💔💘 *SAKACI* 💘💔
0⃣7⃣
© Fatima A Garba.
Cikin Mama ya shiga wata tara, sak'on kira ya riskesu daga Lamido cewan mahaifinta bashi da lafiya.
A washegari suka shirya zuwa Wase don zuwa duba mahaifinta, amma lokacin da suka isa rai yayi halinsa, Mama ta yi kuka sosai ta kuma shiga damuwa fiye da tunani.
Lokacin da mahaifinta ya yi kwana bakwai da rasuwa Lamido ya kira Baba ya shaida mishi yana so ya bar Mama har sai bayan ta haihu kafin ta koma.
Babana bai wani damu ba kuma ba ta re da 6ata lokaci ba ya amince.
Koda Lamido ya samu Mama da maganar ta yi farinciki sosai ko ba komai zata d'an samu nutsuwa.
Satin Mama biyu a Wase ta haifi d'a namiji, Lamido yayi farinciki mara misaltuwa, koda aka sanar da Baba bai zoba har sai ana gobe suna kafin yazo, Lamido yamai fad'a sosai karshe ya kare kanshi da cewa yanayin aikinshi ne.
A lokacin da Baba ya shiga d'akin da aka warewa Mama wanda zatayi jego aciki, ya samu Innayo ta gama yiwa yaron wanka ta shiryashi, bayan ya gaisheta suka d'an ta6a hira kafin ta mik'a mai yaron amma ga mamakinta Baba yak'i kar6an yaron.
Tashi ta yi ta d'aura mai yaron akan cinyarsa ta yi ficewarta saboda tana tunanin kunya ce ta hanashi kar6a.
Ahankali ya sauk'e da idanuwan shi a kan yaron, atake yaji wani irin k'aunar yaron ne ya d'arsu acikin zuciyar shi.
A hankali ya fara shafan kanshi wanda ya cika da kwantaccen suma, a hankali kuma ya fara murmusawa.
Gaishe shi Mama ta keyi amma sam bai san tanayi ba, wani farinciki ne ya baibayeta ganin yadda Baba ya rungumi d'anshi.
"yanzu fa ka fara tsufa" zuciyarshi ta ankarar da shi.
Da ga nan zuciyarshi ta fara tunano mai da burinshi ta re da wasu burika marasa kyau.
Kamar wanda aka tsinkara ya tashi da zafin nama gami da dungurar da yaron a gefan Mama, kafin kuma ya fice cikin 6acin rai.
Cikin k'ank'ani lokaci fuskar Mama ta sauya daga farin ciki zuwa damuwa, ta rasa mai yake damunshi, wani irin ra'ayi ne dashi, ita toh ina zata sa ranta.
Gudun d'aurawa kai damuwa yasa ta zuba tambayoyin da zuciyarta ta ke neman ansoshin su a kwandan shara.
Ranar suna yaro yaci sunan kakanmu wato Hamidu.
Tun daga ranar Baba bai sake zuwa d'akin da Mama ta ke ba har ya koma domin komawar tashi ma a bakin Innayo takeji, daga Innayo har Lamido basu ta6a lura da rashin shigar Baba wurin iyalinshi ba.
Haka Mama ta cigaba da rainon Ya Hamid har suka cika wata uku, anan Lamido ya umarci su Innayo da sumaida Mamana d'akinta bayan ya aika an sanarwa da Babana.
Bayan Mama ta koma ne kakarmu wato wacce ta haifi mama, ta koma garinsu tunda dama ita y'ar gombe ce.
Ba yadda Lamido baiyi da kakarmu akan ta cigaba da zama a garin Wase y'an uwanta suka k'i yarda.
Ranar da ana washegarin Mama zata tafi sunyi kuka sosai ita da mahaifiyarta k'arshe suka dangana.
***
Ba laifi da Mama da ta koma ta d'an samu sauyi dangane da zamanta kewanta da Baba, ya rage sosai daga abinda ya ke mata.
Mama ba ta jima da komawa ba aka tura Babana k'aro karatu a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, da ga ma'aikatarsu, amma bai tafi da Mama ba yace ta tsaya ta k'arashe karatunta tunda shima ba zama zaiyi ba, haka ya tafi yabar Mama sai dai yazo lokacin da yaso.
Wannan tafiyar da yayi yabar Mama da k'aramin ciki wanda itama sai bayan tafiyarshi ne ta fahimci hakan wannan karan sam tak'i nuna alamun akwai juna biyu a tare da ita tunda ita ba mai laulayi ba ce, kuma bata da girman ciki.
Cikin Mama na da wata shida Baba yazo gari sosai Mama bata bar wani gurbi da zai fahimci tana da juna biyu ba, har ya gama kwana biyunsa ya koma.
Tunda ya tafi bai sake waiwayen gida ba har sai da cikin Mama ya shiga wata tara, aranar da ya dawo kuwa Mama ta ga tashin hankalin da bata ta6a zata ba.
K'arshe korarta yayi, ya ce ta barmai gidanshi, bata wani tsaya bashi hakuri ba, ta fice domin ba ta ga dalilin hakan ba, duk da damuwa ce fal cikin ranta domin bata da kud'in da za ta yi kud'in motar zuwa Wase ga Ummi ta yi tafiya.
Wata dabara ce ta fad'o mata nan ta d'auki wasu atanfofi da aka bata na barkan haihuwan Hamid dama bata d'inka ba, shi ta d'auka ta kaiwa wani mai shago a kasuwan yantifa ta siyar duk da ba'a siyesu da daraja ba amma dai ta samu kudin da zai kaita Wase, daga kasuwan tasha ta wuce da Hamid goye a bayanta.
Lokacin da taje Wase Lamido ranshi ya 6aci, a ta ke ya tusa d'an aike akan yana son ganin Baba a washegari.
Baba yasha fad'a a wurin Lamido sai daga bisani ne ya tambayeshi dalilinshi na korar matarshi, Baba yasan bazai ta6a fad'awa Lamido dalilinshi ba shiyasa yace Mama bata jin maganarshi ne kawai.
Lamido ya yiwa Mama fad'a gami da nasiha mai shiga jiki duk da bai yarda da abinda Baba ya fad'a ba, tunda yafi kowa sanin halin Mama.
Kafin daga bisani ya koma ga Babana
"Manu"
Lamido ya kira sunan Babana, cikin ladabi Baba ya d'ago kai ya dubi Lamido kafin kuma ya ansa da "na'am".
Cikin 6acin rai Lamido ya ce.
" Manu ka ban mamaki matuk'a ban ta6a zaton ko da wasa zaka iya korar y'ar uwarka daga gidanka ba duk kuwa da girman lafin da ta aikata maka, na yi zaton koda ace laifin da ta aikata maka girmanshi yafi gaban a kwatantashi kai mai iya yafe mata ne"
Lamido ya d'an dakata kad'an, kafin kuma ya cigaba.
"Duk ranar da kasake cewa ta fita ma a gida kokuma ka bud'e baki ka saketa, ban yafe maka ba koda kuwa bayan raina ne, Manu ina rok'onka da ka rik'e Sakinatu amana bata da kowa sai kai, don haka karik'emin ita amana idan kaci amanarta Manu amana zata cika, kuma ka tattara matarka kutafi kayita hakuri domin haka aure ya gada karna sa ke ji ko na gani".
Haka Baba ya ya d'auki Mama suka koma, ba don fad'an Lamido ya shige shi ba.
Washe garin ranar da suka koma Mama ta haihu nan ma namiji ta haifa, a wannan karan ba irin bak'in ciki wanda Mama bata fuskanta ba domin ya rage kashi kusan saba'in na daga d'ari a cikin hidimar gida da yakeyi.
kayan da za'a sawa jariri ma bai siya ba, na Hamid aka cigaba da mai anfani dashi.
Duk wata kulawa ta mai jego mama bata samu ba, ranar suna Lamido ya aiko da raguna biyu da kayan abinci yaro kuma yaci suna Abdallah.
Lokacin da kayan abincin da Lamido ya aikowa da Mama suka k'are lokacin ne Mama ta kuma shiga tashin hankali domin Baba sai yayi wata hud'u biyar bai zoba aikema sai yaga dama ya ke musu, sai dai wani lokacin Lamido yakan mata aiken kud'i ko kayan abinci, lokacin ne ta ke samu sauki.
Haka Mama ta cigaba da rayuwar aurenta cikin wahala, ya Abdallah na da shekara biyu Allah ya kar6i ran Lamido bayan yayi y'ar gajeruwar jinya, jama'ar Wase sunyi kukan rashin shugaba nagari, mama tafi kowa kuka da shiga damuwa domin gani ta ke gatan ta ya kare bata da wani sauran gata aduniya, Lamido shi ne komi na ta.
Bayan kwana arba'in mutanan Rugar Fulani suka nemi Baba da ya kar6i sarauta Lamido amma sam Baba yak'i kar6a.
Haka dai saurata tabar gidansu Baba, ba k'aramin 6acin rai y'an'uwan Lamido suka shiga ba amma ba yadda zasuyi haka suka hakura.
*****
Wata hud'u da rasuwar Lamido, Mama ta fahimci ta na da shigan ciki, nan fa hankalinta ya ya tashi matuk'a, ta tabbata bata da sauran dabara, sannan wannan cikin yazo mata da sauye-sauye sa6anin na baya, sam bata iya jurar yunwa, wani lokacin har ta na mamakin yawan abincin da ta keci ga yawan kasala.
Da daddare bayan sun gama cin abinci Mama ta samu Baba ta sanar mai ta na d'auke da juna biyu.
Cikin k'ank'ani lokaci fuskar Baba ta sauya tamkar bai ta6a dariya ba, idanunshi sun kad'a sunyi jajir, yadda ya ke nunfashi abin har saida ya ba Mama tsoro.
Bakinshi har kumfa ya ke yi,
Fad'a ya ke tamkar zai ari baki, a k'arshe ya tabbatarwa da Mama dole ne azubar da cikin domin bazai laminci hakan ba.
Mama bata mai gardama ba, ta tabbatar mai da amincewarta, domin ita kanta ta gaji da halin ko inkula da ya ke nuna ma ta, ita da yaranta, bazata so ta cigaba da haihuwa a cikin wannan halin ba.
Wannan amincewar da Mama ta yi, ya rage kashi talatin cikin d'ari na daga haushinta da ya keji.
Washe gari da kanshi yaje ya nemo mata saiwan da yasan suna zubar da ciki ya kawo ma ta yace ta jik'a tasha, ba ta re da gardama ba Mama ta jik'asu.
~Ummu Hanan~
No comments:
Post a Comment