Saturday, 10 December 2016

Dan Adam 3

DAN ADAM
@Rufaida Omar
  (03)

"Assalamu Alaikum." Cewar Yaha alokacin da ta murd'a k'ofar falon ta sanya k'afa. Wata dattijuwa wacce ke zaune, wata budurwa mai kimanin shekaru sha shida. Tana zaune a k'asan lallausan kafet tana daddanna mata k'afa. Ta nutsu sosai, kamar kace arr! Ta arce. 
   Ummi dai kallonsu take, daga yanayin yanda ta ga Hajiyar na dubanta, ta  sha jinin jikinta, da alama dai matar ba ta da mutunci don kuwa fuskarnan nata babu ko alamun fara'a. 
    "Ranki ya dad'e baya goya marayu, barkanki da hutawa."
  Hajiya tayi wani murmushi, da alama ta ji dadin wannan kirari na Yaha. Ummi dai kallon ikon Allah take, yanayin shigarta da komai ma, sun isa shaidar tana cikin rayuwar daula. Wani kallo da Yaha ta watsa mata ne ya sanya ta ba shiri russunawa sosai gami da rankwafar da kanta ta gaisheta. Hajiyar bata ko amsa ba, saidai ta k'ura mata ido tana k'are mata kallo. Can kuma ta yamutse fuska ta rausaya kai gami da maida dubanta ga Yaha.
   "Wannan ce?"
Yaha ta washe baki tana jinjina kai.
"Kwarai kuwa ranki ya dad'e uwar gida ran gida, itace, sunanta Hasiya amma Ummi ake kiranta."
   Ummi dai sai zazzare ido take kamar shege a rabon gado, Hajiya Madina tayi murmushi, ko babu komai takan ji dadin wannan kirari da Yaha ke mata. 
  "Tayi sosai, na tabbatar, zata iya dukkan ayyukan da na na bata. Ince dai bata da son jiki?"
  Yaha har lokacin bakinta ya k'i rufuwa don ji take kamar ta shid'e don dad'i domin kuwa ta sha kawowa Hajiya Madina yara, basu yi mata ba.
    Ta janye k'afafunta, gami da kallon budurwar batare da tace uffan ba, ta mik'e ta wuce don ko Hajiya batayi magana ba, ta karanceta, wato dai ta basu guri.
    Bayan komawarta ciki ne, Hajiya Madina ta dubi Yaha.
  "Yahanasu, ina fatan kin shaida mata cewar banason wasa, ba kuma na son son jiki. Dukkan wasu ayyuka da na sanyata, inaso ta kammala su alokacin da ya kamata. Ba kuma na son k'azanta, ta kula sosai don kuwa naga yanayinta, da alama k'azamar ce."
   Ummi ta sunkuyar da kai tana sosa gashin kanta wanda amosani ya bi ya takura mata, idan ma ance da kwarkwata lallai babu musu don bata da gatan da Saude zata wanke mata kai. 
    "Kiyi hakuri, na tabbatar ba zaki samu wannan matsalar ba. Sau daya aka gwada mata yanda zata gyara jikinta, na tabbatar babu wata matsala da zata biyo baya."
  Hajiya Madina ta jinjina kai alokaci guda ta yamutse.
  "Yauwa, don kinsan banason abinda wadancan shirmammun zasu samu damar zagina. Ko kusa banason wani mishkila ya fito daga d'akina."
   Dariya Yaha tayi, ta gane Hajiya Madina tana nufin kishiyoyinta, Hajiya Rakiya da Hajiya Munira. 
  "Ai kin wuce nan Hajiyata, baya goya marayu. Kar kiji komai, yarinya ce mai kaifin basira. Zata bi dukkan umarninki batare da kin 6ata rai ba.
  Kwarai, ta ji dadin kalaman Yaha. Daga nan ta mike da nufin zuwa gabatar da sallar la'asar, bayan ta umarci budurwar nan da ta ambata da Amina, da ta nunawa Ummi wajen kwanansu.
    Amina a gaggauce ta bi umarnin Hajiya. Suka wuce tarr har Yaha wacce zata d'auro alwalar sallah itama. Ummi ta dubi d'akin, katifa d'aya ce sai filo, a gefe kuma jakar kaya ne. Sai kofa daya wacce ta ga Yaha ta shiga ciki, wannan ya tabbatarwa Ummi, bandaki ne. An malale dakin da ledar tsakar daki. Fentin dakin mai wani kyalkyali ne, fari da ruwan hoda, saidai babu komai na more rayuwa ciki. 
    Acan kusa da jakar kayanta, ta ajiyewa Ummi nata da murmushi saman fuskarta ta dubi Ummi, haka kawai ta tsinci kanta da murna sosai, ko babu komai ta samu abokiyar hira. 
   "Nan zaki dunga kwana."
  Ummi ta mayarmata da martanin murmushin, saidai har lokacin bata saki jiki ba don kuwa ko k'arar k'ofa ta ji sai ta firgita. Ta riga da ta saba da hakan.
   Yaba ta fito ta shimfida dardumar dakin ta tayar da sallah. Itama Ummi ta shiga, saidai tayi turus don kuwa bata saba da bandakin yan gayu har haka ba. 
  "Bari na nuna maki yanda zakiyi."
  Cewar Amina daga bayanta, wannan yasa Ummi matsawa, ta shigo. 
   Nan ta gwada mata komai, Ummi tayi godiya cikin muryarta sassanya sannan ta shiga ta d'an kara k'ofar don ta tsorata, bata so ta rufe ta kasa bud'e kanta. 
     Bayan tayi alwala, irin yanda ta saba ganin mutane nayi don kuwa ko alfarmar zuwa makarantar islamiyya, Ummi bata samu ba. Tayi yanda ta iya sannan ta fito ta tayar da sallar. Tasan ana yin sallah raka'a hud'u a lokacin nan  hakan yasa ta soma babu wani karatun kirki don babu abinda ta iya.  Ta idar ta zauna tana motsa baki sannan ta yi jugum tana kalle-kalle.
   Bayan Yaha ta kammala suka fita, Ramma ta basu abinci, nan suka ci sannan Hajiya ta sallami Yaha ta tafi da abin arziki. 
    Sai lokacin idanun Ummi ya yi kwal-kwal. Ta soma matsar kwallah tana sosa kai.
  Hajiya ta ja tsaki ta dubi Ramma.
  "Ramma, fita da yarinyar nan ki dubamin kanta, idan da matsala kiyi mata dukkan abinda ya dace don Allah."
   Ramma ta mike.
"Angama Ranki ya dad'e."
   Ta ja Ummi wacce ke faman ajiyar zuciya da sheshsheka suka fita. 
   Bayan ta tabbatar da cewar tana da kwarkwata, ta koma ga uwardakinta ta amshi kudi ta sanya gyalenta ta ja Ummi suka fice daga gidan.  Kai tsaye wani gida k'arami wanda Ramma ke zaune ciki da 'yan marayun yaranta maza uku suka nufa, ta dubeta.
  "Ki zauna ki jirani ina zuwa."
  Ummi ta gyad'a kanta da sauri.
  Ba jimawa Ramma ta dawo da kullin ledoji har da fiya-fiya.
   Nan ta zauna ta gyare kan Ummi tsaf, ta wankeshi da karkashi a karshe, Ummi ta sha kuka don azaba. A karshe ta mik'a mata wani zani  bayan  ta sanyata tayi wanka.
  "Goge gashin naki, yarinya mai gashi haka kin barshi ya wulakanta? Kai Allah Ya kyauta dai."
  Ita dai Ummi bata tanka ba, ta kara jan zani ta rufe jikinta sosai sannan tayi amfani da wani zanin da ta mik'o mata tana goge kanta. basu bar gidan ba saida Ramma ta taje mata ta sanya man zaitun sannan ta koma ta dauko mata kaya kala d'aya na Amina don duk cikin kayan Ummi babu wani na arziki na sanyawa. 
   Riga da zanin atamfa ne har sun soma kod'au, saidai sun fi nata daraja sau dubu, sannan suka fice.
   Ita kanta Ummi ta ji dadin gashinta, a farfajiyar gidan suka iske wata bus katuwa ta irinta 'yan makaranta ta tsaya. Yanmata ne su biyar sai yan samari uku, daya zaikai shekaru goma sha bakwai, yayinda dayan zaikai kimanin shekaru goma sha daya sai na karshen wanda baifi shekaru bakwai ba suka fito daga cikin motar gaba dayansu cikin kayan makaranta. 
    Ramma ta dubesu da fara'a.
"A'a yau dai kun dawo da wuri tunda ba'a kai da kiran Magariba ba."
   Ta k'arasa fad'in hakan a zolayance tana sauke idanunta akan d'anliti direba.
   Fuska a daure ya amsa.
"Sai ki dunga zuwa daukarsu mana ke."
  Gaba daya yaran suka dara, dan saurayin mai sha bakwai ya dan bugi motar.
  "An gaida dan autan direbobi!"
Sun riga sun saba zolayarsa don kuwa wani sa'in ba shi da wasa, idan kuma ya so, wataran sukan yi raha iyakar raha. Toh haka yake da Ramma ma.
    Daya cikin yanmatan nan ta dubi Ummi fuska a yamutse.
  "Wannan kuma fa Ramma?"
  Ramma ta amsa fuska a sake.
  "Ummi ce, sabuwar 'yar aikin Hajiya ce."
   Ta bi Ummi da kallon raini a karo na biyu kafin ta kad'a kanta tayi gaba tana fad'in.
  "Ita kam Hajiyarku ba dai kwashe-kwashe ba."
  A fusace ta ji saurayin ya bata amsa.
   "Ta fi wacce fad'anta ke korar 'yan aiki. Banza kawai da ke!"
   Ta juyo ta dubeshi ranta a 6ace.
  "Uwata ka zaga?"
  Ya d'aga kafad'a yana duban su Ramma.
  "Kunji na ambaci sunan wata?" Ai kuwa ta fashe da kuka gami da yin Allah Ya Isa. Da gudu tayi ciki don kuwa tasan muddin ya cafketa ba  zata ji ta dad'i ba. 
  Danliti ne yayi saurin rik'eshi..
"Haba Adnan, kana babba kana jan kannenka da fad'a? Shige ka wuce don Allah."
   Adnan yayi kwafa ya dauki jakar islamiyyarsa yayi ciki yana fad'in.
( "Stupid Girl kawai.") 
  Daga haka sauran suma sukayi ciki.
  Ummi dai tana ta kallon ikon Allah, ita tsoron budurwar ma ta ji ganin irin kallon rainin da ta bita da shi.
   Ta bi bayan Ramma da sauri sukayi ciki.
  K'aramin yaron da budurwa d'aya ta ga sun k'ara yin ciki sun mik'a hanya. Abin ya bata mamaki, tayi zaton nan kad'ai ne a gidan ashe dai yana da girma. Shi kuwa Adnan da macen d'aya ta ga sun yi inda aka kawota, wajen Hajiya Madina.
   Anan tsakar falon suka iske Adnan yana labartawa Hajiya abinda ya faru yana dariya alokacin da ya bud'e firij ya d'auki robar ruwa d'aya da niyyar sha.
  Hajiya ta girgiza kai tana nunashi da yatsa.
  "Ka dai kiyaye Adnan, banason tsokana."
  "Eh mana, kyace bakyason tsokana tunda burinki ya cika an jefamin bak'ar magana. Toh wallahi bari Alhajin ya dawo, bazan lamunci rashin tarbiyyar yaranki ba. Banason cin kashi."
   Gaba daya tuni sun maida dubansu ga k'ofar shigowa falon, Ummi ta kurawa matar ido wacce ke rik'e da labule batare da ta karasa shigowa ciki ba tana faman bambami. Bak'a ce, irin bak'in da hutu ya gama ratsawa, ta ci ado har ta gaji don kuwa ita ce a fadar Alhajin nasu. Sai zuba uban k'amshi takeyi.
  Hajiya Madina batace uffan ba, sai murmushi kawai da tayi. Ko babu komai har ranta ta ji dad'in abinda Adnan ya fad'a saidai dole a fili ta k'i gwadawa don ko kusa bazata so Alhaji ya soma ganin rashin mutuncinta ba. Gwara acigaba da rayuwar gidan a haka. 
  Itama matar tsaki ta ja sannan ta fice cike da jin haushin rashin tankawar da dukkansu basu yi ba. Bataso hakan ba ko kusa. 
   Bayan tafiyarta Adnan ya ja guntun tsaki ya dauki jakarsa ya fice yana fad'in.
  "Ni kaina har ya soma ciwo ma."
  Sama-sama ya jiyo muryar Ramma tana magana don har ya fice daga falon zai nufi dakinsa.
  "Kayi sallah ka zo akwai lafiyayyen tuwo da miyar kuka mai man shanu, ka ci ka sha magani."
   "Shiyasa nake sonki Rammatuwa."
  Ya fad'a cikin d'aga murya har ya basu dariya. 
   Kiraye-kirayen sallar da aka soma ne ya sanyasu barin falon. Itama Ummi ta shige dakinsu. Anan ta iske Amina tana kokarin sanya hijabi.
Murmushi tayi mata.
  "Har an wanke?"
  Ummi ta gyada kanta murya ciki-ciki ta amsa da eh tana mai kunce daurin dankwalinta. Amina ta zaro ido.
  "Masha Allah, kina da gashi ashe."
  Ummi dai murmushi kawai tayi.
  Jin masallacin kusa da gidan sun tayar da ik'ama ya sanya Amina shimfid'a darduma da sauri tana fad'in.
  "Kiyi alwala mana."
   Hakan yasa itama Ummi ta shiga da saurinta. Saida ta rage cikinta ta ja ruwa bayan tayi tsarku kamar yanda Amina ta gwada mata yanda zata ja d'in sannan ta dauro alwala ta fito. 
   Bayan sun idar suka zauna jugum, Amina na faman addu'o'i ita kuwa kallonta kawai takeyi, idan ta gaji ta hau duban dakin.

    
   
    
   
  

No comments:

Post a Comment