[2/9, 7:09 PM] Ummu Abdoul👸🏼: KURURUWAR SHAI’DAN
© Ummu Abdoul
(4)
Tana amince ma k’awancen kenan wasik’a ya shigo, bud’ewa tayi nan taga daga sabuwar k’awarta ne Kaska mai Ruwan dadi, hoto ne ta turo na wasu mata biyu suna aikata masha’a, kafin ta gama (downloading) hoton wani sak’o ya shigo.
“Inama inama ni da zoba ta Sadiya ne a hoton nan.”
Sandarewa tayi anan zaune amma sai ta sami kanta da hasaso su suna aikata wannan b'arnar. Zumbur ta mik’e tana fad'in
“Astagfirullah, Ya Allah ka shirya ni,Ka kareni daga fad'awa halaka." Nan ta aje wayar ta fad’a duniyar tunani. Wani sashi na zuciyarta sai hasko mata hoton nan take yayin da d’ayan sashin na nuna mata halakar da take neman jefa kanta a ciki.
Kiran sallar da akayi ne ya dawo da ita duniyarmu da ga duniyar tunani, tashi tayi ta sallaci Azahar bayan tayi nafila kafin tayi, da ta idar ma ta sakeyi. Ayar K’ur’ani yayi ta mata yawo akai inda Allah yace “Lallai sallah na hana mutum aikata alfasha da munkari (Sa6o)” Murmushi tayi tace Allah ba zai barni na fad’a tarkon Kaska ba, bara kawai na maida mata da martini.
Wayar ta sake d’aukowa ta shiga facebook ta aika ma Kaska da
“Hahaha! Lallai sai fa zoba, nifa bana wannan harkar sannan ina miki nasiha da ki tuba ki daina kema." Ta aika cikin mintuna kad’an ta sake maido mata da martani
“Ni ma ai bana cikin masu aikata abinda kike tunani”
“Don Allah dai, amma kike aiko min da sak’on nan”
“Sadiya kenan, toh ai muna yi ne don rage kewar Oga, maigida na a Warri yake aiki, soja ne ni kuma ina Kano”
“Kai amma kina shan kewa, ni Ogana yaje taro ne a k'asar Singapore ina sa ran nan da kwana biyu zuwa uku zasu kammala ya dawo”
Haka dai hira ta 6arke tsakanin Sadiya da Kaska, har sukayi musayar lamba don yin Whatsapp. Sunyi sati da had’uwa kuma hirarsu kullum bata wuce gaisuwa, idan tayi tsawo ne tambayar iyali. Ganin Sadiya ta saki jiki da ita nan Kaska ta tsiro da turo mata labarai nan batsa duk akan alfasha tsakanin jinsi d’aya. Yau ma kamar kullum ta turo mata wani da yayi mata dadi wanda labari wata yarinya ke badawa wacce ta kasance mai tarbiyya da wata ta yaudare ta daga had’uwa a Whatsapp suka fara kiran juna da love. Group din da suka had’u karatun addini kawai akeyi don ma tana daga cikin masu kawo gudunmuwa a wannan fannin, kwatsam selai wata tayi tambaya tana so a fad’a mata ya zatayi ta kare kanta don duk kawayenta yan mad’igo ne, nan kuwa ustaziyar nan ta fara tsine tsine da zage zage tana nuna musu halakar da suke ciki, a ranar k'awarta da ta ke kira LOVE ta k’uduri aniyar sa ta a harkar itama taji inda dad’i. Ba’a fi wata uku ba suka yi alkawarin had’uwa da juna, nan sukayi a gidan Love zasu had’u kasancewar ustaziyar budurwace kuma tana karatu a garinsu Love ne.
Ranar had’uwarsu a ranar Love ta cinma burinta domin kwayoyin tada sha'awa ta sa mata a ruwan lemun da ta kawo mata, kwayoyin na fara aiki kuwa taja ta zuwa d’aki nan suka fad’a duniyar Alfasha. Duk da ustaziyyar batason abinda sukeyi amma kwayoyin data sha yasa ta kasa hana wa, tana ji tana gani tayi amfani da abubuwan da turawa suke had’awa domin masu wannan harkar (Sex toys) aka kawar mata da mutuncinta.
Tayi bak’in ciki amma tun daga ranar ta fara wannan aikin, kuma tana alfahari da samun nutsuwa ta wannan harkar. Tana alfahari tayi amfani da hanyar da aka shigar da ita ta janyo matan aure da ‘yanmata fiye a kirga. A k'arshe kuma take ma ustazai nasiha da su daina tsine ma masu wannan harkar su dinga yi musu wa'azi, addu'a da nasiha zai fi.
“Mtswww wawuya kin so ne.” Fadin Sadiya bayan ta kammala karanta karshen.
“ Ta ya ma zan bari social network ya lalata min tarbiyya ta Zoba?" (kasancewa haka suke kiran junansu yanzu) ta aika ma Kaska.
“Hakane fa, Allah dai Ya sa mu dace, bara na kwanta." Ta aika mata tana mai sauka daga Whatsapp din.
Sunfi sati d'aya basuyi magana ba saboda Kaska tace mata bata da (data), ranar da ta dawo sak’on bidiyo ta aika ma Sadiya wanda yai dai dai da kwana biyu da tafiyan mijinta k'asar Turai don yin kwas na wata biyu, nan kuwa ta bude, bidiyon batsa ne tsantsa kuma jinsi d’aya, maza na nasu mata na nasu duk a waje d’aya. “Wa iya zubillah” Ta fadi tana mai kashewa. Sai kuma ta sami kanta da kunna wannan bidiyon. Sai da ta kalla tsaf,wanda hakan ya janyo wanka ya hau kanta.
“Inama Inama” Hakan ta aika mata a matsayin nuni da ta kalla.
“Zoba na san kin jik’e ko” fadin Kaska
“Hmmmn” Ta aika mata had’e da dan aljanin nan mai nuni da jin kunya (Emoji)
“Dan turo in gani Zoba, nasan tagwaye na sun mik’e tsaye suma” Ta sake aika wa sadiyar.
Maimakon Sadiya tayi mata wa'azi kamar yanda ta saba duk sanda tayi mata maganar batsa,kawai sai ta tashi kamar wacce aka mintsila ta fara daukar hoto tana tura wa.
Tun daga wannan ranar Kaska zata aiko mata da bidiyo mai d'aga hankali, sai ta sa ta ta turo mata hotunan wasu sassa na jikinta sannan su cigaba da aika ma juna kalamai na batsa da watsewa.
( Wa’iyazubillah. Anan nake kira ga yan uwa masu irin wannan harkanlr da wanda basa yi, kar kice kinfi karfin fad'awa sannan kar kice kina addu'a, ki kuma cigaba da harka da masuyi addu'ar ki zai kar6u. Sam kiyi addua sannan kiyi kokari ki yak’i shaid'an, duk da haka suke farawa tun suna tunawa da istigfari har su rasa imaninsu gabad’aya. Sai kunyi kakuri zan dinga amfani da wasu kalamai da zasuyi shigen batsa, duk don na isar da sak’on da kyau ne, Allah ya shirye mu da zurianmu)
[2/9, 9:48 PM] Ummu Abdoul👸🏼: 👹 KURURUWAR SHAI'DAN 👹
©Ummu Abdoul
(5)
Cikin k'ank'anin lokaci wata k'azamar shak'uwa ya shiga tsakanin su, abu ya munana don Sadiya har wasa take da kanta tana d'aukan bidiyo ta tura ma Kaska.
"Zoba kin k'i turo min naki kullum saidai na tura miki"
"Haba Zoba! Kinsan camerar wayata ta samu matsala ne, kuma kishiyarki tak'i siya mini sabuwar waya"
"Hmmmn shike nan" Ta fad'i, nan take Kaska ta sauya labarin, suka faranta ran juna.
Ana cikin haka ne Sadiya ta samu sabon gayyatar zama aboki a Facebook (friend request) da kamar ba zata amince ba sai kuma ta amince duk da kasancewarsa namiji.
"Assalamu Alaikum" Sadi Hadi Yusuf (sabon abokinta) ya turo mata.
"Waalaikumus salam" Ta bashi amsa ta sauka.
Tun daga ranar duk sadda ta hau yanar gizo zata iske sak'onshi na sallama ko gaisuwa.
Tsakaninta da Kaska wani sabon shak'uwa da kauna ne ya k'ullu. Tayi dukkan k'ok'arinta wajen 6oye ma mijinta da mutanen da ke tare da ita muguwar d'abi'arta.
*************************
"Na shiga uku" Ta fad'i da karfi kuma a firgice. Kulle idanunta tayi ta sake bud'ewa, fita tayi daga Facebook d'in ta koma whatsapp don ta tabbatar da zatonta. Ilai kuwa, babu abinda ya bambanta. Sak sak'on da Kaska ta turo mata shi Sadi ya turo.
"Wanene kai?" Ta aika masa bayan ta d'an tattaro natsuwarta kad'an.
"Masoyinki"
"Masoyi kuma?"
"Haba Sadiya ko sai na zo nayi wasa da 'yan biyu na" Wannan da ta karanta yafi d'aga mata hankali, don abinda ta aikama Kaska kenan, tana son ayi wasa da 'yan biyunta.
"Don Allah wanene kai, twins na gidan kakarsu dazu Abbansu ya kaisu"
"Hahhhhh kyal kyal kyal"
"Don Allah malam ni matar aure ce"
Abinda ya turo yafi komi d'aga hankalinta domin kuwa gaba d'aya zantuttukanta da Kaska na yanzu ya watso mata. Fitsarin tsaye ne kawai bata yi ba da ta gani.
Komawa tayi wajen Kaska ta tambaye ta wanene Sadi. 'Yan Aljanun nan masu nuni da gwalo ta turo mata. Nan ta rud'e amma ta daure ta sake tambayarta, amsa d'aya dai ta sake samu
[2/11, 5:35 PM] Ummu Abdoul👸🏼: 👹 KURURUWAR SHAI'DAN 👹
©Ummu Abdoul
(6)
"Wai idan kika gano ni namiji ne ya ya zakiyi?" Fadin Kaska.
"Don Allah fad'a min gaskiya kinga ba zancen wasa a ciki"
"Hahhhhh!!! Lallai kam babu zancen wasa, sai kin fad'a min wane irin mataki zaki d'auka idan kin san jinsi na"
"In namiji ne kai zamuyi sallama ne kawai"
Sa'kon magana aka turo mata, cikin rawar jiki ta bud'e, dariya ne irin ns gardawa marasa imani, nan da nan taji gudawa ya zo mata.
"Kin san dai ina da lambarki da hotunan sassan jikinki, wallahi kika ce zaki katse alak'ar mu zan yad'a ki a duniya."
Sak'on da aka turo mata kenan.
"Sunana Sadi, bana harka da 'yan mata sai dai matan aure, yanzu dai ki shirya zan shigo Katsina, kuma zamu had'u burinki duk zasu cika lokacin kinga babu ke babu inama inama."
Fadin tashin hankalin da ta shiga ma b'ata lokaci ne, tayi kuka kamar ranta zai fita, tayi NADAMAR abubuwan da ta aikata, "Yanzu namiji nayi ta tura wa sak'o"
Abinda tayi ta nanatawa kenan.
Tashi tayi ta kama hanyar gidansu bayan ta kira maigidan ta nemi izini, duk da yaso yayi gardama amma fad'in da tayi mamanta ke kira ya barta ta tafi
[2/11, 6:19 PM] Ummu Abdoul👸🏼: 👹 KURURUWAR SHAI'DAN 👹
©Safiyyah (Ummu Abdoul)
KARSHE
Da sallama ta shiga gidan Hanif da Hanifa suka zo a guje suka rungumi mahaifiyarsu, "Ummi kin ciyo min chocolate" Fad'in Hanifa da bakinta da baiyi kwari ba.
Rungume su tayi sannan ta shiga wajen mahaifiyarta wacce take aminiyarta. Kuka ta fara sanda ta shiga d'akin ta d'aura kanta a cinyar mahaifiyarta.
"Sadiya magana zakiyi ba kuka ba meke faruwa". Nan ta kwashe komi ta fad'a mata. Sannan ta k'ara da cewa "Yanzu Mama namiji nayi ta tura ma hotunan, ya zanyi da rayuwata?"
Hankad'eta mahaifiyarta tayi,kuka ya kwace mata dakyar ta tsayar ta dubi Sadiya
"Au ke baki ga laifin aika ma mace 'yar uwarki ba sai namiji? Toh kisani bacin zunubin zina kina da na mad'igo kuma hukuncinki kisa ne, a jefo ki daga abinda yafi komi tsawo a garin nan, yanzu zan kira mahaifinki."
Da sauri Sadiya ta k'ara rarrafowa wajenta
"Mama wallahi bamu aikata ba"
"Amma ai kunyi ta waya ko, kinga zunubinki na nan no shaking"
Kuka sosai ta fara, yanzu in mijinta yaji da wani ido zata kalleshi yanda ya yarda da ita.
"Mama ki tausaya min kar asiri na ya tonu yanda ake ganin darajata ga Hanifa kuma"
"Wai sadiya kin manta wannan ne kika fara, kuma wani rufin asiri, ranar lahira a bainar dukkan halittun duniya za'a yi hisabi kin gwammace kunyar lahira da ta duniya kenan"
Kuka takeyi ainun don ta hango fushi da kyamarta a idanun mahaifiyarta. Waya batai mata rana ba, maganar mamanta ya katse mata tunani.
"Sadiya ina kika kai haddarki, ina kikai zuwanki islamiyya da karatun da kika koya. Kinfi so ace ya zama hujja a akanki kenan. Ta ya akai kika bari KURURUWAR SHAI'DAN ya d'ibe ki. Tun kina ganin laifin abin har zuciyanki ta mace .
Ba social media ya 6ata ki ba, kin gagara tsarkake zuciyarki ne.
Ina shafukan da ake 'karuwa a ciki, ina shafukan da ke da mutane masu mutunci, amma da hannunki kika bi mara mutunci.
Akwai labarai masu ma'ana amma kika zabi wanda zai tada sha'awarki. Dutse kike kokuwa ke Ma'asuma ce.
Bahaushe yace "Abokin 6arawo 6arawo ne" yayin da bature ke cewa "Show me your friend and I will tell you who you are"
Kinga shafukan da kike bi a yanar gizo, groups dinki a whtsapp, kalamanki a social media su zasu fad'i ko ke wacece.
Kin san lokacin da zaki mutu ne? In da mutuwar ta riske ki yayinda kuke 6arnan nan se kice ma Allah mene.
Abinda zakiyi yanzu, kiyi blocking account din, ki kuma yi deleting account dinki na whtsapp, kiyi tuba tsarkakkakiyar tuba sannan ki yawaita istigfari. Allah yana son masu tuba a gareshi".
"Nagode mama, ki yafe min cin amanar tarbiyyan da kikai min"
"Babu komi sadiya Allah ya miki Albarka, ya shirya min ke da sauran zuria na. Aameen..."
*******
Wannan labari ya faru da gaske, ban rubuta ba sai da izinin wacce ya faru da ita, asali ma ita tace na rubuta don akwai wa'inda KURURUWAR SHAI'DAN ya kwasa da dama ba wai rashin tarbiyya ya sa suka fad'a ba.
Allah Ubangiji ya jik'anmu ya shiryar damu Ya karemu Ya bamu ikon fin karfin zuk'atanmu.
Na sadaukar da labarin nan ga 'Daukacin MAKARANTA littafin nan. Godiya gareku duka.
Godiya ta musamman ga 'yar uwata, my half Rufaida Omar Ibrahim da ko da yaushe ita ke mik'ar da ni tsaye yayinda na nuna gajiyawata akan rubutu, Allah bar kauna (duk da muna fad'a 😜😏) da kuma HDY writers association don da bazarsu nake rawa.
No comments:
Post a Comment