Tuesday, 13 December 2016

KARNINMU 8

KARNINMU....
©FIKRA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA TAKWAS

Tun da Hajja Bilkis ta shiga cikin gari ba ita ta koma gida ba sai la'asar, hakan ma saboda kiran Yaya ne da ta mata na cewar su Kande mai jigilar yan aikatau fa na can gidan ta su na jiran ta. Zaune su ke falon baki.

Hajja Bilkis hakince kan kujera, Kande zaune can gefe guda ita ma bisa kujera. Ita ko Habi zaune ta ke kan carpet gaban su, ta ci ado cikin kayan sallanta atamfa na kamfanin soso, fuskar nan sai shekin mai ta ke, ga kullin kayanta da ke cikin ɗan kwali ta rungume bisa cinyar ta. Kande da su ka jira sam ba ta nunawa Hajja Bilkis k'osawar ta ba, nan su ka gaisa, sannan ta na mai gabatar da Habi ta ce.

"Dama Hajiya Zinaru ce ta ce na kawo mi ki yar aikatau, ga ta nan sunan ta Habi, kar ki ji komai gwanar aiki ce sam ba ta k'iwa"

  Hajja Bilkis ta kai duban ta ga Habi, wacce ta durkusa ta gaishe ta cike da ladabi. Sai da ta k'are ma ta kallo da kyau, cikin gamsuwa da yanayin Habi, dan kuwa ba kamar Jummai ba, daga ganin ta a natse ta ke. Hajja Bilkis ta amsa da.

"Lafiya lau, Kande Yaya ta mi ki bayanin abin da ya sami waccan yar aikin tawa da ya sa na nemi  ita wannan ɗin, ya ma ta ke da suna?"

"Habi! eh" Kande ta amsa mata a takaice.

Sannan ta k'ara da "Eh ta ce da mu Jummai ba lafiya, ai har na duba ta ma ai, na yiwa Iya dudu ya mai jiki"

  Hajja Bilkis na mai yamutsa fuska ta ce "Ina dai fatan dai ita wannan ɗin lafiya lau ta ke"

"Lahiya lau ta ke..eh ko ba Habi ba, ga tanan lafiyayya ce, ga tsafta" Cewar Kande ciki jaddadawa.
 
Hajja Bilkis na mai duban Habi ta ce "Toh ke sai ki saurare ni da kyau, gidan nan ba laifi akwai aiki tuk'uru, amma ni ma zan biya ki da kyau"
 
Habi ta jinjina kai, ta na mai durk'usar da kai k'asa. Hajja Bilkis ta cigaba da fad'in.

"Ina da yaro k'arami, wanda za ki dinga kula da shi, tashinsa daga bacci, ba shi abinci, wankansa, zuwan da dawowarsa daga makaranta da dai duk abin da ya kamata. Dan ni ba zama na ke a gida ba. Babu ruwan ki da girki wannan aikin Iya dudu ne, sai dai shara da wanke-wanke, gyaran nan ɓangare na, da na Honourable sai kuma nan na baƙi "

Kande ce ta amsa da "Kar ki ji komai in dai Habi ce, za ki ji daɗin aikin ta"

"Allah dai ya sa, in dai yanda ki ke faɗa hakan ne ko Jummai ta warke sai dai ta nemi wani aiki" faɗin Hajja Bilkis.

Yayinda Kande ta tashi tsaye ta na mai faɗin "Ni bara na bar ku lafiya, kin san mutum mai sabgogi, albashin na ta kya iya ba ta idan lokaci yayi, ke kuma Habi sai ki na ajiyewa idan na sake dawowa sai na amsa na kaima gyatumar ta ki"

  Hajja Bilkis ta sa hannu a yar jakarta da ke ajiye gefe, kuɗi ta fidda sabbi kyal, ba tare da ta kirga ba ta mik'awa Kande.

"Ga wannan ba yawa"

Jiki na rawa, cikin washe hak'ora Kande ta sa hannu biyu ta karɓa, ta na mai cewa.

"Toh madallah kuwa, kya ce ba yawa wannan kuɗi haka wuri na dukan wuri! Ke da yar uwar ki ba kwa gajiya da ɗawainiya, Allah ya saka da alkhairi, ya sa ku fi haka"

"Aameen  Aameen! idan kin fita kya kira min Iya dudu. A sauka lafiya" cewar Hajja Bilkis. In da Kande ta amsa da "Toh toh,yanzu ma kuwa" gaba ɗaya ta ruɗe saboda kuɗin da ke rike hannun ta. Za  ta fice ta na surutai ta ma manta da Habi, sai da ta ji ta ce Iya Kande Allah ya kiyaye,sannan ta juyo ta mai washe baki ta ce.

"Yo Habi ai na manta da ke ai, Allah ya sa ayi aiki da kyau, sai Allah ya daɗ sada mu da alkhairi"

Sannan ta fice ta bar Habi nan kai sunkuye gaban Hajja Bilkis. Jim kaɗan Iya dudu ta shigo. Hajja Bilkis ta Umarce ta da ta sauki Habi ɓangaran su na masu aiki, sannan ta nuna mata duk abun da ya dace. Habi ta tashi rungume da kullin  kayan ta. Har sun kai ga bakin kofa Hajja Bilkis ta tsaida su ta hanyar kiran Iya dudu,wacce ta dawo da sauri.

"Honourable ya dawo ya sake fita ne bayan fita ta?" Ta tambaya ta na mai duban Iya dudu. Wacce ta amsa mata da.

"Ah ah be dawo ba,dan ɗazu ma da na je kai masa abincin rana ma haka na tarar da na safe ko taɓawa ba a yi ba...."

Cikin nuna ɓacin rai ta ce
"Ban tambaye ki wannan ba! Na san ko gyara ɓangaran na sa ba a yi ba, ki nunawa Habi ta gyara yanzun nan, shin an kai Jummai asibitin?"

"Iro ne bai dawo da wuri ba, amma yanzu idan ya dawo daga ɗauko Hanif daga islamiya zai kai ta" Iya dudu ta amsa ma ta.

Kai kawai Hajja Bilkis ta gyaɗa mata alamar ta sallame ta. Iya dudu da Habi su ka tafi, in da ita kuma Hajja Bilkis ta ɗau yar jakar ta, ɓangaranta ta wuce, in da ta yi kwanciyar ta a falo bisa doguwar kujera hankali kwance.

Kamar yanda Kande ta faɗa sam Habi ba ta da lalaci, da taimakon Iya dudu wacce ta nuna mata yanda za ta yi tuni ta gama gyaran ɓangaran Ahmad tsaf ta na mai mamaki daular da aka tara a gidan, wannan shi ne aljananan duniya. Har ta hau kan kayan da Hajja Bilkis ta kwaso daga ɗakin Ahmad bayan ta gamsu da yanda ta gyara ɓagaran na sa ne, ta buɗe mata uwar ɗaka, nan ma ta ce ta gyara, sannan ta kwaso fararan inner wears ɗin shi da ya tara ta ce idan ta gama da ɗakin da banɗaki, ta wanke inner wears ɗin ta shanya.

Habi ba ta samu ta gama wankin nan ba sai yamma likis, ta na cikin shanya ne Ahmad ya dawo. Har zai shige ba tare da ya kalli ɓangaran Hajja Bilkis ba, ya hangi fararen singileti da gajerun wandunan sa jere bisa igiya, wata yarinya da be ma taɓa gani ba ita ce mai shanyar,  ta dage sai matsewa ta ke ta na shanyar ta hankali kwance. Cike da mamaki da takaici ya k'arasa in da ta ke, ya na mai duban igiyar. Cikin ɓacin rai ya furta..

"Ke wa ya baki wannan kayan? wa ya sa ki aikin nan?"

A gigice Habi ta juyo jin maganar ta shi kamar saukar aradu dan kuwa zuciyar ta ɗaya
ba ta yi zato ba. Ganin Ahmad a tsaye wanda ya mata kwarjini tuni ta fara kame kame.

"Ehye.....iyiii....na'am...wai ni?????"

                           ***

Kofar da ya bi ta tsare da idanu kafin chan ta sauke su a hankali,  ta daɗe tana fuskantar ire-iren cin fuskan da ya mata amma babu wanda ya tsaya mata a rai kamar wanda Ahmad ya mata.

   "Don Allah kiyi hakuri,  da na san hakan zai faru da ban yarda kun haɗu  ba,  don Allah ki yi hakuri,  kuma Ahmad sai ya san ya ci min fuska, don ba ke ya mawa ba ni yayi mawa "  ya karasa yana durkusawa  alamun neman gafara.

Murmushi ta sakar masa,  ta sa hannu ta ɗago shi duk suka mik'e suna kallon juna

   "Kar ka damu,  ai na saba jin fin haka,  ai ba karya yayi ba ko,  ni har wani fuska gare ni balle har ya ci? "  ta faɗi kasa-kasa tana kashe masa ido ɗaya.

Rungumo ta yayi sannan ya ce
   "ki daina faɗin haka,  Gimbiya kike mai babban daraja,  kin san mutum baya taɓa tsallake kaddararsa. Allah sa muyi kyakkyawan karshe."

Janye jikinta tayi ta tsare shi da idanu,  so take ta ga iyakar gaskiyanshi.  Rashin gane abinda take son yasa ta faɗin

"Bani takardun kar dare ya min a nan. Nayi na Goggo alkawari,  banso ta gaskata yan son ganin faɗuwata" ta faɗi tana murmushi.

Ya Mika mata takardun kwangilar samar da littafai ga makarantun primary da sakandare,  wanda gwamnatinsa ta ɗauki alwashin samarwa kyauta.
   Ya mika mata wani takarda daban sannan yace
   "wannan aiki ne gare ki Gimbiya,  a sashin kula da ilmi na Kasar Haurobiya da ke nan birnin. Kin san iyakar gatan da zan miki kenan,  fatan zaki rike Amana" 

Ba tare da ɓata lokaci ba ta rungume shi,  tana mai gode ma Allah a bayyane.  Nan suka ɗan taɓa  baɗala sannan ya sa aka maida ita gida.  Shi kuma ya cigaba da aikin da ke gaban sa.

                       ***

Bayan tashi daga karatun yamma. Mallam Baso ya sa Muazze rubutu, gashi Hamze ya dame shi da kukan yunwa abin ku da sabon shiga bai saba ba. Hakan ba da son ran Muazze ba ya bar shi ya ɗau roba suka fita bara tare da sauran yara yan uwansa. Hammze ne yayi sallama a wani gida da ke nesa da makarantarsu.

         “Assalamu'alaikum Iya koran kanzo, Iya almajiri yana bara, Iya nayi baran nayi baran ban samu ba, Iya nine ɗanki Muhammadu, fisabililah!".

      “Mtss wa'yanna almajiran kun cika naci kunyi bara ɗaya biyu ba'a amsa ba sai ku tafi mana mtsssw" faɗin matar da ke zaune da mijin ta suna hira a tsakar gida

      “Almajiri zo ka karɓa"faɗin mijin,  nan ta haɗe fuska don ta tsani halin mijin nata na ba almajirai abinci.

Da sauri Hamze ya zo da gudu ya tsuguna akan gwuiwansa.

         “Gani ".

“Mtssw kawo robar. Ke ban sauran abincin yarannan abasu" mijin ya faɗi yana kallonta

Abincin da yara suka ci suka gama jagwalgwalawa suka rage shi ta dauko aka basu duk da akwai raguwan abinci da dama da zata iya ɗiba musu kuma ba tare da ta sa na ta iyalin  a takura ba

Suna fita suka soma wawa akan abinci, Hamze da shi ya karɓo abuncin ya na ji ya na gani loma ɗaya kacal ya samu.....

No comments:

Post a Comment