Sunday, 25 December 2016

Sakaci 13

     💔💘 *SAKACI* 💘💔

    

                  1⃣3⃣

© *Fatima A Garba*

Muna tsaye a bakin emergency, duk kan mu kuka mukeyi sosai inka cire Ya Umar da ya dafe kanshi ba abinda ya keyi sai ajiyar zuciya.

Dr ne ya fito daga d'akin da Mama ta ke, dukanmu muka rufamai muna tambayarshi halin da Mama ta ke ciki, cikin damuwa yace

"ku biyo ni office"

Bayan Dr ya cire safar hannunshi gami da wanke hannun kafin kuma ya zauna, kasa hakuri Ya Umar yayi, cikin zak'uwa ya ce.

"Dr ya jikin nata please ka sanar damu" gyara zama Dr yayi gami da kallon mu sannan ya ce.

" Umar you are a Doctor cool down, zata iya farkawa zuwa ko wanne lokaci, sai dai fa akwai matsala"

A take gaba na ya yanke ya fad'i zama nayi jagwab ina cewa

"shikenan na shiga uku na gama yawo na kashe uwata"

Ya Abdallah ne ya ce "ke ki rufe mana baki ko ki bar nan wuri kafin na miki illa" ya fad'a cikin d'aga murya.

Ya Umar kuwa wani kallo ya aikomin dashi wanda yayi sanadiyar kad'awan hanjin cikina, toshe bakina na yi da hannu na.

Ya Umar ne ya sa ke cewa " muna sauraronka Dr"

Dr ya cigaba da cewa "gaskiya ina tsoron sanar daku mamanku ta kamu da ciwon zuciya, kuma damuwa kad'an zai iya janyo zuciyarta ta sake bugawa, wanda kuma zai iya zama sanadiyar rasa rayuwarta, don haka dole ku kula idan kuna son ta cigaba da rayuwa, yanzu dai munci nasarar ceto ranta"

Kuka sosai muke yi nida Ummi da Ya Abdallah, Ya Umar baiyi kuka ba amma damuwar da na gani a ta re dashi ya tabbatar min da daurewa kawai ya keyi.

Takardar magungunan da za'a siyawa Mama Dr ya bamu, Ya Umar ya ce mai zamu iya shiga mu duba ta ya ce eh amma za'a canja mata d'aki ma, yanzu ya je fara biyan kud'in.

                   ***
Zaune nake a gaban Mama na sata a gaba ina kuka, a hankali ta rik'e hannuna ta na k'ok'arin bud'e idanunta.

Ganin ta bud'e idonta yasa na fad'a gaban gadon ina rok'onta gafara, ga mamakina sai ta ce "ki daina kuka kinji"

Cikin kuka na ce "Mama ni mai laifi ce, nayi kuskure,  ki yafemin wallahi bazan k'ara ba"

Murmushi Mama ta yi wanda nasan na dauriya ne, kafin kuma tace "Farida bakiga d'akin ba mu kad'ai bane, ko so kike ki tonawa kanki asiri? Duk kibar wannan maganar har Allah ya bani lafiya mukoma gida kinji" gyad'a kai na yi.

A hankali ta kira Ya Umar gami da nuna ni, ta ce "Umar kaje da ita a ma ta gwajin ciki da na k'anjamau"

                "Dam"

Naji gabana ya fad'i, domin tunda abun nan yake faruwa ban ta6a wannan tunanin ba.

Fita ya Umar yayi ba tare da yayi min magana ba, sai Ummi ce ta ce na ta shi na bishi, haka na cigaba da binshi jikina ba k'wari har zuwa inda ake gwaji (LAB) d'in.

Da shike ba nisa tsakanin Lab d'in da asibitin, sanar dasu yayi irin gwajin da yakeso a yimin, kafin kuma yaje ya biya kud'in ba tare da 6ata lokaci ba suka fara aikinsu kasancewar sun san shi.

Ranar duk tsorona da allura haka na daure aka d'ebi jinina don na tsorata da Ya Umar, bayan sungama gwajin suka bamu sakamakon, wannan lokacin ma Ya Umar baiyi magana ba gani nayi ya fita nima na bishi.

Jin sakamakon gwajin nawa yasa hankula da dama ya kwanta, domin ba'asamu cututtukan a jikina ba, sanna ba ciki, amma sunce na dawo bayan wata uku a sake yimin gwajin HIV.

                ****

Ni da Ummi ne muka cigaba da jinyar Mama, Ummi ba ta barina naje ko'ina idan wani aike ne sai dai Ya Abdallah yaje idan kuwa baya nan to ita da kanta ta ke zuwa.

                     ******

Kwanan Mama shida a asibiti aka sallameta, a wannan kwanakin na rame na lalace bani da aiki sai kuka, kuma ba wanda ya tayar da abinda ya faru a cikinsu.

Ranar da muka dawo gida haka matan gida da makwabta suka cigaba da shigowa gaishe da Mama.

Bayan mun idar da sallah isha'i lokacin Ya Abdallah ya dawo daga masallaci, Mama ta dubeni ta ce.

"Matso nan Farida" ta nuna min gabanta bayan na zauna ta dubi Ya Abdallah tace " bawan Allah (sunan da Mama take yawan kiran Ya Abdallah dashi kenan) kaje falo ga abincinka can kaci zanyi magana da Farida, kaima kuma anjima akwai maganar da zamuyi"

Toh yace sannan ya fita, Mama ta juyo gareni ta d'an kalleni na d'an wasu dak'ik'u, ni kuwa na sunkuyar da kaina domin bazan iya had'a ido da ita ba, gyaran murya Mama ta yi sannan ta fara magana kamar haka!

"Farida inaso kiji tsoron Allah ki fad'a min gaskiyar duk abinda na tambayeki idan kinaso na yafe miki, idan kuwa kika yimin karya tofa babu tantama Allah zai kamaki kuma idan nazo na gane k'arya kika yimin, ba zan yafe miki ba"

Cikin kuka nace "wallahi Mama zan fad'a miki gaskiyar duk abinda kika tambayeni" na k'arashe cikin zubar hawaye, Mama tace!

"Ki share hawayenki ba kuka nace kimin ba" share hawayena nayi sannan Mama tace.

" Yaushe kuka fara aikata zina ke da Hassan?"

"Ya kai shekara biyu, tun wani lokaci da yazo ya sameni ina kukan yunwa yace na bishi na kar6a abinci, tun daga ranar ya fara wasan ta6ani"

Mama ta girgiza kai sannan ta ce "Mai yaja ra'ayinki harki ka amince mai, wanda a wannan lokacin ba kikai shekarun da sha'awa zata rinjayeki ba, wanda kwata-kwata lokacin baki wuce shekara goma sha biyu ba"

Ban 6oyewa Mama komai ba, Na fad'a ma ta komai.

Cikin wani irin yanayi Mama ta ce " mai yasa kika 6oye min wannan babban al'amarin, mai yasa baki sanar dani ba tun wuri"

Nace "na yi k'ok'arin sanar dake tun farkon lokacin da ya fara ta6ani amma kika hauni da fad'a karshe kika gargad'eni, da ga baya kuma shi ya dinga tsoratar dani......" Nanma na sanar da ita.

Hawayen da nagani a idon Mama da kuma kalaman da take fad'a shi ya tayarmin da hankali matuk'a!

"Ina tsoron gamuwata da Allah, ban rik'e amanar da ya bani ba, na yi sanadiyar lalacewar tarbiyar ku"

Ina kuka na ce "Mama mune da laifi mune muka kasa hakuri da juriyar jarabawar da Allah ya aiko mana, Mama na tuba ki yafemin sannan ki rok'a min Allah ya yafemin"

Cikin wani irin kuka Mama ta ce " na yafe miki Farida amma tabbas nayi *SAKACI* wurin baku tarbiya rauni na ya hanani na nuna muku illar aikata abubuwa da dama, wannan ne yaba wasu a waje damar d'auraku akan gur6ataccen tulba, sannan suka baku fatawa wanda suka kasance na k'arya da yaudara, ku yafemin yarana, Farida karki sake 6oye min duk wani abu da ya shige miki duhu"

"Na miki alkhawari Mama na miki alkhawari"

Rungume Mama na yi ina kuka, mun d'auki tsawon lokaci muna kuka kafin Mama ta rarrasheni.

Cikin dare inaji Mama suna tattauna maganar da Ya Abdallah wanda shima ta yi mai nasiha sosai.

Haka washegari ma suka zauna da Ummi suka tattauna karshe Ummi ta kirani ta yimin nasiha mai shiga jiki.

~Ummu Hanan~

No comments:

Post a Comment