Sunday, 25 December 2016

Sakaci 21

          💔💘 *SAKACI* 💘💔

  

                  2⃣1⃣

© *Fatima A Garba*.

Wanna karan Baba ne yayi magana.

"Jiya bayan sallar isha'i, mun fito daga masallaci nida Alhaji, muka had'u da kawun shi Ahmad, bayan mungaisa, ya ce ya zo ne akan batun aurenku, mukace muna saurarensa, yace dama suna so a d'aga d'aurin auren"

"Nidai ban iya magana ba, ga Alhaji nan shi ne yace toh mai yasa basu fad'a da wuri ba sai da aka gama gayyatan jama'a, sai shi kawun nashi yace shi dai d'an aike ne"

"Alhaji ya sake cewa toh idan an d'aga har zuwa yaushe ne, sai kawun nashi yace zuwa lokacin da suka kammala shirye-shirye amma idan kin samu miji kafin nan toh fa kar a jirasu a aurar da ke"

"Tabbas alokacin da zan fad'i na tabbata zan rasa wani 6ari na jikina, ni nasan na yi *SAKACI* tun farko amma ance danasani k'eya ce"

"Waya na d'auko da zummar yin kira amma Alhaji ya ce wa zan kira nace zan fara sanar da jama'a anfasa ne, Alhaji yace min waya ce anfasa, tabbas gobe za'a d'aura miki aure"

"Nace anya Alhaji kaji abinda mutanan nan suka ce da kyau kuwa, yace yaji, kuma abinda ya fad'a d'in ma ba fashi za'a d'aura miki aure amma wannan karan ba da Ahmad ba, da Umar za'ayi"

"Nace wa Alhaji hakan ba zai yuwuwa ba, ba za asashi dole ya aureki ba sai dai idan ya yarda, zai aureki"

"Umar d'an albarka ne, yaron nan ana zuwa mai da maganar ya amince ba gardama, ya kuma k'ara da cewa, basu isa su wulakantaki ba, idan dama niyarsu kenan"

Baba ya d'an dakata kafin ya d'aura " Farida bani da abinda zan sakawa bayin Allah nan dashi sai addu'a, sunyi min komai, kuma ina rok'onki don Allah kiyiwa Umar biyayya, Allah sarki Sakinatu"

"Ki yafemin d'iyata ni ne silar komai, da badan na yi *SAKACI* da baku kulawa ba da ba wanda ya isa ya wulak'antaki, ki yafe min"

Hawaye ne yake zuba daga idanuwanshi yana gogewa, bayan Baba yayi shuru Ummi ta ce.

"kiyi hakuri Farida, nasan an tursasaki amma kiyi biyayya" 

Saurin zuwa ta yi ta rungume Ummi gami da cewa "haba iyayena mai yasa zaku dinga rok'ona bayan ni kuka rufawa asiri, ni kuka taimakawa alokacin da kowa yake guduna"

"Mai yasa zakuyi tunanin zan bijire muku, wanda yafi dacewa da ya bijire ya muku biyayya ni wace ce da zan bijire, ku yanke duk hukuncin da kukaso akaina ni kuma zaku sameni mai biyayya agareku, na yarda da kaddarata Baba kadaina damun kan ka haka Allah yaso"

Dukansu sai da sukayi hawaye, Ummi ta rungumeta ta na cewa "Allah ya miki albarka d'iyata gidan yayanki shi ne gidan da za ki zauna hankalinki a kwance ba ta re da an goranta miki ba"

Haka Innayo suka yi ta yiwa su Ummi addu'a, sannan a karshe suka sawa  Farida albarka.

 
                 ****

Lokacin da Mariya taji labarin auren babbar hauka ce kawai batayi ba, kuka ta ke tamkar mahaukaciya ta na cewa.

"Wallahi ka munafurce, saboda ni baka d'auken da mutunci ba Dr sai yau da za'a d'aura auren ne zaka fad'a min"

Cikin rarrashi Dr yace "Mariya bani da nufin 6oye miki, abun ne yazo a kurarren lokaci kiyi hakuri"

"Cike da rashin kunya ta ce " wallahi k'arya ne, ai dama tunda naga ka gina wannan gidan harda yin wani shashi kace na iyayenka ne, wai ni zaka munafurta"

"Kuma idan ba cin amana ba ka rasa wacce zaka aura sai ita, tabbas nasan karshen zamana a gidan nan yazo, kuma Allah ya isa tsakanina da ku"

"Mariya wa kikewa Allah ya isa" Dr ya fad'a cikin hasala, cike da rashin kunya tace "da duk wanda ya ke da hannu aciki"

Ba zai iya cigaba da sauraranta ba dan zai iya aikata abinda baiyi niya ba, don haka yayi fitarshi ko bi ta kanta bai sake ba, aikuwa fitan nashi da dad'a tunzurata.
 

A ranar ta tattara yaranta su uku ta koma gidansu.

Fad'a sosai akayi tsakanin Alhaji da abokinshi, shi Alhaji Sama'ila gani ya ke Alhaji ya wulakanta mai y'arshi.

Yace kuma ta yi zamanta bazata koma gidan Dr ba, ba yadda ba'ayi dashi ba yace idan har anaso d'iyarshi ta koma toh fa sai dai a warware wannan auren, shikuwa Alhaji ya ce tasha zamanta.

                  ****

Da daddare aka kawo Farida d'akinta bayan tasha kuka sosai, shashin da Dr ya gina a matsayin na iyayenshi idan suka zo Bauchi  nan ne aka sa Farida, bayan anyi mata jere.

Kowa sai yaba tsaruwa gidan ya ke, kwata-kwata mutanan gidan basu wuce wata guda da tarewa a ciki ba.

Gidan ba wani girma ne dashi na tashin hankali ba, gida ne dai-dai misali amma ya tsaru matuk'a, yana d'auke da sassa uku, kuma ajere suke, na maigidan shi ne a tsakiya, sai kuma d'akin masu aiki a baya.

Bayan y'ankawo amarya sun tafi, ya rage saura amarya ita d'aya.

Har wurin karfa sha d'aya na dare ba ta ga idon ango ba, toile ta shiga ta d'an watsa ruwa ko ta d'an ji dadi a jikinta, rigar bacci kawai ta saka, ta gaji tana bukatar ta kwanta, aikuwa bata jima da kwanciya ba bacci ya d'auke ta.

Ba ita ta tashi ba sai da asuba, taso ma ta makara don haka a gurguje ta shiga toilet ta d'auro alwala.

Bayan ta idar da sallah, ta jima ta na azkar d'inta kafin kuma ta d'auko qur'ani ta cigaba da karatunta, sai da gari yayi haske sannan ta ajiye qur'ani bayan ta yi addu'a.

Bayan ta fito daga wanka ba ta wani tsaya yin kwanliya ba, powder kawai ta murza sai man baki, kafin kuma ta zura doguwar rigar atamfa.

Da gyara gado ta fara gami da kintsa wasu abubuwa kafin kuma ta fito falo, wanda tsaruwarshi ya burgeta

"Falon ba wani girma ne dashi can ba, d'an madai-daici ne amma fa ya tsaru, ba'a zuba mai wasu tarkace ba, duk yadda ka kalli falon sai yabaka sha'awa.

Falon yana d'auke da d'akunan bacci biyu ko wanne da toilet aciki, sai kitchen shima madedeci mai kyau, lek'awa ta yi ta ga komai a kintse.

Wannan fa duk kayan da Dr ya siyamin ne bai san gidanshi za'a kawo ba, tabbas Dr ya iya za6e" ta fad'a zuciyarta.

Ledar da ta gani akan fridge d'in ne ya d'au hankalinta, zuwa ta yi ta bud'e, gashashshiyar kaza ce a ciki, ga kuma ledar juice da ruwa agefe,  tabbas ya shigo bayan ta kwanta.

Cirewa ta yi a ledar ta juye akan faranti mai fad'i, sannan ta sakashi a cikin fridge had'e da kunnawa, su juice d'in ma ciki ta saka su.

Ta gama share gidan had'e da kunnna turaren wuta ko ina ya d'au kamshi, shigowa yayi sanye da farar jallabiya, fuskarshi sai wani shek'i ta ke, wannan kamshin na shi na ko yaushe ya na tare da shi.

Sunkuyawa ta yi had'e da gaisheshi, ya ansa da "lafiya" fuskar nan a tamke, kafin kuma ya ce

"Ya kika tashi, da fatan ba wata matsala?"  "Lafiya lau, Alhamdulillah" ta ansa, ya sa ke cewa.

"Madalla, idan kina buk'atan wani abu sai ki kira ni a waya" ya na gama fad'an haka ya yi ficewarshi.

Kama baki ta yi gami da cewa "lalle akwai aiki ja agaba na, toh yanzu haka zamu cigaba da zama da bawan Allah nan, tabbas ina bukatar juriya da hakuri".

Ranar dai bata yi zaman kad'aici ba domin jama'a da dama suna ta zuwa, shi kuwa gogan ba ta kuma sakashi a ido ba sai washegari da safe.

Kullun da safe zai shigo yaga lafiyanta haka duk wani abun buk'ata na gida da yasan za'a buk'ata ya na aiko ma ta, amma har wannan lokacin ba sakewan fuska kuma ba wata magana ta fahimta da ta shiga tsakanin su.

                ****

Kwanan Mariya hud'u ta dawo, ba ta re da anje biko ba, shi kanshi Dr sai da yamma ya ga yaran, kuma bai lek'ata ba, halin ko inkulan da ya nuna akanta ya dad'a sawa taji ta tsani Farida.

Satin Farida d'aya a gidan Dr amma har wannan lokacin bai ta6a kwana a d'akinta ba, da yamma ta na zaune kallo ta keyi, wayarta ta yi k'ara ta na dubawa ta ga number shi ne, ma6allin ansa wayar ta latsa kafin kuma ta kara a kunnenta.

"kije elpis (asibitin shi) akwai marasa lafiya ki dubasu, idan kingama ki jirani akwai surgery da zamuyi" cewar Dr.

Dama ta gaji da zaman gidan don haka da murnarta ta shirya ta fita.

Bayan ta gama duba marasa lafiya ta d'an fito wani wurin da sauran likitoci suke zaune ta zauna anata hira da ita, ganinshi ta yi a gabanta fuskarshi a tamke ya na aika ma ta da harara sunkuyar da kanta k'asa ta yi.

Cikin maganarshi ta isa ya ce "ki sameni a office" oh ita ya zatayi da bawan Allah nan, tashi ta yi ta bishi jiki babu k'wari, ta na addu'ar Allah yasa ba laifi ta yi ba.

~Ummu Hanan~

No comments:

Post a Comment