KARNINMU...
©FIKRA WRITERS ASSOCIATION
BABI NA SHIDA
Bayan sun zauna Malam Baso ya kalli Malam Tanko, cikin sakin fuska da fara'a ya ce.
“Kamar yanda kasan tsarin makarantar ko wani yaro za'a fara masa da ga farko, watau daga Alu an baki, sai su shiga wasula kafin su fara Alqur'ani, ba laifi muna sa ido sosai a kansu, ai Muazze na da hazaka kuma ba ruwan shi da yan rashin ji" Ya karasa maganar yana kallon fuskar Malam Tanko.
“Hmmm!".
Malam Tanko ya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya mai nuna gamsuwa.
“To MaashaAllah! ni dama fata na kenan su yi karatu mai kyau su zama manyan Malamai".
Cewar Malam Tanko tare da zura hannusa cikin aljihun babban rigansa ya zaro kuɗi. Hannnusa ya tofe da miyau, kafin ya fara kirga yan tsofin kuɗin da ya tarasu.
Malam Baso ganin ana kirga kuɗi nan ya fara haɗiyar miyau yana binsu da kallo yana kirga su da ido shima. Dan kuwa duk kuɗin da yake k'arba hannun jama'a da sunan sadaka taɓa isar sa saboda rashin wadatar zuci.
Malam Tanko ya mika masa yana cewa
"Akaramakallahu ga wannan sadaka ce ba yawa, Allah saka da alkhairi"
Take Malam Ya washe baki ya sanya kuɗin a cikin aljihu ba tare yana cewa.
“Wa to ina faɗa maka Malam Tanko kar ka damu yara kam kamar sunyi karatu sun gama".
Malam Tanko yayi godiya ya mik'e tare da masa sallama ya nufi tashar mota don ya koma..
Shi kuwa Malam Baso tasa keyar Hamze da Muazze yayi suka nufi cikin rumfar.
“Dallami! Dallami kana ina?".
Tun daga nesa Malam Baso ya ke kwala ma ɗaya daga cikin Garadan da ke makarantar kira.
Cikin sauri ya iso gaban Malam Tanko ya russuna, wuyansa sanye da wata zabgegiyar casbi mai tsayi sosai.
“Malam gani nan".
Yauwa ga wannan yaran ka tafi dasu ana koya Musu karatu da kyau".
“To Malam" nan shima ya tasa keyarsu zuwa cikin wani ɗaki, ko da suka shiga gana masgo ne a jere da kayan ɗalibai, sai robobin baransu da ke ajiye da allunan wasu a ajiye.
***
Ɓangaran Hajja Bilkis kuwa tunda Allah ya wayi gari ta ji sam ba ta kaunar komawa offishin hukumar fasa kauri, dan tabbas ta zauna a daran jiya.
Zaune ta ke gaban mudubi,ta sha ado cikin atamfarta yar ingila kalar ja da kore, ta kafo d'aurin kallabi har goshi. Sakar zuci take yayinda ta ke duban kanta a madubi,ga shi dai yanda ta kaya tsakanin ta da Ahmad a daren jiya, tasan tabbas kwanan taikaici yayi, ita kuwa tun da ta samu ya fita ta sha baccin ta har da munshari. Shin ya za ta yi ta shawo kan sa ya sa baki a sakar mata kayanta ba tare da ta koma ba.
Jim kadan dabara ta faɗo ma ta, ta tashi cikin hanzari, hannun ta ta kai gun turarukan ta tsadaddu da ke jere gaban madubin ta,ta shiga fesawa koina a jikin ta, sai da ta fesa wajan kala huɗu kafin ta k'ara gyara ɗaurin kallabin ta, ta tabbatar da ta yi kyau, sannan ta juya ta na tafiya cikin tak'ama ta nufi kitchen.
Kamar yanda komai na gidan ya ke a wadace,haka ma kitchen din ya ke. Sai dai kash rashin tsari da isasshen tsabta na kitchen ɗin ya sa shi zama koma baya wajan k'ayatuwa. Hakan kuma ya sami tasiri ne sandiyar rashin kula na Hajja Bilkis, ta sakarwa yan aikatau komai, hatta girki su suke mata, sai ta kwana ta wuni ba ta lek'a kitchen ɗin ba.
Ta taradda mai masu girki, dattijiya da ake kira Iya dudu, ta gama haɗin abin karin kumallo. Kamar yanda ta saba ga na Ahmad nan ta shirya a faranti guda ta na shirin ɗauka ta kai ma sa.
Ganin Hajja Bilkis da safiyar Allah cikin kitchen, matar da ko tsinke ba ta ɗaukewa a gidan ta sai dai masu aikatau su mata ya sa Iya dudu rusunawa ta gaishe ta gami da tambayar lafiya kuwa? ko an mata wani abun ne ba daidai ba ya sa ta zuwa kitchen da kan ta.
Cike da tak'ama Hajja Bilkis ta karasa cikin kicin ɗin, kana ta amsa mata da
"Ba ko d'aya,kayan karin Honourable fa? Ina fatan dai an kammala"
Iya dudu ta ce "eh na kammala, sune nan jere kan tire, da ya ke yau mun makara ne, shi ya sa ban gama da wuri ba, a yi hakuri yanzu na ke shirin kai masa"
Hajja Bilkis ta tinkari tiren da Iya Dudu ta nuna mata, kwanuka ne na alfarma uku jere kai. Nan ta sa hannu ta buɗe babban ciki, kamshin ɗumamen tuwo ne na shinkafa da miyar kuɓewa bushashe wanda aka yi da bushasshen kifi, ya ji manshanu ya doki hancin ta, ita kan ta sai da ta haɗiye mugun yawu, dan kuwa Iya dudu gwana ce wajan girki. Ta mayar ta rufe kwanan,sannan ta shiga buɗe sauran biyun ma, wanda su ka kunshi ferfesun kan rago, da kuma wanda wainar kwai ke ciki.
Ganin ta gamsu ta ce da Iya dudu
"Iya dudu, na hutasshe ki, yau da kai na zan kai abincin, ki dai k'arasa gyaran kitchen ɗin , kar a kai min nawa abincin wannan ma ya isa....."
Ta ɗauki cokala biyu ta aje bisa farantin, kafin ta ɗauka ta na mai faɗin
"Wai ina Jummai ne? Maza ki ce da ita na ce ta biyo ni da flask din ruwan zafi, da fatan dai ba ta nan tana bacci asaran da ta saba ba ko? Ta shirya min yaro ta kai shi makaranta!"
Iya dudu da har lokacin mamakin Hajja Bilkis da kuma salon da ta tashi da shi na kai ma mijin ta abinci da kan ta bai bar ta ba. Ta na ɗan soshe-soshe ta amsa mata da
"Eh ai dama shi ya sa na makara yau d'in,ai Jummai ba lafiya........."
Cike da ɓacin rai Hajja Bilkis ta mayar da tiren ta aje, ta na mai faɗin
"Ba ta da lafiya ba hujja ba ne! Yanzu ki na nufin ɗana na nan a gidan nan bai yi wanka ba balle ya karya a kai min shi makaranta? har wani ba ta da lafiya! wannan wani irin sakaci ne!"
Cikin karfin hali Iya dudu da dama ta riga ta san za a yi haka ta ce "Ai tuni na shirya Hanif ɗin, ya karya Iro ya tafi kai shi makaranta, eh ai dama shi ya sa na makara"
Jin haka rai bace Hajja Bilkis ta ɗau farantin tana magana a tsawace
"wato kin yi aikin ki kin yi nata, toh da sake, wata yar aikatau zan sake ɗaukowa, duk sanda ɗiyar ta ki ta warke ta cigaba da aikin ta, kuma ki tuna min idan Iro ya dawo ya kai ta asibiti, Allah ya sa ba irin ciwon nan da ake kwasa ba ne!"
Da sauri Iya dudu ta ce "Ah ah zazzabi ne ranki shidade, zan tuna mi ki, Allah ya k'ara girma"
Hajja Bilkis ta yi hanyar fita,ta na tafiya ne ta na magana. "Ko ma zazzabin ne ta yi nesa da yaro na. Ki biyo ni da flask din" sannan ta fice.
Ajiyar zuciya Iya Dudu ta saki, dan tabbas ta na mamakin rayuwa irin ta Hajja Bilkis, haka kuma ta kanyi mamakin yanda Ahmad ke hakurin zama da ita da wannan hali na ta, dan ko suma yan aiki hakuri su ke da ita, shi ya sa kullum ta ke cikin canza su,in banda Iya dudu da ɗiyar ta Jummai, wanda tun tale-tale su ke gidan, abin har ya zame mu su jiki, da tuni su ma sun cika rigar su da iska.
A hankali ta tura marfin kofar da zai sada ta da falon Ahmad. Cikin murya mai sanyi kamar ba ita ta gama balbale shi a daren jiya ba ta yi sallama, tare da cusa kai ba tare da ta jira jin amsa sallamar ba, dan ta yi zatan ya na can cikin ɗakin sa. Hakan yasa tana ajiye farantin ta doshi ɗakin barcinsa amma ga mamakinta sai ta ga kofar a sakaye.
Hannu ta sa ta murɗa hannun kofar amma sai ta ji sa gam Alamun ya sa mukulli. Juyawa tayi zuwa inda ya ke makala safayen makullansa ta ciro ta dumfari ɗakin don duk a zaton ta ya koma barci ne.
Wayam ɗin da ta tarar a ɗakin ya sa zuciyar ta bugu da sauri. Ta dudduba ko ina amma duk da hakan hankalinta ya gagara ɗauka mata cewa ya fita ne don tabbas duk runtsi sai ya shigo ya mata sallama. Labulen tagar ɗakin ta ɗaga wanda yai saitin ma'ajiyar motocinsu, rashin ganin motarsa Lexus GX 470 yasa ta ajiyar zuciya, nan take ta fara jin haushin kanta.
"mstwww" ta ja wani dogon tsaki kana ta juya ta fita ba tare da ta ɗauki farantin ba
***
Sani kuwa kwana ya yi ya na jujjuya yadda Nuhu ya kubutar da lanto abin nacin ransa,washagri yayi nasarar haɗuwa da Nuhu a hayin magarya. Yana hangoshi ya nufeshi da sauri ya mika masa hannu suka gaisa cikin mutuntawa ya ce
"Nuhu nafa gode sossai bisa kokarinka na ceto kanwata, da baka isa wajen ba Allah kaɗai ya san abinda zasu mata".
"Ba komai Sani yi wa kaine, amma don Allah ka kara kulawa da ita. Kuma in san samune ya kamata ka hanata talla. Saboda ba abune mai kyau ba kana kallo kwanakin baya haka aka samu gawar yar talla bayan makarantar mai gari bayan an keta mata haddi. Yanzu ina daɗi wannan lamari?".
Jikin Sani ya yi sanyi ya ce,
"kwarai haka ne Nuhu inshaa Allah zan yi kokarin kulawa".
Yana san tambayarsa yadda akai ya gano in da suka bi Lanto amma ya kasa can ya daure ya tambayeshi.
"Kanina ya ya akai kasan suna bibbiyar Lanto?".
Murmushi ya yi ya girgiza kai,
"ina zauna ne a hayin Madigu su Rabs suka sameni suna murna hannunsu da kayan maye, cikin takaici nake tambayarsu in da suka samu. Rabs ne ya kada baki ya ke bani labarin Lado ne ya basu domin su yi masa wani aiki.
Naita bibbiyarsu dan jin wane aikine, daga bisani na gano hakan ta hanyar Baaba, basu taɓa kawo zan iya bin su ba. Allah dai ya kara tsarewa".
"Aameen Aameen" inji sani, sannan ya sake masa godiya tare da mikewa suka yi sallama sannan ya tafi.
***
Ɓangaren su Rabs kuwa kwana su ka yi sun jinyar raunin da Nuhu ya ji mu su a daren jiya. In da ya bar su nan wajen zube suna maida numfarfashi,abinka da wa'inda ke buge,a haka lado ya same su kwance jina jina daga gani sun ji jiki, kafar Messi ya ɗan taɓa ai ko ya ta shi a firgice ya ari na kare ganin haka Sauran yan uwan suka rufa masa baya. A guje suka fice daga wajen suna neman tsira.
Tsaye lado yayi yana kallonsu, nan take wani sashi na zuciyar sa ya fara faɗa masa anya ba gamo suka yi ba. Ɗaga kan da zai yi sai ya ga inuwa ya gitta masa, sake rufe idon yayi ya buɗe nan ya fara ganin halittu na masa shawagi a wajen, nan ya fara ja da baya yana daga hannu tare da faɗin
" kuyi hakuri, wallahi ba ni bane, ita ce ta zage ni a kasuwa, Wayyo! Wayyo! Wayyo! " a guje ya fice yana Faɗin "Wayyo!" bai tsaya ko ina ba sai masallacin da ke hayinsu nan ya shiga afujajan yana kiran
"Wayyo! Liman nayi gamo Wayyo! Yi mun rukiyya" ya kankame Liman yana runtse ido da iya karfinsa.
"Anya lado bai samu taɓin kwakwalwa ba, ka san aljanun mangariba haukatarwa suke yi, Liman a kamo shi a kai shi gida kawai" fadin ladan yana gyara zaman rawaninsa.
"a yi haka kuwa, bari dai mu ga natsuwarsa in an mass rukiyya, in ya fi karfin bugun aljanu sai a mika ma iyalansa su nema masa taimako" Liman ya faɗi yana kamo kan Lado. Nan aka fara masa karatu in banda ajiyar zuciya ba abinda yake yi. Nan barci ya fara gaba da shi, sai jin saukan daurina yaji a jikinsa yayin da Liman yai karatu yai karatu yan masallaci suka bada shawaran a zane su tunda sun ki magana suna neman tafiya da lado.
"Wayyo Liman nine kuyi hakuri ku dena duka na" lado ya faɗi iya karfinsa amma hakan bai sa an tsagaita ba har sai da aka ga yana tari da shakuwa.
"sun fita Liman, sannu Lado Allah ya kara tsarewa" Faɗin ladan yana sauke daurina.
Kallon su kawai lado keyi yana antaya musu ashar a zuciya don ya dauki abinda suka yi tsantsan zalunci ne kawai ba komi ba.
No comments:
Post a Comment