Saturday, 10 December 2016

ANA KUKAN TARGAƊE 3

ANA KUKAN TARGADE...
part 3⃣
Avva omar yaro
(Prince av)
09032724001

Ikon allah da kiyayewarsa kadai suka kai chuchu gida lafiya, bawai kwarancewa ko iyawarta da tuki ba.
   Tana zuwa bakin get din gidansu ta danna hon bila adadin, bawai danta dade a wajen ba a'a kawai hakan na nuni ne da matukar bukatuwarta da shiga gidan, aiko mai gadin na zuge get din saura kadan tabi ta kan kafarsa ta wuce, da sauri ya daka tsalle baya kamar an hullashi, zare ido yake cikin tambayar kansa yau me ya samu chuchu, dan yasan hakan ba dabi'arta bace.
Ko parking bata tsaya gyarawa ta balle mirfin motar ta fito da gudu tanufi korridon dazai sadaka da cikin gidan, ba kowa a katon falon sai sautin tangamemiyar plasmar dake tashi na karatun abdurrahman sudees cikin suratul rahman.
  Kai tsaye dakinta dake saman bene ta wuce, tashiga harda murda masa key, bata tsaya cire kaya ba kawai ta fada toilet tareda sakarwa kanta shower, ko kadan zafin da zuciyarta ke mata bai ragu ba, kamar yadda tai tunanin in ruwan sanyi ya ratsata zataji dama dama, batare data kashe shower ba taja kafarta da nufin fita daga baths side din santsin tilies ya kwasheta ta fadi kasa, sai gata tsamo tsamo cikin ruwan shower daya fara taruwa a kasa, saboda dama tun farko bata bude kofar fitar ruwa ba (rariya).
  Wani irin tari ya sarketa ta kamayi ba kakkautawa, a hankali numfashi da hankalinta ke gushewa daga gangar jikinta....
           *        *        *
Ita kam h.deejah tana dakinta tana jera kayanta a Waldrop da direba ya kawosu daga laundry dazu, ko kadan bata ji shigowar chuchu gidan ba, bayan ta gama ne ta mike ta shiga kicin dan karasawa A.A abincin da zaiyi lunching dashi, dan baya cin abinci a ko ina indai yana gari saina gidansa, kasancewar h.deejah ke musu girkin daxasu ci su uku, ragowar masu aikin gidan kuma jemia ce take musu a nasu kitchen din.
  Tana jere Warmer's a dining A.A ya shigo da sanye cikin farar shadda 'yar ciki da wando da alama ya ajiye babbar rigar ne a wani wajen dan yana bukatar hutu, kansa ba hula sai bakar sumar kanuri kwantacciya data kara fito da kwarjini da kamalarsa, "sannu" yaketa jerawa h.deeja kamar wacce tai tseran gudu, ita kuwa banda murmushi ba abinda take aika masa dashi, dan inda sabo ta saba da halin A.A koyaya ta yi aiki ya ringa jera mata sannu kenan.
   "Ina daughter ne". Ya fada yana kallonta bayan ya zauna a kujerar dining din. Batare data dago daga kallon farfesun kayan cikin datake zuba masa ba tace "yau ita da gida aisai karfe 5:00 inma anci sa'a go slow bai tareta ba" da mamaki A.A ya kalleta "kina nufin yanzu bata cikin gidan nan"
    Batasan meyasa yake son tabbatarwa ba, amma dan karta ja zancen da nisa kawai saita gyada kai da cewa "eh" ta fada cikin nuna gamsarwa,   A.A yakuma kallonta a karo naba adadi baiga wani alamu atare da ita dazai nuna masa wasa ko zolaya take masa ba, saima ci gaba datai da serving dinsa da sauran kalolin girkin, jin yayi shiru yasa ta kalleshi danyin shirun ba halayyar A.A bace akwai shi da kalan magana musamman in suna tare, ajiye soup spoon din tayi tareda karasawa inda yake zaune kamar an dasa "lafiyar ka kuwa daddy" sunan datake kiransa dashi kenan, ajiyar zuciya yayi tareda kallonta ido cikin ido tsayin mintuna kafin ya dauke kai "tun kafin habu (direban dake jansa) yai parking naga mota a farfajiyar gidan nan ba inda aka saba parking ba kwata -kwata keda ganin motar kinsan bada nutsuwa akai parking dinta ba, bayan na fito nake tambayar mlm mudi (me gadi) waya fita da motar yake chemin chuchu ce, kuma daga ganin dawowarta yana ganin kamar ba lafiya dan da kuka ma tashigo, dasauri na shigo ciki dan naji meke faruwa da chuchun, amma yanayinki dana gani yasa na gane lafiya qlau koma menene ya sameta, abinda ya kuma daure min kai kuma shine ganin na dawo amma ko gilmawarta ban gani ba, gabana yana faduwa hadiza ki gayamin gsky ina meya sami chuchu"
    Aitun kafin ya karasa ta nufi bakin window da gudu ta zuge net dake yane a jiki, kamar yadda A.A ya fada motar na nan inda aka ajiyeta, da gudu takuma juyawa tai dakin chuchu dake kasan, yayinda shima A.A da gudu ya nufi na saman.
H.deejah kam ta duba duk wani sako da lungu na dakin ba chuchu, tafito tanata faman raba ido, karar dataji a sama yasa tabi step din benen da sauri, A.A ne da guduma yana faman dukun kofar dakin chuchu dake sama, 6allewa kofar tayi ta fada ciki lokaci daya da feshewar da ruwa yai musu, a razane suke kallon dakin dayake shirin zama maliya, ruwa harya kusa taddo katifar dake kan gadon, aibasu damu da ruwan ba suka kutsa kai cikin dakin, A.A ne ya fara bude toilet din dan yaga daga nan ruwan ke fitowa, yana tunanin ko makunnin famfo ne ya lalace, abinda ya gani ya sa shi karasa shiga da sauri "chuchu" ya ambata da sauri ganinta a kwance kasa ruwa yasha kanta, itama h.deejah bude bandakin tai ta shigo jin abinda ya ambata.
     Bai damu ba haka ya durkushe cikin ruwan ya tallafo kanta a cikinyarsa, idonshi ya kada jajir banda "innalillahi....". Ba abinda yake maimaitawa da sauri h.deejah ta karaso itama durkushewar tai "na shiga uku!!! ABUBAKAR  (sunan da bata fada amma yau bata ma san ta fada ba) meya sameta" ta tambaya a gigice tana kwalla dan tasan komai maiya sameta bamai sauki bane ganin halin datake ciki.
   Ganin bashida niyyar magana yasa ta mike "bari na kirawo direba mu kaita asibiti" ruko hannunta yai da sauri "saidai muyi hakuri hadiza allan daya bamu chuchu ya fimu santa, dan haka ya kar6i abarsa......"
  Iya abinda taji kenan itama ta fasa ihu tareda sulalewa kasa cikin ruwan, lokaci daya numfashinta ya fice....
     "Astagfurullah allah mai nai maka" A.A ke fada yana gwara kansa da jikin bango.......
           *         *          *
Shikam kwalisa kota kan md dake dako masa harara bai bi, laptop, hula da key din motarsa kawai ya sura yai gaba yana huci kamar kububuwa.
Md ya dafe kansa daketa faman sara masa kamar ya rabe biyu, shida zai iya driving dinma surar tasa motarsa shima zai ya bar school din, amma a yadda yake jin kansa baya jin doguwar tsayuwa ma zai iya bare jan mota.
Yaf! Ya durkushe a gurin cikin cizon yatsa "ya allah" kalmar dayaketa maimaitawa kenan tsayin lokaci, kafin a hankali nutsuwarsa ta fara dawowa, kusan awarsa biyu a gurin yana hada bara da bana, kafin ya mike shima ya nufi inda yai parking din motarsa kirar continue discussion, ya murzata da gudu tareda ficewa daga cikin makarantar
         *          *          *
Kwanan kwalisa biyar bayaiwa md magana, koda kuwa sun hadu a cikin school dinne, shima md din ya tattarashi ya watsar, shi vocal ma yake nema ido rufe dan yaji a wane hali chuchu ke ciki, to itama vocal din da alama tabi sahun chuchu wajen yiwa makarantar layar zana.
  A kwana na takwas ne ya gaji da zaman doya da manjan dasuke da Kwalisa, ya shirya kai masa ziyara har gida...
     Tangameman falo ne daya sha ado da Kujeru rindima rindima ruwan madara da coffee, labuye da center carpet din dake malale a tsakiyar falon suma duk Kalar kujerun ne, daga cikin falon hajiya iyami ce keta fada kamar bakinta zai yage "bana son shashancin banza mukhtar mekake 6oyemin a mu'amalarka da yaron nan ne, yaron da baya kwana biyu saiya zo har nan ya gaida ni amma yau kwana dai-dai har 9 banji duriyarsa ba, kullum na tambayeka lafiyarsa kalau saika tsaya min inda inda da kwana-kwana, to wallahi inbaka gayamin abinda kaima yaron nan ba yau zaka hadu da fushina"
    Kwalisa dake durkushe gaban mahaifiyarsa yai shiru yana sake saken ya gayamata ko karya gayamata, yasan komai zai cemata akan md ba lallai taga laifinsa ba, tunda yariga ya gama siyeta da kyautatawa gamida kyawawan halayensa, ya bude baki da nufin cewa wani abu sallamar md ta katse masa furucin dayai Niyyar yi, tare suka amsa shida h.iyamin daketa dokawa md murmushi.
Har kasa ya durkusa ya gaisheta, shikuwa Kwalisa gaba dayama kunya ce ta kama shi, ganin yadda md kewa mahaifiyarsa, hakika yasan yadda yake mata biyayya kosu data haifa iya abinda zasuyi mata kenan, amma ya rasa same zai saka masa saida daukewar kai, hannun md ya mika masa sukai musabaha tareda tambayar lafiyar juna, h.iyami ta lura da yadda jikin kwalisa yai sanyi mutuka hakan yasa ta fara zargin akwai wata a kasa, ta dauke kanta daga kallon kurillar datake masa tareda kallon md "lafiyarka qlau md kwana biyu ka dakawa gidan naku yaji" ta karashe da salon zolaya.
Da fara'a shima yace "hajiya lafiya qlau kawai dai jarrabawa ce ta matso shiyasa karatu ya 6oyeni" ya fada yana kallon fuskar Kwalisa dayai sunkui da kai.
  "Md karya ba halinka bace hakan yasa ko kyau batai maka, inka manta bari na tuna in jarrabawa tazo nan kake tahowa kuyi karatun da Mukhtar ko kuma shiya bika can gida, amma wannan karan lamarin naku saiya banbanta? Ko kadan ban kar6i wannan uzurin naka ba"
     Md shiyama rasa karya daxai kwakulo yai mata danya fuskanci kamar ta gano takun sakar dake tsakaninsa da Kwalisa, shikuma harga allah bayason gayawa mata lamarin danbai san da fuskar dazata kalli abun ba.
     Ganin shirun nasa yai yawa yasa h.iyami cewa "indai harda gaske kanamin kallon mahaifiyarka ne to zan iya cewa ban Yafe ba indai ka 6oyemin abinda ke tsakanin da Mukhtar dan nasan ruwa baya tsami banza"
   Bai tsaya shawara ba wajen zayyane mata duk abinda ya Faru tsakaninsu, tun daga farkon shigowar chuchu rayuwarsu da irin wulakancin datake fuskanta daga wajen Kwalisa, har zuwa abinda ya hada musu sa6ani yanzu.
   H.iyami banda hawaye ba abinda idonta keyi har md ya gama bata labarin, wanda duk basu lura da hakan ba sakamakon kansu dake kasa, jin muryata na rawa yasasu dagowa a firgice, bata saurare su ba taci gaba da cewa "mukhtar  dama har yanzu akwai irinku? Akwai maza masu zuciya irinta BUKAR, to inaso ka nutsu danyau nabaka labarin rayuwata da dalilin dayasa nake yawan kukan daka kasa sanin dalili, kukana yanada alaka da..........

Menene labarin h.iyami, waye kuma bukar data kasa mantawa dashi tsayin shekaru? Ina labarin A.A damuka baro a bandaki da gawar chuchu data h.deejah? Ina vocal ta shiga tsayin lokaci?
Duk amsoshin tambayoyin na cikin
ANA KUKAN TARGADE...4⃣
09032724001
prince av

No comments:

Post a Comment