu siyayya mai yawa ta
kayan sawa da kayan kwalliya hatta
mayuka sai da ya siya masu da sauran
kayayyakin gyara dai. Rayuwar sai ta
dawo musu wata sabuwa kamar basu
ba komai nasu tsaf-tsaf Alh ibrahim
ya dauki su bintu tamkar "yayan da
ya haifa da kansa, saboda mahaifinsu
yayi ma dansa halacci dashi kansa
sanadiyyar bintu, gashi yanzu zai
saka masa shima, Yasan ko yana cikin
kabarinsa zaiji dadi, domin yasan
yana tuna marayun da ya bari a
duniya, sai dai muce Allah ya jikansa
ya kai rahama kabarinsa dama sauran
musulmai baki daya. Watan su bintu
daya gidansu jamilu sai da dukkansu
suka koma makaranta yayinda bintu
ta samu gurbin karatu a AL-QALAM
UNIVERSITY KATSINA level 200 yayinda
Aka kai Nabila jami'ar UMARU MUSA
YAR'ADUA a aji daya fatima kau ssce ta
canza sannan ta koma FEDERAL
COLLEGE OF EDUCATION Duk a katsinan
dikko. Idan bintu na tuna baya takan
fashe da kuka, takanji kamar ba ita
bace tayi rayuwar baya mai cike da
kalubale da tashin hankali, idan tana
tunawa takan ce a zuciyarta nafi
tausayin fatima saboda karama ce
acikinmu kuma yarinya mai bukatar
kulawa ta musamman. Wani hutu da
suka dawo gidane, alh ibrahim ya
lura da jamilu kamar yana son bintu
ne dan haka ya tuntu6e shi da
maganar ya kuma amsa cikin kunya,
yayin da itama bintu aka tambayeta
ta amince. Kamar wasa akasa biki da
niyyar zataci gaba da karatunta a
gidan mijinta amma a matakin per
time Asabar da lahadi zataje ta dawo.
Nabila da fatima kuwa sai sukaci
gaba da karatunsu babu tsangama
cikin jindadi, burin Nabila ta zama
Likita yayinda burin Fatima ta zama
Yar jarida, Bintu ce ke son zama
Lauya koba komai zata gaji margayi
mahaifinta, ita kuwa mahaifiyarsu
dama likita ta karanta kuma likitar ce
har Allah yai mata cikawa TAMMAT BI
HAMDULILLAH domin kira dan gyara
ko godiya 08033002473 SADAUKARWA-
A matsayin barka da sallah. JINJINA ga
friends dina na wall dake bina a
wannan labarin musamman irinsu
=Bamai dabuwa =Rabiu Usman dan
hausa =Ummah m ladan =Rukaiyat
Usman =Mustapha Abbas =Ayuba
muhd Danzaki =dalha umar talle
mairua =Mustapha ahmad
nadanjanku=Muhd bello danja= Hakeemah idris YABAWA GA MASU BINA A
GROUP-GROUP DIN -DUNIYAR
MARUBUTA -HANNU DA YAWA
WRITTERS -TSANGAYAR MARUBUTA -
ZAUREN MARUBUTAN HAUSA -
KHALEESAT HYDAR NOVELS -TASKAR
GIDAN LITTAFI Da sauransu Saikun jini
a wani (GAJEREN LABARIN MAI
FADAKARWA) Da fatan wannan ya
kayatar daku *I luv u all my frnds*
Zaidu Barmo MrZaid Jibia Katsina
state

No comments:

Post a Comment