💔💘 *SAKACI* 💘💔
2⃣5⃣
© *Fatima A Garba*
Kasancewar bai kwanta da wuri ba yasa ya makara, d'akin Mariya ya soma shiga, bai sameta a falo ba, jiyo hayaniyar Muhammad (d'ansu na uku) a kitchen hakan ya tabbatar mai da suna kitchen d'in.
Don haka kai tsaye kitchen d'in ya nufa, da gudu Muhammad ya zo ya rungume Babanshi, d'aukanshi Dr yayi yana mai wasa, kafin kuma ya juyo ga Mariya wacce ko kallo bai isheta ba.
Ya lura tunda ya auri Farida sam ya rasa kulawa a wajen Mariya, ita kullun gani ta ke yana fifita Farida akanta.
"Ranki shidad'e baki ji shugowata bane" Dr ya fad'a, ta6e baki ta yi had'e da cewa " ai gani na yi maganar tawa bata fiye zama mai anfani ba, tunda kullun gani ake inada k'orafi, k'iri-k'iri za'a cuceni ace kuma kar na yi magana"
Murmushi yayi gami da cewa "Hajiya Mariya kenan to yau ma na yi lefi ne"
"Dr ka maidani yarinya karama, duba agogo k'arfe goma kana d'akin ta gaban goshin taka, ba labarin office, balle kuma mu musami darajar azo aduba lafiyarmu, su khalil har suka tafi school basu sami ganinka ba"
"Yi hakuri bank'i zuwa dubaku da gan-gan ba, ni kaina makara na yi" Dr ya fad'a,
Ciki fad'a Mariya ta ce " Ai ba sai ka fad'amin kwana kukayi bakuyi bacci ba, nasan da haka, kuma cutar da akeyimin Allah na gani"
Ganin idan ya tsaya ranshi ne zai 6aci yasa ya kama hannun d'anshi suka yi tafiyarsu ya barta ta nata sababi.
Kai tsaye shashin Farida ya nufa domin yana buk'atar ganinta hankalinshi sam yak'i kwanciya, sanin da yayi jiya ya barta cikin halin damuwa.
Goge kujerunta ta keyi, suka shigo, Muhammad ne yazo gareta cikin sakewan fuska ta rungumeshi ta na "oyoyo Alhajina".
So yake ya had'a ido da ita amma sam tak'i yarda, kallonta ya ke sosai tabbas ta bashi tausayi duk da bata bata bari ya kalli cikin idonta ba.
Amma idanunta sun kumbura wanda yasan ba tantama kwana ta yi tana kuka.
"Ina kwana" ta katse mai tunani ba ta re da ta kalleshi ba, cikin sanyi muryar da ya bata mamaki ya ansa, sannan ya ce "kintashi lafiya"
Tambayar da ya mata yafi mata kama da ta rainin hankali, domin haka bata ansa ba.
Ya d'auki lokaci mai tsayi yana zaune a wurin har taje ta had'awa Muhammad tea ta dawo bai motsa ba, abun sai ya mata wani irin, domin bai ta6a kwatanta hakan ba.
"Ki shirya ranar juma'a zamuje Jos mu gaishe su" ya katse mata tunani, gyad'a kai ta yi, alamar " toh"
Sai da ya tashi tsaye kafin ya ce "Alhaji na barka wurin Mamanka zaka taya ta hira ko" yaro ya gyad'a kai alamr " eh "
Ranar haka suka wuni da Muhammad, tabbas yaron ya d'ebe mata kewa.
Ita kuwa Mariya ba ta yi tunanin gun Farida Dr ya kai Muhammad ba, ta yi zaton suna ta re ne, da tana da masaniya da tuni tazo ta d'auke d'anta.
Sai da yamma da yaji hayaniyar y'an uwanshi suna wasa awaje, ya fita ya, daganan ne bai sa ke dawowa ba.
*****
Da wuri ta kammala shirinta ta na fargabar zuwa Jos d'in amma kuma ta na son taje ta ga Ummi.
Sanin Dr ya siyawa su Ummi gida a unguwar Ibrahim tayo, yasa fargabanta ya ragu, domin ba taso ta kuma lek'a unguwar da al'amura da dama suka faru acikinta.
Anayin sallah juma'a Dr ya umarcesu da su fito, Mariya dai gudun 6acin ranshi ne kawai yasa zata je amma bawai don tana so ba.
Ita a tunaninta salon a wulak'anta ta ne kawai yasa aka tsiro da tafiyar da ita.
Koda suka fito da saurinta ta wuce Farida harda bangajeta ta shiga gidan gaba, azuciyar Farida ta ce
"Hmm ke gaba ya dama da kinyi hakuri ma ni ba shiga zanyi ba"
Tafiyar kurame sukayi a motar ba wani mai magana d'an gara Farida ta biyewa yara suna ta ma ta surutunsu na yara.
****
Da gudu taje ta rungume Ummi, cike da farinciki Ummi ta ce "oh ni wai Farida Umar sai kin k'arasa ni"
"An zo wurin" Mariya ta fad'a a zuciyarta, yak'en dole kawai ta keyi amma ba karamin haushi sunan ya ke bata ba.
Sosai Ummi ta ke farinciki, duk motsin da Farida zata yi idanunn Ummi na kanta.
Cikin k'ank'anin lokaci aka wadatasu da kayan ciye-ciye da na sha, sai da sukaci sukayi dam kafin suka tashi suka gabatar da sallah la'asar.
Mariya ce ta ce "na fito ne ka saukeni a gidan Auntyn tawa" ta fad'a lokacin da ta ga yana shirin fita.
Fuska ba walwala Dr ya ce "sai da daddare "
"Don girman Allah ka kaini yanzu" zaiyi magana Ummi ta katseshi da ce wa
"A'a tunda ta had'aka da girman Allah ka kai ta"
Ba zai iya musu da Ummi ba yasa ya kad'a kai kawai gami da ce wa "ba da yarana za kije ba" "toh" kawai ta ce domin tasan dole akayi mai bawai don yana so ba.
Bayan sun tafi yara kuma ansa musu kallo, Ummi ta kamo hannun Farida gami da ce wa " d'iyata me yake damunki ne, dubi yadda kika rame"
Murmushi Farida ta yi kafin kuma ta ce "me kika gani Ummi ba fa komai, ni ba abinda yake damuna"
Ummi ta ce "Farida kalli cikin idona ni ba yarinya bace a gabana aka haifeki don haka babu abinda za ki boye min, idan har kin d'aukeni a matsayin uwa Farida ki sanar dani abinda ya ke damunki"
Hawayen da ta ke mak'alewa ne ya fara zubowa, cikin muryar kuka Farida ta ce "Ummi ki raba auren nan please"
Murya mai cike da damuwa Ummi ta ce "wani abu yayan naki yake yimiki, sanar dani Farida karki 6oyemin komai"
"Ummi ba komai nidai ki taimaka ki sakashi ya sakeni idan ba haka ba wallahi ciwon zuciya nima shi zai zama ajilina kamar Mama"
Rungumeta Ummi ta yi gami da cewa " shi d'in waye wallahi bai isa ya wukantaki ba, bai isa ba wallahi dani ya ke, kwantar da hankalinki Faridana wallahi Umar bai isa ba, ni zanyi magani komai, ki manta dashi kinji, karna sa ke jin batun ciwon zuciyar nan"
~Ummu Hanan~
No comments:
Post a Comment