Saturday, 10 December 2016

Ɗan Adam 4

  DAN ADAM

@Rufaida Omar
          04
     
"Sannu Ummi."
Muryar Amina ta katsemata tunani, ta dubeta, sukayi murmushi a tare.
  "Yauwa."
  Amina ta ninke abin sallar ta ajiye a gefe. Zama tayi a gefen katifa kusa da Ummi tana dubanta.
   "Daga wane gari kuke?"
"Ringim." Ta amsa a takaice. 
"Lallai, baku da nisa sosai."
Ummi zuwa yanzu ta dan saki jiki da Amina ganin irin yanda take janta a jiki.  Wannan yasa itama bata ji nauyin tambayarta ba.
  "Ke ba anan kusa kike ba?"
Ta gyada kai.
"Anan dai nayi rayuwata, amma mahaifina d'an Maradi ne can cikin jamhuriyar Nijar. Zama da neman abinci ne ya kawoshi Nijeriya sukayi aure da Innata, amma yanzu ya rasu, ya barmu mu hudu yaransa. Ni ce 'ya ta uku a cikinsu."

  Ummi ta d'an tallafi kumatunta.
"Kema aiki kike yiwa Hajiya?"
Amina ta murmusa.
"Ni ina yiwa Hajiya Mama aiki ne, kanwar Hajiyarnan ce, abinda yasa kika ganni a gidannan, sunyi tafiya ne da mijinta da yaransu, shine dalilin da yasa na dawo nan da zama kafin su dawo."
    Ummi ta jinjina kai cike da gamsuwa. A ranta ta ji babu dad'i, kenan itama wataran zata bar gidan ta barta? 
   "Ya dai Ummi? Kinyi shiru ina magana."
  Ummi a sanyaye ta girgiza kai.
"Bakomai."
  Jin haka yasa Amina yin murmushi.
"Shikenan, tashi muje mu tattara falo da kicin kafin Hajiya tayi magana, ki dunga lura da dukkan abinda nakeyi, nasan karshe ke zaki maye gurbina."
   Ummi bata ko damu ba, idan ana sabo da aikin wahala, ai yaci kuwa ace ta saba, ina take samun damar yin cikakken awa sadda tana gidan babanta batare da an had'ata da wani nannauyan aikin ba? Gashi anan har gatan da za'a gyara mata kai a bata wajen kwana tsaftatacce da abinci mai kyau ta samu. Ai babu abinda zata ce ga Ubangiji sai godiya.
   Haka ta bi bayanta zugui-zugui suka fita. A falon suka iske Adnan da kannensa su biyu, wadanda ta ji Ramma ta ambacesu da Ihsan, Hanifa da Fahad wanda shi ne auta a d'akin nasu. 
    Adnan hankalinsa kacokam yana kan wayar hannunsa yana faman latse-latse, yayinda Ihsan ta dukufa wajen koyawa kannenta aikin gida da aka basu a makaranta. Shekarun Ihsan goma sha uku a duniya zata shiga na hud'u, sa'ar Ummi ce. Hanifa kuwa, tana da shekaru goma sha biyu bata da tazara tsakaninta da Ihsan, Fahad ne mai shekaru takwas a duniya. Daga kansa kuma, Hajiya Madina bata k'ara haihuwa ba. 
   Yaranta gaba daya su takwas ne cif, mata uku ne kafin zuwan Adnan duniya, Rahila, Na'ima, Aisha, gaba dayansu ukun suna gidajen aure.
      Shigowarsu falon ne yasa su d'ago kai su dubesu. Adnan ya k'urawa Ummi ido fuskarsa a sake sannan ya maida dubansa ga Amina.
  "Ummi sunanta ko?"
Amina ta gyada kai tana murmushi wanda ya riga ya zamto jikinta, ko kusa bata rabo da shi.
   "Itace." Ummi ta durkusa ta gaisheshi da saurinta sannan ta gaida su Ihsan. Ai kuwa  su Ihsan suka tuntsire da dariya. Adnan ya dauki filon kujera yana dariya ya jefi Ihsan da shi.
  "(See you), mene abin dariyar?  Ai na isa a gaisheni, kune dai daga yau kada ki k'ara gaishesu, na tabbatar kin girme musu." Ya karashe yana maida dubansa ga Ummin.
   Ihsan ta jinjina kai.
"Tab, wallahi saidai mu tafa, na tabbatar bazata girmeni ba. Kuma idan ma aka ajiye wannan a gefe ai 'yar aikinmu ce dole ta girmama mu."
   Ta karashe tana jifan Ummi da kallon eh sun isa. Ummi dai ta kara sunkuyar da kanta. Amina batace komai ba don kuwa bata fiye shiga harkar Ihsan ba, sanin da tayi mata na cewa ta tsani wasa da duk wani wanda yake karkashinsu. A ganinta, bai kai har a zauna a sakar mishi fuska ba. 
  Abin yakan bawa Amina mamaki, yarinya tun bata tafasa ba tana neman k'onewa? Ta tabbata nan gaba idan Ihsan tafi haka za'a ga abu.
   "Zaki fara ko?" Cewar Adnan lokacin da ya mike tsaye.
  Ihsan ta dara a karo na biyu sannan ta dubi su Hanifa.
  "Malamai ku maido hankalinku mu cigaba. Nasoma jin bacci wallahi."
  Wannan yasa su Hanifa nutsuwa don suna d'an shakkarta kasancewarta itama wani sa'in akwai masifa. Hakanan ta iya kaiwa mutum bugu, kodan ita din tana da jiki kamar kazar gona. 
   "Muje Ummi."
  Sai lokacin Ummi ta mike, Amina daman tana tsaye bata russuna ba. Tasan Ummin itama don yau ta zo ne, amma ita kam tuni an wuce wajen, don wani lokacin bata daukar rainin Ihsan, saidai duk randa ta biyemata suka yi cacar baki ko yaya ne, toh fa tana shan zagi da gori wajen Hajiya Madina. Sam, bata daukar cin mutunci akan yaranta, komin girmanka, muddin ka ta6a mata yara toh fa zatasan yanda tayi ta rama. Idan kuwa daga matan gidan ne, acan fadar maigidan ake k'ulla musu k'ullalliya. Shi kuwa ya hau ya zauna.
      Haka Ummi ta taimaka suka kammala gyara komai na kicin sukayi wanke-wanke. Lokacin ana gabatar da sallar isha'i a masallacin unguwa. 
  A gurguje suka fito suka tattara falon, Ummi na lura da komai, a karshe bayan sun kammala, Amina ta fiddo dukkan abinda tasan zasu bukata wajen cin abinci ta jera bayan ta shimfid'a babbar ledar cin abinci a tsakar falon. Daga nan ta dubi Ummi.
  "Jeki kiyi sallah, zan sanarwa Hajiya mun kammala."
"Toh."
  Daga haka Amina ta mik'a wani d'an (Corridor) ita kuwa ta nufi dakinsu. 
  Har ta idar da sallar Amina bata dawo ba, nan kuma ta zauna ta soma gyangyadi don kuwa ba karamin gajiya tayi ba. Ta kwanta saman katifar dake shimfide ta mutum d'aya, wani dadi taji ya ratsata, yayinda iskar fanka ke kad'ata.
  "Ashe nima zan kwana saman katifa wataran?"
  Ta fad"a a fili. Tana nan kwance ta ji shigowar Amina. Da sauri kuma ta mik'e zaune tana mutsistsika ido.
  "Har kin soma bacci wai? Taso mu ci abinci."
  Ta mike ta bi bayanta, falon wayam, kadan-kadan ta dunga jiyo sautin dariya da hirarrakinsu daga can cikin da batasan iyaka zurfi da yanayinsa ba. 
  Amina ta kammala kwashe komai ta wanke na wankewa, tayi mamakin yanda bata nemi tayinta ba. Suka zauna suka ci tuwo da miya sukayi nak, a karshe suka sha ragowar romon kifi wanda duk an jagwalgwalashi da k'ayoyi, haka suka dan tsinci na tsinta suka zubda sauran. 
  Bayan sun kammala, Amina ta rufe kicin din bayan ta kashe fitila, ta rage fitilun falon sannan suka shige dakinsu suma.
  "Bazasu dawo falon ba?" Cewar Ummi.
Ta gyada mata kai. "Ai kuma shikenan, acan babban falon Hajiya suka fi zama, matukar kinga sun shige, toh sai kuma wata safiyar, don daga nan kowa makwancinsa yake nufa."
   Ummi ta jinjina kai kawai.

  Bayan shigarsu Amina ta dubeta.
"Idan kika bi shawarwarin da zan baki, toh lallai zaki zauna da kowa lafiya a gidannan. Yanzu na lura kina tattare da gajiya, ki kwanta ki huta, gobe ma yi maganar idan Allah Ya kaimu da rai da lafiya. Kinji ko?"
  Ta gyada kanta tana murmushi, haka kawai ta ji tana kaunar Amina.
  "Toh Anti." Antin da ta kirata da shi ya sanyaya ranta sosai, itama ta ji tana kaunarta kamar yar uwarta ta jini. Tana mamakin uwar da ta haifi yarinya kyakkyawa har haka, ta juma iya barinta ta fito aikatau. Kodayake, rayuwa ce ke sanyawa wani lokacin, ba don rai yana so ba. Ita ta ta6a zaton zatayi wani aikatau? Ko a mafarki a'a. 
   Ta barwa Ummi katifa; ita kuwa tayi amfani da bargo ta shimfida a gefenta ta kwanta. Ummi na jin sadda take zuba ruwan addu'o'i, abin ya bata sha'awa. Daga nan bacci ya kwasheta batare da ta shirya ba.
    
   ■●♣♣♣♣♣▪▲♥♥♥★★★★★
      
Washegari dakyar ta iya mik'ewa saboda dad'in baccin da ta ji. Amina ta jima tana tashinta, har daga karshe ta hakura tayi sallah sannan ta k'ara dawowa ta tasheta. Sai lokacin ne kuma ta farka. Ummi harda su miyan bacci. 
  Bayan ta idar da sallah tana shirin komawa ta kwanta Amina ta dubeta tayi dariya kad'an.
  "Lallai Ummi kinaso Hajiya ta bud'emiki wuta. Ai muddin yaranta zasu makaranta to bacci fa ya k'are mana. Sai an had'a musu shayi an dafawa Fahad indomi don kuwa kullum da shi yake tafiya. Sauran kuma wani sa'in shayin ma ba shansa sukeyi ba haka suke tafiya basu damu ba. Sannan akwai gyaran dakunan yara da Hajiya. Sauran ayyukan da ya shafi kicin da falo da tsakar gida, duk ba namu bane, yana cikin aikin Ramma, sai da daddare ne ma tattara falo da kicin yake dole a kanmu. A yanda nasani kenan yanzu, bansani ba ko kema haka zata d'oraki akai ko kuma zata chanja tsari."
  Ummi dai tayi shiru kawai tana sauraronta. Suka fita falon. Amina ta kunna fitilu wanda ta tabbatar ita da ta kashe d'in, ita ta kunna don babu wanda zai fito. Adnan ko zai tafi masallaci, zagaye yakeyi ta k'ofar waje ta d'akinsa. Ummi 'yar mik'omin wannan da wancan ce, tana lura da abinda Amina keyi. Haka kuma tana biye da ita da fahimta. 
   Komai suka hada, Amina ta zuba Indomin a filas din Fahad na makaranta, ta had'a shayin sannan suka fito. A falon suka iskesu, kowannensu na shiri. Ihsan ta shirya Fahad tsaf cikin riga ruwan goro da bulun wando na makaranta. Itama ta shirya cikin riga fara da siket ruwan toka, sai farin hijabi da safa fara, ta saka bak'in takalmi. Shima Adnan irin kayan Ihsan ne saidai wando ne nashi dogo, da farar hula (Face cap) wanda aka buga tambarin makarantar daga gaba. Shima bak'in takalmin ne sai farar safa, wanda hakan ya kasance tsarin makarantar.
   Ba karamin kyau da burge Ummi sukayi ba, gaba d'aya sai ta shagaltu a kallonsu tana murmushin inama itace ta samu wannan gatan na zuwa makaranta. Tana son karatu sosai saidai bata da mai mata gatan nan. 
  Adnan na kokarin zura (belt) na wando ya ankara da ita. Ya dubeta batare da ya cigaba da abinda yakeyi ba, bai kai ga magana ba, tayi sauri ta durkusa ta gaisheshi, ya amsa sannan ta juya ga Ihsan wacce take zura littafi cikin jakarta ta makaranta, itama gaisheta tayi. Ihsan ta amsa tana hura hanci cike da jin ita d'in ta isa ta kai. Adnan ya girgiza kai ya ja karamin tsaki. "Na gayamaki ki daina gaisheta ko? Kodayake don kanki zaki bari ai."
   Ihsan ta turo baki. "Nidai wallahi broda kana ban kunya a gaban 'yan aiki. Kaga banason irin haka, wannan jawomin raini ne fa."
  Harararta kawai yayi baice uffan ba. Ta dubi Amina. "Ki zubomin shayi."
  Amina ta juya bayan ta ajiye na Fahad a gabansa da biredi da bota. Can sai gata ta fito da kofuna biyu a hannunta. Ta ajiyewa Ihsan d'aya, sai Adnan wanda take yace bazai sha ba. Ta ajiyewa Fahad filas d'in abincinsa sannan ta ja Ummi suka fad'a d'akin da  Ihsan da Fahad ke kwana. Karamin daki ne sai gado mai hawa biyu na yara. Saman an saka zanin gado kalar ruwan hoda mai zanen (Barbie), na k'asan kuwa an saka bulun zanin gado mai zanen (spider-man). A gefe kuwa, kwabar kaya ne guda biyu, shima d'aya ruwan hoda da fari, dayan kuma bulu da fari. Sai kafet mai duka kaloli ukun da aka kawata tsakar dakin da shi, da kuma k'arami na takawa a daidai hanyar bandaki. Daga can kuwa, karamin madubi ne, sai kwaba da abu mafi yawa akansa, kayan kwalliyar Ihsan ne. Fanka ce kawai a d'akin, sai bada wadataccen iska take. Ba k'aramin burge Ummi dakin yayi ba. Ta saki baki tana kallo. 
   "Ummi ki dunga lura kina rike abubuwan da nakeyi fa, don kuwa gobe zai iya kasancewa ke d'aya zakiyi. Da zarar Hajiya Mama ta dawo zan tafi."
  A sanyaye Ummi tayi magana. "Yaushe zasu dawo?" 
  Tana murmushinta na sabo ta amsa. "Hausa nayi miki, ni kaina bansan sadda zasu dawo ba amma na tabbatar ba zata kaisu da nisa ba tunda an koma makaranta, yara zasu je. Nufina yau idan ina nan gobe bana nan, kece zakiyi."
  Ta jinjina kai. Tare sukayi aikin, har inda ake daukar sabon zanin gado idan na kai sunyi datti saida Amina ta nunamata. Suka fito, tuni yan makarantar sun tafi lokacin takwas ma ta wuce, saidai sam Hajiya bata lek'o ba. Saida suka shiga dakin Adnan nan ma suka gyarashi tas, shima madaidaicin daki ne, da katifa babba wacce bata da bukatar katakon gado. Komai na dakin adon fari da bulu ne, babu wani tarkace a dakin sosai. Amina ta barta da gyaran gado don taga yanda zatayi, sai kuma ta bata mamaki don tayi kokari ba laifi. Ta dan gyaggyara inda baiyi ba sannan Ummi ta share dakin, anan kam ko Amina ba zata nunamata iyawa ba. Bayan sun fito, shayin suka zuba suka sha da sauran biredin sannan suka maida komai kicin suka koma dakinsu. Suna daga kwance Amina ta soma magana.
  "Zanso kafin na fad'amaki halayen mutanen da zakiyi zama tare dasu, na soma gayamaki tsarin gidansu don ya dace kisan da wadanda zaki zauna."
  Ummi ta muskuta tana dubanta gaba daya ta tattara hankali da nutsuwarta ga Aminan. Ganin haka Amina ta soma.
   
       ★★★★★★★★★★★★

"Maigidan, sunansa Alhaji Muhammad Modibbo. Shi d'an asalin garin Adamawa ne, bafulatani ne. Hajiya Madina 'yar uwarsa ce, saidai ita mahaifinta anan Kano ya rayu, anan ya tara zuri"arsa. Soyayya ta kullu tsakaninsu har ta kaisu ga aure lokacin shi Alhaji Muhammaf ya dawo Kano da karatu ya kuma kama aiki anan.  Yana da mata biyu bayan ita, Hajiya Binta itace wacce kika gani rannan, sannan amaryarsa Hajiya Lubna, ita 'yar Maiduguri ce, yanzun ma da baki ganta ba, taje biki can Maiduguri da yaranta su hud'u gaba d'aya. 
   Hajiya Madina tana da yara takwas kamar yanda na fadamaki, ita kuwa Hajiya Binta yaranta shida. Iklima itace babbar budurwar 'yarta sannan Hanif, Sadiya, Nafisa, Usman da Jabir.

  Ita kuwa Hajiya Lubna, yaranta biyun farko 'yan biyu ne mace da namiji. Hassan da Hussaina, sai Adam da Hajara.
    Bar ganin gidannan kamar ba shi da girma Ummi, sai kin shiga can 6angaren zaki k'ara tabbatar da girmansa. Sashe hud'u ne har na Alhajin. 
   Saidai duk haduwar sashen matan bai kai na maigidan ba.

  Saidai duk haduwar sashen matan bai kai na maigidan ba, da girma da komai. 
   Hajiya Madina duk ta fisu fada a wajensa, ko don tana ganin ita din 'yar uwarsa ce kuma tana da daurin gindi wajen mahaifiyarsa Gwaggo ne? Bani dai da masaniya. Amma tabbas Gwaggo bataso ko kusa Hajiya ta kai k'ararsa wai ya 6ata ranta, yanzun nan zata bud'emishi wuta. Shiyasa daga Hajiya Binta har Hajiya Lubna, basu kaunar zuwan Gwaggo Kano, kawai saboda bambancin da take nunawa tsakaninsu da Hajiya Madina. Hakanan tafi zuzuta kaunar 'ya'yan Hajiya Madina har yakai ma bata iya 6oyewa.
    Bada son ranta akayiwa Hajiya Madina kishiyoyi ba, saidai kawai don Hajiya Madina ta nunamata tafison kwanciyar hankalin mijinta akan tashin hankali da damuwarsa. 
  Gaskiya Ummi a wani 6angaren, Hajiya Madina tana da mutunci duk kuwa da cewar bata kama k'afar Hajiya Mama ba. Hajiya Mama ciki d'aya suka fito, saidai ita bata da raina 'yan aiki kuma yaranta sunsan girman ★DAN ADAM★ basu rainashi ko yaya ne. Toh yanda Hajiya Mama take, hakanan itama babbar yayarsu, Hajiya Fatima take. Su uku daman cif a wajen babansu, daga su bai kara haihuwar wasu ba kuma matarsa daya, Baba Ummahani.
  Ita a Abuja take zaune. Tana da yaranta hudu samari manya, sai yan mata biyu. Ta aurar da yaranta maxa biyu na farko, matan da ragowar mazan biyu sune dai basuyi aure ba. Mijinta tsohon soja ne kafin daga baya yayi ritaya. 
     Amina ta d'an tsagaita sannan ta d'ora tana duban Ummi wacce gaba daya kacokam ta maida hankali gareta tana sauraro.
  "Hajiya tana da saukin hali idan kika zama mai bin umarninta kan lokaci, sannan tafiso kafin tayi korafi akan bakiyi aikin da kika san kina yi ba toh ki kammala shi. Ko kusa bata son kazanta, hakanan bataso kice zaki wulakanta abinda ta haifa. Batason kuma shigen d'akunan abokan zamanta, idan kika kiyaye bakinki daga daukar magana ki kai wani dakin toh fa zaku d'asa da ita. Ba ruwanki da shishshigi a lamuranta matukar ba ita ta so ki tanka ba. Ki kiyaye kawo mata gulma, nan ma zaku 6ata da ita. Sannan ko wani abu marar dacewa kikaga ta yi, bataso ki tanka mata, nan kuwa zaku 6ata. Batason ta kamaki da cin amanarta. 
Yaranta suna da saukin hali Ummi, matukar kika kama kanki ba zasu rainaki ba. Ihsan ce ma mai matsalar, ita kuma kiyi kokarin fita harkarta. Idan dai ta sanyaki aiki kada ki k'i, kiyi hakuri kiyishi hakan saboda itace ma musabbabin da yan aiki basujin dadin zaman gidan. 
     A duniyar nan, kawai dai ki tsare abinda za'a ci mutuncinki ko yayane, kedai ki tsaya matsayinki baruwanki da cusa kai kinji ko?"
    Ummi ta danyi murmushi alokaci guda hawaye suka zubomata ta sharesu, wai yau itace da samun mai bata shawara a lamarin rayuwa? Itace ta samu wannan gatan har haka? Wani irin kaunar Amina ya k'aru a zuciyarta. 
  Amina da mamaki ta mike zaune.
"Ummi kukan kuma na menene?"
Ummi ta girgiza kai.
"Bakomai."
Amina ta ji wani tausayi ya dabaibayeta. Tasan akwai wata matsala a rayuwar Ummi, tafi kuma tunanin bata da iyaye. Ta numfasa, batason ta matsa mata da tambaya, ta tabbatar wataran don kanta zata gayamata tarihinta. 
   "Komai yayi zafi maganinsa Allah Ummi. Ki bar damun kanki da lamuran rayuwa har haka kinji ko? Ki rik'i addu'a da karatun Alkur'ani da sallar dare. In sha Allah komai zakiga ya wuce."
   Ummi da fuskar tausayi ta dubeta.
"Nifa bansan komai na Addini ba wallahi. Kawai dai ina yin sallah idan naga lokaci yayi mutane sunayi."
  Mamaki karara ya bayyana saman fuskar Amina, batasan ya akayi ta jefomata tambaya ba.
"Wai Ummi, iyayenki basu raye ne? Shekarunki nawa yanzu?"
  Ummi tayi k'as da kanta ta soma hawaye. 
"Mahaifiyata ta rasu tun ina jaririya, babana yana raye. A hannun matarsa na taso."
  Kwallah ta cika idanun Amina, ta gano bakin zaren. 
  "Idan ba damuwa ki sanarmin tarihinki mana."
  Tiryan-tiryan ta sanarmata da irin rayuwar kuncin da ta rayu ciki. Cikin muryar kuka tace.
  "Kalmar da ta kasa ficemin a rai bai wuce da babana yace wai ko birnin sin ne na tafi ba shi ba damuwarsa bace. Babana baya sona yanda yakeson kanwata Mariya."
  Kuka sosai takeyi, itama Amina tana tayata. Wani kaunar Ummi ya k'aru a ranta, ji takeyi tamkar kanwarta ce ta jini. Dakyar Amina ta rarrasheta tayi shiru sannan ta dubeta da kulawa.
                
"Karki damu Ummi, ki cigaba da hakuri sa mik'awa Allah lamuranki. Komai kika gani, daga gareshi ne. Watarana zaki ga komai kamar ba'ayi ba, nan gaba zakiji dadi a rayuwa in sha Allah. Kada kiyi bakinciki da zuwanki gidan Hajiya, na tabbatar ko a kwana d'ayan nan da kikayi, kinga chanjin rayuwa ballantana kuma idan ya zamana kin shure satittika anan. Nasan dai duk wani wuya da zaki ci anan bazai kai rabin wanda  kika labartamin ba. Hajiya bata duka, bata zagi haka kawai, saidai idan ka ta6a jininta, zata budemiki wuta tayi fada sosai harma idan baki taki sa'a ba ta goranta miki. Duk kuma wani abu na rayuwa ki daukeshi mukaddari ne daga Allah, ba wanda zai tsallakewa kaddararsa kinji ko?"
  Cikin jin wani sanyi ta gyad'a kanta. 
"Toh Anti nagode."
Amina tayi murmushi. Baccin safen da basu samu komawa kenan ba, sukayi ta hira a karshe Amina ta mike ta shiga wanka. Bayan ta fito Ummi itama ta fad'a. 
  Ta kammala ta fito, Amina tuni ta shirya cikin doguwar riga ta yadi, daga gaban rigar, anyi adon duwatsu, ire-iren dai wanda take samu daga Hajiya Mama ko yaranta. Ummi ta dubeta, tayi mata kyau, zata soma duba jakar kayanta ta ji muryar Amina.
  "A'a Ummi, ga kaya ki saka."
Ta juyo don ganin ko ta ciro mata ne, saidai ta ga wasu da ba nata na asali ba, riga doguwa ce ta abaya. Ta dubi Amina ido a waje.
  "Lah, anya kayanki zasu yimin Anti?"
Amina ta murmusa.
"Wannan na jima bana sakashi, na kuma tabbatar ba zai k'i yi miki ba. Kedai gwada mugani. Idan kin kammala ki fito ki gaida Hajiya, nasan yanzu ta farka."
  Ummi ta amsa da toh, Amina ta fice. Rigar ta kar6eta kwarai tayi mata kyau kasancewarta farar yarinya. Ta dauki dankwalin ta d'aure gashinta wanda idan mutum yaga yanda yayi mata, zai iya cewa tayi d'aurin acuci. 
   Saida ta dauke shimfid'a ta d'an gyara d'akinnasu duk da ba daud'ar azo a gani don Amina akwai tsafta, sannan ta bi bayanta.

      

    A falon ta tarar da Hajiya Madina zaune cikin kwalliya tana karyawa, Amina bata nan, ta karasa ta durkusa ta gaisheta a ladabce. Hajiya Madina ta amsa fuskarta a sake, bai wuce ganin yanda Ummin tayi fes ba don ita ba mace ce mai son zama cikin k'azanta ba, bar dai Ihsan, wani sa'in saika rantse ba ita ta haifeta ba don k'azanta da rashin kula.
    Ummi ta zauna, idanunta akan talabijin, saida Hajiya ta kammala sannan ta umarceta  da d'auke kayan, ta d'aukesu ta kai kicin. Acan ta had'u da Ramma tana faman gyare-gyare. Ta gaisheta a mutunce, Ramma ta amsa har tana zolayarta wai har ruwan birni ya soma kar6arta ta chanja saidai k'ashin wuya. Ita dai murmushi tayi kawai. 
   Tana shirin fitowa sukayi kici6us da Amina, hannunta rik'e da tsintsiya da kwandon shara. 
  "Kinga yayi miki kyau ko? Nima na gyaro d'akin Hajiya ne, kije tana kiranki ma."
  Ai da sauri Ummi ta fita don amsa kiran. 
  
    
    
  
     

   

No comments:

Post a Comment